← Book details Ni Bora Ce Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 6 OF 23

Sashe 6

Ni Bora Ce Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

A gidan gaba na zauna har mukaje shagon saida sark'ok'i da zobunan azurfa da gwal , Fitowa mukayi nidashi muka jera har cikin wajen , kowa dake wajen idansa akanmu , harda wad'an da basa iya shuru sai sun taka suka fara fad'in " wannan had'in yayi kyau sosai Allah yabaku zaman lafiya , nifah duk abinda suke fad'i ba ganewa nakeyiba shiyasa banwani damuba , wani glass Ya Zunnur ya bud'e yana d'auko wani Zobe me shegen kyau har wani d'aukar ido yake , Hannu na naji ya rik'o yana k'ok'arin sakamun , yana samun kuwa zoben ya zauna daram tamkar danni akayishi , Abinka da fararen yatsu dogaye dasu take suka d'auki wani kyau sosai , Ya Zunnur wani murmushi yayi yana duban hannun , sai wata a zurfa daya d'auko me farkon Sunan Z ajiki yasamun a hannu , sai kuma yasa wata me farkon sunan H yacemin " in ansa insaka masa , ina ansa ya mik'omin hannu nasaka masa , take 'Yan wajen suka fara tafa mana suna fad'in " wannan Abu yayi Allah yabar Soyayya , duk jinayi kunya takamani nayo waje da sauri ina Murmushi , Kud'in zobunan ya biya sannan yafito muka tafi.....

Washe gari tun sassafe suka shirya muka rakasu har filin jirgi suka tafi , duk yadda muke murna da tafiyar su musamman ma Ya Zunnur saida mukaji rashin dad'i lokacin da mukaga sunhau jirgin suntafi , muna dawowa gida nakoma duk wata mara sukuni , Afrah sai tsokana ta takeyi wai ina kewar Masoyina , samun kaina nayi da duban zobuna na wanda yasaka min su musamman me farkon sunan Z d'in.....

Bayan kwana biyu da tafiyar su Ya Zunnur katsam saiga Kawu Idi yazo , da kwatance yazo gidan su Ya Zunnur , lokacin har nafara zuwa sch nida Afrah , Bayan sun gaisa da Ammi yafara yi mata fad'an yayi shuru shuru munk'i dawowa shiyasa yazo yaga ko lafiya ? Nan Ammi take gaya masa ai Yayan ta yace bazasu koma ba anan zata zauna , Nan Kawu yayi tsalle yace sai dai ita ta zauna ita kad'ai tunda itace tazama dolen sa , Amman nikuwa k'afata k'afarsa bazai bar 'yar gidan 'Dan uwan sa ta taso a wani garin ba , Nan yadung sababi Ammi ita kuwa banda kuka ba abinda takeyi , tabbas tasan za'ayi hakan , shiyasa kullum cikin zulumi take tana tunanin Yadda rayuwar Hanan zata kasance gidan Kawun nata , da k'yar Kawu Idi yayi kwana biyu a gidan nan yace in shirya zamu wuce.......

*Littafina* *Na* *Kud'ine* *Ne* *Duk* *Meso* *Yamin* *Magana* *Ta* *Wannan* *Number* 07046107812 *Kuyi* *k'ok'arin* *Mallakar* *Naku* *Akan* 200 *Kacal* _kusiya_ _kukaranta_ _Cikin_ _Aminci_ 🤝🏻🥰

*Nagode* *Masoya*

*'Yar* *Mutan* *Kanawa* _Ce_ 😍🌹
[1/29, 16:19] +234 704 610 7812: *NI* *BORA*
_Ce_ 👩🏿‍🦳👩🏿‍🦳

*Na*
_Zee_ _MD_ ✍🏻

*Hamdala* *Writer's* *Association* 💪
https://www.facebook.com/111403834371046

✨✨ *{{* *H.W.A* *}}*✨✨

*Bisimillahir* *Rahamanir* *Rahim*

*Littafina* *Na* *Kud'ine* *Duk* *Meso* *Yamin* *Magana* *Ta* *Wannan* *Number* 07046107812 *Kuyi* *K'ok'arin* *Mallakar* *Naku* *Akan* *Naira* 200 *kacal* *kukaranta* _Cikin_ _Aminci_ 🤝🏻🥰

🆓 page. 8

Washe gari duk Hanyar danasan zata had'ani da Ya Zunnur nak'i binta , yini guda ina cikin d'aki sai k'arya nayi nace ciwon Kai nakeyi , har magani Umma takawomin tasani agaba sai dana sha , Ammi na tana can d'akin da aka sauke ta , ko lek'owq batayi taganni ba danagaji da zaman d'akin dole na fito nashiga d'akin Da Ammina take , sai dai me ina shiga naga wanda nake gudun had'uwa dashi a zaune suna hira da Ammi , har zan juya naji Ammi tace " Hanan ina zakije kuma ? bakiga nida Yayan ku bane ai bawani bak'o bane kinsan shi , shigowa nayi jiki a sanyaye nasamu guri na zauna , Dubansa nayi nace " Ina yini Ya Zunnur ? tamkar gonar auduga haka ya bud'e baki yana dariya ya amsa min , ni abinma mamaki yabani natsaya ina dubansa , mutumin da ko murmushi bayayi amman shine da wannan fara'a , na dubi Ammi nace " shine ko kizo dubani Kinjini shuru ko ? murmushi tayi tace " ai gaki yanzu kinzo ke kuma nasan lafiyarki k'alau , turo baki nayi ina cewa " nidai Ammi dan Allah gobe muhad'a kayanmu mutafi nifah nafara gajiya da garinnan , tuni naga fuskar Zunnur ta canza tamkar anyi mishi albishir dawani mugun Abun, jinayi yana cewa " Ammi indai ita tagaji ahad'a mata kayanta gobe Haidar yaje yakaita , sannan ya dubeni yace " ita kuma Ammi tadawo kenan dan baza mubarta ta koma Jos ba , daman shirin tafiya taho da ita muke kuma yanzu tazo kenan , shuru nayi masa batare da nace komai ba ....

Bayan Zunnur yafita nadubi Ammi wacce naga tayi nisa a dogon tunani nace " wai lafiya kuwa Ammi ? yaufa kwata kwata naga bakya cikin walwala ko wani Abunne ? Murmushi Ammi tayi sannan tace " Hanan d'azu dasafe munyi magana da Yaya wato Abban su Zunnur kenan , yace bazan koma Jos ba , dole sai dai nazauna a gidan nashi har Allah yakawomin miji nayi aure , babu irin rok'on danayi masa Akan ya hak'ura yabarni sai na aurar dake nadawo yace "bazai yadda ba , kuma kema yace makarantar da Afrah ke zuwa ita za'a samar miki kidinga zuwanta , shuru nayi ina sauraran Ammi , Taci gaba da magana " ni bada muwata zaman dazanyi ba a'a kawai ina tuna Kawun ki inyaga munk'i komawa dole zaizo yace saiya d'aukeki , tunda akwai lokacin da Yayan yace sai nadawo nan d'in dazama wallahi dana gayawa Kawun ki cewa zamu tafi da Yaya cewa yayi " wai inna tashi tafiya inbar masa ke a wajensa , kece kad'ai wacce yake kallah yaji dad'i saboda rashin d'an uwan sa , Tuni idanun Ammi suka kad'a sukayi Ja tamkar zatasa kuka , nima cikin zuciyata tuni nafara jin babu dad'i , tabbas zanso zaman garin nan Amman mutuk'ar Zunnur yana gidannan nikam bazanyi walwala ba , kuma banajin zanbi Kawu nabar Ammi na anan garin bazan iyaba , shurun da Ammi taga nayi yasa ta dafamin kafad'a tace " tun muna yara indai Yaya yayi magana ba'a musa masa , dan haka nasan zaiyi wuya na koma Jos dazama , addu'a ta d'aya yanzu itace " Allah yasa Idi ya amince kiyi zamanki a nan wajena , Dubanta nima nayi sannan nace " Ammi kece fa kika haifeni kinfi kowa iko dani a halin yanzu , taya za'ace wani zai miki iko da abinda kika haifesa ? Ammi tace " karki k'ara kiran kawunki wani Hanan , kinsan duk tak'amar mutum dole da dangin Uba zaiyi ado , a yanzu in aka tashi aurenki bawanda za'asamu sai shi , inhar kinga mun aurar dake to kitabbatar da Babu ran Kawunki , yana da iko akanki tamkar 'Yar cikinsa , saboda bakida kamarsa a dangin Mahaifinki cikinsu d'aya da Mahaifinki , Shuru nayi dan jikina ya riga dayayi sanyi , tabbas Nasan abu me wuya ne ace kawu ya yadda na zauna a gun Ammi na , Amman zamuga yadda Allah zaiyi damu nida ita......

Kwana biyu wasan b'uya mukeyi da Ya Zunnur , duk inda zanbi nagansa yanzu banabi , Afrah kuwa duk gidan yamata rashin dad'i , saboda Ya Zunnur yakasa ya tsare ko k'ofar gate bata zuwa , Yauma muna Zaune nida ita tana ta mitar wayar ta da Ya Zunnur ya k'wace saiga Ya Haidar ya shigo , kallon mu yayi yace " Hy 'Yan mata ya kuke ? Murmushi nayi nace " Ya Haidar abin harda tsokana kuma ? shima Murmushin yayi yace " kutashi kushirya kurakani ganin gari tare da partyn Abokina , aikuwa da sauri Afrah ta mik'e tana fad'in " da gaske Ya haidar damu zakaje ? ya kalle ta yace " kefa har yau bakya girma sai na jiki , da wasa nake muku kenan ? tuni muka mik'e dan canza kaya daman munyi wankan mu , fita yayi yace musa mesa cikin motarsa ......

Dukan mu shiryawa mukayi cikin wani Less me mugun kyau , Abban su ne ya d'inka mana shi iri d'aya nida Afrah tamkar 'Yan biyu , Abinda nafita shine haske da tsayi , ita kuma ba fara bace choculate kala ce , tana da jiki amman ba sosai ba , kayan sunyi mana kyau sosai d'inkin riga da siket ne kowacce ya zauna a jikinta zam , takalma masu tsini mukayi amfani dasu , sai maya fai kalar takalmin mu ba k'aramin kyau mukayi ba , muna fitowa ya dube mu yace " wow kyawawan k'anne na tabbas zaku fito dani bari muyi pic , wayar sa ya d'auko k'irar Samsung yafara yimana pic , fukan mu sai da muka d'auka tare dashi sannan yayi mana dani da Afrah muka tafi......
Chapter 6 · 0% Book details