Sashe 10
Ni Bora Ce Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Hanan ko kallon wajen da Nasma take batayi ba ta mik'e tafita , d'akinta ta nufa prizer d'inta ta bud'e ta d'auko wata leda da Alhaji taga yashigo mata da ita yasaka a ciki , tana bud'ewa taga Balangu ne da biredi , sai kuma damammiyar fura da nono a roba , tuni ta d'auko furar tare da gutsiro biredi da kuma d'ebo nama takuma fita , tana zuwa wajen k'ofar Babban palor taga Nasma zata fito , tarar ta tayi sannan tace " Aunty Nasma inaso kisan yadda zaki d'aukomin yarinyar nan zan bata fura da biredi taci , Nasma ta zare ido tana fad'in " wai meyasa bakyajin magana Hanan wallahi wannan Abun dakike k'ok'arin yi Babbar kasadace , kuma inhar aka ganoki wallahi Daddy zaiyi miki hukunci me tsauri , Hanan tace " wallahi koda kasheni zaiyi sai nabata , bazan tab'a iya bacci ba ina ganin yarinya k'arama tanajin yunwa , inbanda mugunta taya za'ace adunga had'awa manya da yara abinci , kuma abincin ma bawanda mutum zai k'oshi ba , Nasma tace " Meye naki nadamuwa Hanan kawai kikoma d'akin ki kiyi musu addu'a Allah yakawo mafita , Hanan tuni ta shige cikin palor Nasma na ta k'wala mata kira amman tak'i dawowa , tana zuwa ciki tasamu yaran kowanne ya kwanta yayi lamo alamar dai basu k'oshiba , can tahango Yarinyar tana tsotar hannunta tana rufe da idonta alamar bacci zatayi , Hanan na zuwa ta lallab'a ta d'aukota ta fito da ita bayan d'akin sannan tafara bata Fura da biredi tana ansa , wani irin ci yarinyar takeyiwa biredin da fura tamkar tsohuwar mayya , kafin kace me harta tada furar da biredin , Naman tabata shima ta cinyeshi tas , Hanan tace kin k'oshi yanzu ? kai ta d'aga alamar ta k'oshi sannan Hanan tace " muje ki kwanta kinji Saikuma dasafe , cikin hausar ta ta gwaranci tace " zaki kuma kawomin wani da safe Ummata ? Hawaye Hanan taji yana zuba a kuncinta sannan tace " ae zankawo miki , maidat cikin 'Yan uwanta tayi sannan tafito taga Nasma a inda tabarta , dubanta Nasma tayi tace " kinbata taci kinji dad'i , inaso kisani karkisaba mata da abinda kikasan ba d'orewa zaiyiba , dakin barta a haka zata saba tamkar yadda muka saba kuma gashi har muka rayu ahaka , Hanan tace " Nasan koda bazai d'oreba nidai zancigaba da kulawa da ita , dan duk cikin yaran ai ita tafisu k'ank'anta dole a tausaya mata....
[1/29, 16:19] +234 704 610 7812: *NI* *BORA*
_Ce_ 👩🏿🦳👩🏿🦳
✍🏻 *MD*.
13.
Bayan kwana biyu tuni Hanan tasaba da aikin wahalar gidan Alhaji Nasir , Sosai Hanan take kula da wannan k'aramar yarinyar me suna Aisha , koda yaushe sai sungama cin Abinci a had'e da sauran 'Yan uwanta sun kwanta sannan Hanan zata lallab'o tazo takuma bata , tuni Aysha tasaba da Hanan wacce take kira da Umma , duk wannan Abin da Hanan keyi sauran matan gidan bawacce tasani sai Nasma kad'ai , Hanan tana zaune a cikin d'akinta tana tsefe kanta saiga Nasma tashigo cikin d'akin d'auke da Sallama , amsa Hanan tayi Nasma tasamu guri ta zauna , duban Hanan tayi tace " yau tsifar kai kikeyi kenan ? Hanan tace "ae wallahi kan nawa yayi datti dayawa shiyasa na tsefeshi kuma gashi bansan waye zaiyi min kitsoba , Nasma tace " wannan ma wata dama ce daza musamu dan muje gurin Matar da Daddy yasaka , Hanan ta dubi Nasma cike da son jin k'arin bayani , Nasma tace "kin manta nagaya miki cewa wacce Daddy ya saketa sannan ya aureki tana nan yanzu haka ita bata mutu ba , Hanan da sauri tace " ea na tuna wacce kikace sunanta Suwaiba ko ? Nasma tace ea "ita nake nufi yanzu kinsan yadda za'ayi ? Hanan ta girgiza kanta alamar A'a . Nasma tace " yanzu tashi zakiyi kije d'akin Hajiya Hajjo tunda Daddy baya gari kice mata zakije kitso , Nasan bazata hanakiba saboda tanason taga ana fita in Daddy bay nan saboda tasamu shedar ce masa mace nafita yawo in baya nan , kinsan a kullum ajin haushin auren da Daddy yakeyi take , intaji yayi saki har murna take sosai ranar saboda jin dad'i , Hanan tace " ni wallahi mamaki ma take bani akan wannan kishin nata da takeyi , yanzu inbanda Abinta meye abin kishi a wajen Alhaji Nasir ? Mutumin dayake mu'amalar aure da mace ta baya sannan cikin gidan sa bawani kwanciyar hankali , irin wannan rayuwar ta gidan nan yanzu har wata abar so ce , Nasma tayi d'an Murmushi dan tanajin ciwon halin Mahaifin nata dayakeyi , sai lokacin Hanan ta tuna da cewa Alhaji Nasir fa Mahaifin Nasma ne kuma duk lalacewar sa dole zata kirasa da sunan Uba , cike da jin Nauyin Nasman tace " kiyi hak'uri Aunty Nasma dan Allah akan abinda na fad'a game da Mahaifinki , Nasma tayi Murmushi sannan tadafa kafad'ar Hanan tace " babu komai ai halinsa ne kuma nima na tsani halin nasa , yanzu dai tashi kije kitambayi Hajiya Hajjo d'in sai kisameni a k'ofar gate ina jiranki .......
Koda Hanan ta tambayi Hajiya Hajjo bata samu wata matsala ba ta amince mata , Hanan ta shirya tasaka Hijab d'in ta tafita , tunda aka kawota gidan Alhaji Nasir yau tafara zuwa k'ofar gate d'in gidan , tana fita ta hangi Nasma a tsaye sanye da Hijab itama , tana k'arasawa suka fita titi suka hau Napep suka nufi gidan su Suwaiba , dayake Nasma tasan gidan ta sanadiyyar Zuwan datayi lokacin da Baban Suwaibar yarasu , suna tafe Hanan tacewa Nasma "yanzu yazamuyi da kitso kuma ? kar mu koma gida Hajiya Hajjo taga banyi kitsoba fa , Nasma tace " in munfito daga gidan sai muje gidansu wata k'awata ta iya kitso sosai sai tayi miki , Suna zuwa suka sauka Nasma tabiya kud'in sannan suka shiga lungun gidan su Suwaiba.....
Zunnur tunda yaji labarin Hanan ta koma Jos hankalinsa duk yabi yatashi, Allah Allah yake suyi exams. Su samu hutu yanufi Jos dan ganin halin da Hanan ke ciki , Haidar so dayawa zai saka Zunnur a gaba yana tambayar sa ko lafiya ganin Yadda ya canza gaba d'aya , amman kwata kwata yak'i fad'a masa sai dai yace ba komai , a haka har suka fara Exams. Suka kammala , koda suka kammala Zunnur yayi shirin zuwa garin Jos batare da yafad'awa Haidar ba , kawai yace zaije gurin wani Abokinsa amman kwana biyu zaiyi yadawo , a haka sukayi sallama ya nufi Hanyar Jos......
Lokacin da Zunnur ya iso Jos dak'yar yagane Unguwar su Hanan , yana zuwa gaya gidan duk ya canza tamkar ba gidan ba , tsayawa yayi a k'ofar gidan yana neman yaron da zai aika cikin gidan , yana tsaye saiga wani yaro yazo wucewa . da sauri Zunnur ya tsayar dashi sannan yace Ya shiga cikin gidan yace ana kiran Hanan inji Yayanta , yaron yashiga cikin gidan ya sanar da sak'on Zunnur , lokacin Kawu Idi yana zaune yana cin Abinci , duban yaron yayi yace " wacce Hanan kuma kake nema ? ai Hanan d'ayace a gidan nan kuma anyi mata aure , Yaro yanajin haka ya fito waje dan sanar da Zunnur , Kawu ya dubi Safara'u yace " kiji wani tsohon zance wai ana kiran Hanan , ai yanzu Hanan sai dai mufara maganar zuwan 'Danta , Safara'u ta tab'e baki sannan tace " to katashi ka lek'a kagani ko wani d'an uwan naku ne tunda naji ance Yayanta , Kawu tuni ya mik'e dan fita yaga waye ke neman Hanan d'in ......
Lokacin da Yaron da Zunnur ya aika yadawo masa da zancen wai ance ta dad'e dayin aure sai da yaji k'irjinsa ya buga , sake tambayar Yaron yayi yace " Hanan kace kuwa ? saiga Kawu Idi ya fito yana duban Zunnur d'in sannan yace " Sannu da zuwa d'an samari amman bangane daga inah ba , Zunnur ya gaida Kawu cikin girmamawa , shima amsawa yayi cike da sakin fuska , Zunnur yace " ni d'an gidan Yayan Ammin Hanan ne daga Lagos , nazo ne inga lafiyar ta shine abinda yakawoni , Kawu najin hakan ya canza Fuska sannan yace " au to dan na d'aukota shine aka ce muku bata cikin k'oshin lafiya ? To kasani nafi kowa iko da Hanan shiyasa naje na d'aukota kuma na Aurar da , wata irin zabura Zunnur yayi yana duban Kawun , cikin wata murya yace " wanne irin aure kuma ? Hanan d'in nawa take da zaayi mata Aure fisabililkahi , Kawu yadubi Zunnur yace " sokake saita janyo abin kunya za'ayi mata kenan , to kasani banshirya d'aukar rainon shege ba a gidana , inaso inka koma ka shedawa Uwar tata cewa na aurar da Hanan , kuma dama ai nine ma d'aurin aurenta ba wani ba , Zunnur wanda yakejin zuciyar sa nawani irin tafasa saboda Takaici , jiyake tamkar ya shak'o wuyan Kawun Hanan d'in ya haushi da duka saboda abinda yayi , taya zai aurar da Hanan alhalin Mahaifiyarta ma bata saniba , Yanzu yazaiyi da soyayyar Hanan wacce a kullum takeyi masa Barazana tamkar zata haukatashi , tabbas yasan wannan auren ba inda zaije mutuk'ar yana Numfashi , dan bazai tab'a barin Hanan tayi rayuwar Aure da wani ba indai ba mutuwa yayi ba , kallon Kawun yayi yace " inaso arakani gidan Hanan d'in dan inganta , Kawu Idi yadubi Zunnur yace " kasan bazan tab'a d'aukar k'afa na raka ka gidan Hanan ba , taya ma zakaje musu gida kana k'ato dakai ko sokake ka kashe mata auren ne ? Zunnur yace "aa taya zan kashe mata aure daga zuwa ganinta kawai , Kawu Idi k'eme me yak'i yace baza a raka Zunnur gidan Hanan ba , dole haka Zunnur ya hak'ura yabar k'ofar gidan , cikin gari yashiga dan yasamu Abinci yaci yasan Abinda zaiyi ......