← Book details Nawaff Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 50 OF 51

Sashe 50

Nawaff Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read

Da hakadai suka fara shirin tafiya Spain wanda da 'kyar papa ya yarda atafi da yasmeen amma da sharaďin idan cikinta yakai wata takwas zai dawo da ita gida ta haihu, da sauri ya amince kuwa.
Suka fara shirin tafiya,, ya kaita gidansu ta wuni acan tayi musu sallama, gidansu mas'ud ma yini tayi, ranar juma'a suka ďage cike da kewar mutanen 9ja, suma sun barsu da kewarsu, dan tunda suka tafi gidan kamar anyi mituwa kowa yayi sukuku, har papa daba zama yake sosai dasuba shima sai yaji gidan yay masa wani iri.
Ya ce, "ummulkhairi kinga daga tafiyar yarannan yau har gidan yazama wani iri gashi babu auta, dagamu sai Abdallah sarkin rashinji, momcy tayi dariya wlhy Alhaji har wani zazza6i nakeji fa, Abdallah ma saida yasha magani yana ďaki kwance, shiyyasa akace sabo akewa kuka ba mutuwaba, balle yasmeen yarinyace mai shiga rai sosai.
Papa ya ce, "gsky ne yarinyar tanada ha'kuri gatada girmama nagaba da ita,, wlhy danma ba zaman gida kakeyiba shiyyasa, amma modebbo ya dace da mace tagari mai addini kam.
Papa yay dariya aidama haka ALLAH ya ke, sai yabaka abinda bakaso yazama alkairi arayuwarka, idan na tuna randa na sanarma modebbo auren yarinyarnan tamkar zai kwala min ihu koya hau bori, saiya bani dariya randa nace baxai tafi da ita Spain ba tamkar zai min kukafa, momcy ta tuntsure da dariya, itama ďin yasmeen kalar marasa lafiya tazama, shiyyasa nace kawai kabarsu su tafi, cikin yana shiga wata takwas idanma bai kawotaba ni zanje na ďakkota ne aii.
To ALLAH ya kaimu lokaci, yakuma sauketa lafiya,, ameen momcy tafaďa.

Sumadai ALLAH ya saukesu lafiya, suna zuwa barcin gajiya yasmeen tashiga yi, gashi dama jikinta babu 'karfi, Nawaf kam fita yayi dan yanada abubuwan yi masu yawa.
Tadaďe tana barci, saida ta warware a gajiyar data kwaso sannan ta mi'ke da addu'a abakinta, wanka tashiga tayi a haďaďan bathroom ďin, azuciyarta ta ce, "kaga masuyi dan ALLAH, wannan bathroom haka ai ďakin watane a 9ja, tagama wankanta tafito tayi shiri cikin 'kananun kaya, tana cikin fesa turare Nawaf yashigo rungumeta yayi tabaya suna kallon kansu amadubi, ya ďora hannunsa saman cikinta yana shafawa, my baby kabaro 'kasarka zuwa wata 'kasa wadda ta ri'ke maka dadyn ka ko?, yasmeen tayi dariya, to dadyn nasa yabarta mana, gefen wuyanta ya sumbata yana faďin inhar momy ta amince anjima ma saimu ďauki hanyar 9ja.
Hannu tasa tana shafo fuskarsa sunama juna murmushi ta madubi, ta ce, "A'a ban aminceba muyi zaman mu, Nawaf yatashi tsaye yana dariya to zomuje kici abinci babyna yanajin yunwa.
Falo suka koma dakansa yabata abincin taci sosai kuwa, ta ce, "lallai andace, tashi ďaya kikaci abincin nan batareda kin kusheshiba balle yatsina fuska.
Yasmeen tayi dariya nifa wlhy bammasan ina yatsina fuskaba idan banason abinci, okey bari sai ankawo wanda bai mikiba idan kinayi zan ďauki hotonki, kace terere zakami kenan?, babu wani tarere Nawaf yafaďa yana gyara wajen.
Haka rayuwarsu ta Spain tacigaba da tafiya cikin soyayya da jin daďi, suna bama juna kulawa, cikin yasmeen yanata girma, yakan fita yawo da ita taga gari idan yasamu lokaci, idan zasuje wata 'kasar buga wasa da'kyar suke rabuwa idan kuma tafiyar ta wuce kwana biyu to tare suke tafiya.
Komai yana tafiya musu yanda sukeso, suna waya da 'yan 9ja sosai, dakuma su yaseer, kosu haďu a yanar gizo, yasmeen tayi 'kyau abinta tayi 6ul2 ga cikin yayi mata 'kyau, mijinta yana kula da ita dabata farinciki, dan mace mai ciki tana bu'katar kasancewa cikin farinci.
To yanzu cikin yemeen yashiga wata na takwas, momcy fa tafara damun Nawaf da zuwan yasmeen gida, kwata2 bayaso yasmeen ďin tatafi saboda shi bashida damar zuwa 9ja yanzu amma yazaiyi, dole ya ďauki uzuri na kwana ďaya yakawota 9ja ya juya.
Su momcy sunyi farincikin ganinta, sosai nannama kulawa aka shiga bata ta musamman aďaki momcy take zaune, tunda cikinta yashiga watan haihuwa momcy tadawo kwana ďakin dan kar haihuwa ta risketa batareda an saniba.
Awata safiya litinin yasmeen ta tashi da na'kuda babu 6ata lokaci momcy ta kwasheta zuwa asibiti, kar6arsu akayi cikin gaggawa dan haihuwarce gadan2, Alhmdllh yasmeen ta zullu'ko 'katon ďanta maikama da ubansa namiji, karkuso kuga murna wajen wannan family, Abdallah yafara kiran Nawaf yasanar masa, tsalle yaytayi namurna gashi zasu shuga wasa alokacin, wannan farincikin ne yasashi nuna bajinta awajen wasan, saida ya zura kwallo sau uku, wannan lamari yayima koch nasu daďi ba kaďanba.
Tuni hotunan baby boy sun cika masa waya, kowa sai turo masa yake takafa sada zumunta, yaro ďan gatan dangi, zuwa yamma aka sallamesu dan komai normal, sundawo gida yayinda 'yan uwa da abokan arzi'ki suketa tururuwa wajen ganin ba'kon duniya, tsaf aka shirya yaro cikin kayan sanyi masu 'kyau da laushi, yasmeen ma tashirya tsaf tagyara jikinta, bayan taci ta'koshi ta haye gadon momcy.
Tana kwanciya wayarta tahau 6urari, cikin murmushi ta ďauka, cikin kissa ta ce, "ALLAH yabarni da baban baby,, Nawaf yasaki wani lallausan murmushi kamar yana gabanta, ameen dear fancy face, ina fata dai kina cikin 'koshin lafiya, keda sweet babyna ?, yasmeen tayi murmushi lafiya lao muke habibina, ykk kaima??, ya ce, "nima Alhamdllh, sannu da aiki fancy face nagodema ALLAH kema kuma nagode miki da kika haifomin 'katon ďana zuwa duniya,, yasmeen tayi dariya, kai habibina kaida baka gansaba ya akayi kasan 'katone??, yayi dariya lallai fancy face ai inagama narigaki ganinsa, aituni Abdallah da mas'ud suka sambaďo mini pic nasa, insha ALLAHU duk yanda zanyi sainayi nazo 9ja nextweek, to shikenan habibina ALLAH yakawo mana kai lafiya.
Amin xarah na yanzu ina babyna samin naji numfashinsa mana, hhhh ai yana falo wajensu momcy nikuma ina ďaki kwance,, ya marairaice murya to kije falon mana, ido tazaro lah habibina sokake ace banida kunya babu ruwana wlhy.
Yay dariya to sarkin kunya yizaman ki kar ace bakida kunya, amma kiďau al'kawari da an maidoshi kiyimin vedeo ďinsa ki turomin, karka damu naďau al'kawari, daganan hirarsu suka cigaba dazubawa cikin so da 'kauna, sun daďe suna hira, sannan suka kashe, ana kawo baby ďakin kuwa tacika al'kawari tayi video ta tura masa, tsalle yaytayi yana kallo saikace wani 'karamin yaro, ranar abinda yakwana yi kenan, haka yayta kallo yana maimaitawa.
Haka rayuwar take gudu da sauri, yasmeen tana ta jego, hargashi gobe suna, aranar kuma Nawaf ya iso 9ja, dangi sunyi farincikin ganinsa, shima yayi farincikin ganinisu, yarungume ďansa yana maijin 'kaunarsa jiyake kamar yatsaga jikinsa yasakashi, ranar ahanununsa baby ya wuni, da daddarema saida momcy ta koreshi waida nan zai kwana wajen yasmeen.
Washe gari akayi suna yaro yaci sunan MUHAMMAD ubangiji ALLAH yaraya muhammad amin, bayyana muku yanda sunan yakasance 6ata lokacine amma nabawa kowa dama ya kiyasta azuciyarsa, shagali akayi bana wasaba, hardasu hajja 'yan saudiyya,, lallai munra'kashe mun kwalle ranar💃💃💃💃💃kai harma 6arararrajewa mukayi, lol😜.
Bayan sati ďaya dagama suna Nawaf yakoma, yabar su yasmeen suna jego abinsu.

Sunyi arba'in yayinda yaro yayi 6ul2 abin sha'awa, nisainajima kamar subani😘😜lol, su yasmeen an zagaya dangi ko 'ina, kowa yana sambarka da wannan yaro.

Bayan wata uku.
Nawaf yadawo gida hutun 'karshen shekara, tarairayar yaronsa yake sosai, damma wani lokacin su momcy suna masa fin 'karfi saisu kwaceshi ya wuni awajensu shan nono kawai yakesa akawoshi wajen yasmeen, idan papa yana gida shima saiya kwace saikaga kowa yana zum6ura baki, dan kowa yanason ďauka, amma dole ya ha'kura tunda papa ya amsa, na ce, "kaga ďan dangi yanashan tarairaya,, hakadai rayuwa taci gaba da tafiya MD yana girma da 'kara wayo, dole su Nawaf suka barma su momcy, suka koma nunama juna soyayya da fatan suma ALLAH yabasu wani.
Chapter 50 · 0% Book details