← Book details Ni Bora Ce Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 3 OF 23

Sashe 3

Ni Bora Ce Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Bayan wani lokaci Safara 'u Abin nata ya k'ara girmama dan kusan kullum saita yadawa Ammi magana , tun Ammi na k'yaleta har wata rana ta tanka mata suka hau fad'a ....
Lokacin ne Baffa da Kawu Idi suka shiga tsakaninsu , tundaga lokacin kowa yadaina kula kowa , nikuwa kullum cikin shiga d'akin Safara'u nake tana koroni , lokacin ina da shekara Hud'u a duniya kuma har lokacin Safara'u bata haihuba itama kuma Ammi bata k'ara Haihuwa ba , wani daren Alhamis Baffa na yatashi da Amai da gudawa , Kafin aje Asibiti Allah ya amshi Abinsa , Bak'aramin tashin Hankali Ammi na tashiga ba , dan suma tayi saida aka kaita asibiti , Kawu Idi shima Mutuwar ta dokeshi sosai , Bayan angama zaman Makoki Ammi taci gaba da zama dan yin takabar ta a d'akin mijinta , tun daga nan Ammi takamu da hawan jini , nan rayuwar ta ta koma shuru batason yawan magana , Nikuma Kawu Idi yasani a makaranta , lokacin Safara'u tasamu ciki zokuga iyayi da gwalli , aikima hanata yi Kawu yayi wai sai dai Ammi tafito tadunga yin aikin , haka Ammi ke fitowa tana shan aiki Safara'u tana mata rashin mutuncinta....

*Littafina Na Kud'ine* *Duk* *Meso* *Yamin* *Magana* ta *Wannan* *Number* 07046107812 *Kuyi* *k'ok'arin* *Mallakarsa* _kukaranta_ _cikin_ _Aminci_ *Saina* *jiku* *Masoyana* 🤝🏻😍

*'Yar* *Mutan* *Kanawa* _Ce_ 😍🌹
[1/29, 16:19] +234 704 610 7812: *NI* *BORA*
_Ce_ 👩🏿‍🦳👩🏿‍🦳

*Na*
_Zee_ _MD_ ✍🏻

*Hamdala* *Writer's* *Association* 💪
https://www.facebook.com/111403834371046

✨✨ *{{* *H.W.A* *}}*✨✨

*Bisimillahir* *Rahamanir* *Rahim*

*Littafina* *Na* *Kud'ine* *Duk* *Meso* *Yamin* *Magana* *Ta* *Wannan* *Number* 07046107812 *Kuyi* *K'ok'arin* *Mallakar* *Naku* *Akan* *Naira* 200 *Kacal* *Kukaranta* _cikin_ _Aminci_ 🤝🏻 *Saina* *jiku* *Masoyana* 🥰😍

🆓 page. 6

Bakowa bane face Zunnur , gyaran muryar da mukaji a saman kanmu yasa ka dukan nin mu mik'ewa cike da jin kunya , Abban sune shida Haidar suka shigo , sai kuma Afrah dake binsu a baya d'auke da jakar kayan su , duban Haidar nayi ina cewa " sannu da zuwa Abokina , Haidar yayi murmushi yace " wai daman kinanan shine ko neman mu bakyayi ? ai nayi fushi dake yanzu bama Abotar , Abban su yasamu gu ya zauna yana Murmushi yace " Abotar ku tana nan ba inda zataje kar kusa su Afrah suyi muku dariya , kowa waje yasamu ya zauna sannan aka fara gaisawa ana musu ya hanya ......
Saida suka gama gaisawa sannan Umman su tace " ga Abinci can yana jiranku inkun gama gaisawar , Ammi tace " kamata yayi sufara yin wanka suhuta sai su zo suci Abincin , Nan suka mik'e sukace "shawar Ammi zamubi bari muyi wankan sai mufito.....
Bayan sunyi wanka sunfito dukan mu muka had'u akan Dinning table , dancin Abinci , nida Afrah aka ce mutashi muyi savening d'in kowa dake gun , Afrah tace nidai zanzubawa Ammi da Ya Haidar , kekuma sai kizubawa Abban mu da Ya Zunnur , ita kuma Umma daman ta k'oshi da k'amshi tun d'azu , Dariya suka saka dukansu Amman banda Zunnur wanda Murmushi kawai yayi yana duba wayar sa , mik'ewa nayi na janyo kulolin Abincin nafara zubawa kowa dake gun , Bayan na kammala kowa na tura masa gabansa sannan nazuba nawa nima nazauna , fara cin Abincin mukayi kowa sai santi yake tamkar muna Resturen , nikuwa nakasa sakin jiki naci Abincin saboda duk d'agowar dazanyi sai munyi ido biyu da Zunnur , duk ilahirin jikina banda rawa babu abinda yakeyi , cikin Zuciya ta nafara tambayar Kaina " wai meyasa nakejin haka game dashi ? meyasa saishi kad'ai nakejin hakan akansa ? ina ta wasa da cokali a cikin Abincin nakasa ci , Muryar Umma naji tana cemun " Hanan lafiya kuwa naga tun d'azu kink'i cin Abinci sai wasa kike da Cokali ? Murmushi nayi nace " Umma banajin yunwa ne saboda bandad'e da karyawa ba , Afrah tayi tsagal tace " Bawani Umma kawai inajin kunyar Ya Zunnur takeji , tunda naga shikad'ai ne baya magana a wajen nan , Hararar Afrah nayi sannan nace " Kunyar sa kuma saikace sirikina , Abban su yace " Kwaji dashi dai keda Afrah , mik'ewa yayi yana fad'in Alhmd nidai na k'oshi yabar wajen , Umma su ma tashi tayi tabi Bayansa , Ammi daman tuni tagama ta mik'e tabar wajen , yarage dagani sai Afrah da Haidar da Zunnur , sai da aka kwashi minty kusan goma sannan Haidar ma ya mik'e yana fad'in " tonidai nagaji dayawa , zanje nayi Bacci zuwa k'arfe biyar , Hanan innatashi zanzo muyi hira sosai dake , Nayi Murmushi nace " Afito lafiya Aboki , Haidar ya wuce 'Dakinsu yabar mu a gurin , Afrah mik'ewa tayi tafara kwashe kwanunkan da akayi Amfani dasu tana Nufar kitchen dasu , Zunnur yana Zaune sai latsa wayar sa yake tamkar baisan Ina wajen a , Mik'ewa nima nayi da zummar barin wajen kamar daga sama naji ance " Dawo ki zauna inason muyi magana , juyowa nayi na dubesa tamkar bashi ne yayi maganar ba , Mamakine yakamani Nadawo na zauna ina wasa da yatsun Hannuna , d'agowa yayi ya dubeni yace " Yaushe kukazo keda Ammi ? cikin sanyi nace " Munyi sati biyu yanzu haka , cike da isa irin tasa yace "kuma kwana nawa zakuyi kafin ku tafi ? Nan a nace masa Sati Uku daman zamuyi saboda munkusa komawa hutun Makaranta , kuma mun komawa zamu fara pepar ta kammala SSCE , dubana yakuma yi sannan yace " Inafatan dai bakya wasa da karatunki dan yana da mutuk'ar Amfani ga 'Ya mace kodan 'Ya'yanta Nangaba , amsa nabashi da " Ae bana wasa da karatuna , jefomin wat tambayar yayi yace " Ina fatan bakya kula Samari dan ked'innan ba isa kikayiba ? wannan Tambayar ce nakasa bada amsar ta , dan indai kula samarina yariga da ya makara , shurun dayaji nayi yasa ya d'ago sosai yana dubana , cikin alamar yaji rashin dad'i da shirun danayi masa yace " ko kurma kika koma kinaji ina miki magana kinyi min shuru , jikina tuni yafara rawa nace " Bana kula kowa ni , kallo na yayi yace kintabbata ? Nace E . Zai sake magana kenan saiga Umman su tataho , wani dad'i naji ya rufeni dan daman akan k'aya nake , irin wannan Tambaya tamkar d'an jarida , Umma na k'arasowa tace " Hanan ina Afrah take kuzo in aikeku yanzu , Mik'ewa nayi ina fad'in Bari nadubata nagani tuni nabar wajen....

Afrah naje nagayawa Umman su zata aikemu , cike da zumud'i tace " wallahi daman Hanyar fita nake nema tund'azu , saboda Anas yanason muhad'u amman yanzu bani ba had'uwa dashi a cikin gidan nan tunda du Ya Zunnur suka dawo , kallanta nayi nace " aikuwa indai muka fita kika kulashi tabbas saina fad'awa Ya Zunnur ya caskala ki , dariya tayi tana had'e hannuwan ta alamar ban hak'uri , fitowa mukayi wajen Umman su tabamu aiken datace zamuyi mata , har mun ansa munyi haryar tafiya mukaji Muryar Ya Zunnur yana cewa " Ke Hanan ahaka zaki fita ne kamar wata yarinya ? tsayawa nayi tsam ina duban jikina , Doguwar rigace sai mayafinta danayi Rollyn dashi , Umman su ce naji tana ce masa " To me kayan jikin nata yayi dazaka dakatar da ita ? cike da jin badad'i yace " nidai nafad'a mata mutuk'ar bata d'auki Babban gyale tayafa ba to tadawo ta Zauna , da sauri Afrah tace " Bari naje na d'auko mata tasa sai mutafi , nikam abin nasa ma mamaki yabani , duba da yadda yake b'ata rai tamkar wani mijina , Umma kuwa cewa tayi "Allah ya kyauta maka da wannan halin naka , Matar ka zaka dinga yiwa wannan ikon ba yaran mu ba ta wuce tayi cikin 'Dakinta ...
Afrah tana kawomin gyalen na ansa na yafashi , tunda na yafa gyalen yake satar kallo na Haka muka saka kai muka fice daga cikin gidan......
Saida mukaje aiken da Umman tayi mana sannan muka biya wajen wani Garden , Afrah takira Saurayinta Anas tafad'a masa inda muke , Muna Zaune na dubi Afrah nace " kinsan Allah tsoron Ya Zunnur nakeji sosai , kwata kwata baya dariya tamkar ba 'Dan gidankuba , Afrah tayi murmushi tace " wallahi haka yake da wannan miskilancin , magana ma saiya ga dama yakeyinta , Sannan ga fad'an tsiya shiyasa insuka dawo hutu wallahi duk ata kure nake , Suna cikin hira saiga Anas ya k'araso , Nan muka gaisa yasa mu guri shima ya zauna , Hira suka fara shida Afrah nikuma na mik'e nabar musu gurin , Samun wani guri nayi na zauna ina kallon yadda masu kud'i suke shigowa su da 'Yan matansu wasu kuma Matansu da yaransu , Ina Zaune naji ance min Aminci agareki Tauraruwa ta , da sauri na kalli wajen bakowa bane face " Muktar yana mun murmushi , Mamakine yakamani taya yasan ina nan gurin ? kamar yasan tambayar danakewa Zuciya ta kenan yace " Afrah ta turamin test tace kuna cikin Garden nazo intayaki hira tana da bak'o itama , Cikin Zuciya ta nace " Afrah akwai rashin mutunci , a fili kuwa nace " Sannu da zuwa yakake ya hanya , Zama yayi kusa dani tamkar zai shige jikina har sai da na matsa , shi kuwa ko ajikinsa ya fara k'okarin rik'emin Hannu , 'Bata Rai nayi ina cewa " Kasan banason irin wannan Abun haka , Muktar yayi Murmushi yana fad'in " Am sorry my luv bazan k'ara ba , d'agowar da zanyi mukayi Ido biyu da Zunnur yana nufo wajen mu a fusace , take naji wani fitsari ya ziyarci marata , tuni na mik'e tsaye jikina inbanda rawar Banjo babu abinda yakeyi , yana k'arasowa ya damk'i wuyan Muktar ya haushi da duka tamkar wanda yakamashi da Matarsa , ai tuni na nufi wajen da Afrah take da gudu bansan inada gudu ba ma sai ranar........

*Littafina* *Na* *Kud'ine* *Duk* *Meso* *Yamin* *Magana* *Ta* *Wannan* *Number* 07046107812 *Kuyi* *K'ok'arin* *Mallakar* *Naku* *Akan* 200 _karku_ _Bari_ _Abaku_ _labari_ _Kusiya_ _Kukaranta_ _Cikin_ _Aminci_ 🤝🏻🥰

*'Yar* *Mutan* *Kanawa* _Ce_ 😍🌹
[1/29, 16:19] +234 704 610 7812: *NI* *BORA*
_Ce_👩🏿‍🦳👩🏿‍🦳
Chapter 3 · 0% Book details