← Book details Nawaff Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 34 OF 51

Sashe 34

Nawaff Part 1 Complete Hausa Novel · about 5 min read

.....Yasmeen ta ďauke numfashi, sai 'kirjinta ke dukan tara2, ga jikinta yana rawa, tamaba Nawaf dariya kwarai da gsk, amma saiya gimtse.
Kaďan yara6u da jikinta, yakai hannu bisa key ďin dake 'kofar ya kulle.
Tanaji yana sakama 'kofa key sai rawar jikinta ta 'karu, tazame 'kasa ta zauna da6as, ta tura kanta tsakiyar cinyoyinta, tana ambatar sunan ALLAH.
Ya bita da kallo bayan yagama kulle 'kofar, kai ya girgiza yan ta6e baki, kamar wanda yaga wani abin daba'a so.
Bayi yashige domin yin wanka abinsa.
Bayan wasu 'yan mintina taji motsin ruwa, amma tsoro yahanata tashi daga wajen, tama kasa ďago kanta, itafa har yanzu ta zata Nawaf yana awajen tsaye😜.
Shima yana wanka yana murmushi, ashema yarinyar nan matsoraciya ce?, to ita da mitake tunanin zan mata ne?, yay wata 'yar dariya, ashedai ana tsoron iya iya inji 'yar mayya, yarinya kamar farar kura, ga tsoro ga jan faďa, dahaka yagama wankan yana zancen zuci, yafito
Abin yabashi mamaki daya ganta a inda yabarta, kuma kanta a6oye har yanzu, ya murmusa yana dogara 'yar sandarsa, abakin gado yazauna yana cije le6e dan har yanzu 'kafar tana ďan masa zafi, tunda bata gama sakiba gaba ďaya, ya shafa mai tareda shirin barci, harkokinsa yaketayi batareda ya'karabi takan yasmeen ba, yagama shirinsa tsaf, ya haďa shayi yasha da magungunan sa.
Saida ya kwanta sannan ya ce, "k anan zaki kwana ne??, tayi shiru babu amsa, yay tsaki waike ba'kya jina ne?, yay maganar cikin tsawa.
Da sauri yasmeen ta ďago tana kallonsa baiwar ALLAH ashe barci takeyi ahaka, ya ce, "bazaki tashi a 'kofar nanba nane??.
Yanda yay maganar yana zaro idanu gashi ya haďe girar sama data 'kasa, saitaji bazata iya maida masaba, dan Nawaf yanada kwarjini, idan ya haďe fiska ko kai waye dole kaji tsoronsa, ta mi'ke jiki na rawa ta shige bathroom.
Nawaf ya girgiza kai yana lumshe fararen idanunsa, gaba đaya kansa a kulle yake, yakamata yanemi shawarar mas'ud, amma kuma bayaso kowa yasan sirrinsa, to kenan zai cigaba da zama da damuwa azuciyarsa, gashi wadda yakeyi dan ita batasan yana yibama, yafitar da huci maizafi daga bakinsa,, lallai lokaci yayi dazai gwada karfinsa yacije le6ensa na 'kasa, yakai hannu bisa 'kafarsa mai ciwo yana girgiza kai, afili ya furta akwai sauran lokaci!!!👌🏻.
Tadaďe a bayin zaune dan babu abinda takeyi, saima duniyar tunani data lula, ta manta da inda take zaune.
Nawaf sarkin saurin jin haushi har ya sha'ka, ya mi'ke yana masafa, yaja sandarsa zuwa 'kofar bayin, da 'karfi ya buga 'kofar bathroom ďin, "k wai wane irin iskancine wannan?, mikikeyi a cikin bathroom ďin??.
Yasmeen ta ce, "wankafa nakeyi.
Yaja tsaki yana faďin A'a iyo kikeyi 'karewar wanka, wlhy idan baki baki fitoba saina 6alle 'kofarnan, kuma jikinki saiya gaya miki.
Ta murguďa baki kamar tana gabansa, a zuciyarta ta ce, "wlhy idanma wani abu kake 'kullawa to kama kwance sa, dan ALLAH bazai ta6a baka sa'a a kainaba, mugu kawai, amma afili sai ta ce, "aii dai ganinan fitowa ko.
Kwafa Nawaf yayi yakoma kan gadon yakwanta yana jan 'kafa, yana mamakin miskilanci irin na yasmeen.
Na ce, " kunji wani 'karfin hali, tomiye na damuwa da fitowarta, kuma shi ya manta da nasa miskilancinne??,😏
Yakai kusan minti goma da kwanciya sannan yasmeen ta buďe 'kofar ta fito, babu wani alamar wanka datayi, zuwa sanan Nawaf ya daďe dayin barci, saboda magungunan daya sha.
Ta bishi da harara tana 'kun'kunai, saman kujera ta zauna, ta tsurama 'kya'ky'kyawar fuskarsa idanu, barci yake amma tamkar yana murmushi, ko afili bazakaga fuskarsa hakaba, lalle tayarda mijinta handsome ne, kuma Gentle man ne, domin komai nasa mai ajine, tafiyarsa, maganarsa, bare idan yana 'kayataccen murmushinsa mai kashe zuciyar 'yammata.
Yanada kwarjini na musamman wanda dole ma'abota tarayya dashi su girmamashi, gashi da tausayi da son jama'a, tunda take tareda shi bata ta6a ganin ya wula'kanta waniba dukda ďaukaka da ALLAH ya bashi, jarumi wanda duniya tasani, kuma take alfahari dashi, tunda yasamu ciwonnan gidan radio da tv mujallu da jaridu suketa yayatama duniya, yanzu ta'kara tabbatarwa Nawaf sananne ne a duniya, yakan girmama masoyansa, gashida 'kyauta, yakan taimakawa na 'kasa dashi bashida rowa ko kaďan, tasaki wani lallausan murmushi yayinda taga fuskar Nawaf ma tana bayyana murmushin. Yajuya kwanciyarsa zuwa ďayan 6angaren.
Tazame ta kwanta saman kujerar dan ganin ya 6oyema ganinta, babu daďewa barci yay awon gaba da'ita.
Na ce, "mukwana lafiya.

Da asuba yarigata tashi kona ce, "tare suka tashi, badai ta nuna ta farka bane, tana kallonsa yami'ke yana dogara sandarsa zuwa bayi, alwala yayo yafito, ya canja kayan barcinsa zuwa jallabiya fara, ya ďauki abun sallah ya shinfiďa, saida taga ya kabbara sallah sannan ta tashi ahankali itama tayo alwalar, abayansa ta kabbara tata sallar.
Bayan sun idar kowa ya zauna yana addu'a, Nawaf yajuyo da zummar tada yasmeen tayi sallah, sai kuma yaganta abayansa, ya ďauke kai tamkar bai gantaba, itama tayi burus dashi kamar batasan da zaman wani ďan adam a wajenba.
Ya tashi ahankali yana dogara sandarsa, yafice batareda yabi takanta ba, murmushi yasmeen tayi tatashi ta haye gado ta kwanta abinta.
Shikam wajan motsa jiki yanufa dake a hotel ďin.
Yasmeen tasha barcinta sosai, dan Nawaf bai dawoba, yanacan wajen motsa jiki, har saida ma'aikaciya tashigo, yasmeen ta fito waje dan bata damar gyara ďakin, saida tagama sannan tadawo tashiga wanka.
Tafito ta shirya tsaf cikin siket da riga na golden brown ďin material, ta naďa ďaurin ďankwali mai tsari, dukda bawata kwalliya tayiba tayi 'kyau sosai, tana fesa turare Nawaf yashigo sai hura hanci yakeyi daka gansa kasan yagaji matu'ka.
Momcy tashigo itama, da sauri yasmeen ta tsugunna tana gaisheta, momcy ta amsa cikin fara'a, ta ďora da faďin ďiyata, ga mijinki nan nakula yagaji matu'ka, daga wajen motsa jiki yake, kisamu ruwa mai zafi ki gasa masa jikinsa danya samu ďan'karfi kinji.
Yasmeen taďaga kai atsorace kuma cikin kunya, momcy tadafa kan Nawaf tana masa sannu, ya amsa yana ďan murmushi, karki damu momcyna komai zai dawo normal insha ALLAH, wannan motsa jikin shine zai taimaka mini sosai.
Momcy ta ce, "to shikenan abu na ALLAH ya'kara lafiya kaji, amin my dear mom, momcy ta ce, "bari naje, ďiyata agasa 'kafarnan sosai, dan ya ce, "jiya da daddare ba'ayiba.
Yasmeen ta ce, "to mom.
Momcy tafice taja musu ďakin.
Chapter 34 · 0% Book details