← Book details Nawaff Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 16 OF 51

Sashe 16

Nawaff Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read

Da yamma ta saci jiki tashige gidansu Ameena, umma tana d'aki bata saniba, tazata yasmeen d'in tana d'akine, tunda tasaba yini a d'aki, bare yau ana sanyi a garin.
Yasmeen kam tana can sunata hirarsu itada ameena da bello yayan Ameena.
Saida taga ana kiran wayarta sannan ta mi'ke zaram, number yaseer tagani, tad'aga da sauri tana fad'in bro's yaya dai??.
Ya ce, "kina ina?, anata nemanki.
Yasmeen ta gwalalo idanu waje tana fad'in naga ta kaina ganinan zuwa.
Ameena ta ce, "kije kisha fad'an umma, dan satar fita kikayi, kuma akwai zunubi
Hararta yasmeen tayi tafice da sauri batareda tabama Ameena amasaba.
A 'kofar gida tayi turus, dan ganin Nawaf jingine a jikin mota, kansa a 'kasa yana danna waya, yana sanye cikin shadda milk, d'inkin iya guywarsa, yayi 'kyau sosai sai 'kamshin tutare yakeyi, yaseer yana gefensa tsaye.
Jiki a sanyaye ta 'karasa wajensu.
Yaseer ya ce, "sisto wai dama kina nan gidan tund'azu??.
Kai kawai ta d'aga batare da tayi magana ba, ta ce, "miyasa kuka tsaya nan??.
Yaya ne ya ce, "mu tsaya muga inda zaki fito.
Yasmeen ta kai dubanta ga Nawaf wanda tunda tazo ko d'ago kai baiyi ya kalletaba, yanata danna wayarsa kamarma baisan dawata yasmeen a wajenba.
Saida tad'an turo baki sanan ta ce, "to kumuje mana, Nawaf ko motsi baiyiba dan haka yasmeen tayi gaba abinta.
A falo ta iske umma, umma ta hauta da fad'a, itadai yasmeen fad'i take umma kiyi ja'kuri ALLAH gidan ne naji shiru shiyyasa na fita.
Tsaki umma taja ta ce, "aii yayi miki 'kyau tun d'azu mijinki yazo yake jiranki, kinacan inda ba a aikekiba.
Shiru yasmeen tayi dan tasan batada gsky.
D'an abinda umma tahad'a yasmeen ta d'auka tanufi falon abba, azaune ta tadda Nawaf yana kallo, ita a zatontama har yanzu bai shigoba.
Ta dire tiren a gabansa sanan ta koma nesa dashi ta zauna.
Suduka kowa ya share kowa, dan Nawaf har yanzu ko kallonta baiyiba, itama saita shareshi taci gaba da harkarta.
Sunkai tsawon minti30 ahaka, yasmeen ta daure ta ce, "nikan gsky inada abinyi dan haka zan 'kara gaba.
Harara ya watsa mata batareda yayi maganaba, ya d'auki remote ya 'kara 'karan tv dan bayaso umma taji hayaniyarsu, tsam ya mi'ke yanufo inda take zaune.
Atu naninta zama zaiyi, dan haka tashiga matsawa tana 'kan'kame jiki.
Tsaki Nawaf yayi ya'karasa gabanta, gashinta ya dam'ko ya matse da 'karfi, gaba d'aya jijiyoyin kan yasmeen suka fito, tasaki wani walallen kuka tana 'ko'karin ri'ke hannunsa, gashi ya toshe mata baki da hankacif.
Ya zare mata fararen ida nunsa masu girma, ya ce, "wayace kifita??
Yasmeen babu damar yin rashin kunya, saidai hawaye dake fita daga idanunta, ya saki gashin yana fad'in gobe idan kin tashi ki kuma fita bada izininaba, kiga abinda zan miki, baki ta murgud'a masa ta ce, "mugu ALLAH saiya saka mini.
Hannu yakai zai kama hannunta ta kauce da sauri, yaja gefe danya kamata saita fad'a jikinsa, mai makon ya ri'keta saiya kama d'an yatsanta, tako daddage ta galla masa cizo a d'ayan hannunsa.
Da sauri ya saki hannunta yana yarfe nasa hannun, abinka da fari gurin har yayi jajur, ga shatin ha'koranta awajen rad'a2.
Nawaf ya rintse ido yana murza wajen, dariya sosai yasmeen takeyi, ta ce, "kaji idan da dad'i kaima.
Ya bud'e ido yana cije le6ensa na 'kasa, har yanzu wajen zafi yake yi masa, ya ce, "ni kika ciza ko??.
Baki ta murgud'a😏 masa, gobema idan ka 'kara gwada mini mugunta saina yimaka wanda yafi wanan, mugu kawai.
Wani murmuahi Nawaf yasaki mai kamada ya'ke😜ya ce, "banza kuriya🐅, wlhy idan na kamaki zaki gane kuranki.
😜gwalo yasmeen tayi masa ta ce, "saidai mu gane kurenmu wlhy.
Kwafa yayi ya ce, "yarodai baisan wutaba saiya taka.
Nunata yayi👉🏻👩🏻yana fad'in kuma wlhy kifad'ama wannan jahilin daya sakeki aka 'ka'kaba mini, daga yau nasake jin yazo gidanna saina sa an 6atar dashi, dagashi har jahilin ubansa, idan kunne yaji jiki ya tsira.
Kemad'in bance karki 'ki fitaba, saidai idan kika cigaba da karya dokata zaki cigaba da shan ba'kar wahala ne, danni ba sa'anki bane.
Yana kaiwa nan ya fice dama har anfara kiraye2 sallar magriba.
Dariya tasaka harda tafa hannaye, ta ce, aii dai kasha cizo azzalumi kawai, aii wlhy na daina 'kyaleka kana sakar min kwanjinka a banza, idan kafi karfina aibakafi karfin cizoba, zakayita shan cizone harsai hannunka yakoma da zanen ha'korana ko ina.

_______________________
D'aki tanufa tayi sallar magriba, tana nan zaune tana karatun alkur'ani har akayi sallar isha'i.
Bata fitoba dan tasan umma tana ciki da ita, saida tabari yaseer yadawo sanan tafito, ganin baya falo yasa tanufi d'akinsa.
Saman gado ta tarar dashi ya bud'e waya 'katuwa akwalinta yanata kallo yana murna, NAWAF ne ya sayamasa.
Yasmeen ta murtike fuska, cikin masifa ta ce, "yaseer yaushe kazama munafiki, kai har ka fifita bare akan ni 'yar uwarka??.
Ubanwaye yasaka gayama wancan mugun faisal yazo gidanan da safe??.
Yaseer ya had'e fuska, kai kaji sisto d'innan koda ban fad'aba ma aii abba ya fad'ama abbansa, kuma nasan zai gaya masa, zaki wanizo kina zagina, yafad'a yana turo baki gaba.
Tsawa yasmeen ta daka masa dallah malam rufe min baki, munafiki kawai, wanda bai iya ri'ke sirrin gudansuba, saboda an kawo maka waya kazauna kasaki baki kana zuba gulma da tsigudidi.
Wlhy daga yau nakuma jin maka manciyar wanan maganar saina daka ka agidanna, idan kaji 'karya ka 'kara, sakarai kawai, tayi waje.
Yaseer yabita da kallo yana murgud'a baki, an fad'a d'in, kumani ba magulmaci bane.
Kinason mutum kina wani kauce2, ai tuni na harbo jirginki😜ooooh, yafad'a yana dariya.

Nawaf kam cikin haushi yaje gida, koda yayi sallar magriba da isha'i bai nemi mas'ud ba, dan yanada aikin yamma shiyyasa basuje tareba.
D'aki yadawo yay kwanciyarsa, kad'a2 saiya kalli inda yasmeen ta cijeshi, wajen yayi jajur.
Yasaki murmushin mugunta, wlhy yarinya sakinyi dana sanin cizonan dakikamin, mara kunyar banza kawai, yay kwafa yana gyara kwanciya.
Ahaka mas'ud yazo ya sameshi, ya zauna yana fad'in angon yasmeen kabarota lfy??.
Banza Nawaf yay masa.
Mas'ud yay murmuahi oh baza'a amsa miniba angon yasmeen??.
Cikin masifa Nawaf ya ce, "kasan ALLAH mas'ud ka daina had'ani da wanan yarinyar inkuwa ba hakaba zamu sami matsalane.
To miye dan munsami maysalar alhaji???, wata ran basai mu shiryaba.
Nawaf yatashi zaune yana fad'in wlhy mas'ud saina koyama yarinyar nan hankali kwanannan.
Hummm mitayi maka dazaka koya mata hankali.
Hannunsa ya nuna masa ya ce, "kalla ka gani waini yarinyarnan ta ciza.
Mas'ud yatuntsire da dariya, kai saikace wata kura??.
Ai tafi kura Nawaf yafad'a yana gyara zama, nan yabama mas'ud labarin abinda ya had'asu.
Mas'ud ya ce, "Ah wanan laifinkane alhaji, aiba haka ake hukunta mutumba idan yayi laifi.
Tsaki Nawaf yaja ya ce, "wanan kuma matsalar kace.........................✍🏻

©2016

💞Bilyn Abdul💞
💞Mrs Abdus'salam💞
💞luv u oll my fan's💞
[1/12, 8:59 PM] mrs bilkisu: ☆☆☆☆☆☆☆
🎾 NAWAFF 🎾
☆☆☆☆☆☆☆

NA BILKISA IBRAHIM💞

page👉🏻23 & 24

......WASHE GARI...su papa sukazo shida 'kaninsa dayazo daga katsina, dakuma Abban mas'ud, bayan angama gaishe2 suka shiga tattauna abinda yakawosu.
An 'kar'kare magana za'ayi shagalin biki nanda sati hud'u masu zuwa, (1monch )sananan su Nawaf sun gama wasan kofin africa kenan, kafin yakoma Spain sai asha shagalin biki kawai.
💃💃💃💃kai zamu shabiki, kowaya yashirya masu karatu😜.
Bayan an 'kar'kare magana yasmeen tashigo ta gaidasu, 'kanin papa ya yaba kam da tarbiyyar yasmeen , yanada tabbacin Nawaf yayi dace!!!!!!!.
Chapter 16 · 0% Book details