← Book details Rabon Kwado Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 23 OF 26

Sashe 23

Rabon Kwado Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Kuka nasha sosai dan ummi sam taqi amincewa na nada mata dukan da zata daina numfashi.
Da uncle ma yaji shida yaya cewa sukai zasu kai qara kotu ta haka ne za'a gano duk wani mai laifi.Amma fir ummi taqi amincewa acewarta abin kunya ne mu tsaya shari'a da yanuwan mahaifinmu,kuma koshi yana raye tasan bazai goyi da bayan hakan ba don hk mu barsu da allah ai shi ba azzalumin sarki bane.

Badan uncle yaso ba yabar mgnr,amma yasa aka kori duk wasu masu hidimar gidan don yace da hadin bakinsu komai ke faruwa.

Daqar ya yarda aka samo sabon get man,mai bawa shukoki ruwa sai kuma wadda zata ringa taimakawa ummi da abinda ba'a rasa ba,amma itama bata shigowa part din gidan tanacan part din da aka tanada domin masu aiki,kuma idanma ta kama zata shigo to iyakacinta falon qasa.

Durqushewar A.A motors yasa aka siyar da sauran Kadarorinsa domin farfado da company din.

Tunda yanuwan abba suka samu abinda sukeso suka dauke qafa daga garemu,akasin da da kullum suna tafe a hanyar gidanmu.hakan ya qara tabbatar mana da cewa komai daga garesu ne.Kamar yadda basu qara neman mu ba muma sai muka manta dasu.

Tasowar bikinsu mufida yasa ummi ta matsanta sai munje wajensu mun sanar dasu domin a yanxu bamuda wasu dangin mahaifa da suka wucesu.

badan raina yaso ba na tattaro yara muka zo domin zuwa wajen dangin mahaifinmu.

Gaba dayanmu kwanmu da kwarkwatarmu muka tafi tsohuwar unguwar da suke zaune.Munsha wahala sosai don har mun fadda tsammani zamu koma gida domin duk yadda ummi take musu kwatance kowa muka tmby sai yace baisan wadanda muke nema ba.

Wani mai kanti mukai sa'a ya gano kwatancen da muke dan kusan shekara 8 kenan rabonmu dasu.

Hajia ai idan kwana kuna tambayar auwalu da qaninsa sani bazaki sani ba,nima dan dai na dade a unguwar ne yasana gano wadanda kuke mgn akai,mgnr gsky yanxu duk ahalinsu sun tashi daga wannan unguwa.Akwai wata sabuwar unguwa da ake kira sabuwar abuja can suka koma wajen shekaru 4 da suka wuce.yanxu hakazan muku kwatancen unguwa kuna zuwa ku tmby kigan hajia shatu mai jan kai na tabbata duk wanda kuka tmby zai nuna muku"

Duk cikinmu ba wanda ya iya mgn saboda mamaki da al'ajabi ni kuma mamaki nake har yanxu baba shatu na raye.

Yaya ne ya miqa masa hannu suka qara musabaha,mudai mota muka koma muka barshi yanawa yaya kwatancen unguwar da zamu nufa.

Har muka dauki hanya ba wanda ya iya cewa komai.
Kamar yadda dattijon yayiwa yaya bayani hk muka isa unguwarmai qarancin jama'a da zirga zirgar ababan hawa.

Yayane ya fara parking don dama motarmu ce a gaba inda yake tuqamu sai ni a gefensa sai shahid,zaid,zarah da shahida a back seat.
Dayar motar kuma driver ne sai ummi,mufida,mubina da kuma iman.

Mun dade a cikin mota kafin yaya ya samu wanda zai tmby inda aka kwatanta mana.
Dawowa yayi muka qara gaban wani qaton gida wanda za'a kira da estate.

Yaya ba'a samu gidan bane?"nace ganin ya tsaya kuma baice komai ba.

Nan dai wanda natmby ya nuna min,amma ina tunanin gsky banan bane"yace yana nuna estate din.

Wangale daya daga cikin manya manyan get din estate din yasa muka maida hankali ga rantsattsiyar motardata sako kai waje.

Da hanzari yaya ya fita don gani motar na shirin wucewa,gashi na waje baya iya hango na cikin motar.

Ganin mamallakin motar ya sauke glass suna mgn da yaya yasa na fito kamar yadda naga ummi ma ta nufi wajen.

Kafin mu qarasa mai motar ya maida glass din tare da bawa motar wuta yayi gaba tare da budemu da hayaqin motar,kana gani kasan da gayya akai hakan.

Saida hayaqin ya lafa kafin muka samu qarasowa ida yaya yake a qame kamar an dasa shi.

Ba gidan bane ba koh?"muka fada a tare nida ummi.

Gidan ne,don fu'ad ne ya fita a mota yanxu"yace yanason boye damuwarsa.

Fu'ad?fu'ad fa kace"muka sake tmby kamar hadin baki.

Eh shine,kawai mu koma gida don ya sanar dani babu mai sauraronmu tunda ba'asan da zuwanmu ba"ya fada yana tpy dan komawa mota.

Eh lallai,shi fu'ad din har yaushe yayi baki da arziqin da zai fada mana haka?sbd rashin mutunci harda budemu da hayaqi,to wallah yau komin bala'i sai mun shiga gidan nan koda shugaban qasa ne a ciki"na fada na nufar get din da aka rufe baba dadewa.

Muje zuwa don jin yadda zata kaya.shin suna nasarar shiga gidan ko kuwa?idan sun shiga wace iriyar tarba zasu samu wajen masu gidan?

Er mutan ungogo💋💋
[09-11, 7:57 PM] Cwt-besty: 💙💙💙RABON KWADO....💙💙💙

Er mutan ungogo💋💋💋💋

🅿196-🅿200

Gaba daya jikina yayi sanyi da jin lbrnsu,inda tausayinsu ya mamaye min xcy.
Sosai na jinjinawa qoqarinsu don idan bakaji lbrnsu ba bazaka taba tunanin sunada wata matsala ba.

Amma khadija bayan abinda kk fadamin dazu akan fadanku da broh babu wani abu daban"ta tmby ni.

A iya sani na babu komai aunty anisa,koshi yace nayi masa wani abu?"nace ina kallonta.

Kamar zatayi mgn kuma sai tayi shiru.

Shikenan dai kiyi bacci yanxu kinga dare yayi sosai"

Haka na kwanta inata jujjuya lbrn a zcytah,na dade banyi bacci ba kafin sarkin barayi ya sace ni.

Banyan munyi sallar asuba ma banyi wani bacci mai yawa ba sbd rashin sabo,dan hk qur'ani mai girma na shiga karantawa.

Dana gama ma na qara kwanciya amma baccin yaqi zuwa,don hk na shiga nayi wanka.
Dakinsu mufida naje sunata sharar bacci,dan haka na dauki kayana na sakatare da kafa dauri duk da banyi kwalliya a fuskata ba.

A hankali nake takawa ina qarewa falon saman kallo,kafin na fara saukowa daga stairs din.

Can saman kujera na hango ummi da littafin azkar da alama karantawa takeyi.

Qarasawa nayi na zube kan rug ina gaisheta.
Kamar ko yaushe ta asma cikin kulawa kafin tayimin nuna dana koma kan kajera,murmushi kawai nayi ba tare dana koma ba.

Hk muka kasance tsahon lkc,ganin ta gama azkar din yasa nayi mgn.

Ummi akwai wani abu daza'a taimaka dashi?"

Aa diyatah yi zamanki,akwai mai aiki zata gudanar da komai,zuwa yanxu ma nasan ta kusa kammalawa.Su wadancan kasoshin har yanxu baccin suke?"
Murmushi nayi ina qara qasada kaina.

Bude qofar falon da akai yasa muka kalli gurin a tare.

Sanye yake cikin suit ash colour,fuskarnan tashi kamar kullum,amma kana ganinsa zakasan akwai abinda ke damunsa,dan tafiya yake kamar yana tausayin qasa,akasin da da yake tafiya cikin kuzari,qasaita da tafin jarumta.
A cikin sakwanni da basu wuce 10 ba na gama karantar yanayinsa,kafin na dauke kai kamar ban damu da sanin wanda ya shigo din ba.
A dan nesa dani ya zauna tare da lankwasa qafa sannan ya shiga gaida ummi.

Fuskarta ba yabo ba fallasa ta amsa a taqaice ba tare data kalleshi ba,hakan zai tabbatar da akwai wani abu a qasa.

Nima gaidashi nayi kamar anyi mini dole,shima a taqaice ya amsa yana satar kallon ummi da alama bashida gsky.

Su shahid sun tafi school ne?"yace.

Aa kai ake jira kazo sai ka shiryasu ka kaisu"ummi ta fada still bata kalli inda yake ba.

Tsam ya miqe ya isa inda take ya zauna tare da riqo hannunta.

I'm so sorry umminah,wlh indai a kan mgnr jiya ce na janye tunda bakya so,kinsan dai banason ganin wannan yanayin a fuskarki"
Batai masa mgn ba don hk ya cigaba.

Ummi jiya kwata kwata kasa bacci nayi,rabona da abinci tun jiya da safe,plzz ki tausamin,kuma bazan qara mgnr ba tunda bakyaso"

Rashin bacci ko cin abinci duk kaine ka jawowa kanka,tunda kana zaman zamanka zaka jajibowa kanka wani aure,kuma inhar kanaso mu shirya dakai karna qarajin makamanciyar wannan maganar daga gareka"

Allah sarki ummi ashe duk akan mgnr aure take wannan fushin,data amince yayi aurensa kawai maybe yana buqatar hakanne.

Sama sama suke mgn akan abinda ya shafi company,kafin ya sanar mata cewa a satinnan yakeson zuwa dubai wajen wasu abokan kasuwancinsu daganan zaije US dan ganawa da uncle.

Tashi ummi tayi domin samo masa abinda zaici nidai har lkcn kaina a qasa don bazakayi zaton ina falon ba ma.

Jiya su Ammi na gaidake"najiyo shi.

Ina amsawa"na fada a qasan maqoshi ba tare dana dago ba.
Gashi ta bani saqo wai inji qawarki"

Da sauri na dago dan nasan bani da wata qawa sama da nusaiba,don sosai nake missing dinta kawai dai daurewa nake,bama ita ba duka family dina,musamman ma su muhibba,sauqinta ma ina ganinsu shahida inajin dadi.

Ina dagowa naganshi yana danna waya kamar bashine yayi mgnr ba.

Ganin ummi ta taho yasa banyi mgn ba.

Madaidaicin farantin hannunta ta ajiye.Ganin zata fara hada tea yasa nayi saurin tashi don karba domin bai kamata tana aiki ina zaune ba.

Batai musu ba ta bani na shiga hada tea din ita kuma ta zauna tana ganin kayan da yak nuna mata a waya ko za'a siyawa su mubina.

Ina gama hadawa naje ta gefensa na miqa masa,banyi aune ba naji ya kama harda hannu na kuma yaqi saki ya wani basar ya cigaba dayi mata bayani batare daya kalleni ba bare yasan yanayin danake ciki.

Duk a firgice nake dan banaso ummi ta dago taganmu a haka,amma shi bashida niyyar saki na.

Sunyi kyau sosai,bari na tasosu su gani,idan sunyi musu sai kowacce ta zabi colour"ummi tace tana miqewa,amma inada tabbacin zata ganmu shiyasa ma nayi qasa da idona.

Tana dan nisa kamar jira yake ya hanyoni har tea din na zuba akan hannu na.

Qara na qwalla kadan sbd zafin danaji,inda shi kuma ya rude ya ajiye tea din a centre table ya shiga fifitamin hannu da iskar bakinsa.

Ba qonewa nayi ba don kadan tea din ya zuba a hannun amma ganin ya rude yasa na qara langwabewa ni a dole zafi nakeji.

Fahimtar da yayi kukan na shaqiyanci ne yasa yayi smiling tare da janyoni jiknsa.

Nernah rigima"ya radamin a kunne da sexy voice dinsa hakan yasa naji yani yarrrrr.

Plzz ka sakeni kar ummi ta dawo"nace muryata na rawa jin numfashinsa akan wuyana.

Zan sakeki idan kin fadan dalilinku na gudowa kuda yara kuka barni ni kadai,nernah jiya kwata kwata kasa bacci nayi sbd ummi fushi take dani dan nace zanyi miki kishiya,ummi bata taba fushi dani irin haka ba"
Chapter 23 · 0% Book details