← Book details Ni Bora Ce Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 12 OF 23

Sashe 12

Ni Bora Ce Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Gidan Alhaji Nasir yanzu yadawo shuru sosai , dan kowa bayason magana bare hayaniya mussam Hanan , Nasma lokacin ta koma Sch amman hankalinta duk baya kan karatu yana ga matsalar dake cikin gidan su ...
Yanzu Alhaji ya koma basu Abinci me dad'i dan andaina yin tuwo a gidan yanzu , kullum cefane yakeyi me rai da lafiya tare da sakin kud'i wanda har gyara gidan aka kumayi , dai dai da funutures d'in gidan duka saida ya canza musu shi , yara kuma ya yi musi d'inkuna kala kala tare da d'auko malami yana koya musu karatun boko da islamiyya , kud'in da Alhaji yakuma samu cikin satuttukan yana da Uban yawa , a nan Hanan ta kuma tsorata sosai , dan ko baka da hankali inkaga yadda Alhaji ke facaka da kud'i wallahi saika rik'e baki , kusan kullum saiyazowa da Hanan buk'atarsa ta inda yasaba yi , kullum cikin kokawa suke ita dashi dan yanzu tayi mugun tsanarsa , amman dayake k'arfinsu ba d'aya ba haka zai danneta har saiya gamsu......

Safara'u kuwa tunda ta koma gida take k'ulla yadda zata kashe auren ta da Kawu taje ta auri Alhaji ta koro Hanan , Har ita Hanan zata wulak'anta ? tabbas saita yi dana sani yi mata abinda tayi mata , dan inta shiga cikin gidan Alhajin saita kori kowacce mace ta maida Hanan 'Yar aikinta sannan ta dunga juya Alhajin shima kansa , tundaga ranar tafara yiwa Kawu Idi tujara iri iri tamkar me iska , shikuwa tunda yaga haka sai yarage dawowa gida da wuri saitayi bacci......

Yau gidan su Hanan tsit tamkar ba d'an adam , hakan yabawa Hanan damar fitowa daga cikin d'akinta sadaf sadaf , Nasma wacce ta taho zata gun Hanan d'in tana ganin Hanan d'in nayin sand'a sai itama ta b'oye kar Hanan d'in taganta , dan tanaso taga me Hanan d'in zatayi take sand'a haka ?
Hanyar d'akin Daddyn su taga tayi , tunda take bata tab'a ganin anshiga d'akin Babansu ba sai sanda Suwaiba tafad'a musu tashiga , itama samun kanta tayi dabin bayan Hanan d'in har tashe b'angaren nasa , a hankali Hanan take tafiya harta shiga palor sa , tsaruwar da palor yayi tsayawa ma fad'a b'ata bakine , haka tagama kalle kallenta kafin ta fara dube dube tamkar wacce tayi ajiya tazo d'auka , ganin bata samu komaiba yasa tayi gaba zuwa wani d'aki data gani cikin palor , a hankali ta tura k'yauren d'akin sannan tasaka kai , hango wani k'aton gado tayi yasha gyara tamkar ba'a tab'a kwanciya a kansa ba , can tajiyo motsi tawani lungu a cikin d'aki , tsoro ne ya kamata amman ta dake ta tunkari gurin , tana lek'awa taga wata k'atuwar k'warya me zurfin samun kanta tayi da lek'awa aikuwa tayi karo da abinda ya furgitata , da sauri taja da baya zata fasa k'ara , jitayi anyi maza anrufe mata bak'i , take takuma tsorata tana fad'in " shikenan nakawo kaina wajen mutuwata........
[1/29, 16:19] +234 704 610 7812: *NI* *BORA*
_Ce_ 👩🏿‍🦳👩🏿‍🦳

✍🏻 *MD*.

14.

Dukansu sai da labarin ya firgitasu sosai dan Hanan har wata irin zufa ce ke karyo mata , Suwaiba ta share hawayen idanunta tace " wallahi nayi dana sanin auran Alhaji Nasir ba iyaka , ta dubi Hanan tace " kitashi tsaye da ibada dakaiwa Allah kukanki dan kina cikin babban tashin hankali , ni ajikina inajin nakusa mutuwa saboda irin azabar danakeji a cikin jikina , sosai su Nasma suka tausayawa Suwaiba nan sukayi mata addu'ar samun lafiya , mik'ewa sukayi sukayi mata sallama Nasma ta bata dubu biyu tace tasai magani , sosai taji dad'i tare da yi mata godiya suka tafi......

Zunnur tunda yabaro gidan Kawun Hanan yasamu wani Resturen yaci Abinci , yana gamawa yabiya kud'in tare da nufar Hotel dan yakama d'aki ya kwana kafin gobe ya wuce .....

Hanan da Nasma tunda suka fito daga gidan su Suwaiba kowacce takasa magana , suna tafe tamkar kurame Hanan tace " wai yanzu inane gidan k'awar taki dakikace zatayi min kitson ? naga munyi yamma dayawa , Nasma tace " munkusa zuwa dan nima haka wallahi nafison muyi sauri muje tagama miki mu wuce gida , Hanan sauri tayi ta bud'e jaka ta d'auko Nik'af tasaka saboda tanaganin tamkar zasuyi karo da Alhaji Nasir , dan yanzu wani mugun tsoronsa takeji tamkar karta koma , suna tafe har suka iso gidansu k'awar Nasma sunyi sa'a kuwa tana nan , ba wata wata Nana tahau yiwa Hanan kitso , tana gama mata sukayi sallama suka fito.......
Napep suka tare sai dai sun tadda akwai mutum d'aya a ciki , ganin Magriba tayi yasa suka hau batare da b'ata lokaci ba , Zunnur dake cikin Napep yana d'auke da face mark a fuska yad'an b'ata rai ganin anhad'ashi da mata , Hanan ce kusa dashi sai Nasma a k'arshe , Hanan itama Nik'af ne a fuskar ta shiyasa ba wanda yagane d'an uwansa , a haka har suka sauka daga cikin Napep d'in , anan Hanan ta manta da jakarta saboda Sauri kar Alhaji yadawo......

Sai da sukayi nisa da sauka sannan Zunnur yaga jakar tasu , da sauri yacewa me Napep " kaga matan da suka sauka sun manta jakar su , Me Napep yace " sunyiwa kansu ai dan bazan koma neman suba , inka bibiya babu komai a ciki sai kayan kwalliya , Zunnur samun kansa yayi da son ganin meye a cikin jakar , hannu yasa ya d'auka ya zugeta kud'i yagani aciki dubu uku , sai d'ank'aramin mudubi dakuma wani hoto wanda fuskar sa yake a kife , jiyayi yanason ganin hoton hannu yasaka ya d'auko shi yana dubawa yaci karo da hotonsa a bayan hoton an tubuta *ILUV* *U* *YAYA* *ZUNNUR* 🌹 Saikuma a k'asan Rubutun aka saka *By* *Hanan*, wata k'ara Zunnur yayi wacce sai da me Napep yataka burki ya tsaya , da sauri ya juyo yana duban Zunnur sannan yace " lafiya kuwa Malam irin wannan k'ara ? Zunnur yace " Plss dan Allah ka juya mu koma wajen da ka'ajiye Matan nan wallahi Ko nawa kakeso zan k'ara maka , Me Napep ya dubi Zunnur yace "saboda me me gida zan koma ? Zunnur ya nuna masa pic d'in sannan yayi masa bayani a cikin jakar yagani tabbas yasan wacce yake nema ce , tuni me Napep ya gamsu da hujjar Zunnur ya juya zai koma wajen da ya'ajiye su Hanan........

Hanan itace tafara shiga cikin gida , tayi sa'a batasamu kowa a tsakar gidan ba har ta shige d'aki , tana shiga d'aki tacire hijab d'inta a nan ta tuna da jakar ta , take gabanta ya fad'i Allah yasa dai ba a Napep ta manto jakar nan ba ? Babbar damuwarta itace hoton ya Zunnur datake ajiye dashi tuntuni , kullum dashi take kwana a kan k'irjinta ta riga tasaba indai a Napep tabaroshi shikenan tadaina bacci me dad'i , fitowa tayi ko Allah zaisa ace jakar na gurin Nasma ta d'auko mata , tana fitowa sukayi kicib'us da Hajiya Hajjo . Dubanta Hajiya Hajjo tayi sannan tace " kindawo shine bakije kinfad'amin kindawo ba ? Hanan cike da jin tsoro tace "yanzun nan nadawo kuma dama fitowa nayi nazo nafad'a miki nadawo , Hajiya Hajjo ta zubawa Hanan ido tana nazarin ta kafin tace " kije kitchen ki kad'a mana miya dan itace ba'ayi ba , Hanan tace " to cike da girma mawa sannan ta juya ta tafi .....

Zunnur suna k'arasowa wajen da suka ajiye su Hanan yafito , dubasu ya shiga yi lungu lungu amman babu ko masu kama dasu , dayake unguwar duk manyan gidaje ce dan haka bata da yawan Jama'a , haka suka gama dube dubensu batare da sunga me kama dasu Hanan ba ma bare su , hak'ura Zunnur yayi tunda dare yayi ya nufi Hotel dan kama d'aki saidai Jakar tana gunsa dan bazai iya rabuwa da itaba.......

Hanan harta k'arasa kad'a musu miya amman duk yanayin ta babu dad'i , gashi tunda tashigo bataga Nasma ba haka tagama ta nufi d'akinta tashiga wanka , tana fitowa tanemi wata riga marar Nauyi tasaka sannan ta kwanta , tunane tunane tunane tashiga yi akan zamanta a gidan Alhaji Nasir , tabbas ta tausaya wa Suwaiba mutuk'a Amman yanzu itama abar tausayice , yau kwata kwata bataje gurin da suke had'uwa suci Abinci ba dan ko yunwar bataji , tunaninta guda d'ayane shine Aysha dan tasan zata dunga nemanta taga bata ganta ba ....

Washe gari suka tashi dawata annoba a cikin gidan nasu , guda biyu daga cikin yaran Alhaji antashi dasu duk sun sank'ame ga wani jini nafita ta k'asansu da kuma bakinsu , kafin kace me tuni sunce ga garinku nan , tuni gida ya cika da koke koken mutuwa , sauran yaran gidan sai kuka sukeyi na rashin 'Yan uwansu , tashin Hankalin da Hanan tashiga ita da Nasma yayi yawa , tuni suka keb'e waje guda suka fara tattaunawa akan Mutuwar yaran....

Hanan datake sharar hawaye tace " wallahi nafarajin tsoron zama a cikin gidan nan , cikin mutuwar wannan yaran wallahi akwai lauje cikin nad'i , Nasma taja Numfashi tadubi Hanan sannan tace "Nikaina al'amarin Daddy yafara bani tsoro , tunda aka haifeni a cikin gidan Nan Ummata ta ajiye ta fice daga cikin gidan nan har yanzu bansan a inda take ba , a gurin Hajiya Hajjo nataso tun ina k'arama na saba da wahalhalun cikin gidan nan har na girma , ba kalar matar da bangani a cikin gidan nan Daddy ya aura ba , nasha ganin tashin hankali kala kala amman bantab'a cin karo dana yau ba , tabbas Mutuwar Abbas da Faruq akwai lauje cikin nad'i , kuka itama takeyi dan tana son k'annan nata duk daba uwa d'ayace ta haifesuba , Suna zaune suna tunanin yadda zasu b'illowa lamarin cikin gidan sukaji ana ihu.......
[1/29, 16:19] +234 704 610 7812: *NI* *BORA*
_Ce_ 👩🏿‍🦳👩🏿‍🦳

*Zee* *MD* ✍🏻

17.
Chapter 12 · 0% Book details