← Book details Ni Bora Ce Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 22 OF 23

Sashe 22

Ni Bora Ce Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Tun daga lokacin 'Yan gidan su Safara'u suka fahimci Alhaji Nasir matsafine , tunda ga ranar suka fara taka tsantsan suma dan sun tsorata sosai , Safara'u kuwa hauka take tuburan tana zabure zabure , tuni suka fara fafutukar nema mata magani.......

Alhaji Basir tuni suka gama magana akan zuwa Jos ansowa Hanan takardarta ,dan baza tai ta zama da igiyar aure akanta ba , Kawu yace " kayi zamanka kawai basai kajeba tunda nine nahad'a to kuwa nizan rabashi , Hakan kuwa akayi Kawu ya shirya yayi musu sallama ya koma...

Hanan tuni jikinta yayi sauk'i sosai , yanzu ma Alhaji Bashir yayi magana da Zunnur akan asamar mata makaranta tafara zuwa , Zunnur tuni ya sanar da Umman sa yanason Hanan , sosai taji dad'in Abin amman tace yabari komai ya lafa sai ayi magana , Abban su Zunnur dagewa yayi akan Hanan ta dawo gidansa amman Alhaji Murtala yak'i , dole haka yabar ta taci gaba da zama a gidan , Nasma kuwa tuni dangin Hajiya Asma'u suka d'auketa Kano zataga 'Yan uwa , Haidar sosai yaji dad'in zuwan Nasma kano , dan tuni suka koma sch sunfara shirye shiryen kammala Degree d'insu ,

Kawu Idi so biyu yana zuwa gidan Alhaji Nasir amman a kulle , ko megadi baiganiba cikin ransa yace " kowa ya gudu kenan , Anan yasamu labari ba kowa a gidan shima megidan kwana biyu ba'a ganin gilmawar sa , dawowa gida yayi anan ya had'u da k'anin Safara 'u yabashi labarin Abinda yake faruwa da Safara'u , ko kad'an Kawu Idi bai tausaya mata ba saima Allah yak'ara dayace , ya kad'a kansa yayi gida dan shiyanzu tsoron duniyar ma yakejin , yanzu yagama magana da wata bazawara zasuyi aure sati me zuwa .....

Hanan tafara zuwa sch ga wayar ta me kyau da Hajiya Asma'u tasiya musu ita da Nasma ,

Suna waya da Zunnur sosai kusan kullum suna manne a waya , tuni Alhaji Bashir sunje kotu an ansawa Hanan takardar sakinta wajen Alk'ali , dan kwata kwata annemi Alhaji Nasir anrasa .....

Nasma tadawo Lagos wajen Hajiya Asma'u da zama , karatun ta taci gaba dayi gefe guda kuma suna tare da Haidar suna zabga soyayyar su.......

*Kuyi hakuri wlh yau fita nayi*🙏🏻🙏🏻
[1/29, 16:19] +234 704 610 7812: *NI* *BORA*
_Ce_ 👩🏿‍🦳👩🏿‍🦳

*Zee* *MD* ✍🏻

28.

*THE* *END*
*THE* *END*
*THE* *END*

Ranar suna yarinya taci sunan Ammi wato Hadiza suke kiranta itama da Ammi , sosai Ammi taji dad'in karar da akayi mata , Su Hanan ma sosai suka tayata farin ciki , Ana cikin shagalin suna saiga Safara'u tazo , Da Hanan tafarayin karo a tsakar gida ita da su Nasma , sunkuyar da kai tayi k'asa kamar munafuka tana tafiya a hankali , Hanan kuwa tayi murmushi sannan tace " Aunty Safara'u sannu da zuwa ashe kinanan ? Safara'u ta yashe baki tana fad'in "la Hanan kune agari haka sannunku da zuwa , Ina Ammin ki ? Hanan tace tana cikin wannan d'akin , da sauri Safara'u tashige cikin d'akin ta addu'ar Allah yasa Ammi tasa baki Kawu Idi ya maidata......
Afrah tadubi Hanan tace " Sister wannan ai kamar matar Kawu ta da ? Hanan tayi murmushi sannan tace "ea itace kinga yadda takoma ko ? ta dubi Nasma tace itama fa saida ta auri Daddynki kinganta nan duk ta lalace tamkar me Hiv , Nasma tace " ai tunda naji kince aunty Safara'u naganeta , Allah ya kyauta daman ai wanda ya hau motar kwad'ayi zai sauka a tashar wulak'anci .......

Safara'u koda tashiga cikin d'akin da Ammi take kasa ganeta Ammi tayi , da k'yar tagane ta suka gaisa Ammi tashiga mamkin yadda Safara'un takoma , duk da Kawu yabasu labarin Abinda tayi kaf amman saida ta tausaya mata , nan Safara'u tafashe da kuka tana rok'on Ammi gafara duk abinda tayi mata , Ammi tausayin tane yakamata tace " Allah yayafe mana baki d'aya , Sa'ade ce tashigo cikin d'akin Safara'u ta kalleta , ko ba'afad'a mata ba tasan wannan itace matar da Kawu Idi ya aura , dan yaranta insunje suna gayamata yadda take yi musu komai tamkar uwar data haifesu , Safara'u tagaida Sa'ade tare dayi mata barka , Sa'ade bata gane taba amman ta amsa cike da fara'a , Ammi tacewa Sa'ade " Babar su Baffa ce fa naga baki ganeta ba , Sa'ade tace " au itace Safara'u wallahi bansanta ba shiyasa , sake gaisawa sukayi Safara'u tayi mata godiyar hidima da yara , Sa'ade tace " bakomai yiwa kaine ai .....

Kawu Idi yashigo gidan ai anshi Abincin su shida Abokansa , Safara'u yagani take ya canza fuska tamkar bashine me dariya ba , tuni ta zube kan gwuiwoyin ta tana kuka tana neman gafarar sa , kowa dayake gidan saida yatausaya mata ganin yadda takoma , Sai da Ammi tasa baki sannan yace ya yafe mata , batun komowa gidan sa kuma yace tayi hak'uri bazai iyaba Allah yabata wani mijin ........

Washe gari su Ammi suka shirya komawa gida , dan Zunnur yadamesu da sutafi yagaji kuma ogansa kwana biyu yabashi , haka sukayi wa su Kawu sallama suka d'au hanyar lagos......

Bikin su Hanan sai tahowa yakeyi , dan tuni Hajiya Asma'u tasasu gaba su ukun suka nufi garin kano za'ayi musu gyaran sati biyu , tunda da suka sauka A gidan su Hajiya Asma'u kwanan su d'aya suka nufi gidan *MD* me gyaran Amare da da k'amshi , tuni tafara yi musu dilka da gyara na musamman saiga su sunfara canzawa , Hanan tamkar balarabiya haka takoma saboda tsabar kyau , Zunnur kullum suna mak'ale a waya tamakar su cinye kansu , takuramata yayi da tayi masa pic d'inta ta turo masa yayi missing d'inta sosai , Hanan tace " My Dear kayi hak'uri bazaka k'ara ganina ba sai acikin gidanka , Shagwab'e mata Zunnur yayi tamkar k'aramin yaro yana kukan wasa , itama kwai kwayonsa tashigayi tana masa dariya , sunyi nisa a hakan Nasma tashigo ta d'aga mata duka tace " to Laila da Majnun ki fito Mama tana kira , kinwani shige cikin d'aki kamar zaku cinye juna , Hanan ta gallawa Nasma hararar wasa tace " wai meyasa kika rainamu mufa yayyenki ne dan haka ki bimu a hankali , Afrah ce tashigo tana fad'in "Sister Mama na kiranki fa zakisha tsuminki muma duk munsha namu , Hanan ta dafe kai tana yiwa Afrah nuni datayi shuru waya take , Zunnur dayake jinsu duk abinda suke cewa a hankali yace " Dear kije a tsumamin ke kinsan zansha aiki ranar , da sauri Hanan ta katse wayar tana dariya......

Sati biyun da sukayi sosai suka sha gyara , inkagansu saika zata wankan inji akayi musu saboda kyau , ga wani sihirtaccen K'amshi dake tasowa a jikinsu gaba d'aya tamkar an musu b'arin turare , tuni Haidar ya iso kano dan yace yagaji da rashin Habibty d'insa , sosai Yabawa su Hajiya Asma'u dariya ganin yadda ya susuce daga ganin Nasma , haka suka tattaro suka baro kano a jirgi saboda Haidar yace baza akalle masa mata ba......

Suna dawowa gida suka shiga rabon katin bikinsu , Zunnur k'ememe yahana Hanan yawon rabon kati sai Nasma da Afrah sune suke rabawa ,
Ranar Kamu a gidan Alhaji Bashir akayi wato gidan su Zunnur , sosai Amare sukayi kyau cikin shigar lifaya sai k'amshi suke , an yi musu kamu sannan *Aunty Hadiza D Auta* tayi musu lacca me ratsa zuciya akan zaman gidan aure , sannan taja hankulansu da yin biyayya da mazajensu tarufe taro da addu'a , Washe gari Hajiya Asma'u ta shirya musu Dinner lafiyayya a wani Babban holl , komai ita tad'auki nauyinsa nan ma amare sosai sukayi shigar Alfarma da angwaye , Anci ansha anzubar da kud'i sosai Mawak'iya Nabeela sosai ta wak"e Amare sannan aka tashi ....

Sai kuma Angwaye suma suka shirya Reception suda abokansu da Amaren da k'awayensu , Ankashe kud'i sosai tamkar ba neman su akeyiba.....

Washe gari aka d'aura aurensu su a k'ofar gidan Alhaji Murtala , Kawu Idi shine waliyin Hanan da Nasma aka bashi sadakinsu dukansu , Nan aka d'aura aure aka sha yinin biki.....

Magriba nayi tuni Zunnur ya turo da motocin da za'a d'aukar masa Amaryar sa , sai tsokanar Hanan akeyi akan Angon ta yafiye zumud'i itakuwa jikinta yayi sanyi takasa yimusu magana , Nan aka kaita d'akin Ammi dan tayi mata fad'a za'a wuce da ita , Ammi kasa magana tayi kawai tace Allah yabasu zaman lafiya....

Hanan kuka tashigayi tamkar k'aramar Yarinya har aka fito da ita , lokacin motocin d'aukar Nasma suma suka zo , haka aka Sakasu cikin motocin tafiya gidansu aka kaisu , Unguwar su d'aya da Hanan da Nasma , Afrah ce Unguwar ta daban tayi musu nisa amman ba sosai ba , gidan Hanan aka fara zuwa ka kaita sannan suka wuce gidan Nasma , sosai gidajen su ya had'u matuk'a ga kayan Furniture da aka jera musu sosai falukan su suka had'u , dan komai iri d'aya akayi musu babu bambanci , sai muyi musu fatan zaman lafiya da junan su....

Tuni Abokan Zunnur sun rakoshi suntafi dan cewa yayi bayason dogon zance , dariya sukeyi sosai suna tsokanar sa har suka fice , gidan Haidar ma suna zuwa sukaga tuni ya kulle gidan sai waya sukayi masa suna tsokanar sa....

Zunnur yana shigowa yasamu Hanan tana kuka , da k'yar ya lallab'ata tayi shuru yace tatashi ta d'auro Arwala , sunyi sallar godiya ga Allah sannan yadafa kanta yayi mata addu'ar neman tsari da dukkan wani abin k'i , bayan ya kammala ya mik'e ya d'auko musu ledojin daya shigo musu dashi , kajine a ciki da lemuka tare da sauran tarkacen kayan k'walam da ma k'ulashe , janyota yayi jikinsa yana lallab'ata har saida taci ta k'oshi , shima ci yayi sannn ya d'auki sauran yaje yasa a frizer....
Chapter 22 · 0% Book details