← Book details Ni Bora Ce Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 20 OF 23

Sashe 20

Ni Bora Ce Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Dubansu tayi dukansu tace " nasan zakuso jin taya nakasance Mahaifiyar Nasma ko ? to kafin kusani inaso dan Allah ku nutsu sosai ku dubeta sannan kudubeni nasan ko a hakan zaku gamsu da wani Abun , dukansu kafawa Hajiya Asma'u idanu sukayi sannan suka fara duban Nasma itama....

Safara' u koda taje gida Iyayenta basu damu ba , dan suma sarakan san kud'ine gado itama tayi , nan suka karb'i maganar Alhaji Nasir tare da tsaida rana sati d'aya yazo a d'aura masa aurd da ita , tuni Alhaji Nasir ya jik'asu da kud'i dan yaga suna buk'ata dayawa , yana tafiya suka fara murna suna suma kwanan nan zasu faso gari , Nan Safara'u tafara hura hanci tana wani jan Aji ita a dole zata auri me kud'i..........
[1/29, 16:19] +234 704 610 7812: *NI* *BORA*
_Ce_ 👩🏿‍🦳👩🏿‍🦳

*Zee* *MD* ✍🏻

25.

Kawu Idi yadubi Hajiya Hajjo yace " dan Allah ina Hanan take ? tab'e baki tayi sannan tace " ai sunfi sati biyu basa gidan nan ita da yarinyar wajen Alhaji , kuma yadda yace mana wai sun gudu ne saboda sunyi masa sata shima neman su yake , sosai Kawu Idi yashiga mamakin maganar Hajiya Hajjo , sallama yayi mata ya fice cikin ransa yana fad'in dole ya shirya yaje Lagos ko Hanan taje can .........

Alhaji Nasir nashiga cikin d'akin sa tuni yayi zindir yafara kiran dodon tsafinsa , suna fara ganawa kenan saiga Safara'u tashigo cikin d'akin dai dai lokacin da Alhaji yake shan jini yana wanka dashi a cikin wata k'warya , yanayi yana zagaye yana fad'in " Safara'u ! Safara'u !! aikauwa tuni Safara'u k'irjinta ya buga tafara ja da baya tana ganin wani k'warangwal d'in kai yana zubar da kud'i kuma fuskar kamar ta matar Alhaji Nasir d'in data mutu , juyowa Alhaji Nasir yayi sukayi ido biyu da Safara'u tuni yayo kanta da sharb'ebiyar wuk'arsa , ai tuni Safara'u tajuya tafice da gudu tana neman matsera , Hajiya Hajjo taganta da gudu tana ihu tana fad'in " Alhaji zai kasheni wallahi shan jini yakeyi , Hajiya Hajjo batagama jin Maganar Safara'u ba taga Alhaji Nasir zindir shima yataho da gudunsa , tuni itama ta juya da gudu tana neman matsera , Alhaji Nasir yana ganin haka yatuna a yadda yafito tuni ya juya yana cizon yatsa na rashin kama Safara'u dan wallahi yau dasai dai wata ba itaba , amman yanzu ma tunda har tagansa wallahi saita mutu dan bazata tona masa asiri ba ......

Safara'u tuni tafice daga cikin gidan sai gudu take tamkar zata ci da baka , duk nisan dake tsakanin gidansu da gidan Alhaji bata ganiba tuni takawo gida , da gudu tashigo tana ihu ba gyale ba d'ankwali bare takalmi kuma , tana shigowa ahaka suma suka mik'e suna neman matsera , dan cewa take gashinan da wuk'a zai yankani yasha jinina.....

Hanan ansamu Nassarar yi mata aiki , Alhaji Murtala shine ya biya kud'in da akayi mata aikin , lokacin Ammi ta yanke shawarar zuwa tasamu Abban su Zunnur tagaya masa duk abinda ke faruwa , waya ta kira ta tambayi Umman Zunnur tace mata yana gari , dan haka tashirya daga asibitin ta wuce tabar Nasma a wajen Hanan d'in , dama da ita da Nasma suke kwana a gunta Hajiya Asma'u kuma kullum sai tazo takawo musu Abinci...

Lokacin dataje gidan tasamu Yayan nata da maganar Hanan d'in , sosai yayi mata fad'an rashin gayamasa dabatayi ba , sannan yayi Alk'awarin zuwa Kano wajen Kawu Idi yaji dalilin dayasa yayi wa Hanan d'in hakan , kuma sosai ya jinjinawa Zunnur da irin k'ok'arin dayayi wajen kawo su Hanan d'in Nan , Afrah najin ance Hanan tazo tana asibiti tuni tafara shirin bin Ammi dan tace saitaje taga Hanan d'inta....

Zunnur tunda yaji Ance Hanan ba lafiya dama gashi sunsami hutun sati Uku , tuni suka had'o kayansu suka nufo Lagos....
Afrah tana ganin Hanan tasaka kuka ganin yadda Hanan d'in takoma, dak'yar Ammi ta lallab'ata Nasma ma tasa baki sannan tayi shuru , Hanan kuwa haryanzu bawani gane mutane take ba saboda wuyar datasha sosai , dan likitan dayayi mata aiki cewa yayi data k'ara wasu watannin da tsutsotsi ne zasu fara fitowa ta gabanta , gashi dole zata koma tana neman maza ko mata kuma ta baya , lokacin daya fad'i wannan maganar sosai su Hajiya Asma'u da Ammi sukayi kuka , Abban su Zunnur shima sunzu shida Umman Zunnur sosai suka tausayawa Hanan , sosai yayiwa Alhaji Murtala godiya ganin yadda yanuna damuwa akan Hanan d'in tamkar shine ya haifeta , kullum daga gidan Su Afrah sai ankai musu Abinci nan ma......
Su Zunnur suna da wowa ko hutawa baiyiba yashirya ya nufi Asibiti , yana zuwa lokacin Hanan tana bacci su Ammi da Afrah da Nasma suna zaune a reception sai hira suke , shima zama yayi yana d'an tayasu kafin Hanan d'in tatashi .....

Safara'u tuni tazama k'aramar Mahaukaciya , dan kullum cikin zabura take tana ihun fad'in gashin yazo da wuk'a zai yankata , lokacin da Alhaji Nasir yazo guduwa tayi d'aki tasa sakata tafara ihu , Babanta yace ya k'yaleta kawai intaji sauk'i ta dawo , haka Alhaji Nasir yatafi yana shirya ta yadda zai d'auketa daga gidan...

*Bayan kwana biyu*
Hanan sosai jikinta yayi sauk'i , har hira suke ita dasu Zunnur daya tare a Asibitin , Haidar ma yana zuwa sosai saboda yaga Nasma dan yana ganinta yaji tashiga ransa , itama sosai take sakin jiki suyi hira da shi , ga Afrah data zama tamkar 'Yar uwarta saboda shak'uwa , Koda jikin Hanan yayi sauk'i sosai aka sallamesu suka koma gida....

Kawu Idi ne ya dira a gidan su Zunnur , Yayi sa'a kuwa yasamu Alhaji Bashir wato Baban su Zunnur d'in , nuna masa yayi baisan Hanan tazoba saboda yaji da wacce yazo , aikuwa Kawu ya karkace yanafad'in wai Hanan sunyiwa Alhaji Nasir sata ita da 'Yarsa sungudu , shine yazo nemanta ko Allah yasa sunzo nan , aikuwa tuni ran Alhaji Bashir yakuma b'aci tuni yafara fad'a " Hanan sunzo nan tunda acan ana neman kasheta bata da gata , Nan yashiga yiwa Kawu sababi tare da sheda masa komai da Alhaji Nasir yakeyiwa Hanan d'in , tuni jikin Kawu Idi yayi sanyi yafara hawaye sosai , Alhaji Bashir yaci gaba da cewa " karka ga wannan abun dakayi ko Allah zai barka dole sai Allah yasaka mata , kana matsayin Mahaifin a gunta saboda san abin duniya ka d'auketa kabawa me shan jini ita , sosai Nadama ta shiga Kawu yadunga kuka yana neman afuwa tare da cewa araka shi gidan Ammi yaga Hanan d'in ya rok'eta gafara , tare suka shirya shida Alhaji Bashir suka nufi gidan Ammi.....

Alhaji Nasir yanzu hankalinsa a mugun tashe yake saboda Dodon tsafinsu yana buk'atar jini , gashi Hajiya Hajjo ta kwashe yaran gidan duka sungudu har Alawiya ba wanda aka bari , neman duniya yayi musu amman bai gansuba , dan tun randa Hajiya Hajjo tagansa da wuk'a tafara yadda da rad'e rad'in mutane , shiyasa ta sulale ita da yaran gidan suka gudu tare da Alawaiya .....

Lokacin da Kawu yaje gidan Ammi suna ganinsa Hanan ta b'uya a bayan Hajiya Asma'u , gaisawa sukayi da Hajiya Asma'u itakuwa Ammi ko kallonsa batayi ba , sosai Kawu yanuna nadamar sa akan Abinda yayiwa Hanan d'in , Anan yakejin Nasma 'Yar gidan Alhaji Nasir itama ta had'u da Mahaifiyar ta , sosai yayi dad'i tare da neman afuwar Hanan d'in , tayafe masa inda suka tsaida ranar tafiya Jos dan zuwa karb'owa Hanan takardar sakinta...

Alhaji Nasir cikin dare ya fito da niyyar zuwa gidan su Safara'u , dan Dodonsa yabashi kwana biyu akan indai bai zubar masa da jini ba to duk zai nemi dukiyar sa yarasa ta , yana zuwa gidan su Safara'u yasamu gidan nasu a bud'e ba'a rufe ba , lokacin zafi akeyi duk suna tsakar gida a kwance , yana zuwa yafara lalub'en Safara'u ita kuwa lokacin tana cikin d'aki tana surutan ta wanda tasaba , aikuwa kamar an mintsineta tafito tsakar gida aikuwa sukayi ido biyu da Alhaji Nasir take ta kurma ihu tana fad'in " gashinan yazo yankani wayyo , dukansu suka mik'e aikuwa sukaga Alhaji Nasir tuni suka bishi da gudu aikuwa yayi maza ya fad'a motar sa yagudu........
[1/29, 16:19] +234 704 610 7812: *NI* *BORA*
_Ce_ 👩🏿‍🦳👩🏿‍🦳

*Zee* *MD* ✍🏻

24.
Chapter 20 · 0% Book details