Sashe 8
Ni Bora Ce Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read
Hanan Sosai tayi Bacci har saida akayi isha'i , lokacin Hajiya Hajjo ta aiko kiranta akan tazo ta d'ora musu Abincin dare , Hanan ganin anyi sallar isha'i duk a tunaninta ai har angama abincin dare amman saiga aiken kiran ta nan yazo , mik'ewa tayi ta nufi wajen kiran Hajiya Hajjon , dan Nasma ta gaya mata duk lokacin da Hajiya Hajjo ta kiraka to kome kakeyi kayi k'ok'arin barinsa kaje , dan hakan shine samun sauk'in ka a wajenta , Hanan na isa gurin Hajiya Hajjo tasamu tana tsaye tana jiranta , rissinawa tayi tace " gani Hajiya , Hajiya Hajjo tace " ga garinan maza kije ki tankad'e ki d'ora mana tuwo , inkingama saikizo ki anshi kayan miya ki d'ora miya , da sauri Hanan ta anshi garin ta wuce cikin kithen d'in , tunda tashiga kitchen d'in tafara tunanin ta inah zata fara , gashi bataga ko giftawar Nasma ba bare ta taimaka mata , shuru tayi tana tunani taji alamar shigowar Mutum ta bayanta , waigowa tayi da sauri sukayi ido biyu da Nasma tana mata murmushi , zatayi magana Nasma tayi mata alamar tayi shuru , Nan take Nasma tafara had'a wuta suka d'ora tukunya sannan suka hau tankad'e gari , Nan ma Hanan bata b'oyewa Nasma komai ba gameda Abinda Daddynsu yakuma yimata d'azu , duk da a hankali sukeyin maganar gudun kar wani ya lek'o yaga Nasma a ciki , Nasma ta tausaya wa Hanan d'in sosai , fara tunanin yadda zasu samu mafita yadaina kusantar ta ma kwata kwata suka shiga yi , a haka har suka kammala tuwo suka d'ora miya , Hanan tace " gaskiya Aunty Nasma bazan kuma kwana a d'akina ba , inajin wajenki zantaho mudunga kwana tare saboda banason Abinda Daddyn ku keyi dani , Nasma tace " aa Aunty Hanan zuwanki d'akina akwai damuwa dosai , kicigaba da hak'uri har allah yasa mugama samo mafita , yanzu haka naji labarin wacce Wata Suwaiba da Daddyn mu yasaketa ya aureki tana nan bata mutu ba amman bata da lafiya , inaso naje gurinta kozan samo mana wani k'arin haske game da abinda zamusa gaba , Hanan tace " yauwa Allah yasa dai karta mutu ni wallahi tsoro ma nakeji sosai , Nasma tace " nace miki kisaki jiki kidaina nuna tsoro yin hakan zaisa yarage saka miki ido har yafara barinki fita daga haka zamu b'illo da shirinmu , cikin hikima Nasma tadunga tsarawa Hanan yadda zata saki jiki da Daddyn nasu har susamu sugama shirinsu , sosai Hankalin Hanan ya kwanta dan tana jin maganar Nasma sosai tunda ta girmeta , motsin tahowa sukaji alamar antaho cikin kitchen d'in da sauri Nasma ta b'oye bayan wasu shirgin kaya.......
[1/29, 16:19] +234 704 610 7812: *NI* *BORA*
_Ce_ 👩🏿🦳👩🏿🦳
*Na*
_Zee_ _MD_✍🏻
*Hamdala* *Writer's* *Association* 💪
https://www.facebook.com/111403834371046
✨✨ *{{* *H.W.A* *}}*✨✨
*Bisimillahir* *Rahamanir* *Rahim*
*Littafina* *Na* *Kud'ine* *Duk* *Meso* *Yamin* *Magana* *Ta* *Wannan* *Number* 07046107812 *Kuyi* *K'ok'arin* *Mallakar* *Naku* *Akan* 200 *Kacal* *kusiya* *Kukaranta* _Cikin_ _Aminci_ 🤝🏻🥰
*Last* 🆓 page. 10
Kuka babu irin wanda banyiba akan Rabuwa da Ammi , Koda aka kira Number Yayan Ammi aka gaya masa Kawu yazo zai tafi dani Cewa yayi " Abawa Kawun wayar , komai yace masa Amman Kawu yak'i Amincewa , haka Abban su Afrah yace da Ammi " tabari yatafi dani kawai inyadawo zasu san yadda za'ayi , haka muka rabu da Afrah tana kuka tamkar zata shid'e.....
Ammi kuwa kasa magana tayi har muka fice daga gidan nida Kawu , Tunda muka fita yaketa min fad'a akan nadameshi da Kukan Munafinci , harda cemin ai shine dole na duk inda akaje , cikinsu d'aya da Mahaifina dan haka bazai bari 'Yar Yayansa tarayu a wani guri daban ba , ahaka har muka isa tasha motar mu takama Hanyar Jos......
Tunda muka sauka garin Jos duk wani farin ciki bana cikinsa , Ammina kawai nake tunani da halin datake ciki yanzu , duk danasan Ammi tana cikin gidan da ko tari tayi sai antambaye ta lafiya , nice yanzu Abar tausayi.....
Muna isowa cikin gidan mu nafara karo da muryar Aunty Safara'u wato matar Kawu , fad'a takeyiwa 'Danta Mahmud wanda yaci sunan Baffa na wai yazubar mata da tsakin tuwo , tana ganin mu mun shigo ta dubeni shek'ek'e tana tab'e baki , Sallama Kawu yayi yashigo cikin gidan dayake yatsaya gaisawa da Abokinsa a waje , amsawa tayi tana fad'in " wato zuwa kayi ashe kadawo dasu saboda Jaraba irin taka , dubanta yayi yace " Nine Jarabar Kenan Safara'u ? nadawo gida ko sannu da zuwa bakiyimin ba nayi tafiyar kwana biyu sai kitareni da rashin mutunci kin kyauta , shigewa cikin d'akin yayi , nikuma na durk'usa ina gaida ta , Amsa min tayi ciki ciki sannan tace "Ina ita Uwar taki take ? Nace batare muka taho da itaba , sai Sannan naga tasaki fara'a tana yashar baki tamkar anyi mata albishir me dad'i , dubana tayi tace "kice ita bazata dawoba kenan? wannan karon haushi ne yakamani na mik'e tsaye nace " Nima bansaniba na wuce na nufi d'akin mu.......
Tunda nadawo gidan mu bank'ara samun kwanciyar hankali ba , kullum nice nake aiki acikin gidan tamkar zan mutu saboda wuya , ga Abincin da Aunty Safara'u kebani d'an kad'an ne , wani zubin ma k'anzo take bani saboda mugunta , duk nabi na rame na lalace , Tunda aka koma Sch banje ko sau d'aya ba sun hanani zuwa , Wai Inna tafi waye zai dunga yimata aikin cikin gidan ......
Tun ina damuwa inshiga d'aki insha Kuka harnazo nafara dangana , dan yanzu *NI* *BORA* _Ce_ acikin gidan nan , kowa ya kwaso shirginsa niza ace nayi masa wanki , gashi duk arrabani da k'awayena wanda nake dasu wai suna zugani ....
Kamal kuwa Saurayina wanda yakesona tun kafin mutafi Lagos Kawu ya dakatar dashi wai bashida sana'ar arzik'i..
A haka har nayi wata Hud'u da dawowa nasaba da wahalar cikin gidan Kawu , inada masoya sosai masu zuwa suce suna sona Amman kawu daga yaga babu na lasawa sai yace " Yayimin miji , indai kaga Kawu na rawar jiki da Saurayi inyazo gurina to tabbas zai moreshi ne , ana haka Har Allah yakawo Alhaji Nasir " wato Mahaifinki Nasma , lokacin dayazo sosai Kawu yayi Murna , Dan tashin farko Alhaji Nasir yasiyawa Kawu Abin Hawa wato Machine , Sannan yabashi jari metsoka , tuni Kawu yacewa Alhaji Nasir yabashi ni kawai yaturo a d'aura aure , Alhaji Nasir bai b'ata lokaci ba yaturo da kud'in Aurena , Sati Uku Aka saka tamkar angaji dani , lokacin da Alhaji Nasir yazo wajena nagansa bantab'a jin inason sa ba ko sau d'aya , duk zuwan dazai yi inna fito bana cemasa cikanka , sai dai shi yak'araci surutunsa yagama yatafi , Aunty Safara'u tamkar itace Amarya haka tashiga gyara d'akinta harda canza funutures , kud'in da Alhaji Nasir ke bawa Kawu haryaso yayi yawa , dan tuni aka gyara gidan mu tas harda saka k'aramin gate , Kawu har wani tumbi yayi saboda kud'i .....
Kullum ina cikin d'aki ina Kuka tamkar zanyi hauka , gashi banida wayar dazan nemi Ammi na in gaya mata damuwata , bani dawata k'awa wacce muke tare kowacce Kawu ya koreta , A haka Biki yak'araso Saura sati d'aya ..
Ranar ina Zaune naji Aunty Safara'u nacewa Kawu "wai kagayawa Uwar waccen yarinyar Bikin kuwa ? jinayi Kawu yana cewa " Banfad'a musu ba haryanzu , kinsan haushina sukeji dan naje nataho da ita , dana barta ina zansamu wannan Abin Arzik'in , wallahi sai dai su mutu dan Haushi , Shewa Aunty Safara'u tasaka tana fad'in " ai inajin ma Hajjin Bana in Allah yaci damu kaga ya biya mana , da sauri Kawu yace " Yaci dani dai , ke yanzu in anbiya miki Hajji a dalilin wa kenan? Cike da rashin kunya tace "au Abin harda gori kenan ? Kawu yace " ba gori ba ko goruba zakice nayi , tunda bikin nan yataho banga kina yiwa yarinyar nan gyara naku irin na mata ba , kuma na tabbata da 'Yarki ce saikin gyarata , a hakan kike jiran a biya miki aikin Hajjin yajita ba gyara , Safara'u ta tab'e baki tace "Kaima inka gyarata ai ba fad'uwa kayi ba ......
Haka akayi Bikina Nida Alhaji Nasir batare da Ammina tasani ba ita da 'Dan uwanta , dan Kawu yace bazai gaya musu ba tunda suma basu nemeni ba , Haka aka kawo ni gidan nan naku gashi yanzu nafara ganin wata rayuwar bacin waccd nabaro......