← Book details Ni Bora Ce Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 15 OF 23

Sashe 15

Ni Bora Ce Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Bayan anyi sadakar Ukun Aysha komai ya lafa , amman duk wanda zaka gani a cikin gidan Alhaji Nasir a tsorace yake , walau Babba walau yaro kowa yatsorata da gidan , Yauma kamar kullum dare yayi kowa ya koma bacci da ido d'aya , yaran ne masuyin bacci saboda yarinta , Hanan da Nasma suna kwance amman ko wanne a cikinsu tunani yakeyi , dan rabonsu da bacci tun randa Aysha ta Rasu , wajen k'arfe d'ayan dare sukaji anbud'e k'ofar d'akin dasuke ciki , tuni suka mik'e tare da kashe k'wan d'akin , da sauri Hanan tace " Nasma shikenan muma kashemu zaiyi wallahi Alhaji ne , Nasma ta toshewa Hanan baki a hankali tace " bazai kashemu ba insha Allah zo mushiga toilet mufita ta windor ciki , a hankali suka sauko daga kan gado rik'e da Hannun juna suka shige toilet d'in , suna shiga sukayi maza suka saka masa sakata sannan suka nufi wajen windon ciki , Hanan tace " wannan windon yanzu kina ganin zamu iya fita ta cikinsa ? Nasma tuni ta taka kan tudun abin wanka tafara k'ok'arin b'allo glass d'in , Hanan itama takowa tayi tahawo wajen tafara taimakawa Nasman , aikuwa dai dai lokacin glass d'in ya yanki Hanan tayi wata k'ara da sauri Nasma ta toshe mata baki gudun kar aji suna ciki , aikuwa sai ji sukayi anfara girgiza k'ofar Toilet d'in ..........

*Juma'at Kareeem Mutanena* 🤝🏻🥰

*Karku Manta da Karanta Suratul Khafi Aya Gomar Farko*

*Yin Salati Ga Shugaban Halitta Annabi Muhammad S.A.W*🙏🏻🙏🏻

*'Yar Mutan Kanawa* _Ce_ 🌹😍
[1/29, 16:19] +234 704 610 7812: *NI* *BORA*
_Ce_ 👩🏿‍🦳👩🏿‍🦳

*Zee* *MD* ✍🏻

20.

Da sauri Nasma ta dubi Hanan tace " meye hakan ke kuma kodai bakya gani ne ? sai a lokacin Hanan ta dawo dai dai tana maida numfashi , maganar Direbance ta katsesu yace musu " Bayin Allah ku kuwa me kukayiwa wad'an can garadan mazan suke binku ? Nasma tace " wallahi babu abinda mukayi musu kawai 'yan iska ne , Dayake gari bai fara haske ba shiyasa har suka shigo cikin tasha Hanan bata kula da wanda ta fad'a jikinsa ba , suna iso ciki kowa ya fito daga cikin motar Hanan tadubi Nasma tace " kinsan a koda yaushe Alhaji zai iya sakawa a kuma biyomu, wallahi da da kud'i a hannun mu da Lagos zamu tafi wajen Ammi , Nasma tace " yanzu yadda za'ayi muje gidan Kawun ki sai mugaya masa komai kozai samo mana mafita , Dasauri Hanan ta dubi Nasma tace " anan gurin dai baki kawo shawara wacce zata yiwuba , ai zuwan mu gidan Kawu tamkar komawace gidan Alhaji Nasir , dan ko me zamuce wallahi Kawu bazai yadda ba......

Shuru sukayi suna nazari dan basu san ta yadda za'ayi suje Lagos ba , can Hanan taga giftawar wani Saurayi ta kusa dasu zai wuce , da sauri ta mik'e tana nufar wajensa tana fad'in " Dan Allah bawan Allah muna neman taimakon ka , juyowa yayi saboda jin muryar wacce a ko yaushe yake mafarkinta , aikuwa Idanunsu suka had'e waje d'aya , da sauru Zunnur yace " Hanan kece haka ? Hanan batasan sanda tafad'a jikinsa ba tare da fashewa da kuka wanda batasan na meye ba......

Yaran Alhaji Nasir tuni suka kirasa a waya suka gaya masa komai daya faru , cikin fusata yadunga yi musu fad'a akan sakacin dasukayi har su Hanan suka gudu , Anan suka yi masa Alk'awarin zasu duba kaf cikin gari dan nemo masa su , kashe wayar yayi batare da yace komai ba tabbas yayi mugun sake da har yabari su Hanan suka san sirrinsa , dole zai nemosu duk inda suke a fad'in Nageria jininsu ya riga dayayiwa dodonsu Alk'awarinsa..........

Da k'yar Hanan ta saki Zunnur tana share hawayen murna , dan yazo musu a lokacin dasuke da buk'atarsa , Nan yajasu gefe yana dubansu yace " dama kune aka biyoku kuka shigo cikin motar mu ? Nasma tace " mune . Zunnur yace " me kukayi musu haka suke binku kuma ke Hanan ai ance anyi miki aure ina mijin naki yake ? Nasma tace " wannan zancen ba na nan bane yanzu dai dan Allah ka kaimu wani gurin ka b'oyemu , da sauri yadu besu yaga jikinsu duk yabaci gashi kowacce da ciwo a jikinta , cikin zuciyar sa yafara tunanin yanzu ina zai kaisu Kano ko kuma Lagos ? wata zuciyar tace inka kaisu kano a inah zaka ajiyesu kawai ku nufi Lagos , da sauri yadubesu yace " kujirani Anan ina zuwa yanzu zandawo , da sauri ya juya yanufi cikin tasha lokacin har mutane sunfafa fitowa , wani P.O.S na cikin Tasha yashiga Nan ya kira wani Abokinsa yagaya masa ya turo masa kud'i , Baijima ma ya turo masa kud'in nan ya ansa tare da nufar wani guri yasiya musu Hijabai manya dan kayan jikinsu ma duk sun yage , koda yadawo samunsu yayi cikin wani lungu wanda ba yawan mutane , basu Hijab d'in yayi yace susaka sai su tafi , ansa sukayi suka saka sannan yabasu face mark shima suka saka nan suka bar cikin Tashar , a hanyarsu ta fita daga cikin tashar sukayi karo da Yaran Alhaji sukuma zasu shigo......
Ta gaban su Hanan suka wuce batare da sun gansu ba , su Hanan suka kuma tsorata sosai Zunnur yace " ku nutsu kar kuyi abinda zaisa aganeku , haka suka hau motar yace akaisu airpot dan Lagos yakeso su nufah.....

A can b'angaren Ammin Hanan kuwa tashi tayi da zazzab'i da Amai , dan haka ta d'aga tafiya zuwa gobe ko jibi intaji sauk'i , sai dai tunda tatashi gabanta yake mutuk'ar fad'uwa , kwata kwata batajin dad'in komai , Hajiya Asma'u tana ganinta hakan ta anshi aikin girki tace mata taje ta kwanta ta huta ......

Tafiyar Awa d'aya da Rabi sukayi a jirgi suka isa Lagos , sosai Nasma take mamakin garin Lagos d'in , mutane sutacewa akwai cunkoso a lagos babu gidaje masu kyau to itadai bata cunkoso ba sai kyau da kuma tsaruwa, Tunani Zunnur ya shiga akan inah zai kai su yanzu gidansu ko kuma gidan Ammi , kawai ya yanke ya kaisu gidan Ammi tunda yasan gidan daman , hawa motar da zata kaisu gidan Ammi sukayi suka nufi can , Hanan batasan inah zasuje ba tunda basanin gari tayi ba kawai dai jitake kamar ta mik'e ta hau taka rawa saboda farin cikin zataga Ammin ta , duk wata fargaba da suka taho da ita kwata kwata babu a gun Hanan dan har wani murmushi takeyi da jin dad'in zataga Ammin ta yau.....

Alhaji Nasir tuni ya hau motar sa ya nufi gidan Kawu Idi , tunani yakeyi ko su Hanan suje can su gaya masa abinda yafaru dasu....
Yana zuwa yasamu Kawu Idi yana k'ok'arin fita , yana ganin motar Alhaji ta tsaya yafara fara'a ya nufi wajen motar , Alhaji Nasir ya fito fuskar sa kadaran kadahan ya mik'awa Kawu hannu sukayi musabiha , Kawu yace " ina fatan dai lafiya ba Wannan ja'irar yarinyar ce tayi ma wani Abunba ? Alhaji Nasir najin haka yasan Hanan basuzo gidan Kawu ba , wata zuciyar tace " kodai sunzo sunfad'a masa shine yakeso ya raina masa hankali , gyara murya Alhaji Nasir yayi sannan yace " daman neman su nazoyi ita da yarinyar wajena , dan tuntuni suka gudo daga gidan ba inda ba'a duba ba amman ba'a gansuba shine nayi tunanin ko sunzo Nan , salati Kawu Idi ya shiga yi yana duban Alhaji sannan yace " wallahi basu zoba amman lafiya kuwa suka gudu ko wani laifin suka aikata ? Alhaji Nasir yashiga shirgawa Kawu k'arya ganin baisan komai ba yace " wallahi sunyiwa Uwargidana duka akan rabon Abinci , kuma ni ba dukan da sukayi bane damuwa a'a ba'asan inah suka nufa ba shine damuwar , ko kuna da wasu 'Yan uwan a nan ko can sukaje ? Kawu yana salati yace " tabbas wannan aikin Hanan ne itace zata kawo wannan banzar shawara ta dukan Hajiyar , Maganar 'Yan uwa kuwa bamu da kowa sai dai gidan su Safara'u me d'akina , dan ko ita Uwar Hanan d'in kasan na fad'a maka cewa tana can Lagos wajen d'an uwanta , kuma bana tunanin zasu gudu can d'in , sai dai ko ita yarinyar wajen naka ko tajata sunje danginka , Alhaji Nasir yace " gaskiya ba wasu dangina da Nasma ta sani bare suje , amman kakira min me d'akin naka kozata yiwa 'yan gidan nasu waya muji , da sauri Kawu Idi ya nufi cikin gida dan yiwa Safara'u magana........
Chapter 15 · 0% Book details