← Book details Rabon Kwado Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 15 OF 26

Sashe 15

Rabon Kwado Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Tashi kawai nayi na shiga dakin Ammi na fada gado tare da cigaba da kuka na.

Allah sarki uwa!Ammi ce ta zauna kusa dani tare da dora kaina akan cinyarta tana gogen hawayen fuskata.

Ya isa haka kinji auta?kar kije kanki yayi ciwo.kiyi hqr nasan ba'a kyauta miki ba,kullum da zancenki nake tashi a raina,amma ina mgn Abbinku zai fara fada,ko yanuwanku ba yadda basuyi zasuje ganinki ba ya hana,a cewarsa a barki zuwa wani lkcn sai aje"

Amma kuma Ammi..."

Dan allah ya isah haka auta,ki tashi kije cikin yanuwanku kamar yadda kuka saba,Abbinku ya fita shima yana dawowa kije ku gaisa"

Dan dole na tashi na fito fallon,inda sukayo kaina caaa.

Waikina nufin har yanxu baki cire komai a ranki ba khadija?kalli yadda kk rame dan allah"ya aisha tace.

Nidai kawai kallonsu nakeyi daya bayan daya,dan basu san halin da nake ciki ba,kuma na daukarwa kaina alqawari ko naman jikina ake gutsira a gidan nan bazan taba fada ba,idan na mutu dai sai suje su dauki gawata.

Ganin Ammi tana kallona yasa na saki jiki idan anyi abin dariya nayi dan hira da raha akeyi kamar yadda al'adar gidanmu take indai muna tare to fara'a bata barin fuskokinmu.

Ana haka Abbi ya shigo,inda ya zauna shima aka taba hirar dashi kafin ya tashi.

Zumbur na miqe.

Ammi bari naje gidansu nusaiba"

Kin tambayi mijinki zaki wani wajene bayan nan?"ammi tace tana kallona.

Komawa kawai nayi na zauna dan bani da amsar bayarwa.

Ke kuwa auta sallah guda ko lalle baza kiyi ba"ya ruqayya tace.

Ya ruqayya kenan,a wannan anguwar ina zanga mai lalle?ni kinga kaina nema ya damenu ba kitso,kiyi mun ko kalba ce"nace tare da cire dan kwalin kaina.

Ke wai yaushe kika zama qazama ne,ga kanta Ammi dan allah"ya zee tace tana tamin kai.

Ammi dai bata ce komai ba,sai ya ruqayya data miqe tsaye.

Ina wayarki take"tace tana kallona.

Ni nama manta inada waya dan can na barta a kan gado.

Wayar ammi ta karba ta fara kira,bansan wazata kira ba,nadai naji tace wai dan allah zamu fita tare.

Jin tace na tashi muje naji fita yasa na zira mayafi mukai waye.

Can wajen salon din bakin titin layinmu mukaje.

Mun dan sha zama kafin kazo kanmu.

Sosai nakeji iska na shiga kaina bayan an wanke min relaxer ana gyaran kan.

Tsaf aka gyaranshi yanata qyalli da gamsu,ya ruky ta biya kudi muka fito.

Gidan mai lalle mukaje duk da yamma ta fara haka muka samu daqar tayi min hadadden jan lalle na son kowa qin wanda ya rasa😉

Cikin qanqanin lkc na dawo mace sai dai rama da duhun dana qarayi.
Ana kiran sallar magriba muka dawo gida.

Kowa yaita yaba lallen,kafin suka fara shirye shiryn tafiya.

Yaya yanxu yaushe zakuxo"na fada kamar nayi kuka.

Munason zuwa auta amma abbi ya hana mu kuma bamusan dalilinsa nayin hakan ba,kedai ki cigaba da haquri zakici riba insha allah"

Haka ina gani suka tafi,na dawo muna hirar yaushe gamo da ammi dan su shahida suna wajen abbi.

Ammi dan allah ki barni naje gidansu nusaiba"na fada a shagwabe.

Ba hanaki nayi ba auta,mijinki shike da ikon barinki fita bani ba.

Cikin hikima ta ringa min nasiha tare da nusar dani akan muhimmancin haquri dayiwa iyaye biyayya.

Har bayan issha muna jiran dan milkin baixo ba,ni kuwa addu'a nake allah yasa ma yaqi zuwa mu kwana.

Zuwan almajirin ammi yasa na rubuta gajeren saqo a paper nace yakai gidansu nusaiba.

Ai kuwa cikin qanqanin lkc sai gata ta bayyana a gidanmu.

Daku muka qule bayan mun gama ihun ganin juna.

Lallai nusaiba manyan qasa,ai banyi tunanin xaki xo ba"

Kinji ki maizai hana ni zuwa nida nake son ganinki"

Ba wani da kinason gani na ai xakixo inda nake"

Wlh ki tambayi ammi ina zuwa nace ayimun kwatancan gidan,ammin ce tace wai abbi ya hana kowa zuwa dan dole na hqr"

Nima haka dazu tace,nusaiba na rasa gane dalilin dayasa abbi yayi haka"

Ke bafa komai,kawai dai ya fison ki nutsu ne,sbd idan kina ganin yan gida xakiyita tada hankalinki ne"

Uhmm,ni kuwa ina ya sadiq dina?"

Wata muguwar harara ta kwada min kafin tace.

"badai kina nufin har yanxu kina wahalar da kanki akan abinda kk san bazaki samu ba?"

Kamar ya?"

Kamar yadda wanda kk wahala a kanshi,kk kasa nutsar da hankalinki ki rungumi mijinki sbd shi,shi kuma yaje yayi aure tuni ya manta dake dan yanzu matarsa nada qaramin ciki🤰.

🙊🙊🙉🙆🙆🙆🙆🙆

Manage it plss.
[07-23, 20:47] Sistoh: 💙💙RABON KWADO...💙💙

Er mutan ungogo💋💋💋💋

🅿96-🅿100

Karya ne,wlh karya kk nusaiba kice ya sadiq zai manta ni hakakuma qarya ne kice zai auri wata bayan ni"na fada ina riqo wuyan hijab din jikinta.

Kallona kawai ta tsaya tana yi.

Khadija wai yaushe zaki dawo hankalinki ki daina abubuwa irin na jahilai?da aurenki kk dakon soyayyar wani?to gsky ce bazan fasa fada miki ba kuma zan qara maimatawa ya sadiq yayi aure ya manta dake"tace tana fizgewa daga riqon da nayi mata tare da ficewa a dakin.

Kifa kaina nayi a katifa ina maimaita maganganun nusaiba.

Ya sadiq why?meyasa xakayimin haka?da gsk ka manta dani?ka manta dumbin soyayyar danake maka?wayyoo...

Jin an zauna a kusa dani yasa nayi saurin dagowa.
Ammi ce take bina da kallon tuhuma.

Kukan me kk?"ta jefomim tmby.

Shiru nayi ina qoqarin tsayar da kukan dan bansan amsar da zan bata ba,gashi banga alamar wasa ko sassauci a fuskarta ba.

Meya hadaku da nusaiba najiyo hayaniyarku?"ta kuma tmby.

Nan ma shirun nayi tare da qasa da ido dan ko hauka nake bazan iya cewa ammi sbd ya sadiq yayi aure nake kuka ba.

Khadija!

Da sauri na dago dan na manta rabon ammi da kirana da wannan sunan.

Saboda Abubakar yayi aure kike kuka?ko kinason ki fada min har yanxu baki cireshi a ranki kin manta dashi ba?"

Nan ma banyi magana ba.

Kin dauka yadda baki da hankali da tunani haka shima yake da zaita dakon soyayyarki kina matar wani?ko kuwa so kike yayiwa iyayensa butulci kamar yadda kika yiwa naki iyayen kika kasa xama da mijinki lpy?kin zata tunda ya rasa ki shikenan bazaiyi aure ba?ko zaman jiranki xaiyi ki kaso naki auren kixo ya aure ki?"

Wlh,wlh,wlh khadija idan baki gyara rayuwar aurenki kin xauna da mijinki lpy ba xaki sha mamaki na.shashasha kawai,ki tashi ki ficemin anan mijinki nacan na jiranki."

jikina ba qarfi na miqe dan gsky ran ammi ya baci sosai dan bantaba ganinta a wannan yanayin ba.

Mayafina na dauka kafin na nufi dakinta,dan tuni ta fito ta barni anan.

tana zaune a gefen gadon naje na tsugunna a gabanta.

Ammi dan allah kiyi hqr"nace cikin kuka.

Ke zan bawa haquri khadija,kije ki gyara rayuwar aurenki wannan ne kawai zaisa na sakko.ki tashi kin barsu suna jira.

Haka na fito ina kuka inda Abbi ma yayi min fada nidai kuka kawai nake na shiga mota muka tafi.

Shiru motar sai shassheqar kukan da nakeyi.

Aunty me akayi miki kikeyin kuka?"shahida dake gefena tace.

Jin banyi mgn ba yasa ta mayar da tmbyr ga daddynsu.

Daddy me akayiwa Aunty take kuka?"

Ummina gata nan ki tmbyta nima bansani ba"yace yana cigaba da driving dinsa.

Tun daga nan ba wanda ya kuma cewa komai har mukaje.

Dan tuni iman ma tayi bacci.

Jin munxo yasa na fita ban jira kowa bai nayi gaba abina.

Sosai na raya daren da kuka,tare da roqar allah ya ciremin son ya sadiq daga raina,dan nasan yanxu yayi min nisa,son maso wani kawai nake.

Washegari ma ko falo ban iya fitowa ba,sbd kaina da yakemin axababben ciwo.

Aunty ki shiryamu inji daddy zamuje park"Iman tace tana jijjigani.

Baby bazan iya ba kaina yana ciwo kinji?"

Daga kai tayi ta fita a dakin.

Nidai ina kwance kawai ihun shahid na jiyo.

Bansan lkcn da na tashi da gudu nayi kitchen inda ihun yake fitowa ba.

Inannalillahi!

Na fada na riqo shahid dayake ta tsalle yana riqe da hannu,da dukkan alamu qonewa yayi da ruwan zafi,sbd ga cattle nan da ruwa a yashe a qasa.

Shahid meya kawoka kitchen? dama kuna zuwa kitchen?"na fada a rude dan ganin yadda yake kuka,amma ba wata qonewa bace mai yawa.

Cak!na tsaya dan ganin daddynsu tsaye a bakin qofar kitchen din da sauran yaran.

Riqo hannun shahid din yayi tare da tmbyrsa garin yaya ya qone?

Wanka zanyi kuma ba ruwan zafi a heater din toilet dina shine nazo na diba anan shine na qone"na fada yana kuka.

Kallona yayi wanda bazan iya fassara ko wani irin kallo bane yaja yaransa sukai gaba.

Nima jan jiki nayi na koma daki ina tunanin to kallon na menene?nidai bani nace yaje ya dibi ruwan zafi ba,asalima bansan zaiyi wankan ba.

Sbd mugunta shine kikeso ki kashemin da ko?to na gaji da wannan abun naki bazan iya ba"daddynsu shahid ya fada yana figoni daga kwancen da nake.

Nima na gaji,wlh na gaji da wannan abin naka,ko anfada maka baiwa aka kawo maka?"nima na fada a fusace dan da gsk na gaji da wannan rayuwar rashin yancin.

Ni kike fadawa haka koh?sbd....

Aaaaa,karka fara,karka fara dabi'ar daba taka ba babanah,dukan mace?"

Da sauri na bude ido dan jin muryar ummi,domin na shirya kawai saukar mari nake jira.

Aunty anisa ce ta kamani tana sharen hawayen fuskata wadanda bansan ma suna zuba ba.

Inda ummi ta ja shi suka fita yana wani huci.

Khadija me kk yi masa haka har ya fusata yake qoqarin kai miki hannu"?aunty anisan ta fada.

Kukan da yazo min ya hanani mgn,inda suka rufu akaina sunata rarrashi na,dan gaba dayansu sukazo.

Kafin wani lkc zazzabi mai zafi ya rufeni.

Daqar naci wani abun mubina ta bani magani nasha na kwanta.

Sosai naji relief bayan na farka,inda suka shiga nan nan dani dan har lkcn suna gidan.

Bayan na idar da sallah aunty anisa ta zauna tana fuskanta ta,domin a lkcn mu kadai ne a dakin dan su mufida sun fita.

Khadija!

Naaam"na amsa da dasasshiyar muryata.

Inaso ki dauka cewa yanxu kina tare da fatima zaki ita fada min duk abinda na tmbyki,domin nima ina miki kallo matsayi daya danasu mufida"
Chapter 15 · 0% Book details