← Book details Nawaff Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 33 OF 51

Sashe 33

Nawaff Part 1 Complete Hausa Novel · about 5 min read

A yaune su mas'ud suka iso shida Anwar da Abdallah, Nawaf yayi matu'kar farin cikin zuwansu, haka suma sunyi farincikin ganin yafara samun lafiya, dan zamu iya cewa saura kaďan, yausu anan suka wuni yasmeen ma no'kewa tayi ta'ki zuwa wai kanta yana ciwo.
Suma a hotel ďin dasu yasmeen suke anan aka musu masuki, da daddare suka haďu akasha hirar 9ja, saidai papa ya ce, "kowa yaje yakwanta sanan.
Nawaf yakira Anwar ya ce, "yakaima yasmeen wayar, tana 'ko'karin kwanciya taji an buga 'kofar, saida ta le'ka taga Anwarne sanan ta buďe, Anwar lafiya dai ko??, ya mi'ka mata wayar yana faďin yayane ya ce, "nakawo miki wayar, yana bata yajuya yana faďin mu kwana lafiya.
Ta maida 'kofar asanyaye tarufe ta ce, "to ALLAH yakaimu, saman gado tafaďa ta kwanta, tayi addu'ar barci dan Nawaf bai kiraba ita kuma wlhy bazata kirashiba.
Ta kammala addau'ar ta lumshe idanu amma badan barciba, dan tana bu'katar jin muryar Nawaf, kamar daga sama wayar tafara 'kara alamar kira, tayi Burus da wayar harta tsinke, yasake kira, saida yakira sau uku, nanma ta'ki ďauka, sai ana huďu ta ďauka zuwa sanan Nawaf yacika fam da haushi.
Ta ďauka kuma tayi shiru, shima shiru yayi sai huci yake kamar yana gabanta, cikin masifa ya ce, "waike wace irin "'yar rainin wayoce, dan wula 'kanci tunďazu nake kiran wayarnan kika 'ki ďauka kuma nasan kina kallonta.
Yasmeen ta ta ta6e baki, tayi shiru kuma, wannan yasa Nawaf 'kara hawa sama, yacigaba da masifa, "k wlhy kishiga hankalinki dani, karkiga ina kwance a gadon asibiti kice zaki raina mini wayo, kinsanni kinsan halina, kodan kinga ina kulaki shine zaki min hauka, daga yanzu idan kinga na sake shiga harkarki kiyimini abinda kika ga dama, tsowww yaja tsaki tareda yanke wayar.
Yasmeen ta dafe kai tana hawaye, wai ita miyasama ta 6atama Nawaf rai, miyasa bata ďagaba tun akiran farko, gashinan wajen jan aji ta 6ata komai, itada take fata tajawo hankalinsa gareta, gashi nan ta na 'ko'karin nisantasu da juna, sai kawai tahau kuka.
Na ce, "tofa kaga wani ďigimi, wai dukan sauro da 'kota.
Shikam Nawaf wurgi yayi da wayar ta fashe, yamaida kansa ya kwanta yana hargitsa sumarsa, zuciyarsa cike da ba'kin ciki, yarasa wane irrin 'kiyayya yasmeen take masa haka, wace irin tsana take masa wai, ya rintse idununsa yana fitar da huci, dolene yaďauki mataki akan yarinyarnan, yakamata yafita harkarta gaba ďaya, dan yakula 'yar kulawar dayake bata ta kwana biyunnan ce takeson jawo masa raini a wajenta.
Zai tureta daga zuciyarsa yacigaba da harkokinsa, inyaso yamutu da sonta azuciyarsa mana, ahaka doctor yazo yasameshi.
Bayan yaďan dubashi ya ce, "yana bu'katar ya kwanta yahuta, dan haka allurar barci zai masa.
Nawaf ya ce, "A'a baya so.
Doctor ya ce, "aii tazama dole, babu 6ata lokaci ya zurkuďa masa, barci kuwa yay awon gaba dashi.
To itamadai yasmeen barcin ne ya saceta bayan tagama koke kokenta.
_________________________________ a yau aka fara koyama Nawaf tafiya, yana ri'ke da sanda guda biyu likitoci guda biyu suna gabansa saikuma wasu ma'aikatan abayansa, a harabar asibitin suke, dan haka su yasmeen suna gefe suna kallo.
Nawaf sai matse idanu yakeyi yana dogara sanduna, ga zufa daketa tsatstsafo masa, sunďanyi nisa da tafiya, aka kar6e sanda ďaya, to dagananfa Nawaf ya 'kara shan wahala, zufa kuwa aii kamar ana kwara masa ruwa.
Yasmeen tai 'kasa da akai tana hawaye, suma su Anwar haka, aka 'kara kar6e ďayar sandar, yafara tafiya da 'kafafunsa, daganan jikinsa yafara rawa, dauriyarsa ta 'kare, hawaye suka fara ambaliya a fiskar Nawaf, gsky koni yabani tausayi, gashi mugaye likitocinnan sun'ki cewa ya zauna.
Tun yana daurewa yana ďaga 'kafar har yakoma janta, daga bayama saiya faďi, daga nan suka ďaukesa aka maidashi ďakin dayake, zuwa sanan yafita hayyacinsa.
Momcy ta rungume yasmeen tana rarrashi, dukda itama hawayen takeyi.
Harzuwa dare an hana kowa ganinsa, sai ha'kura sukayi suka koma masauki.
Washe garima dasukaje basu ganshiba, sai lokacin da aka fito dashi domin motsa jiki, yaukam yamafi jiya shan wahala, saboda 'kafar tayi tsami jiya, haka suka kwasheshi suka maida.
To ayau rana ta uku sai ya kasance da sau'ki, dan yau baisha wahalarba, dakansama ya koma ďaki.
haka rayuwar tacigaba da tafiya, Nawaf yana samun sau'ki, kuma kullum ana fita dashi dan motsa jiki safe da yamma, saidai yafita harkar yasmeen gaba ďaya, ko zuwa sukayi dubashi daga gaisuwa babu abinda yake shiga tsakaninsu, saima 'yar harara da murguďa baki, amma kowa yana ma'kale da son ďan uwansa, babu wanda yafahimci halin dasuke ciki sai mas'ud, dan basayi gaban su papa, da su Abdallah, amma gaban mas'ud yin abunsu sukeyi.
To yaudai an sallami Nawaf, gidan dayake zaune suka nufa, ya haďa duk abinda zai bu'kata suka koma hotel ďin inda su momcy suke.
Papa ya ce, "akai masa kayansa inda matarsa take, gaban yasmeen yashiga faďuwa, miyasa baza'a kama masa ďakiba, kosu zauna da mas'ud, itako batason su kasance đaki đaya da Nawaf, bare yanzu daya tsaneta, ta lura ko ganinta baya sonyi, amma babu yanda zatayi tunda umarnin papa ne.
Nawaf ya mi'ke yana dogara sanda yanufi ďakin yasmeen yana faďin bari naje nayi wanka saida safenku, kowa ya ce, "ALLAH yakaimu, momcy ta ce, "yasmeen tashi kema kije saida safe.
Badan tasoba ta mi'ke dan cika umarnin momcy.
Ta tura 'kofar tashiga jiki a sanyaye kamar wadda kwai yafashemawa aciki, Nawaf yana zaune bakin gado yana cire kaya, kallo ďaya yasmeen tayi masa ta kawauda kai.
Shiko aii ko kallon inda take bayyiba, tayi tsaye a tsakkiyar ďakin tana wasa da yatsun hannunta.
Ya mi'ke yanufo inda take dagashi sai ďaurin guntun tawul, ahankali takeja baya azatonta wajenta yataho, daya matso saita matsa, yamatso ta matsa, haka sukaitayi har zuwa jikin 'kofa, ta rintse idanu dan sunje 'karshe, ta manne da 'kofa sosai ga idanunta a runtse, ya'karasa takowa ahankali gurinta yakai jikinsa kusada ita kamar zai ringumeta fuskarnan murtuk ya tsare gida...........................✍🏻

Assalamu alaikum
Nagode da sakwannin gaisawa da addu'ar samun lafiya dakuketa ďawai niyar turomini, harma dama su kirana, , Nagode kwarai da 'kaunarku gareni, nima ina 'kaunarku a duk inda kuke, ALLAH ya barmu tare, ya bar mana zuminci😍😍😘😘💓💓💚💜💖luv u oll!!!!!!!!!!!!!!👌🏻👌🏻

©2016

💞bilyn Abdul💞
💞Mrs Abdus'salam💞
💞luv u oll my fan's😍💞
[1/12, 9:00 PM] mrs bilkisu: ☆☆☆☆☆☆☆
🎾 NAWAFF 🎾
☆☆☆☆☆☆☆

NA BILKISA IBRAHIM💓

Page👉🏻41 & 42
Chapter 33 · 0% Book details