← Book details Rabon Kwado Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 22 OF 26

Sashe 22

Rabon Kwado Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Nernah inason yin aure amma wata zuciyar na rayamin idan nayi haka kamar ban kyautawa fatima ba,ki bani shawara dan allah""

Shiru nayi ina jujjuya maganganunshi,wato shi baya ma daukata a matsayin mata?Eh mana ai dama ya jiga ya sanar dani a mai yiwa yaransa hidima zan zauna nice dai na zaqe gashi na janyowa kaina na fada tarkon sonshi.

Ki fada min yadda zanyi nernah,inaso ne a hada bikin dana su mubina amma bansan yadda mutane zasu dauki mgnr ba,musamman ma ummi plzz ki fadamin mafita"

Tirqashi!!

Idan kece khadija wace iriyar shawara zaki bashi?shin xaki bashi shawara yayi auren ne ko kuwa?

Khayratie er mutan ungogo💋💋💋💋

Ya Abdul kayi aurenka kawai?ya fatima ta riga ta tafi bazata dawo ba,mgnr mutane kuwa ka toshe kunnuwanka domin Allah ne halarta muku auren mace fiye da daya idan har zakuyi adalci,bare ya fatima bata raye.Ka sanarda ummi insha Allah zata amince"nace muryata a rauna ne.

Jin yayi shiru bashi da alamar mgn yasa na janyeshi a jikina na fara sauka a gadon.

Ina kuma zakije?"najiyo shi.

Ban jiyo ba illa qoqarin mayar da kwallar data taru a idona da nayi.

Zanje na kwanta ne dare yayi"nace cikin dauriya domin kadan ya rage na fasa ihu.

Kizo ki kwanta anan mana?"

Banyi mgn ba sai ma hanyar fita dana nufi da sauri jin kukan takaici ya taho.

Ya bari idan yayi aurn ya samu hakan daga matarsa,dama yace bazan iya daukar dawainiyarsu shida yaransa ba,dan hk daga yau na daina yarda ko hannuna ya taba,kamar yadda yace shi yayana ne zanzauna a matsayin qanwarsa,soyayyarsa kuwa zanyi ta dakonta har lkcn da allah zai yayemin ya bani mafita.

Haka na raya daren da kuka da addu'ar neman sassauci,saida naji zcytah wasai kafin na nemi makwanci cike da qissima abubuwa iri iri.

[09-07, 12:55 PM] Cwt-besty: 💙💙💙RABON KWADO....💙💙💙

Er mutan ungogo💋💋💋

🅿191-🅿195

Bugun get din na shigayi ba tare da tunanin wani abu ba,hkn yasa su ummi nufo inda nake cikin hanzari.

Jin wata tsawa ta cikin gidan yasa na tsaya da bugun da nakewa get din.

Wani murdadden soja ne ya fito kakkaura mai jini a jika,siffarshi ma kanta abar tsoro ce.

Masifa yake da gurbatacciyar hausarsa.ganin yaya sun qaraso yasa na harareshi tare da murguda baki🙄😏

Yaya ne ya shiga bashi hqr tare dayi masa bayanin gurin masu gidan mukazo.

Hajia yasan da zuwanku?"itace kalmar data kuma batamin rai da sojan ya fada.

Wai yaushe mutanen nan sukai arziqin da ganinsu ma sai an nemi izini?

Kince mini ke yaronsu ne,bari na kira hajia a waya,idan yace abarku ku shigo to"sojan ya fada yana shigewa ciki.

Lallai ma mutanen nan wato Duniya sabuwa suka samu suke cin karensu babu babbaka"na fada cikin takaici.

Malama kiyi mana shiru"yaya yace ganin yanayin ummi.

Su mubina ne suka tattaro yaran suka biyomu don ganin mu a tsaye.

Leqowa sojan yayi tare da yafito mu don hk muka shiga qatuwar farfajiyar wadda ta qunshi bangarori guda shida.yanayi da tsarin gidajen duk iri daya ne kamar yadda suke a jere bibbiyu bibbiyu.
Daga gefe wajen ajiye motoci ne da kuma qaramin masallaci.

Hajia yace a shiga daku,daya dauka masu neman taimako ne sai da nace a mota kukazo,kinsan hajia bayason talaka"sojan yasa yana murmushi.

Mu duka ba wanda ya kulashi,bayansa mukabi ganin ya nufi daya daga cikin gidajen.

Knocking yayi wata matashiyar yarinya ta bude,inda yayi mata bayanin mune baqin hajia sannan tayi mana iso.

Qaton falon nabi da kallo ina qissima kudin da aka kashe masa,gsky mutanen nan sun sami duniya,kardai ace wannan rubabbiyar tsohuwarce a ciki?

Zama mukayi akan kujerun ni harda miqe qafa.

Hajia na hutawa,amma nan da 1hour zata fito"yarinyar ta fada tana komawa inda ta fito.

Shiru mukayi kowa da tunanin da yake ganin yaran kamar sun takura yasa na janyo remote control din dana gani kan centre tble na kunna t.v.

Hararata ummi tayi nayi murmushi kawai.

Wai me wannan tsohuwar take nufi ne?sai kace munxo neman wani abu,ko kuma bamu da aikinyi ne?"yaya ya fada cikin bacin rai ganin mun haura awa daya a zaune.

Ayyah babanah,ka qara hqr mana har lkcn da zata fito,idan muka abinda ya kawomu ba shikenan ba"

dama sabon shigar arziqi ai sai ya nuna kansa,bare wadanda suka samu sama ta ka"na fada ina qara bararrajewa kamar ina falon ummi😊.

Anisa na qarajin bakinki ranki zai baci"ummi tace.

Jin alamar bude qofa yasa duk hankalinmu yayi wajen.

Dariya ce ta kusa subucemin ganin baba shatu a while chair,kai da ganinta sakasan taci duniya,kamata yayi zuwa yanxu tana ta istighfari domin mutuwa ko yau ko gobe,amma sbd budurwar zcy sanye take da rantsattsen less don masifa harda kafa wani dauri a goshi.
Harara ummi ta gallamin hakan yasa na gintse dariyata ina kallon ikon allah don yan mata biyu ke turota.

Bangama shan mamaki ba saida naga sun shimfida mata wani rug sun shimfideta akai tare dayi mata matashi sa cushion,ta wani kishingida kamar wata sarauniya.

Saida ta kuma dai daita zaman glass din fuskarta kafin ta fara binmu da kallo daya bayan daya.

Gaisheta muka shiga yi,kafin ummi tayi mata bayanin mu suwaye da kuma abinda ya kawo mu.

Shuru tayi tana qara binmu da kallo kamar tanason gano wani abu,kafin daga bisani tayi murmushi.

Dama nasan wannan ranar zata zo,dama kuma wannan ranar nake jira,domin nasan dole akwai ranar da zaku nememu,kuma na godewa allah da ina raye wannan rana tazo,ranar da ahalin abubakar suke durqushe a gabana suna neman wani abu gareni nida ahalina"

Kallon kallo muka farayi danjin abinda ta fada,ita ta dauka abu mukazo nema a gurunsu?ai duk lalacewar goma tafi biyar albarka.

Mannira!mannira!Ta shiga kwala kira.wata budurwace ta fito tana wani yauqi.

Nifa shiyasa banason zuwa bangarenki hajia,kita batawa mutum suna kuma kullum sai na fada miki munirat sunanah"

Kedai kika sani 'yar nema,maza kirawon iyayenki kice inason ganinsu yanxu yanxu"

Ficewa tai batare datayi mana mgn ba,muma ko kallo bata ishemu ba.
Muna nan zaune raina in banda suya ba abinda yakeyi,sbd yadda baba shatu take zuba mulki saika rantse jinin sarauta ce.
Su mufida kallo daya zaka musu ka gano bacin ran da suke ciki musamman ma mubina,bare kuma oga kwata kwata daya hade fuska yana danne danne awaya.Ummi ma dauriya ce kawai ta lullube damuwarta.

Uncle sani ne ya fara shigowa kafin sauran suka fara zuwa daya bayan daya.Bayan gaisuwa ba wanda yake qara mgn.
Ni dariya suke bani ganin yadda suna shaidamu sai kowa ya fara cin magani da shan qamshi.

Kamar yadda kuke gani wadannanahalin danuwanku abubakar ne,mahaifiyarsu tamin bayini sunxo ne akan mgnr auren wadancan yaran guda biyu.To yanxu dai niba dolensu bace,kune dolensu,don hk idan da akwai abinda zaku iya taimaka musu dashi sai ku basu"

Gsky hajia ta bangarena babu wani abu dazan iya,ban sani ba ko sani"uncle auwal ya fada yana ciccin magani.
Har yaya zaiyi mgn ummi ta hanashi,don hk nima dole na hadiye mgnr da nayi niyyar yi.

Banda abin hjy ai kinsan yanxu bamuda wasu ajiyayyun kudi da zamu iya dauka muyi kyauta dasu,muda muke shirin saka hannun jari a qasashen waje ai muma abin a bamu taimako ne"

Murmushi baba shatu ko nake hajia shatu mai jan kai tayi,kafin ta kalli su aunty hafsatu.

Ku kuma fa iyayen amare ko akwai wata gudummawa?"

Abinda maza suka kasa ai mu mata ba'a sako mu a ciki ba,Allah dai ya bada zaman lpy,ya bada yadda za'ayi"aunty zuwaira ta fada.

To asiya kin daiji daga bakin iyayen nasu,don hk ayi gaba ko za'a dace,ko kuma a fitowa yara da haqqinsu da sunusi ya washe ya kai qasar waje"inji baba shatu.

Allah ya huci ran hajia,dama ba munxo neman wani abu bane,domin alhmdllh bamu nemi komai mun rasa ba ba,tunda har wasu suna samu daga qarqashinmu Suna ci,sannan ta sanadiyyar abinda muke dashi har wasu sunaji kamar sunfi kowa arziqi a duniya.munxo ne domin sanar dasu iyayen nasu domin fita haqqinsu,don koba komai su dangin mahaifinsu ne suna da haqqi akai"

Ke asiya,karki kuskura kizo har cikin gida kice zaki zage mu,idan ba maular ba mezai kayoku inda muke?to wlh salin alin ki tattara kan watsattsun yaranki kuyi gaba tun kafin nasa a wulaqanta ku"aunty hafsatu ta fada tana miqewa kamar zatayi dambe.

Hafsatu kenan,ai watsattsun yara sune wadanda aka ciyar dasu da haram,aka shayar dasu da haram kuma suka rayuwa cikin haram,kuma sanin kanki ne ahalin abubakar sunfi qarfin wulaqanci daga wulaqantattu wadanda suke taqama da dukiyar marayu"

uncle sani ne ya miqe yana huci kamar zai daki ummi.

Barta sani ai idan bata zagemu ba bazamusa zafin talauci ya ratsata ba"baba shatu tace.

A fusace yaya ya miqe yaja hannun ummi suka fice,don haka muma muka kwaso yaran muka fito muka barsu sunata zage zage.
Ni kuwa raina fes,don ummi ta gama min komai data fada musu wadannan maganganun.

Daqar muka samu ummi ta dawo hankalin ta,don hawan jininta saida ya tashi,satinmu daya a asibiti aka sallamo mu,uncle kuwa fada yaitayi akan zuwan namu.shine dashi da wasu daga cikin abokan abba sukai komai daya shafi mgnr aurensu mubina.

Baba shatu da ahalinta kuwa bamu qarajin duriyarsu ba,amma lkc lkc akan yi barna a company,amma zuwa yanxu ni na daina zargin su baba shatu,nafi tunanin ta wani bangare ne muka qara samu maqiya.

Cigaban lbr👌
[09-07, 12:55 PM] Cwt-besty: 💙💙💙RABON KWADO💙💙💙

Er mutan ungogo💋💋💋

🅿186-🅿190

Sosai hankulanmu suke a tashe don iya buncike anyi amma ba'a gano musabbabin zurarewar kudin ba,hakan ya bamu tabbacin na jiki jiki wanda yasan sirrin abbanmu shike aikata hakan.

Addu'ar da muka yawaita yasa asirinsu ya fara tonuwa.

Inna ladi itace shugabar masuyi mana hidima a gidannan,komai idan suna buqata ta hannunta ake basu,hatta albashi ita ake bawa tana basu.kasancewarta dattijuwa yasa muke girmamata,ba kamar ummi data dauki dukkan yarda ta bata.

Azal ce ta ciyota da kanta tazo tana kuka da neman gafara akan duk abinda ake ciki tanada masaniya,domin ita aunty hafsatu(yayar abba)ta bawa wani abu a leda tace ta tabbatar da zuba a abincin abba.washegarin da yaci abincin shine wannan ciwon ya kama abba.
Chapter 22 · 0% Book details