← Book details Rabon Kwado Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 10 OF 26

Sashe 10

Rabon Kwado Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Eh haka ne"suka hada baki.

Yauwa,yanxu kunyi sallah?"

Aa"

To ku shiga toilet kuyi alwala sai kuxo kuci abinci"

To amma zaki kunna mana catoon koh?tunda momy ma tana kunna mana"

Eh zan kunna muku"nace ina tura qeyarsu.

Aunty ni ban iya alwalar ba"iman tace tana kallona.

To muje nayi miki"na fada tare da miqewa.
Saida sukai sallar kafin muka fito falo da taimakonsu na kunna qatuwar plazma din domin kunsan babu a house😜.

Abinci na zubo musu na zauna ina basu a baki muna kallo.
Shahid ne ya fito a dakinsa ya wani rakube kamar na allah.

Kazo kaima kaci abinci"nace ina kallonsa.

Ni bazanci dasu ba"

To kaje kitchen ka dauko plat a zuba maka"

Haka muka zauna suna cin abinci muna hira,naji dadi sosai dan mutum rahma ne,kuma duk sainaji qunci da damuwar danake ciki kashi 50 babu ita.

A hankali ya turo qofar kafin ya qaraso cikin falon da wannan tafiyar tasa ta taqama.sallamar ma ciki ciki yayi ta inda yaran dukansu sukaje suka dane shi.

Iman ya daqa sama kafin ya ajiyeta sunata dariya.

Dama yana dariya haka?ban taba ganin ko murmushinsa ba tunda nake.zuba masa ido nayi inda muna hada ido ya watsomin wata harara.
Ba shiri nayi qasa da kaina.
inaji sunata surutansu nidai nakai plats din kitchen kafin nayi hanyar daki dan naga sun manta da rayuwa a wajen.

Ke zonan"najiyo muryarsa.

Ke?baisan sunana ba daxai kirani da ke?
Tsayawa kawai nayi ba tare dana juyo ba.

Ko ni nazo?"naji ya kuma fada.

A hankali na dawo na nemi guri na zauna.

Shahid kuje zamuyi magana da auntynku"yacewa yaran.

Tafiyarsu tasa falon yin shiru sai qarar tv,inda ya dauki remote ya rage qarar.

Ina fatan kina sane da dalilinki na zuwa gidan nan?idan ma kin manta to ki tuna kinxo gidannan ne a matsayin yar aiki.dan haka yanzu zan kafa miki dokoki kanar yadda ake kafawa duk wata mai aiki idan tazo,haka kuma idan kin saba zan hukunta ki kamar yadda ake hukunta yan aiki."

Inaso kisan cewa gobe monday yarana suna da scul,dan haka kafin 7:30 ki tabbata kin gama shirya su,kin hada breakfast dinsu sannan kinyi musu abinda zasu tafi dashi wani daban ba wanda sukai b/fast ba.ina fata kin gane abinda nake nufi?"

Banyi mgn ba kuma bani da niyyar yi dan bansan mezance masa ba.

Tashi yayi ya kashe tv tare da fita ya rufo qofar.
Nima tashi nayi naje nayi musu wanka inda muka sha tataburza da mutumun shi wlh bazan masa wanka ba,nidai qyaleshi niyi naja suiman muka tafi bedroom dimmu.wannan wayar na dauko dan da alamar yau zatayi amfani,Alarm na saita na 4:30am dan banason wata matsala ta hadoni da wannan mutumin dan naga qiris yake jira ya qaddamar mini.

Ana Tare🤝🤝💙💙RABON KWADO...💙💙

Khayraty Er mutan ungogo💋💋💋

🅿61-🅿65

Qarfe 4:30 na asuba alarm ya tashe ni da yake bani da nauyin bacci.

Alwala nayo na gabatar da raka'atanul fajr kafin na dauko qur'ani na fara karantawa.
Saida akai kiran assalatu kafin na kayo sallar asubahi.

Kitchen na nufa dan fara gabatar da aikace aikace na.

Doya na fara ferayewa sannan na feraye dankali bayan na dora ruwan tea akan cooker.

Soyayyan dankayi da kwai nayi a matsayin breakfast,inda nayi feten doya wanda yaji hanta a matsayin wanda xasu tafi dashi.

7:09 na kammala komai hakan yasa na koma daki na shiga tashinsu.

Da rigima da komai na samu na kallama shiryasu cikin uniform dinsu,inda na nufi dakin oga shahid dan taimaka masa ya shirya dan lkc ya tafi gashi ko breakfast basuyi ba.

Haka muka fafata dashi,ko dan yaga ina cewa yai sauri ya ringa abubuwa kamar mara laka,nidai danaga ya fito a wanka na fito na qyaleshi.

Dinning mukaje na fara hadawa su shahida b/fast din dan 7:30 din harta dan gota.

Kamar kullum da tpyrsa ta taqama da isa ya shigo falon inda sai a lkcn ma nasan akwai kofa da zaka iya shiga bangarensa ta nan falon.

Tashi sukayi sukaje suka rungumeshi,kafin ya sakarwa kowa kiss a kumatu.

Good mrng my angels"naji yace yana shafa fuskokinsu.

Shahid ne ya fito nidai na hada masa nasa abincin,inda nake saqe saqe na gaisheshi ko kuwa?

Kar naje na gaidashi ya yarfa ni,kuma sai nake ganin kamar idan ban gaida shi ba ban kyauta ba.

ina kwana"nace ba tare dana kalleshi ba.

Bai amsa ba hakan yasa nayi dana sanin biyewa dayar xcyta data saka na aikata haka,gashi ya shareni kamar baisan inayi ba.

Shahid sauri fa zakayi kaga driver yana jiranku kar kuyi late"yace yana zama akan kujerar falon.
Saida shahid din ya gama suka dauko lunch-box dinsu dan tafiya,a inda shahid din ya bude dan ganin mene a ciki.

Kai kai kai!Daddy kaga abinda tayi mana,wlh ni baxanje da wannan abin ba yan class dinmu suyi min dariya"yace yana ajiye basket din nasa a gaban daddyn nasu.

Sai lkcn ya kalleni,nidai ina tsaye da plat din da suka gama cin abinci mamaki ya cika ni.
Dan yaje da faten doya shine za'ayi masa dariya?faten da na baje basirata akanshi shine akeyi masa haka?

Kuje wajen motar ganinan,duk ku ajiye baskets din"yacewa yaran.
Aikuwa ba musu suka dire suka fice.

Wato bakiji gargadin danayi miki akan kulamin da yara ba koh?to ki sani kamar yadda na fada indai kk yi laifi zan hukuntaki kamar yadda ake hukunta masu laifi to zan aiwatar da hakan,ki jira purnishment dinki kafin dare,hakan xaisa ki ringa kiyaye duk wani abu daya dangance ni da kuma yara na"

Yana gama fada yayi ficewarsa abinsa.

Guri na samu na zauna inda wasu hawayen takaici suka zubo min.Wato duk qoqarin da nayi na hana kaina bacci nayi abinda yace badan komai ba sai dan banason matsala ta fara daga bangare na amma hakan bai samu ba.Bai yaba abinda nayi musu ba duk da dama ba dan ya yaba nayi ba,amma shine zaice wani zai hukuntani.
Banga laifi na ko kadan ba,sbd bai fada min kalar abinda zanyi ba,bansan wani irin abu suke tafiya dashi ba amma da yake ya tsaneni shine zai dora laifin akaina.

Daki na koma na kwanta ina kuka,dan bacci da gajiya ke damuna amma nasan bazan iya baccin ba.

Haka na wuni sur ni daya a daki saida naji yunwa na neman kasheni na rarrafo na dauki faten da suka bari na fara ci.

Wai wannan abincin ne za'ace baza'aje scul da shi ba?to ko shugaban qasa ya samu wannan abincin ci zaiyi bare su daba yayan kowa ba.

Bayan la'asar zaman dakin ya isheni,ina fitowa falo na ganshi a kishingide.
Wlh na tsorata sosai dan banyi tunanin da mutun a gidan bama duka.

Zo nan"najiyo muryarsa cike da isa.

Can gefe na zauna ba tare dana kalleshi ba.

Kamar yadda na fada miki dazu zan hukuntaki akan lefin da kk yi,yanxu ina so kiyi abinci kala hudu da juice kala biyu,ko wanne ya kasance dai dai cin mutum goma ne,na baki nan da awa biyu idan kk wuce haka ki tabbatar gobe xakiyi wanda ya ninka hakan."

Komai na amfani akwai a kitchen,idan kuma kina buqatar wani abu zaki iya fada in babu sai a siyo."

Tofa!wata daban,da gsk aikin nazoyi kenan?
Ta inama zan fara wannan aikin har kala 4 a cikin awa biyu?kuma ma wai dai dai cin mutum goma.

Ko a gida bantaba yin girkin da mutum goma suka ci ba,amma gashi an kawo ni inda zanyi,allah sarki ni.

Kina batawa kanki lkc ne"na jiyo muryarsa.

Daki nayi ina zuwa na fada kan gado na rushe da kuka.

Abbi why?Abbi meyasa zaka kawoni inda ba'a qaunata?Abbi meyasa zaka daina sona ka hadani aure da mugu mara tausayi?
Ya sadiq kazo gareni dan allah,ina buqatarka a kusa dani,nasan da kana kusa bazaka bari a cutar dani ba....haka na ringa kuka ina surutai,saida nayi mai isata kafin na bawa zcyta hqr na yanke shawarar zuwa nayi girkin.

Tashi nayi na nufi kitchen tare da tunanin abubuwan da zan dafa masu sauqi wadanda baza su ja lokaci ba,dan yanxu ma na kusa cinye awa daya.

Haka na raba hankali na,inda na dora coconut rice akan electric,fried rice a kan cooker,sai kuma blander din kayan miya dana jona a socket,ga blander din fruit itama tana markada min abinda zanyi juice dashi.

Juice din na fara gamawa,inda nayi lemon mangwaro,sai kuma pineapple and coconut juice.

Saida na gama coconut rice din sannan na dora macaroni armlet a electric din.
Da taimakon allah na samu na gama girkin amma kala uku nayi dan bazan iyayin na hudun ba tunda ba fadar allah bace,wannan dimma da nayi nayi qoqari dan sosai na gaji danma abincimasu sauqi nayi sannan na samu kayan aiki masu sauri.

A coolers na zuba abinci,yayin da na zuba juice din a jugs naje na jera a dinning,ni har mamaki nake yadda zaiyi da wadannan abinci masu yawa haka.

A falo na wucesu nayi ciki abina dan tun dazu ina jiyo dawowarsu dan yanxu har an idar da sallar magriba,inacan ina aikin daba godi bare na gode.

Shahida ce ta biyoni.

Aunty wai meyasa bakya zama tare damu da daddy muna hira kamar yadda momy takeyi kafin ta tafi?"

Kamo hannunta nayi muka zauna a gefen gado.

"kinga shahida banason surutu kinji koh?idan kuma kinaso mu bata shikenan"

To na daina"

Yawwa babyna,kije kuyi hira dasu ya shahid kinga na gaji wanka nakeso nayi gashi banyi sallah ba"

Dana shiga toilet haka naita gasa jikina da ruwan dumi sbd rashin sabo,dan yau na aikatu ba kadan ba.
💙💙RABON KWADO...💙💙

Khayraty Er mutan ungogo💋💋💋

🅿61-🅿65

Qarfe 4:30 na asuba alarm ya tashe ni da yake bani da nauyin bacci.

Alwala nayo na gabatar da raka'atanul fajr kafin na dauko qur'ani na fara karantawa.
Saida akai kiran assalatu kafin na kawo sallar asubahi.

Kitchen na nufa dan fara gabatar da aikace aikace na.

Doya na fara ferayewa sannan na feraye dankali bayan na dora ruwan tea akan cooker.

Soyayyan dankali da kwai nayi a matsayin breakfast,inda nayi faten doya wanda yaji hanta a matsayin wanda xasu tafi dashi scul.

7:09 na kammala komai hakan yasa na koma daki na shiga tashinsu.
Chapter 10 · 0% Book details