← Book details Rabon Kwado Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 25 OF 26

Sashe 25

Rabon Kwado Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ina neman afuwarku readers akan rashin jina tsahon kwanaki,hakan ya faru ne sakamakon rashin Nepa da aka fama dashi ina fata za'ayi min afuwa.
Sannan akwai mistake na page number da nayi,last page zai kama 201-205 yanxu zamu tashi 206-210.Ngd.

😍😍Wannan page sadaukarwa ne ga tsofaffin daliban G.G.S.S kwah 2015 musamman B Class.

Khadija isah muhd
Ruqayya musa
Ummahani adam
Hauwa musa bello
Rabi Aminu sulaiman dungurawa.
Bashariyya abdulhamid
Khadija Bala muhd
Jamila ibrahim(jam jam)
Aisha usaini yarkanya
Asma'u Aliyu ungogo.

Kuna raina bazan manta daku ba tsahon rayuwa😍😍

🅿206-🅿210

Tun daga ranar bai qara zuwa gidan ba,kuma in aka kira numbr dinsa batashiga kamar yadda naji aunty anisa ta fada.

Sosai suka shiga damuwa idan ka cire ummi da kullum cikin mita take,yaransa kansu sun faratmby ina daddy dinsu,nidai ko a jikina dan nasan ta hanyar daina ganinshi ne kawai zanyi nasarar cireshi a zcytah.

Jin dadin gidan nake sosai,dan kowa ji yakeyi dani ba kamar ummi da take min kamar ta goyani ko yaya taga nayi shiru xata shiga tmbytah ko ina buqatar wani abu.

Samunsu aunty anisa da mufida yasa na daina damuwa akan rashin yanuwana.
Shirye shiryen biki sukeyi sosai,ba kamar mubina da take ji kamar ta janyo ranar bikin.

Cikin ikon allah na fara nasarar cire daddyn shahid a zcytah domin shidin bai cancanci a so shi din ba.idan na tuno da matsayinshi na mijin ya fatima sai naga butulci ne ace na fada tarkon sonshi.

Ana saura 1month bikin mutanen U.S suka diro ciki kuwa harda mutumin naku.
Sosai matar da suke kira da mum take da fara'a da jan mutum a jiki,tun inajin nauyinta har nazo na sake da ita kamar yadda naga yan gidan sunayi.

Uncle din kuwa kallo daya zakayi ka gano tsantsar kamar da sukeyi da cwt daddyn shahid😜 da kuma ummi,shim na samu karbuwa a gurinsa.

Kwanarsu biyu da zuwa aka fara gyara amare ciki kuwa harda ni,ba yadda na iya dole nake tsayawa duk abinda akayi musu ayi min don mum da aunty anisa sun tsaya kai da fata ai nima amaryar ce.

Cikin kwanaki kadan muka fara canjawa asalin kyawunmu yana bayyana,don abune akeyinsa kamar cin kwan makauniya,safe rana da kuma dare duk da su mum din ba anan suke kwana ba kullum da safe suke xuwa ayi break fast dasu sai idan uncle sun dawo daga company da dare bayan dinner sai su wuce masauki.

Das qamshi ya zauna ajikinmu duk inda muka zauna muka tashi sai mun bar qamshi don hatta wanka da ruwan turare mukeyinsa.

Daddyn shahid kuwa bama haduwa dashi don downstair dinma bama Sauka komai biyomu akeyi dashi.

Duk yadda sukai kyau amma sai suyita zuzita kyauna,nidai kawai jinsu nake dan su da suke farare ai sune zasufi yin kyau.

Yau ta kama saura 3weeks biki,Kamar kullum yau ma abin da mum ta saba dama mana aka dama nidai kwata kwata bana jin dadinsa don haka kowa saiya shanye a barni a baya wataran mum har dura takemin.
Ganin mum ta fata yasa na ajiyeshi a bedside drawer nayi kwanciyata.

Ashe da rabon yau ma ayiwa wata dura"mufita tace.

Sis bazaki gane menake ji idan inashan abin nan ba,kwata kwata babu dadi ko pa suger babu"nace ina gyara kwanciya.

Kowa ma ai babu suger din yakesa,wlh ki tashi kisha dan mum tace yana da matuqar amfani"mubina amarya tace.

A wajenku amare ba"nace ina dariyar mugunta.

Eh koma dai mezaki ce ki tashi ki shanye ko naje na kira aunty anisa"tace tana harara ta.

Wlh har tausaya miki nakeyi mubina,wannan gigin da rawar kan da kikeyi duk a sati daya za'a sauke miki shi"mufida tace muna ci gaba da dariya.

Pillows ta dauka tana dukanmu dasu muna cigaba da dariya.

Zuwan zaid yasa muka dakata da dariyar sai mubina daketa harare harare.

Mommyn shahid wai gashi inji uncle saqonki ne sai yanxu ya tuno dashi"ya fada yana bani wata leda.

Bude ledar na shigayi batare dana tuno da ko wani saqo bane.

Inner wears ne masu kyau,sai pictures din nusaiba dakuma wanda mukayi tare a waya aka wanko,sai kwalin chewing gum da sweet sai kuma letter.

Letter din na hau karantawa don daga note din nagane daga nusaiba take.

Slm sistr

Ina fata kina lpy kamar yadda nake duk da kewa da rashinki a kusa har zuwa wannan lkcn ya kasa bari na nayi rayuwa kamar ko wani dan adam.

Baxan iya kwatanta yadda nakeji a kullum idan na tuno irin rabuwar da mukayi ba,amma hakan ba yana nufin canja miki matsayin a gurina ba.

Wani albishir kuma shine on 7 may bikin sistr dinki,rashin halartarki yana nufin rashin gudanar da biki cikin walwala.

Luv u so much sistr.

Yau nawa ga wata"na tmbyi su mubina ina share hawaye ba tare dana kula irin kallon da suke min ba.

Five"mufida tace.

Tsalle na daka sbd murnar lkc bai wuce ba zanje bikin nusaiba.

Lpy sis"suka fada a tare.

Bikin besty dina za'ayi jibi ai zaku je koh?"na fada ina murna.

Sosai m dama zaman gidan ya isheni,gashi an karbe mana phone kamar wasu prisoners"mubina tace

Amma ummi xata bari?"na tmby

Zata bari insha allah"mufida tace

Ai kuwa muna tmby ta bari harda bada wani purple din material mai kyau wai a dinka mana muje bikin dashi.
Ban gama m
amaki ba saida naga washe gari da yamma an kawo dinkin,dinkin doguwar riga ce qasanta ya bude sosai.Da yake su mubina sun dan fini qiba siririyar ciki na dauka ina gwadawa kuwa dai dai ni,sai lkcn mufida take fadamin aunty anisa ta dauki measurement dina don tuni an kai mana dinkunan biki.
Tun safe na fara shiri sbd zumudi,ga murnar ganin amminah da kuma nusaiba.

Daqar na bari mukai azahar kafin mu shirya mu tafi tare da driver,fadin irin kyau din da mukayi kuwa bata baki ne,kamar wasu triple haka muka fito.

Tun shigowarmu layi nake tuno abubuwa da dama da suka faru tun daga yarinta ta har zuwa lkcn da akai min auren rashin gata😓

A qofar gidanmu m.sabo yayi,jikina a sanyaye na bude murfin na fito don lkc daya fargaba ta shigeni dana tuno yadda mukayi da Ammi a wannan can xuwan.

Tun daga soron gidan zakasan an samu cigaba,dan haka sallama dauke a bakunan mu muka shiga gidan inda nake bin gidan da kallo kamar wata baquwa.

Ammi ce ke qoqarin amsa sallamar tana fitowa daga kitchen.

Banyi sanya ba na tafi da gudu na riqeta tare da sakin marayan kuka.

Aa yau manyan baqi ne a gidannamu"tace tana fara'a.

Ke kuma daga zuwa sai kuka"ta kuma fada tana dago ni a jikinta.

Falo muka shiga har Lkcn inamatsar kwalla,su kuwa su mufida suna min dariya.

Shima falon kamar bashi ba dan komai bana dabane a ciki an gyarashi kamar na yan gayu.

Gaisuwa aka shigayi nidai ina maqale jikn Ammi kamar wani zai kwace min ita.
Ki tashi ki samo muku abinsha kafin abincin ya qarasa,suma su ruqayya sunce zasu xo,ita zainab ma dake kusa kuma ita ba yara ba amma har yanxu shiru"

Ammi suma zasu xo"nace ina mai jindadi.

Eh haka aisha ta fada min jiya da mukayi waya"

Fridge Dana gani a falon na nufa don samo abin sha.kunun aya ne da zobo juice dan haka na dauko mana kafin naje kitchen dauko cups.
Shi kanshi kitchen din kamar na wata amarya Ko yaushe aka samu wannan cigaban oho.

Ammi abbinah pa?Nasan dai yau ba aiki"nace ina tsiyayawa su mubina juice.
Tun daida
suka shigo bayan daurin aure suka fita amma duk inda yake yana kusa da gida don a qasa ya fita"tace tanashiga ciki.

Sallamar ya zee dana jiyo yasa na dire jug din na fita a million.Kamar wata baby haka na dafeta har muna qoqarin faduwa.

Oh my lil sis har yanxu kinanan a yadda kk,kwata kwata gudu da tsalle bayayi miki walaha"

nayi missing dinki ne pa"nace a shagwabe. jin kamar goyo a bayanta yasa nayi saurin sakinta.

Baby boy ne kwance a bayanta yanata sharar bacci.
Ya zee dama kin haihu shine ko a sanar dani"nace hawaye na taruwa a idona.

Kiyi hqr auta wlh munso sanar miki amma...."

Amma abbi ya hana koh?shikenan tunda an cireni cikin family dinnan"nace ina shigewa daki.

kuka na shigayi suka hadu suna lallashina,sai da ammi tasa baki kafin nayi shiru na dauki yaron mai suna muhammad Aameen.

muka shiga hira,suma su mubina warewa sukayi mukaita labaran duniya,harsu ya aisha sukaxo bamu sani ba sai dai kamai mukaga muhibba.rungume juna mukai muna murnar ganin juna falo muka fito Na rasa Gurin wanda zan nufa Kaawai na Fashe da kukan murna.Dama inada wannan bataliyar amma da nake rayuwar kadaici?

Haba auta keda zakiyi murnar ganinmu saiki buge da kuka?common share hawayenki"ya aisha tace tana ruqoni Tare da share min hawaye.

Duka yaran nawa sukayo kaina kowa yanaso Na daukeshi.haka naita dagasu sama muna nishadi abinmu.
Ranar jinta nake kamar sallah danagamun hadu dukanmu muna kwasar dambun ammi,sai naji haushi da bamu taho dasu iman ba da suma sunga yanuwansu ai. Kwata kwata na manta biki mukazo sai da aka fara kiran la'asar kafin ammi ta fara fadan mu tashi mu shiga gidan bikin.

wajen da muka ci abinci Na shiga gyarawa su kuma suna sallah da yake ni ina off.

💙💙💙RABON KWADO💙💙💙

Er mutan ungogo💋💋💋

Rabon kwado fans ina yinku irin totally dinnan,fatana a koda yaushe mu kasance daku domin da yabo da kwarin gwiwarku komai ke gudana.

Ana mugun tare🤝

🅿211-🅿215

Bayan idar da sallar qarayin wata kwalliyar su mubina sukayi,nidai gyara fuska kawai nayi nayi yafen mayafina kamar yadda naga suma sunyi.

Har tym din ammi tana cikin dakinta hakan yasa naje domin sanar mata zamu wuce.

Oh wlh nayi missing gadon nan naki ammi,kai duka gidanma nayi missing,amma ku sam baku damu dani ba kamar an cire ni daga cikin yaran gidan nan"na fada muryata na rawa alamar kuka.

Waya ce miki mun manta dake auta?wlh kullum a gidan nan sai anyi mgnrki,bama ni ba ko abbinku koda yaushe maganarsa ke ce,tayaya za'ayi mu haifi 'ya mu manta da ita?"Ammi tace cikin rarrashi.

To amma Ammi meyasa kowa yayi avoiding dina kamar bani da dangi"
Chapter 25 · 0% Book details