← Book details Rabon Kwado Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 21 OF 26

Sashe 21

Rabon Kwado Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Nace inaso ki kawon tea ne?"yace still yana kallo na.

Shiru nayi jikina duk yayi sanyi.

Nernah"

Har raina naji sunan,har hakan tasa na kasa amsawa sai kallonshi da nayi kamar yadda yake kallona.

Miqon hannu yayi,ba musu naje tare da shigewa jikinsa.

A tare muka sauke ajiyar zcy,na qara lafewa a jikinsa.

Bazaki iya ba koh?bazaki iya kulawa dani da yarana ba na kawo wata koh?"

Da sauri na bude ido dan da na lumshesu sbd rada yakemin a kunne.

Nasan bazaki iya ba dama,sbd kinyi qanqanta da yawa,kawai dai bazan iya qin jinin fatima bane,kuma kinsan wani abu?"

A hankali na girgiza kai.

Wasu lokutan kina min kama da fatima.lokuta da dama kuma idan na tuno alaqarku da ita sai naga kamar naci amanarta,har yanxu fatima kawai nakeso nernah,duk da nasan bazata dawo gareni ba"

Shiru dukkan mu mukayi inda numfashinsa a hankali yake sauka cikin kunne na.

Ni kuwa babu kalmar dakemin tawo sai"har yanxu fatima kawai nake so!!"

Fatima ta dabance na sani,shiyasa na bata kaina da zcytah,amma allah daya fini sonta ya karbi abarsa"ya cigaba.

Fatima......

Bansan lkcn da na fizge daga riqon da yayi min ba,ban jira komai ba nayi daki da gudu,na kifa kai tare da saka kuka.

To kukan me nakeyi?mai zaisa na damu dan yana yabon matarsa? bacin nasan dama can yana sonta?

Ku biyu ni sannu a hankali dan samun cikakkiyar amsar tmbyoyin.

Khayratie💋💙💋💋💋💋💙💙RABON KWADO....💙💙

Er mutan ungogo💋💋💋💋

🅿141-🅿145.

Kuka nake sosai wanda zaka iya dauka dukana akayi ko wani abun daban.

Ni kaina bansan dalilin kukan ba,kawai dai nasan raina ya baci da jin kalamansa.

To meyasa raina zai baci?tmbyr da nake yiwa kaina kenan.Daidai lkcn naji an zauna a gefe na.

Koda ban dago ba qamshinsa ya tabbatar min shine.

Zuwa yanxu ya kamata mu sabarwa kanmu da rashin fatima,duk da nima duk dare nakanyi kukan rashinta.Na sani fatima tana da kirkin da za'a dauki lkc kafin mutum ya manta da ita,kuma banyi zaton wannan mgnr zata saka ki dawo da mutuwar fatima sabuwa ba"

Ya ilahi!!🤦🏻‍♀Fatima!Fatima!!Fatima!!komai fatima?Waya fada masa mutuwa ce yanxu tasa nake kuka?to idan ba mutuwar ba mezaisa nayi kuka?mutuwarce ma kawai ta sakani kukan.Na raya a raina.

Dukkansu suka shigo suka tsaya mufida na tmbyr me akayimin don ina tunanin sunga lkcn danayo daki da gudu.

Kuje kawai ba abinda ya sameta kawai rigima ce irinta nernah"ya fada yana janyoni jikinsa.

A hankali yake busa min iska cikin kunne na,hakan yasa nayi shiru ina sauke ajiyar zcy Har bansan lkcn da bacci ya daukeni ba.

Dana farka ni kadaice a bedroom din,don haka wanka nayi na shirya cikin wata doguwar rigar atamfa.

Mai kawai na murza dan har lkcn banajin dadin jikina kuma bazance taqamaimai ga abinda ke damuna ba.

Mubina ce da iman kawai wai sauran sun fita zasuyo shopping sbd gobe zasuyi resuming school.

Wayata na dauka nahau watsap inda na fara krtnta wani novel a wani grp,duk da ba wani fahimta nake ba amma novel din da alama zaiyi dadi da ma'ana.

Sai daf da magriba suka dawo,saida kowa ya gabatar da sallah sannan aka baje kayan da suka siyo suna duddubawa.

Nidai ina maqele da hannunshi tun lkcn da suka dawo a masallaci shi da shahid ya riqoni.

Yaya ya kamata pa a fara siyan kayan baby tun yanxu"mubina tace.

Nidai kishingida nayi a jikinsa inajin yadda yake murza hannuna a hankali.

Waya fada miki anan zamu sayi kayan baby?zuwa end of dis month nake saka ran tpy Dubai,acan zan fara hado kayan"

Inajinsu sunata hira akan tpyr tasa nidai bance komai ba hasalima idona a lumshe yake dan haka kawai sai naji banaso ya tafi.

Yaya gaskiya babyn nan yana wahalar da sister,ni gani nakema rama yake sakata"mufida tace.

Banji yayi mgn ba sai jin hannunsa nayi akan fuskata.

Karkiyi bacci mana bakici abinci ba"ya fada bayan na bude ido.

Yaya ko Lunch din da mukayi ma bata ci ba wlh"inji mubina.

Aa banason rashin cin abinci kin sani,tashi muje kici abinci"

A baki ya ringa bani ina amshewa,nidai satar kallonsa nake inajin wasu abubuwa game dashi,dan kwana biyun nan bana gajiya da kallonsa,duk da banayi ta yadda zaisan shi nake kallo.

Kwana biyu kin rage walwala nernah kuma kowa cewa yake kin rame,ki fada min damuwarki,kinga ni yayanki ne kuma amanarki Abbi ya bani,banaso ace na gaza wajen kulawa dake"

Qaramin bakinsa kawai na zubawa ido ta yadda yake shiryo zance.

Da can mantawa yayi da amanar yake gasa min aya a hannu?

Ki fadamin mana kinji nernarhnah"

Inason ganinsu ammi ne"na fada dan kawar da zargi.

Murmushi yayi"kinga kuwa indai mukayi waya sai tace na gaishe da auta kawai fada miki ne banayi dan nasan rigimarki"

Ya abdul da gsk?dan allah ka kiramin ita yanxu"nace ina miqewa.

Sai kina cin abinci kuma kinyi qiba sannan,har gida zan kai ki sannan muje gidansu ya aisha"

Haka ya ringa ja min rai har nayi zcy nayi tapiyata daki.

Shirin bacci nayi duk da ba bacci nakeji ba.

Wayata na janyo tare da dannawa aunty anisa kira.

Hira mukasha inda take fada min suma sun kusa tahowa dan fara shirin bikinsu mufida.

Sai da muka gaisa da yaranta tukunna mukayi sallama,kafin na cigaba da karatun novel dina.

Da sallama a bakinsa ya shigo cikin wata shadda sai gyalli yakeyi,nidai har ya qaraso idona a kansa,Domin zan iya irga lokutan dana ganshi cikin manyan kaya gashi sai zuba qamshi yake.

Wayar hannuna ya karba ya ajiye gefe.

Shine kk gudo kk barmu ko?kinga ni fita ma zanyi zanje zance ne,baki ce nayi kyau ba"yace murmushi kwance a fuskarsa.

Saida na rintse idona dan takaici kafin na qaqalo murmushi.

Kayi kyau sosai,saika dawo"

Haka ina kallo ya fita,sakin kuka nayi na tausayawa rayuwata,dan a yanzu na tabbatarwa kaina na fada tarkon sonshi,dan da gsk kishinsa nake.

Wayyo allahnah,zuciya baki min adalci ba,sbd me zakimin hk?why?why?

Kuka nasha na godewa allah kafin nayi addu'a na gyara kwanciyata,dan yau bazan kwana a part dinsa ba,ya zama dole na nisanta kaina dashi tunda kusancin da muke dashi ne duk ya jayo min hk.

Amma kuma sai me?duk yadda naso bacci ya daukeni abin yaqi yiwuwa,ga wani zafi da zcytah takeyi idan na tuno inda mijina ya tafi.

Ta wani bangaren banga laifin zcytah data kamu da son daddyn shahid ba,domin ya cancanta a soshin.

Amma kuma ta wani bangaren nasan yafi qarfina,abinda yake qara sagar min da gwiwa kuma bai wuce kalamansa ba da yasha fadamin su lokutan da suka wuce amma idan na tuno daddyn shahid din da dana yanxu ba daya bane sai naji sassauci kadan.

Haka na ringa juyi a kan gado tare da neman mafita amma ban samu ba.

💙💙RABON KWADO....💙💙💙

Na Er mutan ungogo💋💋💋

Ina alfahari daku Rabon kwado fans,ina gdy da fatan alkhairinku game da exam din da nayi.

Da yardar Allah zan fara subirbido muku rabon kwado.

🅿145-🅿150

Har su mubina suka gama kallo suka dawo daki kusan 11 na dare ba daddyn shahid ba alamarsa.

Gsky zance yayi dadi..

Wai ina yaya yaje ne naga har yanxu bai dawo ba?"mubina tace.

Zance ya tafi inaga acan zai kwana"na fada a qufule ina daukan iman datai bacci don mayar da ita dakinsu.

Dana dawo dukkansu ido suka zubamin,nidai kuma daukar shahida nayi na fice na barsu.

Ina komawa na nemi gado na hau tare da jan bargo.

Bacci fa bai kamaki ba sister"mufida tace.

Idan batai bacci ba fita zatayi ta nemo shi ko kuma ita tace yaje yakai daren?wlh dama nice ke khadija wlh dasai yau mutum ya gane kurensa,sbd rainin hankali da matarka zaka tafi wani zance?"

Ni mgnrma qara bata min rai takeyi,haka mubina ta cigaba da mita,jin dirar mota yasa dukansu suka nufi bakin window tare da daga labule.

Zaiga zance wlh da ummi zan hada shi"mubina tace tana sakin labulen tare da dawowa.

Yadda nakejin zcytah kamar zata fito yasa nayi saurin dafe qirjina kozan samu sauqi.

Nasani dama son maso wani shi zai kasheni tunda nasan yadda na fada tarkonshi bazai taba sona ba.

Namiji kenan!kamar ba shine dazu ya gama yabo da koda ya fatima ba amma 6month da mutuwarta har ya fara neman wata,Allah sarki wanda ya mutu ai ya mutu,nida nake rayenma watana 4 da aure akace ya sadiq yayi aure bare ya fatima da yasan bazata dawo ba.

Sallamarsa cikin dakin yasa zcytah qara gudu wajen harbawa,dan dole na kuma dafe dai dai inda nake tunanin anan zcyr take.

Mufida ce ta amsa sallamar dan mubina rufe ido tayi kamar mai bacci,ni kuwa dama har kaina yana cikin bargo duk da ba sanyi akeyi ba.

Mufida badai har sunyi bacci ba?"yace

Eh mn yaya bakaga qarfe nawa ba?"mufida tace.

Mtw wlh ni kaina bansan dare yayi haka ba,dan taba min nernah ta taso mu tafi daki"naji yace.

Inaji mufida na tashina nayi mata banza harta gaji ta qyaleni.

Barta tunda bazata tashi ba,saina dauketa dan nasan tana jina"

Cak!naji an daga ni tare da janye bargon.

Qoqarin kwace kaina na farayi,ganin haka yasa ya qara rungumeni a jikinsa ya nufi hanyar waje.

kuka na farayi a hankali har saida naji ya saukeni akan gadon.

Dagoni yayi har lkcn idona a rufe yake sai hawaye da yake zuba dan kukan bamai sauti bane.

To menene kuma na kukan bagashi na dawo ba?ki daina banason kuka kinji?"yace tare da saka hannu yana sharen hawayena.

Jin ya daina goge hawayen yasa na bude idanuwa na.

Caraf muka hada ido nayi saurin kauda kai.

Saida naji ya tashi kafin nayi addu'a na gyara kwanciya duk da na fahimci a bedroom dinshi nake ba wanda na saba kwanciya ba.

Da taimakon Allah da addu'ar danake yasa na fara jin sauqi a cikin zuciyata.Gskyr batureda yace"Struggle Never End"ni kuma qaddarata kenan dakon soyayya,na gama ta ya sadiq yanxu na fada ta wani.

Ganin dakin ya dauki duhu yasa na qanqame jikina tare da fargabar allah yasa ba irinta ranar bane,to ai yau banyi masa laifi ba.

Jin an riqoni yasa na kuma firgita tareda qwala qara.

Qara riqoni yayi bayan ya kunna Lamp dake gefen gadon inda haske ya fara kawowa kala daban daban.

Ki rage tsoro kinji nernerh?"yace yana qara shiga jikina kamar mai jin sanyi.
Chapter 21 · 0% Book details