← Book details Nawaff Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 22 OF 51

Sashe 22

Nawaff Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

________________________________ a6angaren yasmeen kuwa sai la'asar ta farka, tayi mamaki data ganta akan gado, itadai tasan ba'a nan ta kwantaba, zata iya cewama tundaga randa aka kawota batasake hawa gadon nanba da niyyar kwanciya, saidai kawai ta gyara masa.
Bayan tagama mamkinta ta sakko, wajen madubi taje tana kallon fuskarta, la66anta sunyi fushi sosai, ta ce, "ALLAH yasaka mini mugu kawai, tunda nake arayuwata banta6a ganin mugun mutum irin Nawaf ba, ruwa zafi taje ta ďebo a kichin, awani ďan bokiti, tazo tazauna gaban mudubi, tasaka wani hankacif ďinsa ta gasa bakinta,, dukda zafin datakeji haka tadaure tana hawaye ta gasa, saida taji ruwan ya huce sanan ta ha'kura, tashiga wanka.
Tafito tayi sallar la'asar, ta shirya tsaf cikin doguwar jalla biya ba'ka, mai duwatsu.
Falo tafito taci abincin, da momcy ta aiko musu, dama har yanzu bata fara abincin ranaba, saidai na safe, da daddarema ba girki sukeyiba, dan kowane daren duniya kayan fruit ne abincin Nawaf, sukaďai yakesha sai shayi na 'ka'ida, wanda saiyasha sau goma arana batareda ya isheshiba😜.
Ta kammala cin abincinta tadawo falo, yasmeen bata cika damuwa da kalloba, idan itace sai ayi sati ba'a kalli tv ba, dan haka tai kwanciyarta saman kujera tana game a waya.
Yaseer ya kirata awaya, taďaga cikin fara'a tana faďin ďan 'kanina nayi missing ďinka wlhy.
Ya ce, "nima haka sisto na, ykk?, ya gida?.
Ta ce, "komai lafiya Alhmdllh, ka'ki kazo ko??.
Karki damu zanzo, school ce ke hanani wani motsi wlhy, amma zuwa weekend zaki ganni.
To ALLAH ya kaimu lfy, yasu ummana da abba??, suma duk suna lafiya wlhy, aii yanzu su yaya Nawaf suka tafi, tun ďazu suke anan.
Yasmeen taishiru azuciyarta ta ce, "mugu, wato bayan yagama mini mugunta ashe gidanmu yaje, taďan murmusa koba komai taji ďaďi...........yaseer ya ce, "hello sisto kina jina kuwa??.
Saida tayi ajiyar zuciya sanan ta ce, "ina jinka, ka ce, "tunďazu yake anan??, eh, shida yaya mas'ud sukazo, bakiga alherin daya kawo manaba wlhy, ki 'kara yimana godiya, gsky aunty kin more miji..
Hummm to uban 'yan surutu anji, yaseer yay dariya, kai sistona daga faďar gsky, ina aunty amina??, tana gidanta itama nima bamu haďuba.
Kai aunty gida biyune fa tsakaninku.
To yaseer basai anbar mutum zuwaba?, ya ce, "hakane kuma.
Sun daďe suna hira, ta ce, "ka gaishemin da umma, itama zan kirata mu gaisa insha ALLAH, dan jiya mun gaisa da abba.
To shikenan zataji insha ALLAHU, saina zo.
Okey to saikazo.
Shiru tayi tana tunanin mijin nata, tana mamkinsa, agaban mutane yakan nuna yana sonta, amma idan su kaďaine sai muguntar tsiya.
Anwar yashigo da gudu yana faďin aunty kina ina??, yasmeen ta tsshi zaune, ganinan Anwar, ya mi'ka mata kofi, yayinda Abdallah ma yashigo da gudu, yatsaya yana hakki yana hararar Anwar.
Yasmeen tayi dariya tana tambayarsu miya faru, Anwar ya tuntsure da dariya, yaya ne ya haďa askirim na ďebo miki, shine yabiyoni zai kwace.
Yasmeen ta ce, "kai Abdallah ALLAH yashiryaka wlhy, nixaka yima rowa.
Ya 'karaso yana faďin ALLAH aunty dama nayi niyyar kawo miki, banfa gama haďawaba ya ďebo, kuma dafarko bake yay niyyar kawomawa ba, kansa ya ďebar mawa.
Anwar yay dariya kaidai yaya faďi gsky.
Dagudu Abdallah yabiyoshi suka fara zagaye falon, yasmeen tana tun tsura musu dariya.
Nawaf yashigo da sallama, bashiri suka nutsu, kowa yana hakki, yasmeen ce kawai taketa dariyarta.
Nawaf yatsaya yana kallonsu kawai, yayin da yakejin kamar kar yasmeen ta daina dariyar dan tayi 'kyau da dariyar.
Su Anwar suka ra6a ta bayansa suka fice, sum2🚶🏼🚶🏼kafin akai musu masga.
Bayan fitarsu Nawaf yay tsaki yashige bedroom, babu daďewa yafito sanye da jallabiya, ko kallon yasmeen baiyiba ya fice.
Tabishi da kallo tana ta6e baki.
Koda yadawo sallah wajen papa yawuce dan amsa kiransa, ya rissina ya gaisheshi.
Papa ya amsa yana faďin zauna sosai mana.
Nawaf ya zauna.
Papa ya ce, "dama inaso na sanar makane ka shirya kaida matarka kuje safana, ku gaishe da jama'a damusu godiyar hidima.
Da sauri Nawaf ya ce, "papa safana fa ka ce??.
Eh, safana na ce, yakamata ka kaita tasan tushenka, tasan kaiba ďankowa bane, talakane kamarta, baka fita da komaiba, wannan 'katon gidan datake gani da taimakon ALLAH aka ginashi, shima saida aka đauki shekaru ba'a gamaba, dan har aka haifeka ban gama ginin nan ba, kuma haka mahaifiyarka ta zauna dani, duk da ita tafito daga wata 'kasa, kuma gidan arzi'ki.
Nawaf ya ce, "to shikenan papa zamuje, amma aranar zamu dawo??, kai papa ya girgiza, ya ce, "A'a, kwana uku zakuyi ku zaga dangi ko'ina, kushiga ko'ina da ina.
Nawaf ya ce, to shikenan zamuje nextweek, dan inaso 'karshen watanan na koma Spain!!.
To ALLAH yakaimu lafiya, saikayi 'ko'karin shrya muku tafiyar, ALLAH yay muku albarka, yabaku zuria ta gari.
A la66ansa ya ce, "amin.
Sunďan daďe suna hira, saida papa ya ce, "yatashi ya je wajen matarsa, anbarta ita kaďai.
Akunyace Nawaf yami'ke yafice.
Papa yabishi da kallo yana murmushi.
Saida yaje wajen hajja yay mata saidai safe sanan yatafi 6angarensu.

Afalo ya iske yasmeen tana kallon hausa film, ya ďauki remote ya canja, wai shi bazai kalli wannan shashancinba, yasmeen ta turo baki gaba, a zuciyarta ta ce, "bagara hausa film ba wataran suna faďakarwa, akan 'yan kwallo da rashin aikinyi yay musu yawa...........Nawaf ya katse mata tunani da faďin "k ina shayina☕??.
Banza tayi masa, tayi kamar batajishiba, ya mi'ke, da sauri ta tashi tsaye itama, tanufi kichin da gudu.
Dariya ta su6cewa Nawaf, ya tuntsure da dariya, cikin dariya ya ce, "kai matsoracima baiji daďin kansaba wlhy.
Babu daďewa ta dire masa shayi agaban sa, tana wani zuzzun6ura baki gaba, ta ajiye zata wuce, ya ce, "k dawo nan, ta tsaya cak ita bata tafiba, kuma bata dawoba.
Cikin faďa ya ce, "wai badake nakeba??, saida ta murgiďa baki sanan ta juyyo, tazo ta tsaya akansa, ya watsa mata harara, wlhy yarinya kishiga hankalinki dani, inba hakaba kin rin'ka shan wahala kenan.
Ta yatsine fuska sanan ta ce, "wlhy saidai musha wahala, kabar ganin ďazu ka kumbura mini le6e na 'kyaleka, zan ramane.
Ya tashi zaune daga kwanciyar dayayi, yasa hannu ya fisgota ta faďo jikinsa, runtse idanu tayi kam, tana rawar jiki, ya matseta kam ajikinsa, bata ankaraba taji bakinsa cikin nata, wata mahaukaciyar sumba yake mata, ga le6enta bai gama warkewaba, dan har yanzu yana mata zafi, amma dan muginta irinta Nawaf sai yahaďe bakinta da nasa sai murza yakeyi.
Itako hawaye kaiwai take zubowa, tana tsunguninsa da hannunta ďaya, amma ko'a jikinsa, dan ya'ki sakinta.
Saida yaga taji jiki sannan yasaketa, tana hawaye, tama kasa tashi daga jikinsa.
Ya lumshe idanunsa dasukai jajir, yamaida kansa jikin kujera yana fitarda numfashi.
Ahankali ta tashi daga jikinsa ta shige bedroom, saman gado tafaďa tana kuka, saida tayi mai isarta sanan ta shiga bayi taiyi wanka, tafito tayi shafa'i da wutiri, tana nan zaune yashigo ďakin tai 'kasa da kai kamar bata ganshiba.
Shima bai kalletaba yashiga cire kayan jikinsa, tashi tayi ta haye kujera takwanta.
Yashiga wanka shima, yafito yagama komai na al'adar rayuwarsa, shafa'i da wutiri, karatun alkir'ani, sanan yaje kichin dakansa yasake dafa wani shayin dan wancan ya huce.
Falo yay zamansa saida dare yayi sosai yashigo, sanan yasmeen ta daďe dayin barci akan kujera.
Kallo ďaya yay mata ya ďauke kai, ya hau gado yakwanta.
Na ce, "mu kwana lafiya, nima wajen nawa handsome ďin nataho😘.
________________________________ WASHE GARI.
lokacin dana iso 'yan aiki harsun gama gyarama yasmeen 6angarenta, tagama haďa break a falo na tarar da Nawaf yana break na ce, "tofa yau ba'a ra'ayin dinning ďin??.
Yasmeen ta fito daga ďaki, hannunta ďauke da littatafai, ko kallon inda Nawaf ya ke batayiba, ta zauna saman kujera tana karatun ta, yaďago yana kallonta, wani abu yana ta6a zuciyarsa, amma yanaji har aransa bazaiyi fatan yafitowarsa filiba.
Yasmeen taji ajikinta ana kallonta, ta ďago tana kallon inda Nawaf yake, ta murguďa masa baki😏.
Ya 'kara ďaure fuska, "k dawa kike??, ta ce, "da wanda ya tsargu mana.
Ya ce, "toni na ysargu.
Ta ce, "matsalarkace.
Ya ce, "kema yanzu zata zama taki!".
Aii tana ganin ya mi'ke ta tashi ta fallah da gudu zuwa waje, dama shiyyasa ta zauna kusada 'kofa.
Nawaf yay kwafa zaki dawo ki sameni aii, matsoraciyar banza kawai😜.....................✍🏻

Assalamu alikum
Masoya littafin NAWAFF kwana biyu kunji Shiru hakan tafarune sakamakon rashin lafiya danayi, amma yanzu komai normal, ngd da 'kyaunarku gareni, luv u oll❤❤❤😘

[1/12, 8:54 PM] mrs bilkisu: ☆☆☆☆☆☆☆☆
🎾 NAWAFF 🎾
☆☆☆☆☆☆☆☆

NA BILKISA IBRAHIM💞

Page👉🏻31 & 32
Chapter 22 · 0% Book details