← Book details Ni Bora Ce Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 4 OF 23

Sashe 4

Ni Bora Ce Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

*Na*
_Zee_ _MD_✍🏻

*Hamdala* *Writer's* *Association* 💪
https://www.facebook.com/111403834371046

✨✨ *{{* *H.W.A* *}}*✨✨

*Bisimillahir* *Rahamanir* *Rahim*

*Littafina* *Na* *Kud'ine* *Duk* *Meso* *Yamin* *Magana* *ta* *Wannan* *Number* 07046107812 *Kuyi* *k'ok'arin* *Mallakar* *Naku* *Kukaranta* _Cikin_ _Aminci_ *Saina jiku* *Masoyana* 🤝🏻🥰😍

🆓 page. 5

A haka har Safara'u ta haihu d'anta Namiji , Ranar suna aka saka masa sunan Baffa na wato Mahmud , Bayan wasu watannin Ammi na taga zama haka bazai mata ba , fara saro kayan miya tana saidawa , Koda Safara'u taga Ammi nasamun Alkairi da Kayan miya sai tashiga tafita tafara sai dawa itama , Ammi tanaji tana gani tadaina saida kayan miya , sai tasamu kud'in tafara sana'ar soya k'osai a k'ofar gida , Alhmd nan ma Allah yasa mata Albarka tana cikini Sosai , da wannan sana'ar Ammi taci gaba da rik'e mu , lokacin Kawu tuni yadaina biyamin kud'in sch , Ammi itace komai nawa har na fara girma ....
Zawarawa dayawa sun fito neman auran Ammi amman tak'i Saboda ni , lokacin Safara'u tana da yara biyar , dan tunda tafara haihuwa take kwanika , kullum cikin yiwa Ammi hassada take gashi ta tsaneni Sosai tamkar takasheni , kuma har lokacin Kawu Idi yak'i ya kammala gidansa bare sukoma subar mana namu , Ina aji k'arshe a primary saiga Yayan Ammi yazo daga Lagos , shida Matar sa da Yaransa guda uku , Ammi tayi murna Sosai daganin d'an uwan nata , Sunyi hirar Yaushe gamo sannan suka shiga hirar Rayuwa , Inadawo wa daga sch naga bak'in damukayi wanda Ammi tadad'e tana bani labarinsu , aikuwa naita murnar ganin 'Yan uwa , Babban 'Dan Yayan Ammi ya girmeni sosai , sai Mai bimasa shima yad'an girmeni sai kuma K'anwarsu wacce zamuyi sa'anni da ita , Sunan Babban Usman suke ce masa Zunnur , saboda sunan Baban su Ammi ne , me binsa kuwa sunan sa Haidar , sai k'aramar su Afra , Maman su tana da kirki sosai , tasaki jiki da Ammi sai hira suke tamkar daman sun san juna , nima nida Afrah tuni muka saba dan kusan kanmu d'aya da ita , Zunnur bashi da yawan Magana kaganinsa kaga miskili , shikuwa Haidar yana da sakin fuska sosai , kwanan su Biyu sukace zasu tafi saboda sch . Ammi tayi tayi suk'ara kwana Amman yace tabari in sunsamu hutu zaikawo su suyi anan , Yayan Ammi yayi mata fad'an tayi Aure zaman haka babu dad'i , kokuma takoma gabansa can lagos d'in ta zauna , Ammi tace zatayi Shawara akan hakan duk abinda ta yanke zata gaya masa , lokacin da zasu tafi sosai nasha Kuka sai nabisu nima , Afrah itama kukan take tana rok'on Ataimaka ataho dani , da k'yar Maman su ta lallab'amu akan zasu dawo nan badadad'ewa ba , Yayan Ammi yabata dubu talatin yace tak'ara ajarin nata , sannan yabawa Kawu Idi dubu goma , sai kuma yabawa Safara 'u dubu biyar , sunyi godiya Kawu Idi yabasu tsarabar kayan Gwari , lokacin da muka rakosu waje Na kalli Zunnur nace " Ya Zunnur sai wata rana tunda kai murna kake zaku tafi , daman tunda kuka zo kake jin Haushi to yau saika saki ranka , kowa a wajen sai dayayi dariya , shikuma murmushi yayi bai ce komai ba har suka tafi....

Bayan wasu shekaru.
Lokacin Na zama 'Yan mata ina Ss 2 a secondry sch , duk wata hailtta ta jikina ta bayyana , nakasan ce Doguwa Fara me d'auke da doguwar fuska , ina da Hanci har baka ga bakina k'arami dashi , idanuwana dara dara dasu cikinsu fari fat sai k'wayar idon bak'a k'irin , ina da siririyar wushirya a tsakiyar hak'ora na , sannan ina da Dimple a gefen kumatuna , Bani da jiki amman kuma ina da k'ugu sosai , Banda cikar K'irji dai dai suke abina , tunda nazama Budurwa Samari suka fara kawomin hari , kuma har lokacin Ammi na tana suyar k'osai a k'ofar gida , Tunda lokacin Kawu Idi yasakoni gaba saboda madu zuwa ta wajen sa, Wata ranar Friday na dawo daga Sch ina tafiya naji ana min magana , dak'yar na tsaya saboda cikamin idanuwan da yayi mutumin , mungai sa yace min dan Allah inbashi kwatancen gidan mu , yanaso yazo dan tsayuwa a hanya ba mutunci bane , Nan na daure nagaya masa kwatancen gidan mu , ya fad'amin sunan sa Kamal nan muka rabu akan zaizo gida.....
Bayan kwana biyu ina zaune nida Ammi muna hirar tafiyar mu Lagos da zamuyi inna samu hutu , kawai sai ga yaro yashigo wai ana sallama da Hanan a waje , Nan nacewa yaron yace Bananan , Ammi tace ace ina nan , turo baki nayi ina fad'in "Nifah Ammi bazanje ko inah ba , kallo na tayi sannan tace " yanzu Hanan inbaki fita ba taya zaki samu mijim da zakiyi aure ? kinsan dai nafad'a miki cewa iya secondry sch zaki gama in aurar dake Hanan , yakamata kifara kula samari ko zaki samu wanda zakuyi daidai , kalaman Ammi sun shigeni sosai dan haka na mik'e nasaka hijan d'ina na fice , Nasan Ammi bata da k'arfin dazata biyamin kud'i nayi karatu sosai , dan haka nima na amince da zancenta ......
Ina fitowa naga Kamal a tsaye , yana ganina yafara sakarmin Murmushi yana cewa " Gimbiya sarauniya gaskiya nazama sarki acikin masoya tunda har aka fito wajena , murmushi nayi sannan na gaidashi cike dajin kunya , Nan ya amsa yafara gabatarmin da kansa , Sosai nasaki jiki da Kamal , kodan yana da Abin dariya ne oho , haka mukaita hira haryamin sallama yatafi , tunda ganan Soyayya ta k'ullu tsakanin mu nidashi , har muka samu hutun Sch muka tafi Lagos da Ammi .....

Zuwana Lagos shine yafara canzamin Rayuwata tafarko , Muna zuwa gidan Yayan Ammi , Sosai muka samu tarba ta musamman , karkuga murnar da Afrah tayi taganina , nima nayi murna sosai da ganinta , tazama Babba sosai dan harta fini girman jiki , lokacin da mukaje su Haidar da Zunnur suna Sch amman suna shirin dawowa gida , dukansu suna karatu a B.U.K a can kano , dagani sai Afrah kullum sai munfita ganin gari , watara rana munje wani Shopping mukayi karo da wani Saurayi , duk abinda muka siya saida ya biyamana kud'in , bayan munfito ya biyomu ya gabayar mana da kansa sannan ya nuna yana sona , Afrah tabasa Addrees d'in gidan su muka wuce muka tafi.....
Tunda ganan Muktar yafara zuwa guna , tun ina sharesa Afrah tasa ni gaba saida nafara kulasa , Muktar irin samari nan wayayyu , wani lokacin in muna hira sai yanemi tab'amin jikina , sai da nanuna b'acin raina Sosai sannan muka dai daita , Ranar dasu Zunnur zadu dawo tun safe muka gyara musu d'akinsu , sannan muka shiga kitchen muka fara shirya musu Abinci lafiyayyau , kafin k'arfe biyu mun kammala komai , dayake a jirgi suka taho lokacin Abbansu har yatafi tahowa dasu , wanka nashiga dana fito na shirya cikin wata doguwar riga da mukaje Shopping Abbansu Afrah yasiyamin ita , nikaina nasan nayi mugun yin kyau Sosai , da haka nafito palor ina k'walawa Afrah kira , hanyar k'ofa nataho zan bud'e shikuma dai dai lokacin zai shigo , aikuwa mukayi karo dashi har wayar hannunsa ta fad'i muka sunkuya atare dan d'aukar ta , Idanuwan mu ne suka had'u waje guda take kowannen mu zuciyar sa ta buga.......

*littafina* *Na* *Kud'ine* *Duk* *Meso* *Yamin* *Magana* *ta* *Wannan* *Layin* 07046107812 *Kuyi* *K'ok'arin* *Mallakar* *Naku* _Karkubari_ _Abaku_ _Labari_ _kusiya_ _kukaranta_ _Cikin_ _Aminci_ 🥰🤝🏻
.

*'Yar* *Mutan* *Kanawa* _Ce_ 🌹😘
[1/29, 16:19] +234 704 610 7812: *NI* *BORA*
_Ce_ 👩🏿‍🦳👩🏿‍🦳

*Na*
_Zee_ _MD_ ✍🏻

*Hamdala* *Writer's* *Association* 💪
https://www.facebook.com/111403834371046

✨✨ *{{* *H.W.A* *}}*✨✨

*Bisimillahir* *Rahamanir* *Rahim*

*Littafina* *Na* *Kud'ine* *Duk* *Meso* *Yamin* *Magana* *Ta* *Wannan* *Number* 07046107812 *Kuyi* *K'ok'arin* *Mallakar* *Naku* *Akan* *Naira* 200 *Kacal* *kukaranta* _Cikin_ _Aminci_ 🤝🏻🥰

🆓 page. 7

Ina zuwa naga Afrah sai hirarsu suke hankali kwance , ganina datayi a firgice yasa ta zabura itama ta mik'e , cike da tsoro tace min " lafiya kuwa Hanan naganki hakan ? Muryata har sark'ewa take nace mata " Ya Zunnur ne yazo , tuni Afrah ta firgice tana cewa Anas " Maza kabar wajen nan wallahi inyazo yaganmu tare zai maka rashin mutunci , kafin Anas yayi wani yunk'uri saijin shak'a yayi ta wuya , kafin kace me tuni yaji saukar Naushi , Kafin Anas yadawo Daidai yakuma jin wani Naushin , nida Afrah duk ilahirin jikinmu Rawa yake , tuni munfara Hawaye saboda tsoro , da k'yar mutane suka kwaci Anas a hannun Zunnur , yadda kasan wani mayunwacin zaki haka jijiyoyin jikinsa suka tashi , kallon mu yayi kawai ya nufi wajen da yayi parking d'in mota , sai abakin mutanen dasuka k'waci Anas naji suna cewa " wanda yafara rik'ewa yana dukansa da k'yar yasamu ya turesa ya gudu Muktar kenan , jikin mu a sanyaye muka nufi hanyar fita daga cikin Garden d'in , wani wawan burki da'aka ja a gabanmu take muka had'e jikinmu waje d'aya muna karkarwa , bamu gama dawowa dai dai ba mukaji an finciki Hannuwan mu an bud'e motar ansaka mu , muna bud'e ido mukayi ido biyu da Zunnur tamkar mayun wacin zaki , shiga motar yayi ya figeta a miliyan yabar wajen......
Chapter 4 · 0% Book details