Sashe 29
Nawaff Part 1 Complete Hausa Novel · about 5 min read
isarta harta koma bani tausayi. Ranar afalo ta kwana,. Washegari Nawaf tunda yafita daga gidan bai dawoba sai dare. Afalo ya isketa zaune ko kallo bai ishetaba shima ďin haka, yay wucewarsa bedroom. Tsaki yasmeen taja tana faďin mugu kawai mai ba'kin hali, koda yashiga ďakin kayansa yashiga haďawa dan gobe zai ďage zuwa Spain, amma bai sanarma yasmeen ba. Yagama haďa komai sannan ya kwanta yana tunanin yanda zaiyi da yasmeen dan shidai bazai sanar mata zai tafi gobe ba, kuma bayaso papa ko momcy suji cewar bai sanar mataba. Yajawo ledar daya shigo da ita, yaciro wata haďaďďiyar waya akwali, yabuďeta ya'kare mata kallo, sannan ya ďakko biro da takarda yafara rubutu📝yagama ya ninke yasaka acikin wayar ya ajiye yay kwanciyarsa. Saikuma wata dabara ta faďo masa, yaďauki waya yana surutu kamar yanayi dawanine, harfalo yafito yana faďin karka damu insha ALLAH gobe zan iso Spain, zan biyo jirgin 'karfe bakwai nasafe da ixinin ALLAH. okey babu damuwa nagode zataji saina iso. Yasmeen tanajinsa, sai abin yabata mamaki, wai kana tareda mijinka amma yagagara sanar dakai zai tafi, wanan wace irin rayuwace, wasu hawaye suka wanke mata fuska, shikuwa tuni yakoma bedroom abinsa. Haka takwana rabi barci rabi tunani, aiko dasafe ta makara, sanda ta tashi 7:30am tadiro dasauri daga kujera tanufi bedroom wayam tagani Nawaf yatafi, hawaye suka shiga yimata ambaliya a fuska, jiki asanyaye tayi alwala tayi sallar asubahi. Tana zaune saman sallaya momcy tashigo, yasmeen taďago da sauri tazata Nawaf ne saitaga momcy, batasan sanda sabon kuka yazo mataba. Momcy tazauna ta rungumota zuwa jikinta tana lallashi, yihakuri barkuka, shiyyasa mijinki ya ce, "kar'a tadaki daga barci, dan tunjiya kike kuka, to kiyi ha'kuri aiba daďewa zaiyiba zai dawo, kuma idan yadawo tare zaku koma kinji. Azuciyar yasmeen ta ce, "wato 'karyar daya shirya muku kenan?, ba komai zanyi maganin shi dakaina agidannan, komai yanada lokaci, nasan nima nawa lokacin yana zuwa. Nan momcy tayita lallashinta, daga 'karshe ta ce, "idan kinajin tsoro kishirya kayanki, ki koma ďakina, idan yadawo saiki komi nan kinji, idan kuma ba'kyajin tsoro tokiyi zamanki anan ďin. Da sauri yasmeen ta ce, "momy zanbiki can. Toshikenan tashi ki shirya kayanki kinji, bari na turo miki Anwar yatayaki ďauka, ta ce, "to. Ta shirya duk kayan dazata iya bu'kata, sai asanan taga ledar daya ajiye, yarubuta nakine idan kina bu'kata. Kai kawai ta girgiza taďauki ledar tasaka cikin kayanta, Anwar da Abdallah sukazo suka tayata ďaukar kayan, suka kashe duk wani kayan wuta na wajen, suka rurrufe ko ina. Tundaga ranar takoma ďakin momcy da zama, tanajin daďin zaman, saidai tunani Nawaf da kewarsa duk sun addabeta, har takanyi mamakin kanta, yanda tadamu da mutumin dabai damu da itaba, wanda bazaman lafiya sukeyiba sanda yana nan, taja 'karamin tsakai tareda gyara kwanciyarta, 'kilama shi yamanta dawata halitta yasmeen. Tasan Nawaf bazai ta6a sontaba sai wani abu ga ALLAH, wanan kuma ikonsane, yakan aikata duk yanda ya so, alokacin daya so. ________《》__________ To shimadai Nawaf hakan take agareshi, tunda yasauka 'kasar Spain bashida wani sukuni, tunanin yasmeen duk yacika masa zuciya da ruhi, bashida aiki sai tunaninta, yakanyi dariya idan yatuna wani faďan nasu, yayi waya da kowa nagidan amma banda ita, yatambayi Anwar ya ce, "baiga ta haďa wayar daya saya mataba. Yana matu'kar bu'katar yin magana da'ita amma yarasa hanyar dazaibi. Ya lumshe manyan idanunsa masu haske, ya maida kansa jikin luntsume miyar kujerar dake falonsa yakwantar, tabbas yasan yafaďa tarkon son yarinyarnan, kuma yalura ita bata 'kaunarsa, haushinsama takeji, saboda har yanzu soyayyar tsohon mijinta tana tareda ita. Ya'karashe maganar kamar xaiyi kuka, yashiga girgiza kai yana faďin A'a FATEEMA ZARAH karkimin haka, nine kawai yadace ki so, domin dani kika dace, jiki yana rawa yaďauki ďaya daga cikin wayoyinsa yashiga kiran Anwar, harta tsinke ba'a ďaukaba, yatuna yanzu yana islamiyya wajen karatun dare. Yamaida akalar kiran zuwa Abdallah shikuma tashi akashe, yayi tsaki, saikuma yakira momcy, bugu ďaya biyu ta ďauka, bayan sun gaisa yatambayi lafiyar kowa. Ta amsa dakowa yana nan lafiya, ya ce, "masha ALLAHU haka akeso, yanaso ya ce, "tabama yaameen amma yanajin kunya, dan haka sukayi shiru suduka, momcy takatse shirun da faďin Abdallah ya ce, "yau da daddare zakuyi wasa ko??. Eh momcy insha ALLAHU, sai a tayamu da addu'a. Babu damuwa kullum ita muke muku ALLAH yabada sa'a. Amin momcyna ngd, bari nabarki haka ki gaida min dasu. To sai anjima zasuji. Yasmeen tana zaune tana jinsu, abin ya sosa zuciyarta, tunda yatafi bai nemetaba, amma kullum yana kiran iyayensa da 'kannensa, đazu datayi waya da yaseer a wayar Anwar yake gaya mata babu daďewa yayi waya da yaya Nawaf, amma ita banda ita, wasu 'yan kwalla suka taru mata agefen idonta, tai saurin sharewa kafin momcy tagani. Su Anwar suka dawo daga islamiyya, suka zauna suka cigaba dahira, dukda ita yasmeen firar bawani daďi takemataba, danma anasako Nawaf a firarne da tuni taje ta kwanta. Suna nan zaune har aka fara kallon wasan su Nawaf ďin, taďanji sanyi data ganshi, tunda wasan Life ne ake nunawa, sai wani murmushi takeyi najin daďi, ana haka su Nawaf sukaci kwallo kuma shine ya zura kwallon. Su Anwar suka shiga murna da tsalle, itamadai taďanyi murnan, damma ganin momcy awajen taďan kanne saboda kunya. Haka rayuwa yacigaba da tafiya yauda gobe sai ALLAH, yau watan Nawaf ďaya datafiya, kuma har yanzu basu ta6a gaisawa da yasmeen ba, ga kowannensu yana cikin muradin son jin muryar ďan uwansa, amma hakan ya gagara, suduka suna cikin begen juna, garama yasmeen tana ganinsa yayin dasuke wasa, takanďan rage damuwa. ________________________________ ____ yauma tana kwance aďakin momcy abin duniya duk yadameta, saitaji wayar Abdallah dake gefenta tana wringing, takai hannu taďauka saida gabanta yafaďi dataga ansa yaya Nawaf, ta rintse ido tabuďe, har wayar ta'katse, yasake kira itama ta katse, ana ukunne ta ce, "bari taďaga. Jiki a sanyaye ta ďaga wayar, muryarsa ta daki dodon kunnenta, tarintse idanu, cikin faďa ya ce, "kai wane irin iskancine anata kiranka ka'ki ďagawaya??, ubammi kakeyi??. Yasmeen tayi shiru takasa magana dan tsoro, shikuma jin anyi shiru yacigaba da bala'insa, ahaka Abdallah yashigo, da sauri ta mi'ka masa wayar....................................✍🏻