← Book details Ni Bora Ce Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 17 OF 23

Sashe 17

Ni Bora Ce Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Alhaji Nasir tunda suka shigo lungu shida Garba yake nazari , tabbas indai wannan lungun ne ai yasan akwai yaransa dayake nema a cikinsa , wayar sa yazaro ya kira wani yaransa har ta katse bai d'agaba , sake kira yayi harta kusa katsewa sannan aka d'aga , cikin muryar Bacci yaron Alhaji Nasir yafara magana " sai megida wanne me k'aran kwanan ne yatab'a mana kai ? Alhaji Nasir yace" inada
Wasu tsuntsaye ne da suka shigo cakwalinku , da sauri ya mik'e daga kwancen dayake yace " kace akwai Nama tare da Zuma bari intashi sauran mufito , Cikin k'ank'anin lokaci duk suka tashi tare da fitowa wajen Alhaji Nasir , su Nasma k'arajin motsi sukayi dan haka suka kuma tsorata , Nasma tacewa Hanan bari naje nagano mana ko dai wani Abin ne , Hanan ta rik'e hannun Nasma tana girgiza mata kai alamun kartaje , Nasma tace " badad'ewa zanyiba fa a hankali zan lek'a naga ko meye yanzu zandawo , a hankali Hanan ta saki Hannunta ta juya tafara tafiya a hankali......

Zunnur mafarkin dayayi shine yayi bala'in tsoratashi da sauri ya farka , tunani ya shiga yi yadda yaga Hanan tana kuka wasu maza na binta tana gudu , wai sai kiran sunan sa takeyi da sunan Ammin ta , tashi yayi yayo arwala tare dayin sallah raka'a biyu sannan yashiga yiwa Hanan addu'ar kariya a duk inda take , Cikin zuciyar sa yana fad'in duk inda kike Hanan gobe sainayi tozali dake , dan tun yanzu zanfita zuwa tasha nasan duk inda akayi sallar asuba dole motoci zasu fara tafiya .....

Nasma na lek'awa taga Daddyn ta tare da wad'an nan 'Yan fashin yana fad'a musu yadda zasu nemo su , Nan yace sufito su zauna cikin lungun da gefen lungu tabbas baza su wuce gurinba , Nan suka zazzauna tare da busa sigari suna cewa " ka kwantar da hankalinka indai suna cikin lungun nan to tabbas kamar sunzo hannunka , dan wancan gidan na Maman Iyabo innan suka shiga da asuba zata korosu da bala'i , Nan Alhaji yace " zaije gida duk abinda ake ciki suyi masa waya , sannan lallai karsu bari yaran nan su tsere......

Nasma da gudu tadawo wajen Hanan tana fad'in " kinga irinta ko Hanan , sai da nace miki tund'azu mubar wannan gidan ni hankalina bai kwanta dashi ba , gashinan Daddy yazo ashe yasan masu gidan nan , wata irin zabura Hanan tayi tana duban Nasma cike da tsoro sannan tace " shikenan kashin mu ya bushe dama bamu fito munsha wannan wahalar ba gashi yanzu abinda muke gudu shine dai zai afku , Nasma tayi jugum dan ita kanta yanzu batasan mafitar suba , ta inah zasu fita daga wannan gidan ? sannan insunce sai gari ya waye nan ma basu tsiraba , tabbas suna cikin tashin hankali , Hanan tuni tafara shashshekar kuka tare da cewa " kiyi magana Nasma kece me nemo mana mafita , Nasma tace dole muzama jarume a wannan lokacin inba haka ba bazamu tsira da ranmu ba tunda har Daddy yasaka a nemo mu har haka , yanzu dole kiyi d'amara dan gudu ne zamuyi sa sosai in anjima kad'an , kinsan dole wad'an nan zasuyi bacci tunda a bige suke to a wannan lokacin zamu samu mufice daga wannan gidan.......

Tun kiran farko Zunnur ya fito ya nufi tasha , Allah yataimakesa yasamu abin hawa , yana zuwa yasamu wata motar me gudu wacce zataje Jos , haka ya hau me motar yace mutum biyu zasu jira sannan sutafi , Nan Zunnur yace " zai biya kud'in Mutum biyun kawai su shige sutafi , take yabiya kud'in Direba ya d'au hanyar Jos.....

Ana kiran sallah Nasma ta zunguri Hanan wacce take gyangyad'in wahala , firgigit ta mik'e tana duban Nasma , a hankali Nasma tace mata " ki shirya Hanan lokacin fitarmu yayi , a hankali suka fito daga inda suka b'uya hanyar waje sukayo a hankali suna sand'a , dayake k'ofar gidan a bud'e take shiyasa basu sha wuya ba wajen zura k'afafunsu suka fita , suna fita sukaga Yaran da Alhaji yasa su kawosu dukansu idonsu biyu , sai dai da alama basu da wani kuzari saboda a buge suke da k'waya , suna ganin su Nasma sunfito aka fara kallon kallo , d'aya daga ciki yace " daman kuna cikin gidan mu kuka wahalar damu haka ? su Nasma suka tattare zani suka ranta ana kare , suma Yaran Alhaji tuni suka mik'e tare da rufa musu baya....

Gudu suke baji ba gani tamkar su tuntsira , suma kuma binsu suke iya k'arfinsu , dayake titi na da nisa da wajen ga duwatsuna shiyasa su Hanan suka fara gajiya , dan tuni tafama ciwonta da ta d'aure sai jini ne yake zuba , Nasma itama a lokacin tayi tuntub'e da wani dutse aikuwa ta fad'i tim a k'asa , take goshinta ya fashe jini ya wanke mata fuska , da sauri Hanan taje tana k'ok'arin tashinta , lokacin Yaran Alhaji tuni sunkusa k'arasowa , a hankali Nasma ta yunk'ura ta mik'e tare da taimakon Hanan suka ci gaba da gudun su , suna fara hango titi suka ga Yaran Alhaji sai k'ara k'aimi sukeyi suka masu , suma k'ara gudu sukayi har suka iso titi , da gudu suka ga wata motar ta taho hannu Nasma ta shiga d'agawa alamar ta tsaya , sunayi suna waiwayen Yaran Alhaji wanda shuka kusa k'arasowa , aikuwa Direban motar da kamar bazai tsayaba sai kuma wata zuciyar tace ka tsaya ko cetonsu zakayi , da sauri yataka burki su Hanan suka tafi da gudu suma Yaran Alhaji suka rufa musu baya , suna zuwa suka ga anbud'e musu k'ofah da gudu suk shige suna rufowa Direban yatasheta da gudu dan yagane biyosu akayi.......
Yaran Alhaji cizon yatsun su sukayi tare da zubewa wajen suna zage zage ,
Hanan tunda ta fad'a cikin motar tajita ta fad'a jikin wani mutum , samun kanta tayi da kuma kwanciya tana maida numfashi , shima wanda tafad'a jikinsa jitayi dai dai saitin zuciyar sa yana bugawa da sauri da sauri........
[1/29, 16:19] +234 704 610 7812: *NI* *BORA*
_Ce_ 👩🏿‍🦳👩🏿‍🦳

*Zee* *MD* ✍🏻

23.

Bayan wasu watanni Matan nan biyu kowacce tasamu ciki a cikinsu , Alhaji kullum cikin yi musu rashin mutunci yake , ina ganin hakan nagama yadda Alhaji bason haihuwa yakeba , a dole naje asibiti sukamin allura na tsaida haihuwa , dan tuni Alhaji yasaki wad'annan matan yarage dagani sai Hajjo , Kuma har wannan lokacin Alhaji baya kulani , gashi yahanani naje naga iyayena , duk nabi nadamu kaina dan haka nafara rama , Nasma na da shekara d'aya da rabi na Yayeta , lokacin Mahaifina yazo garin jos dan ganina tunda ni nak'i zuwa a cewar su , koda yazo sosai Alhaji Nasir yayi masa tarba ta musamman , a nan ne muka shirya dan Mahaifina kwana biyu yayi , randa zai tafi shatara ta arzik'i Alhaji Nasir yayi masa sannan yasa Direba ya maida shi , sosai naji dad'in yadda Alhaji Nasir ya girmama Mahaifina har hawaye nayi lokacin dazai tafi , Bayan tafiyar Babana da kwana biyu Alhaji ya shigo d'akina , Nan yana nuna yana buk'atar mu kwanta amman ta baya yakeso , Nan ma na bijire masa Amman da k'arfi da yaji sai da yayi hakan dani , sosai nayi kuka tamkar raina zai fita gawani rad'ad'i danakeji ta k'asana , Haka nasha kuka na lokocin dayake da Rana ne Nasma tadunga min gwaranci tana gogemin hawaye ....

Tunda ganan nadaina kula Alhaji Nasir nasamu kaina da mugun tsanar sa , ana haka aka kawo masa yaran sa wad'an da matansa suka haifa masa , yana ansar su yabawa Hajjo dan itace yake shiri da ita sosai , Ba'ad'auki lokaci me tsayiba saiga shi Alhaji Nasir yakuma yin aure wasu matan biyu , tunda ganan nashiga tsoron lamarin Alhaji Nasir sosai ......
Wata rana da daddare natashi ba wanda yasani na nufi b'angaren Alhaji Nasir , ina zuwa nasamu a bud'e sad'af sad'af nadunga tafiya har zuwa cikin bedroom d'insa , Anan naga abin Al'ajabi dan Alhaji Nasir nagani zindir haihuwar Uwar sa yana shan wani Abu a cikin k'warya , lab'ewa nayi nashiga lek'owa ina ganin Abinda yakeyi kawai sai gani nayi wani Saurayi ya fito daga toilet d'in d'akin , Shima tsira yake tamkar yadda Alhaji Nasir yake , yana fitowa suka fara aikata Luwad'i shida saurayin , sai wata k'ara suke suna gurnani tamkar wasu zakuna kafin sukawo , ina ganin haka najiyo nabar d'akin ina tafe inah kuka , tundagan nafara neman hanyar barin gidan Alhaji Nasir , kwata kwata nadaina jin dad'in komai a gidan , Komai ya siyo mana bana amfani dashi saboda natsani kud'insa dan nagama ganewa idona tsafi yakeyi , tuni nashiga nadama ta aurensa tare dayin dana sani , gashi haryau bansan asalin Alhaji Nasir ba , wad'anda yasamu ya turosu gidan mu lokacin aurena suma hayarsu yayi , danayi bincike akansa aka tabbatar min bad'an garin Jos bane kawai zuwa yayi cirani ......
Chapter 17 · 0% Book details