← Book details Rabon Kwado Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 16 OF 26

Sashe 16

Rabon Kwado Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Nafi kowa sanin halin broz,kuma nafi kowa sanin wayeshi.Na fahimci akwai matsala a zamantakewarku tun jiya da kukaje gidan ummi,Dan nayiwa broz sanin da kallo yayi nasan abinda yake nufi,kuma lkcn fatima tananan ba haka ya saba yiba dan muka hadu,hakan yasa nace muzo yau dan inason nayi wani abu akan abin kafin na koma"

Dan haka yanxu ki fada min mene ya hadaku dazu?"

Banyi mgn ba sai hawayen da suka zubomin"

Kinga ba kuka nace kimin ba,idan kuma baki yarda dani ba bazaki iya fadan damuwar ki ba shikenan"

Tabbas zan fada mata kodan na samu sauqi a cikin xcyta,duk da akwai wadanda sukafi cancanta na fadawa damuwata kafin ita amma yanxu sun min nisa,ammi danake tunanin zata fahimceni itama fushi take dani.

Dama can ya tsaneni tun ba yau ba,kuma akazo aka hadani aure dashi.ya fadamin tun kafin nazo gidan nan xan zauna ne a matsayin yar aiki......

Haka na bata lbrn abubuwan da sukafi damuna dan nasan bazasu fadu duka ba.

Mundau tsahon lkc ba wanda yayi mgn kafin ta kalleni.

Kina nufin tsahon lkcn nan zaman da kuke kenan?"

Daga mata kai kawai nayi.

Kuma ba wani mataki da kike shirin dauka a kai?kinsan dai rayuwa bazata cigaba a haka ba,kuma idan na fahimceki kina nufin ko abincinki bai taba ci ba,bare aje ga sauke haqqin aure"

Shiru nayi.

Shikenan,insha allah zanyi iya qoqarina kamar yadda idan su mubina ne a irin wannan conditon din sai inda qarfi na ya qare haka kema dan duk daya kuke a wajena,dan haka inason ki bani hadin kai,Domin dole saida hadin kanki komai xai tafi dai dai"

Broz irin mutanen nan ne masu wahalar sha'ani,amma kina fahimtar halayensa kin gama dashi,sbd hk saikin jure"

Tom ngd"

Banason gdy,yanxu ina wayarki?"

Tashi nayi na dauko mata calculator dita.

Karba tayi tana jujjuyata kafin taja tsaki ta miqe ta fita.

Ganin shiru bata dawo ba yasa na koma na kwanta,domin sai naji zcyta sakayau kamar na sauke wani nauyi a kaina,ko ba komai na amayar da damuwata.

Mubina ce ta shigo.

Sannu sis"

Murmuhi kawai nayi.

Kixo ummi na kiranki"

Hijabi na nasaka kafin na fita.

Can gefe na zauna dan ummin ce da aunty anisa sai daddynsu shahid.

Fada ta shiga
yi mana sosai tare da nuna rashin jin dadinta akan abinda tazo ta gani.

Haduwa sukai suna bata hqr nidai kaina a qasa.saidata gama kafin ta tashi ta fita ya bita yana qara bata hqr.

Anjima zan bayar da saqo a kawo miki kinji?ki qara hqr kinsan irin wannan abun sai mutum ya jure dan inaso ki shirya yaqin janyo hankalinsa da mallakar zcyarsa.zuwa gobe nake tunanin zamu koma,amma idan bamu tafi ba zan dawo"

Daga mata kai nayi ina qara jaddada qoqari irin nata,tare da samar mata matsayi a zcyta dan ko ba komai ta nuna qauna da damuwa akan lamarina.
[07-23, 20:47] Sistoh: 💙💙RABON KWADO....💙💙

Er mutan ungogo💋💋💋💋

🅿111-🅿115

Har dare ni kadaice a gidan dan yaranma bansan inda ya kaisu ba,ko su ummin suka bi oho.

Wani nishadi nakeji danasan yana da nasaba da amayar da abinda yake zuciya.

Sosai lamarin auren ya sadiq idan na tuno yake bani mamaki,amma a kalaman ammi sai nake ganin kamar tilasta masa iyayensa sukayi.

Koma yayane nidai na dau aniyar cireshi a raina koda ta qarfin tuwo ne.

Ina kwance shiru bayan nayi shirin bacci,dan yar calculator din ma dana ke sauraran radio ko nayi game mai miciji itama babu,dan da ita nake tunanin aunty anisa ta tafi.

Da sallama ya danno kai cikin bed room din,wanda nayi saurin miqewa daga kwanciyar da nake domin tsahon zamana a gidan bai taba takowa koda bakin qofar dakin bane.

Fuskarsa ba yabo ba fallasa ba kamar yadda na saba ganinta ba koda yaushe a hade.

Ganin ya nemi gefen bed din ya zauna yasa na qara matsawa can qarshen gadon duk da girman daya ke dashi.

Saida ya gama shan qanshinsa da danne dannen wayar data zama kamar ibada sannan ya kalloni.

Ganin yadda na takure yasa ya tabe baki kafin yayi mgn.

Ga saqo nan anisa ta bayar a kawo miki,kuma daga yau ba wani zakina tmby wani abu idan kina buqata ba,ni dana ajiyeki niya kamata ki tmby"ya fada tare da ajiye qatuwar ledar hannunsa ya fita.

Har yakai bakin qofa ya juyo.

Tace ki hada wayar yanxu akwai sim card a ciki zata kiraki"yace ba tare daya juyo ba.

Jin zancen waya yasa nayi saurin durowa tare da bude ledar cikin gaggawa.

Kayan bacci ne masu kyau da tsada kusan kala biyar sai turaruka da banbi takansu ba na dauki kwalin wayar na budeta.

Masha allah!na fada cikin zaquwa tare da raya cewa wannan wai wayata ce?Ipone 7 pa,wayyo dadi ashe nima inada rabon riqe irin wannan wayar.

Jikina har rawa yake na kunna wayar tare da fara processing.

Sosai nake murna da jaddada kalmar nan ta mahaqurci mawadaci.

Banyi mintina da kunna wayar ba kira ya shigo wanda nafi tunanin na aunty anisa ne.

Assalamu alaikum"naji an fada wanda ko ba'a fada ba na gane muryarta ce.

Wa'alaikissalam aunty anisa"

Naam aunty khadija ashe ya kawo saqon?"

Cike da jin nauyin auntyn data kirani dashi nace.

Eh ya kawo na gode sosai"

Nafa fada miki banason godiya.yanxu abinda nakeso dake gobe da safe idan allah ya kaimu kwalliya zakiyi ta kece raini,sannan ki shiga kitchen ki shirya masa kunun gyada da qosai,kafin kije ki kirashi kice yazo yayi b/fast.ki cire wani abu a ranki ko wata kunya kiyi abinda nace,wannan shine matakin farko da zaki fara dauka,dan inason kafin a dawo da yaran ace wannan bangaren mun gama dashi kingane koh?"

Eh"nace ina jinjina irin wannan aiki data sakani mai wahalar aikatuwa.

Kamar yadda na fada sai kinyi hqr kin jure,bawai kinayi so daya ya disgaki zakiyi zcy kice bazaki kuma yi ba,Aa haka zakita jurewa har allah ya karkato miki da hankalinsa.bana tunanin zaiqi cin abincinma dan jiya sosai ummi tayi masa fada kuma naga alamar fada ya shigeshi.Nidai fatana khadija karki bani kunya,kiyi duk abinda nace miki kinji?na taqaitaccen lkc ne insha allah"

Tom aunty anisa insha allah zan qoqarta"

Yawwa qanwata,yanxu kiyi bacci ta yadda zaki tashi da wuri kiyi abinda ya dace,goben zamuyi waya"

Tim saida safe"nace ina zare wayar daga kunnena,tare da fargabar yadda zan tunkari wannan babban al'amari.

washegari kamar yadda Aunty anisa ta sakani haka nayi nayi kwalliya na cakare wanda ni kaina inada tabbacin nayi.zakifi tunanin gasar sarauniyar kyau zani.

Iphone dita na dauko na shiga daukan pictures,inda suka fita yadda ya kamata musammanma da kyan camera ya hadu da good background😊.

Abinka da an dade ba'a haduba haka na bata lkc na wajen daukar picx din kafin na shiga gyara wadrop dan shirya kayansu iman da aka kawo wanki tun shekaran jiya.

Saida na tabbatar na gyara kayansu kafin na fara gyara nawa dan shiryasu yadda ya kamata.

Ledar jiya na dauko tareda zazzage kayan akan bed.

Kayan na fara dagawa wanda nayi saurin cikwikwiyesu na saka a wadrop dan kunya ma kayan suka bani🙈

Turarukan ma sunmin qamshi sosai,inda ba bata lkc na fara turara gidan da turarukan.

Haka na cigaba da aiki na cikin nishadi ina shaqar qamshin turaren.

Ba bada lkc na gama komai dan gidan ba dattine dashi ba.

Kitchen na fada na shirya kunun gyadar tare dayin qosan naje na jera a dinning ina sake saken ta ina zan fara tunkarar sashensa?to idan najema mezance?

Ganin banida wani zabi daya wuce yadda aunty anisa tace yasa nayi qundunbala tare da qunar baqin wake na nufi sashen duk kuwa da fargabar yadda zai karbi baqon al'amarin daya cika min zcy.

Tofa! nafi mintuna 30 a bakin qofar ina tunanin ta yadda zan fara knocking qofar.

Jin an bude qofar yasa naja da baya da sauri tare da diriricewa kamar mara gsky,bayan luguden da zcyta takeyi ganin mamaki kwance a fuskarsa.nasan mamakin bai wuce na ganina da yayi a qofar sashin sa ba.

Ganin ya tsaya riqe da qofa yana kallona yasa nayi qoqarin aro nutsuwa da dauriya na yafa.

Dama inaso na fada maka na gama b/fast ne"na fada cikin dauriya.

Nace ina buqatar abinci ne"ya fada yana qara gyara tsayuwa.

Shiru nayi ina kuma jin takaici a raina.

Tunda bance ina buqata ba zaki iya bace min anan gurin,idiot kawai"yace tare da banko qofar.

A hankali na zame a wajen na zauna dan nasa qafafuna bazasu iya kaini daki ba.

Idiot?nice idiot?meyasa yakeson kira na da wannan sunan?idan zan iya tunawa wannan shine karo na uku daya kirani da wannan sunan.Amma yanxu banga laifinshi ba,da banzo inda yake ba da bazai fada min haka ba.

Why aunty anisa?meyasa kike tunanin zan iya mallakar mutumin dayafi kowa tsanata?meyasa kikeson na cusa kaina inda nakeda tabbacin bazan samu shiga ba?

A hankali na miqe ina goge hawayen fuskata,dan banaso ya kuma fitowa ya sameni a bakin qofarsa,dan bansan me zai kuma fada min ba.

Ina shiga dakin na fizge dankwalin kaina tare da wullar dashi,sannan na kifa na cigaba da kuka dan samun sauqin zcy.

Inaji wayar ta fara qara naqi dagawa,tunowa da ba mai kira sai aunty anisa yasa na share hawayena tare da daga wayar.

Matar broz yaya dai?inata zumudin kira naji bayani dan nasan yanxu broz ya dade da tashi a bacci"

Qaqalo murmushi nayi tare da cewa "ina kwana aunty anisa"

Shiru naji tayi kafin tace"an samu matsala koh khadija?"

Aa"nace da muryata da take rawa dan kukane ya tahomin.

Kiyi hqr kinji?dama na fada miki sai kin jure"

Aa aunty anisa,kiyi hqr wlh bazan iya ba,daddyn shahid da irin mutanen da suke saurin sarrafuwa bane,kuma na sanar dake tun farko baya sona,bai bata min kallon mutunci ina qanwar matarsa ba bare yanxu da nake amsa sunan matarsa"

Haba khadija,bai kamata kiyi saurin karaya haka ba,nasan halin ya abdul sosai shiyasa naje so kema ki gane halinsa kiyi hqr dashi har zuwa lkcn da zaku fahimci juna"

Banason yi mata musu ko gardama a qoqarinta na ganin ta saita min rayuwar aure,hakan yasa nayi shiru kawai ina kuka.

Khadija!

Naam"
Chapter 16 · 0% Book details