← Book details Rabon Kwado Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 12 OF 26

Sashe 12

Rabon Kwado Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ai daddy yace surutu na yana da kyau,kuma journalist zan zama"

Haka dai,shi yana son cigaban yayansa amma bayasan na yayan wasu.gashi qiri qiri yasa mafarkina ya rushe inaji ina kallo an hanani zuwa scul din.

Mutane nawa ne suke neman shiga mkrntr basa samu,amma ni na samu anyimin buqulu.

Makwanci na nema bayan na tofe mu da addu'o'in kwanciya bacci,inda yaran suka sakani a tsakiya.
kwanciyata ba dadewa bacci yai gaba dani dan gajiya.

**-**-**-***-***-*

Washegari daqar na miqe dan baccin bai isheni ba.Amma dana tuno ayyuka da nauyin dake kaina dan dole na hqr da baccin na tashi.

Kamar jiya,yauma saida nayi asuba kafin na shiga kitchen.

kosan doya nayi da kuma sandwich tunda naga su yan gayu ne,kuma ni ai baza'a nunan ire iren wadannan girke girken ba.

Kai Allah ya sakawa ya rukayya da alkhairi data kawo shawarar sakani a mkrntr koyan kwalliya da girki,dan gashi yanxu na fara ganin amfaninta.Dan da ace ban iya ba da nasha takaici a wannan gidan.
To ko dan ya qureni yake bani purnishmeny din girki?tunanina zai iya zama gsky tunda jiya yace kar nayi irin abincin da nayi na sake wasu kalolin.

7:35 suka gama suka fita dan har lkcn daddyn nasu bai zoba.
Tunda suka tafi na gyara ko ina na baza turaren da ummi ta bani dan qamshinsa yayi min sosai.
Ko ina kuwa ya dau qamshi da qyalli dan saida nayi mopping din ko ina.

Wanka nayi na fara aikin abincin da zanyi dan sonake daga yau na dena wannan azabar naji data yaran su kadai.

Cikin ikon allah kafin la'asar na kammala.sai dai gajiya dake nuqurqusa ta dan nasan dole nayi jiyyar kaina.

Dambun cous cous nayi,sai jelop din rice and beans,coconut juice,zobo drink,sakwara,Dan wske,da kuma faten dankali.

A falon na zube ina mayar da numfashi kamar wadda tayi tseren gudu.

Knocking naji a qofar falon,daqar na tashi ina addu'ar allah yasa baqi mukayi dan xaman haka ba dadi.

Wani dogon saurayi ne a tsaye.Sai kwanukan jiya dana zuba abincin da nayi a hannunsa.

Sannu hajiya,dama alhaji ne yace nazo na karbi abincin da akayi"saurayin yace.

Ciki na koma na fara dauko masa abincin,saida na gama na karbi kwanukan na dawo na kwanta dan bayana ji nake kamar ya cire.

Ko ina za'a kai abincin oho"nace a zcytah.

Da yaran suka dawo kawai qarfin hali nayi nai musu wanka na saka musu kaya.
Dambun cous cous din dana diba a cikin wanda nayi na zuba musu.

Aunty gobe ma zakiyi mana irin abinda kk mana yau?wlh akwai dadi ko iman?"Aku shahida tace tana zuba lomar dambu.

Ai wani abin xan kuma yi muku mai dadi wanda yafi na yau dadi"nace ina dry,dan da alama maggi ne ya kama kunnenta take wannan batu.

Da dare har muka kwanta daddynsu bai xo ba,in taqaice muku tun daga ranar saida yayi sati bamu ganshi ba.ni dadi ma naji dan koba komai na hutu da fi'ilinsa.

Yaran ne dai suke isata da tmby dan shahid ma saida ya tmby ni,nidai ce musu nayi yayi tpy kawai tunda bansan me xance ba.

Haka rayuwa ta cigaba da gudana yau da sauqi gobe ba dadi.dan yanxu ma kwata kwata ya daina shigowa bangaren sai dai da dare idan ya dawo su yaran su bishi can falonsa dake sashinsa,saidai na zauna kwalam hakan ke bani damar kukana son raina,dan har xuwa yanxu da nake baku lbrn nan 4months kenan da kawo ni gidannan amma ko quda ban taba gani ba kamar banida dangi,gashi rayuwar gidan bata sauya ba kullum jiya i yau,dan ma bana ganinshi sosai dan sai tashi ta kawoshi yake shigowa bangaren.

Wannan shine asalin labari na.
Ku biyo ni dan jin yadda zata kaya har zuwa qarshen lbrn.

Taku har kullum KHAERATY Er mutan ungogo💋💋
[07-23, 20:40] Sistoh: 💙💙RABON KWADO...💙💙

Er mutan ungogo💋💖💋💖💋

🅿71-🅿75

Ban tashi dawowa daga tunanin ba sai 12:39pm.

Ba shiri nayi Addu'a na kwanta,ina fatan Allah ya bani ikon tashi da wuri dan sallamar yarana.

A hankali nake bude idanuwa na wadanda suka sauka akan qaton agogon dake mannne a bangon daki.

Da sauri na duro daga gadon dan idan ba idanuna bane 6:31am na gani agogon ya nuna.

Alwala nayo cikin hanxari kafin na gabatar da sallah.Yau ko krtn qur'anin dana saba banyi ba haka na miqe ina tunanin ta ina zan fara.

Indomie zan dafa duk wanda yaga bazai ci ba ya batta dan na fara gajiya da wannan tsirfar,ko haka suke yi da ya fatima tananan?ko kuma nice da aka mayar baiwa ake min wannan iskancin.

Cikin muntuna da basu haura 20 ba na kammala indomie sannan na soya kwai.

Kwan na qara fasawa Dan yin alalar kwai(awarar kwai)ko kuma kwai cikin kwai naji wasu na kiransa.

Qullawa nayi a farar leda bayan nasa kayan dandano dana qamshi.

Nan ma ban dau lkc ba na kammala na fito.Amma da yake ban farka da wuri ba dana duba agogo 7:27.

A hanzarce nayi musu wanka tare da saka musu uniform,yau ko shafa musu powder din dana saba banyi ba.

Wajen oga shahid naje inda saida na dakeshi sannan ya maida hankali ya shirya na taso qeyarshi gaba.

Yana zaune a daya daga cikin luntsuma luntsuman kujerun falon yayi crossing din legs yana girgizasu a hankali,ga dukkan alamu mulki da rashin mutunci yake ji dashi.

Kamar ko yaushe wucewa nayi dan Zuba musu breakfast ba tare dana gaidashi ba,dan tun ranar dana gaisheshi yaqi amsawa ban qara gigin gaidashi ba.

Gsky ni baxanci indomie ba"naji shahid ya fada.

Kada Allah yasa kaci,ai kana da hannu zaka iya shiga kitchen ka dafa abinda ranka yake so"na fada a qufule dan yaron ya fara kaini bango.

Jin abinda shahid din yace yasa suma duk suka daina cin abinci,shidai yana zaune baice mana komai ba saima wayarsa da yake latsawa.

Malamai idan bazaku ci ba zan tashi dan ina da abinyi"nace cikin fada dan zuciyata kamar ta fito.

Haba ai abin ya isa hk kullum nice cikin aiki sannan uba yayi min yara su yimin?wlh ina raga musu ne sbd maraicinsu,kuma abinda nasan bazan yiwa yaran dana haifa ba wlh bazan iyayi musu ba,Amma da sbd halin ubansu ne wlh ko kallo basu isheni ba.

A barni da ciwon rabuwa da masoyina mana,a bari naji da kadaici da kewar su ammi dake damuna mana,A barni da baqin ciki da takaicin dake raina na banzatar dani da kowa nawa yayi,a bari naji da aiyuka da dawainiyar da nake kullum mana.
Amma bayan wadannan sai anxo ana min wani fi'ili?
Kawai na sakawa zcytah hqr ne,amma har a gayamin seniority nida nayi bording scul.

Tashi kawai nayi na nufi daki dan idan na cigaba da zama a wajen takaicin zai min yawa.

Bansan lkcn da suka tafi ba nadai kwanciya nayi ina hawayen takaici.

Tunda na shiga dakin ban kuma fitowa ba,dan ko girkin da nakeyi kafin su dawo banyi ba.ni kaina yunwa ce take nuqurqusata tunda ko breakfast banyi ba,wanka kawai nayi dama ina fashin sallah.

Tashi nayi na taimakawa kaina na bude friege na dauki fresh milk na kwankwada sannan na fara dawowa dai dai.

Harabar gidan na fito wanda tunda nazo gidan leqe ma saida dalili.
To nagaji da wannan rayuwar takura kan,fitowa zan ringayi ina shaqar ni'imar ubangiji.

Zagaya gidan nayi tayi harda inda ban taba zuwa ba yau saida naje.Tsarin gidan ya burgeni amma da ace nida ya sadiq za muyi rayuwa a ciki da abin yafi qayatarwa.

Iskar yammar data fara kadawa yasa na qara shagaltuwa dan sosai yanayin yayi min dadi.

Duk wata damuwa saita ragu a zcytah,dan na dade banji irin wannan nishadin ba.

Allah sarki nusaiba,itama tanason iskar yamma,dan ita har ware hannuwa take kiga tanata sakin murmushi.

Zama kawai nake naita mata dariya.
Takance min"Khadija bazaki gane abinda nakeji game da yanayin nan ba,ina imaging abubuwa da dama wadanda bazasu lissafu ba.Amma kuma kinsan masoya sunfi more irin wannan yanayin musamman ma idan suna tare"

Allah sarki sis itama ta manta dani,koda yake kowama bayan su ya zee yake,nidai Allah ya kawo ranar da zan fita a gidan nan naga gari.

Sai wajen magriba sannan na farga da lkcn dana bata a wajen,aikuwa na samu gurin dibe kewa na raya a zcytah.

Iman na fara karo da ita tana rusa kuka.

Babynah menene kk kuka"nace ina tsugunnawa a gabanta.

Ba tpy kikayi kika barmu ba"tace tana shassheqar kuka

Srry kinji iman dina?bazan kuma tpy na barku ba ina tare daku kinji?"nace ina share mata hawaye.

Daukanta nayina saba a kafada dan basa min wahalar dauka,har shahida idan ta rayomin har goyata nake.

Ya fatima taita yimin fada wai nice nake qara sangarta yaran nan shiyasa suke tabara son ransu.
Nidai dariya kawai nake nace"ba dai a shiga tsakanin uwa da yaya ehe"

Sai kiyi tayi ai,ni dai idan mutum ya fara ciwon qirji sannu da dura madara ne kawai nawa"

Allah ka jiqan baiwarnan taka amin.

ina su ya shahidan suke?"na tmby iman.

Tana daki wai abinci xata ci"

Wanka nayi musu kafin suma na basu fresh milk din suka sha dan har lkcn ban huce ba bare na dora abinci.

Ni yunwa nakeji"shahid dake tsaye a bakin qofa ya fada.

Ko kallon inda yake banyi ba,tunda baisan sunana ba kuma bazai iya shigowa ba.

A qasan carpet din dakin muka baje ina koya musu karatun qur'ani kafin daga bisani suka dauko jakunkunan su sukai bitar abinda aka koya musu.

Saida daddynsu ya dawo sannan muka gama,suka tafi wajenshi ni kuma na hau gyaran wadrob.

Aunty wai daddynmu yace kixo"iman tace tana darewa baya na.

Wash baby,lukutar nan dake zaki ringa dare min baya saikin karya ni"
Dariya mukasa dukanmu.

Saida na dade kamar bazaje ba kafin na tashi muka tafi kiran.

Zama nayi ina dora iman akan cinya ta.

Da hikima duk ya kori yaran kafin ya juyo kaina.

"Wato harkin samu damar da zaki ringa yiwa yarana tsawa a gabanah koh?Da kinsan bazaki iya jure duk wata dawainiya tasuba kika ce zaki aure ni"

Saurin dagowa nayi na kalleshi,wato nice ma nace zan aure shi?ko a tunaninsa da son raina akai auren?.
Chapter 12 · 0% Book details