← Book details Ni Bora Ce Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 18 OF 23

Sashe 18

Ni Bora Ce Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Suma sauran matan da ya aura saigasu da ciki , Nan yashiga Jaraba yasasu a gaba yana zagi akan cewa harkud'i yabasu tunkafin suyi aure akan suje ayi musu allura ta hana d'aukar ciki ......
Kaisu yayi akan azubar da cikin amman fir ciki yak'i zubuwa , haka yaraka kowacce gidansu da saki , yana dawowa Nima nadunga rashin mutunci Akan sainaje garin mu naga iyayena , shikuma ya tubure bazanjeba haka na rufe ido naita gayamasa maganganu , aikuwa ya tunzira yafara dukana nikuma ina masa Allah ya isa , muna haka akazo masa da labarin matan da yasaka na farko sukansu sun mutu , da sauri nashiga tsoro ina fad'uwar gaba dan mutuwarsu ta dokeni sosai , Murmushi naga Alhaji Nasir yayi tare da cewa " duk macen data sake tasan sirrina to tabbas bazatayi tsayin rai A duniya ba , yana fad'ar hakan yashige yabar wajen , tuni hankalina yatashi sosai wato Alhaji Nasir yana nufin shine yakashesu ? tambayar dana shiga yiwa kaina kenan , Bayan kwana biyu yakuma zuwar min da buk'atarsa wacce yasaba , nak'i yarda inda yazo zaiyi da k'arfinsa nima na tattaro k'arfina na buga mada murfin sif , tuni goshinsa ya fashe amman bai hak'ura ba haka ya danne ni saida yabiya buk'atarsa ina faman cizonsa ......
Washe gari da sassafe tuni na had'a kayana na gudu , Tare da Nasma nataho gidan dan yadda nakeji bazan iya barinta ba , lokacin danazo gida iyayena sunyi mamakin ganina , nan na sheda musu irin abinda Alhaji Nasir yakeyi , suma sosai sukayi mamaki tare da yimasa addu'ar shiriya.....

Bayan kwana biyu da zuwana Saiga Alhaji Nasir yazo , sosai yabada hak'uri amman nace bazan koma ba , tunda yaji nace bazan koma ba yashiga yin rashin mutunci sannan ya kwace Nasma yace da ita zai tafi , ba yadda ban yiba akan yabarmin 'Yata amman yak'i , cewa yayi indai inason yarinya ta sai dai mukoma gidansa , Mahaifina yace bazan koma ba yaje da 'Yar nima nahak'ura , haka inaji ina gani ya d'auki Nasma yatafi da ita.....

Tundaga nan bank'ara ganinta ba kuma sannan bank'ara zuwa jos ba , nasha jinya tun bayan da yaturomin da takardar sakina , sosai nasha ciwo tamkar bazanyiba har saida aka fidda raina , Allah cikin ikonsa nasamu wani mutun yabani magani na warke , daga nan nafara zawarci har Allah yahad'ani da Alhaji Murtala , sosai yanuna min soyayya , dayake tamkar Yaya yake a guna tuni aka d'aura mana aure , a Lagos yake aikinsa dan haka yataho dani , saida na shekara biyu sannan nahaihu a gidan sa , 'Yan biyu na haifa duk maza sannan na haifi Aminatu da kuma Hafsa , *kunji Labarina*......

ina fatan kungamsu da nice Mahaifiyar Nasma , inbaku gamsuba ma akwai wani d'igo a gefen wuyanta wanda nake dashi nima a duba , a take Ammi ta duba gefen wuyan Hajiya Asma'u aikuwa taga tabon , sannan ta duba gefen wuyan Nasma itama take taga nata , Cike da godiya ga Allah Ammi tace " Allahu Akbar Alhamdulillah tabbas Nasma Yarinyar kice , dan ko yanzu nakuma tabbar dahakan nima ta yadda kuke kama , Nasma take tasaka kukan wanda tarasa nameye na dad'ine ko na meye oho jikin Hajiya Asma'u tafad'a tana kuka , Hajiya Asma'u ta ringumeta sosai tanajin k'aunar 'Yarta na ratsa duk wata gab'a ta jikinta ,
Bayan sun nutsu Ammi ta dubi Zunnur tace " Yanzu bawanda yaganka sanda kashigo garin nan dasu ? Zunnur yace " a gaskiya bawanda yaganmu dan ko gida bamujeba bare aganmu , Ammi taja numfashi sannan tace "Inaso ka kwana d'aya gobe saika wuce Sch d'in , zasu zauna anan banason ko Abban ku yasani dan bayanzu nakeso yasaniba , sannan ina gudun shi wannan Alhaji Nasir d'in karsuzo nan nemansu tunda kaga dole Idi zaikawosa nan , kaga indai sukaje gidan Yaya ai zaice musu Hanan batazo ba , tunda sunsan batasan nayi aureba dole intazo garin zasuce gidan Yaya zata sauka , da wannan shawara ta Ammi sukayi Na'am dukansu , Hajiya Asma'u tace " dole zamu samu Alhaji Murtala muyi magana , dan sai annemo musu maganin tsari sosai , nan suka shiga tattauna yadda zasu b'illowa lamarin Yaran nasu......

*Bayan kwana biyu*

Tuni And'aura auren Alhaji Nasir da Safara'u sosai akasha bidiri a gidan su Safara'u , shikuwa Alhaji Nasir kwata kwata baya cikin nutsuwarsa kawai dan dai dodon tsafi ya nuna ya auri Safara'u shiyasa ya aureta , amman shi yanzu soyake yaga Hanan da Nasma , gashi Kawu Idi yazo har gidansa yayi masa rashin mutunci da ya lallab'ashi yayi masa kwatancen inda Mahaifiyar Hanan take , amman zaije ya jik'ashi da kud'i watak'ila ya kulashi inyaga ruwan nera.....

Ankawo Safara'u gidan mijinta , sai faman hura hanci takeyi tana cika tana batsewa ita ala dole ta auri me kud'i , lokacin da Alhaji Nasir yazowa Safara'u ta Baya ya nuna mata zai kusance ta , nuna masa tayi sam batasan wannan batuba , kud'i ya d'auko ya zube mata dayake yaga daren farko ne tuni Safara'u ta amince masa yayi yadda yakeso da ita , sosai tasha azaba tamkar kayan cikinta zasu fito amman data tuna kud'inta kwata kwata sai zafin yatafi......

Hanan kwana biyun dasukayi har sun murmure , Alhaji Murtala sosai ya tausaya musu dayaji labarin tare dayin Allah wadai da Alhaji Nasir , Nasma kuwa koda yaushe tana manne da Hajiya Asma'u dan jitake tamkar yanzu tazo duniya , lalle Uwa akwai dad'i sai lallab'asu akeyi tamkar wasu k'ananan yara ......

Zunnur tunda yakoma yasamu nutsuwa dan kullum suna tare da Hanan a wayar Ammi , yanzu abinda yarage masa shine yasan yadda zaiyi yakoma Jos yasa Alhaji Nasir yasaki Hanan tunda da aurensa akanta haryanzu..........
[1/29, 16:19] +234 704 610 7812: *NI* *BORA*
_Ce_ 👩🏿‍🦳👩🏿‍🦳

*Zee* *MD* ✍🏻

22.

Hajiya Asma'u tafara basu labari kamar haka.....

Ni 'Yar asalin garin Kano ce iyayen mu mu biyar suka haifa , mu hud'u mata sai Namiji guda d'aya wand Shine autan mu , duka Yayyena sunyi aure saini dana rage inah karatu , lokacin ina zuwa F.C.E kano a lokacin na had'u da Nasir muka k'ullah soyayyah , Nasir d'an garin Jos ne yazo kano karatune , Bayan ya kammala karatunsa ya koma Garinsu amman ko da yaushe muna waya dashi , soyayyar mu tayi k'arfi sosai kwata kwata Mahaifina baya k'aunar Nasir ko kad'an , niko kwata kwata idanuna sun rufe banaji bana gani akan Nasir , da Mahaifina yagaji da halina na korar samari yaga banida niyyar kula kowa indai ba Nasir ba , samuna yayi da maganar incewa Nasir d'in ya turo mutuk'ar da gaske yakeyi , ranar murna a wajena ba'a magana tuni nakira Nasir nasanar mai da wannan sak'on , shima murna yayi sosai tare da yimin alk'awari zaituro iyayen sa cikin satin......

Hakan kuwa akayi cikin sati iyayen Nasir sukazo daga jos , Nan aka tsaida lokacin bikinmu wata biyu masu zuwa , karkiga murna a wajena duk da inajin zanyi kewar iyayena , dan duk cikin Yayyena bawacce aka kaita nesa ..

Akwana a tashi ba wuya saigashi lokacin biki yazo , sosai Nasir yayimin lefe d'an Ubansu ga kaya kamar me dan yawa , nayi mamakin ganin irin kayan da Nasir yasakomin a lefe , tunda nidai yadda yake cemin kullum wai aikin koyarwa yake , saikuma yana d'an tab'a kasuwanci , amman lefena kowa yagani a lokacin saiya k'ara gani saboda yawansu , Anyi biki lafiya angama washe gari aka wuce dani jos , sosai nayi kukan rabuwa da iyayena da kuma 'yan uwana , haka aka kawoni gidan Nasir me kyau dashi aka ajiyeni...
Bayan kwana biyu dangina suka yimin sallama tare da tarin nasihohi akan rayuwar aure sannan suka wuce...

Sosai Nasir yake tattalina tare faranta raina , kullum cikin yimin hidima yake tamkar ya maidani ciki , matsala ta farko dana fara fuskanta shine rashin ganin kowa nashi yazo , kullum cikin tambayar sa nake banga 'Yan uwansa ba amman saiyace min " wai sunsamu matsala tun lokacin bikina da sukace dole saiya auri 'Yar uwarsa ya had'amu mu biyu , haka nagaji da tambaya na k'yalesa har na cika wata uku .....

Matsala ta biyu dana k'ara fuskanta kwata kwata Nasir baya fita ko inah , kullum yana gida daga bacci sai cin Abinci da kallo , gashi koda yashe cikin kashe kud'i yake sababbi tamkar me aikin Bank , Nan ma nayi masa magana yace mun bayason yawan bincike a lamarinsa dan haka ido ne nawa , koda nashiga wata na hud'u a lokacin Allah yabani ciki sosai nakeshan wahala saboda laulayi , kwata kwata yadda na fahimci Nasir baya murna da wannan ciki , kuma a lokacin yabiya kud'in tafiya Hajji , yana ta shirin tafiya na rok'esa a kan ya maidani garin mu can gidan mu inyadawo sai nadawo nima , fir Nasir yak'i yace bayason a nuna gazawarsa dan haka zai kawomin 'Yar uwa wacce zamu zauna tare , duk bankawo komai ba ana saura kwana hud'u yatafi nafa ana gyara d'aya d'akin dake jikin nawa , akazo akayi jere dare nayi naji gud'a ankawomin Amarya .....
Sosai nayi mamakin Abinda Nasir yayimin naci kuka nagode Allah batare da nafad'awa kowa ba , haka ya shigo gidan yahad'amu nida Amaryar sa yayi mana fad'an zama lafiya , Amarya wacce naji yakira da suna Hajjo tace " insha Allah daga gurinta babu matsala nima hakan nace tare da mik'ewa nabar d'akin.....

Ranar Tafiyar sa haka yatafi Saudi'a Abinsa yabarmu da tarin kud'i me yawa , Yadda na fahimci Hajjo tana da son Abin duniya , gata da bak'in kishi tamkar itace uwargida , Anan nakejin wai bazawara ce ita aurenta hud'u duk bata haihuwa shiyasa Nasir ya aurota , Anan nagane maganar ta inda ta nufa wato ni tunda nayi ciki bayaso bari ya auro wacce bata haihuwa , watan Alhaji Nasir Biyu yadawo gida lokacin cikina yafara girma .....
Chapter 18 · 0% Book details