← Book details Nawaff Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 31 OF 51

Sashe 31

Nawaff Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read

A6angaren Nawaf kuwa karaya yasamu a'kafa, yanacan kwance rijif cikin ciwo, amma zuwa yanzu an gyara karayar, harma yasamu barci.
Washe gari suka lula zuwa Spain domin ganin halin da Nawaf yake ciki.
Momcy da papa da yasmeen kenan.
Abdallah da Anwar da mas'ud zasuzo daga baya sukuma.
Bayan sun sauka a masauki sun huta, dukda bawani hutawama sukayi sosaiba saboda hankalinsu yana wajensa.
Wani abokinsa ne yazo yay musu jagora zuwa asibitin, yasmeen sai zare ido akeyi ana kalle2 tun ajirgi, sun isa haďaďďen asibitin na alfarma kuma 'kayatacce, wanda 'yan kwallone kawai sukeda dangantaka dashi.
Bayan kamar minti shabiyar aka basu izinin shiga wajen Nawaf.
Tunda akace sushiga jikin yasmeen yay sanyi, papa ne yafara shiga sannan momcy, Nawaf dake kwance yafara murmushin 'karfin hali dan ganin iyayensa, yasmeen ma tashigo jiki asanyaye, saidai ta la6e abayan momcy.
Ya yun'kura zai tashi amma saiya kasa, ya ďan runtse idanu tareda cije le6e danjin zafi, da sauri papa yamaida shi kwance yana faďin A'a modebbo yi kwanciyarka kaji.
Nawaf yakuma murmusawa yana faďin momcy sannunku dazuwa, momcy tayi murmushi itama ta ce, "yauwa abbuna kaine da sannu yajikin??, ya ce, "Alhmdllh momcy, ina sauran 'kanni na suke??,
Momcy ta ce, "suna gida amma zasuzo nan gaba suma insha ALLAHU, tajuya dan bataji motsin yasmeen ba, saita ganta abayanta ta raku6e, momcy takamo hannunta tana faďin ďiyata 6oyewa kikayi??, da sauri Nawaf yaďago idanu suka haďa ido da yasmeen, tai saurin yin 'kasa da kai.
Taďan rissaina tana gaisheshi da tambayar jikinsa??, ya ce, "da sau'ki, jiyake ciwon nasa ya warke tunda yaga TAURARUWARSA, ya lumshe manyan idanunsa wani sanyi yana kwarar azuciyarsa, shikam saiyace gara da yaji ciwonnan, koba komai tasanadin ciwon yaga yasmeen.
Momcy da papa suka zauna saman kujeru biyu dake ďakin, papa ya ce, "fatima zauna kema, yanuna ma yasmeen gefen gadaon da Nawaf yake kwance.
Cikin jin kunya ta zauna kaďan kamar tana kusada wuta.
Hira suka shiga yi da tambayar yanda akayi abin yafaru, dukda duk sun gani, amma yasmeen bata cewa komai, sai wasa datakeyi da yatsun hannunta.
Sun daďe suna hira daga baya papa da momcy suka mi'ke sukace yasmeen tazauna anan suna zuwa yanzu zasu dawo.
Bayan fitarsu ďankin yay tsit babu wanda yake motsi acikinsu, sai Nawaf daya tsirama yasmeen idanu kamar zai cinyeta ďanya, ahankali yasmeen ta yun'kura zata tashi, da sauri Nawaf ya dam'ke hannunta, ta juyo tana kallonsa shima ita yake kallo, kallon ido cikin ido sukema juna, yasmeen tafara janye nata idanu.
Ahankali Nawaf yafirta 'yammata babu maganane??, yasmeen ta ce, "bana gaishekaba.
Ya ďan murmusa to ina zakije dakike 'ko'karin tashi??, taďan motsa hannunta daya ri'ke, murya 'kasa2 ta ce, "zan koma kan kujerane.
Hummm to idan su papa suka dawofa?, shiru tayi bata amsaba, ya matsa hannunta yana murzawa ahankali, gaba ďaya tsigar jikinta tashi takeyi, tana mamakin wannan wane irin kuma sabon salone Nawaf yazo dashi, cikin rawar murya ta ce, "plz kasakar min hannu karsu mom su dawo su gammu ahaka.
To miye idansun gammu, kinsan babu abinda zasuce aii,, eh, amma da kunya dai,, babu wani kunya malama yafaďa Yana yun'kurawa zai tashi saikuma yay sauri dafe gado yana faďin wash ALLAHNA!!.
da sauri yasmeen ta ce, "yayadai??", ya yatsine fuska yana faďin wlhy mantawa nakeyi inada ciwo, ga 'kafar zafi idan na motsata.
Yasmeen ta ce, "ayya sannu, cikin muryar tausayi take maganar.
Kai ya girgiza mata alamar yauwa, ya ce, "zansha ruwa.
Tajuyo tana kallonsa, ta ce, "ruwa kuma??, ya ce, "eh",.
ruwan dake gefen gadon ta ďakko ta buďe murfin tami'ka masa, ya harareta to dawane hannun kikeso nasha kenan??, ta turo baki gaba ta ce, "toda wayake baka?, kuma aii hannunka lafiya lau yake ko?.
Ya ce, "Ahmad ne yake bani mana, shima ďan kwallone abokinsane ďan kasar saudiyyane, haifaffen amerika, ta ce, "to kakirashi mana yacigaba da aikinsa.
Nawaf ya haďe fuska yana kallonta, ya ce, "mikike nufi?, "k bazaki iya yimini ba??.
Tayi shiru, ya ce, "okey bari momcy tadawo ita saitayi mini aii, kinsan babu yanda za'ayi uwa tabar ďanta ayashe.
Yasmeen tai kwalkwal da idanu kamar zatayi kuka, ta ce, "ainidai ban faďaba ko??, ya ta6e baki yana faďin ai basai kin faďaba malama, yanayinki ya nuna.
Bayanda zatayi dole ta mi'ke taunifi saitin kansa, tami'ka masa ruwan, ya ce, "kinsandai babu yanda za'ayi nasha ruwa akwance ko? Saikin taimaka mini na tashi, koki ďago kaina, yasmeen ta ce, "azuciyarta kaikam kacika matsala wlhy.
Dole ta tallafo kansa, tasaka masa ruwan yasha kaďan yajanye baki, ta ce, "dama shan ruwan gulmane.
Ya ce, "nine magulmacin kenan??, yafaďa yana hararta.
Ta ce, "nidai aiibance kaiba.
Haba yarinya duk wanda yay zagi akasuwa aii yasan dawanda yake barganina akwance ina dai2 dake wlhy .
Kafin tayi magana su momcy suka dawo.
Nawaf ya ce, "papa ina kukaje??.
Munje wajen manyankune kozasu bamu kai mu koma Najeria tare, to papa misukace maku??, hummm basu aminceba, wai baikamata su ďora mana nauyiba, dansuke da alhakin kulawa dakai, kuma anna zakafi saurin warkewa tunda sunada isasun kayan aiki, ingantattu kuma.
To papa kubarsu suyi aikinsu dama nasan dawuya su amince gsky.
Papa ya ce, "babu damuwa ai muna nan tareda kai insha ALLAHU, dama maman kace tadage akan mutafi dakai.
Nawaf yamaida kallonsa ga momcy, ya ce, "sorry my momcy karki damu insha ALLAHU anan ma suna bani kulawa sosai, kuma zan koma daidai insha ALLAH.
to shikenan modebbo ALLAH ya amince mana.
Amin suka amsa harda yasmeen.
Papa ya ce, "to bari mu koma masuki dan suna nuna mana lokacin ziyarku ya 'kare saikuma gobe, ALLAH ya'kara lafiya.
Amin suka amsa gaba ďaya, kafin su momcy su mi'ke tuni yasmeen tafice abinta.
Nawaf ya bita da kallo yana cije le6e, azuciyarsa ya ce, "yarinya dole ki soni!!!.
Tunda suka tafi saiyaji ďakin babu daďi, baigaji da kallon 'kya'ky'kyawar fuskar yasmeen ba, amma babu yanda zaiyi.
Likita yashigo ya dubashi, saima yaymasa allurar barci danya samu hutawa.

Suma su yasmeen masauki suka koma, yasmeen ďakinta ita kaďai, papa da momcy kuma ďaya suma.
Tagama komai na al'adar rayuwarta ta kwanta, amma sai tunanin Nawaf yadawo mata, ta tuna yanda yau yake mata magana cikin taushin murya, babu faďa bare nuna jin haushi, ta kalli hannunta daya ri'ke, hannun ta sumbata tana murmushi, talumshe idanu tareda furta i luv u my Nawaf...., tai saurin rufe bakinta🙊tana girgiza kai.
Na ce, "yasmeen ina saura kuma, sirrin 6oye yafito fili.
Haka tayita juye juye dan takasa barci, daga 'karshema saita mi'ke tashiga bayi tayo alwala, tazo tayita nafil fili, tana ro'kon ALLAH yabama mijinta lafiya da dukkan muslmi al'umar ANNABI......................✍🏻

Asalamu alaikum
'Yan uwa kuyita ha'kuri danifa,karku ďauka ina muku jan raine, A'a kunsan ance lafiya uwar jiki babu mai fushi dake, ina bu'kar addu'arku...
Luv u oll😘😘😍😍

© 2016

💞Bilyn Abdul💞
💞Mrs Abdus'salam💞
💞luv u oll my fan's😘💞
[1/12, 9:00 PM] mrs bilkisu: ☆☆☆☆☆☆☆
🎾 NAWAFF 🎾
☆☆☆☆☆☆☆

NA BILKISA IBRAHIM💞
Chapter 31 · 0% Book details