← Book details Ni Bora Ce Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 19 OF 23

Sashe 19

Ni Bora Ce Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Koda yadawo bamu dad'e a wannan gidan ba muka tashi ya gina mana wani babban gida , gidan yahad'u sosai tamkar gidan wani gwamna , kullum cikin raina mamakin irin kud'in Alhaji Nasir nake , dan kullum yawa suke k'arayi tamkar ana turo masa su , gashi nayi nayi yasanar dani irin sana'ar dayakeyi fir yak'i yafad'an , dan har cewa yayi indai nakuma damunsa to wallahi abakin aurena , haka na hak'ura na k'yalesa har Allah yasaukeni lafiya nasamu 'Ya mace , ba laifi yayi murna amman bai d'auketa ba tunda aka haifeta , Ranar suna Yarinya taci Sunan Ummana Halimatu muke cemata *Nasma* 'yan uwana duk sunzo suna , sun nuna suna so sutafi dani wanka amman fir Alhaji Nasir yahana dole aka k'yaleni..

Bayan wata biyu da haihuwar Nasma nafara ganin sauyi a tare da Alhaji , kullum inyazo min kwanciyar aure sai yace ta Bayana zai kusance ni , nikuma nak'i yadda fir tunda ganan muka fara samun matsala , domin kwata kwata ya fita daga sabgata , gashi yahanani zuwa ganin gida firr , akwana atashi saiga Alhaji Nasir ya auro mata biyu rana d'aya , Nayi mamaki dabai gayamin zaiyi aureba amman haka nakuma dannewa batare da nanuna damuwa ta ba , a kullum banida burin sai son sanin ta ina Alhaji Nasir yake samun kud'i , dan kullum Abin yana bani tsoro sosai , kuma gashi har na haihu dashi amman bantab'a ganin danginsa ko d'ayaba...........

*Kumin Afuwa yau Posting d'in Ni bora ce kad'ai zaku samu*

*Shid'inma kuma kuyi hak'uri bayawa*✍🏻✍🏻
[1/29, 16:19] +234 704 610 7812: *NI* *BORA*
_Ce_ 👩🏿‍🦳👩🏿‍🦳

*Zee* *MD* ✍🏻

21.

Tuni mutane suka fara cika a wajen ana bawa Kawu Idi hak'uri , amman ko takansu baibiba ya shige gidansa tare da rufowa , Alhaji Nasir shima nufar motar sa yayi zai shige yatafi Safara'u tayi tsagal tace " Alhaji dan Allah kataimaka min ka kaini gidan mu , ko jiyowa Alhaji Nasir baiyiba yace tashiga motar kawai......

Bayan su Hanan sunyi wanka Ammi ta d'auko musu dogayen riguna a cikin kayanta , mik'a musu tayi tace " gashinan kowacce tasaka sai kuzo palor kuci Abinci , Hannu biyu suka saka suka ansa tare da cema to , Bayan fitar ta Nasma ta dubi Hanan tace " gaskiya Hanan kinyi sa'ar Uwa tagari gata me fara'a dason mutane , nifah dana ganta wallahi saikace bata haifeki ba gashi tafiki kyauma , Hanan tayi murmushin jin dad'i tace " kedai kawai kice kinkoma Bayan Ammi yanzu nikuma an zubar dani , itama Nasma Murmushin tayi tace " in ma hakan ne ai ba laifi nayi ba dan kinsan Ina ganinta naji tamkar naga Ummata duk da bansan taba , Hanan tace " insha Allah zaki santa nan bada dad'ewa ba , Nasma tace " Allah yasa hakan dan inaso ko yayane nima naji d'uminta atare dani ......
Bayan sunsaka kaya suka fito daga cikin d'akin suka nufo palor , Zunnur tunda suka taho idonsa yake kan Hanan , gani yayi tarame sosai dai dai ta k'ara haske sosai ga idanunta sunkuma fitowa masu shek'i dasu , suna k'arasowa ya d'auke idonsa daga kallonta , samun guri sukayi suka zauna Hajiya Asma'u tuni ta kawo musu Abinci , jollof d'in shinkafa ce data wadatu da kayan lambu sai kuma Naman rago soyayye akai , gefe d'aya kuma ruwan roba ne da lemo , Zunnur shima anzuba masa nasa daban , nan sukayi bisimillah tare da fara cin Abincin su.......

Safara'u tana zaune cikin motar Alhaji tamkar ba itace tasha duka ba , ta dubi Alhaji Nasir tawani kashe murya tace " Alhaji nidama naga baka dace da wannan yarinyar ba kwata kwata , kasan Hanan bata da wayewa ko kad'an mezai hana ka hak'ura da neman ta kawai kamaye gurbinta dani , tawani kashe masa ido ta mirro d'in motar tana wani k'ara turo k'irji , Alhaji Nasir yayi wani guntun murmushi sannan yace " ai duk wannan me sauk'ine , tunda har kinga nayi miki to kije gida kigama idda sai inzo muyi magana , Safara'u wani dad'ine ya rufeta tamkar tamik'e tafara tsalle tace " wacce Idda Alhaji ni ko gobe ka fito da wuri zantaho gareka , ko ka manta bari ya wuce shine ke kawo rabon wani , Alhaji yace " Amman kina ganin mijinki bazai zargin dama hakan ce takawoni ba harna kashe miki aure ? tab'e baki tayi sannan tace " k'yale wannan mara zuciyar ai ko inah gidansa kanuna kana sona dole zai hak'ura yabarmaka ni , bare yanzu yariga da yasakeni agaban mutane , Alhaji tunowa yayi da maganar dodon su dayake cewa " jinin Safara'u zaiyi musu Amfani , take Alhaji Ya Amincewa Safara'u tare da cemata Nan da kwana biyu zaizo neman auren ta , Murna a wajen Safara'u ba kama hannun yaro tuni tafara hango kanta a gidan Alhaji Nasir tana baza mulkinta.....

Kawu Idi ransa ba k'aramin b'aci yayi ba , dama yadad'e yana zargin Safara'u tana son Alhaji Nasir saboda taga yana da kud'i , yau yaga gaskiya da kansa dan haka taje gata ga shinan , Abin kunya be dai ace Hanan na gidansa da aure itama tashiga gidan , tabbas zaisan yadda zaiyi ya hana Alhajin Hana kula Safara'un.....

Bayan su Hanan sungama cin Abinci Nan suka kuma gaisawa da tambayar bayan saduwa , Alhaji Murtala yatashi yafita saboda kiran da akayi masa a wajen aikinsu , Hajiya Asma'u kuma k'anwarta tazo itama ta mik'e suka shiga ciki , yarage sai su Hanan da Nasma da Zunnur da Ammi , Ammi ta dubi Zunnut tace " yaushe kadawo gida banida labari ? Zunnur ya gyara zama sannan yace " Akwai muhimmiyar magana a game da Hanan Ammi , Ammi tace "tunda nagansu haka ita da wacce suka zo nasan ba zuwan dad'ine ba , Nan tace " inajinka kasanar dani komai banaso ko kad'an a boyemin wani Abu , Nan Zunnur ya shiga gayawa Ammi tun randa yaje gidan Kawu Idi da yadda sukayi dashi har takawo zuwansa gidanta shida su Hanan bai b'oye komai ba .......
Ammi tuni taji wani gumi yana karyo mata wato duk mafarkin datake akan Hanan ashe da walakin , Mik'ewa tsaye tayi tashiga yin safa da marwa a cikin Palor , tabbas Idi yaci Amanar zumunci wato shine ya aurar da 'Yar ta batare da tasaniba , ta dad'e ahaka sannan tadawo ta zauna ta dubi Hanan tace "waye mijin naki kuma a ina yake inaso nasan waye wanda ya aura miki ? Dai dai lokacin Hajiya Asma'u tafito ta nufi cikin kitchen , Abincinci ta zubowa K'anwar ta ta fito kuma a dai dai lokacin Hanan ta furta Ya aurar dani ga wani me kud'i wanda ake sakawa a lissafin masu kud'in Jos wato Alhaji Nasir , Tuni farantin Abincin da Hajiya Asma'u ta d'ebo ya sub'uce daga hannunta , jitayi gabanta ya yanke ya fad'i lokaci d'aya jikinta yafara rawa , dukansu juyowa suna kallonta kafin suce " Lafiya kuwa ? sauri tayi ta dawo dai dai tare da cewa " wallahi sub'ucewa yayi daga hannuna , Nasma da sauri ta mik'e ta nufeta tana fad'in " bai dai fad'o miki a k'afa ba ko ? duban Nasman tayi tana murmushi tace " bai fad'oba 'Yata koma ki zauna zangyara da kaina , sunan da takira Nasma dashi ba k'aramin dad'i yayiwa Nasman ba , sunkuyawa tayi tana kwashewa da hannunta tana xubawa cikin filet d'in , Hajiya Asma'u sai k'ok'arin Hanata takeyi Amman tak'i , saida ta gyara wajen tsaf sannan ta koma ta zauna , nan Hajiya Asma'u ta shiga sa mata Albarka ......
Lab'ewa Hajiya Asma'u tayi dan tanaso taji labarin Hanan d'in , tabbas tanaji a jikinta tamkar Alhaji Nasir d'in data sanine za'abada labarinsa .....

Nan Hanan tashiga bawa Ammi da Zunnur labarin Rayuwar datayi tundaga lokacin da Kawu yazo ya d'auketa , har Auranta da Alhaji Nasir da irin wahalar datasha agidansa da kuma yadda Nasma ke taimaka mata tare da yadda yadunga mu'amalar aure da ita bata b'oye musu komai ba , Kuka sosai Ammi takeyi ita kanta Hanan d'in Kuka takeyi Nasma kuwa hawayene ke zuba a idanunta , Zunnu kuwa tuni idonsa ya kad'a yayi jajir , tabbas da yanzu zaiga Alhaji Nasir baiga abinda zai hana bai kaishi lahiraba , wata muguwar tsanar Kawu Idi yaji ta kamashi duban Ammi yayi wacce take kuka har wannan lokaci yace " kishare hawayenki Ammi , Yanzu ba lokocin kuka bane tabbas nayi Alk'awari sai na d'aukarwa Hanan fansar Abinda Sukayi mata , Hanan ta share hawayenta sannan tace " Abinda ya gudo damu yanzu daga gidan Alhaji Nasir yanzu kuma shine yana tsafi yakeyi da shan jini , kuma yanzuma haka neman mu yakeyi yayi tsafin damu , Ammi ta Hanan tace "Itama wannan d'in Matarsa ce ? Hanan tace " 'Yarsa ce ta cikinsa kuma itama harda ita yakeson Halakamu , duban Nasma Ammi tayi sannan tace " Tabbas ke 'Ya tagari amman baki sa'ar Uba nagari ba , Mahaifiyarki tana ganin tashin hankali dan zama da irin wannan mijin tamkar zama a kabarine , Hanan tace " Batasan Mahaifiyar ta ba tun tana yarinya suka rabu da shi ,

Hajiya Asma'u duk labarin da Hanan takeyi a cikin kunnenta taji komai , Kuka takeyi me cike da murna dan tabbas tasan ko ba'a fad'a mata ba tasan Nasma 'Yar tace wacce tabar gidan Babanta tana 'Yar shekara biyu , da sauri ta fito daga cikin kitchen ta nufi wajen Nasma ta rungumeta tana kuka tana fad'in " tun shigowarki cikin gidan nan naji ajikina tabbas ked'in jininace , ashe kuwa hakan ce Nasma ked'in 'Yatace wacce na haifa da cikina , duk labarin da Hanan takeyi inajinku kugafarce ni bana lab'e dan wani abubu sai dan fitowa ta danayi naji Hanan ta ambaci sunan Alhaji Nasir Jos , to daga nan naji inaso insan labarin dazata bayar , tabbas Alhaji Nasir yadad'e yana aikata zunubi a cikin duniya , Dukansu sakin baki sukayi suna duban Hajiya Asma'u tare da tarin tambayoyi da mamaki a bakunansu , tabbas zasu so jin taya akayi Nasma tazamo 'Yarta ? taya tasan Alhaji Nasir ? ....
Chapter 19 · 0% Book details