← Book details Nawaff Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 47 OF 51

Sashe 47

Nawaff Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read

Bayan sundawo gida sun gama duk abinda yake al'adar rayuwarsu suka kwanta dan dare mahuta bawa,, yasmeen tana kwance agefen hannun Nawaf ta ce, "shine zaka nemawa su yaseer makaranta amma ni ka lalata mini tawa ko??.
Yashafa kanta yana murmushi to kina kishi da yaseer kenan dgsk??, babu wani kishi, to miye inba kishiba??, ke aii kingama karatunki,, keda kike cikin babbar makaranta mai cike da aikin lada.
Ta 'kara gyara kwanciyar ta tareda rungumeshi, hakane habibina amma wlhy inason karatu sosai,, yajuyo ya rungumeta sosai karki damu my xarah zakicigaba da karatunki, harma saikince kin haji dan kanki, aikine kawai banyarda dashiba,, damun koma Spain zan nema miki makaranta.
Ta 'kan'kameshi sosai tana murna, ta ce, "wlhy ni dama bana karatu dan na samu aiki, inasondai kawai nazama mai ilimi,, saura karatun islamiyya, kai yaka mata kazama malamina mijina.
Yay murmushi waya gayamiki inada kwarewa anan?,, tab ai momcy tabani labainka tun kana yaro, da 'kiriniyar dakayi, ta ce, "min kai Anwar yagado shiyyasa ga yaronnan akwai ilimin addini, kumama kafishi,, dan haka kawai kabada kai..
Ya ce, "shikenan tunda momcy ta fallasa ni insha ALLAHU zamu fara karki damu.
Sunata 'yar hirarsu 'kasa2 har suka fara jin barci, sukayi addu'a suka lula duniyar barci.

Washe gari jirginsu ya ďaga zuwa 'kasa mai tsarki,, tarba akai musu ta mutunci, 'yan uwa cike da gida sunzo tararsu, aginda hajja tsohuwa mai ran 'karfe suka sauka, yasmeen sai ware ido take yau gata a saudia, kasar da aka haifi (mafificin halitta ANNABI MUHAMMAD SALLALLAHU ALAIHI WASALLAMA) (TSIRA DA AMINCI SU 'KARA TABBATA GA SHUGABAN TALIKAI, MAI CETONMU AWATA RANA MAI CIKE DA HARGITSI DA RUĎANI,, ALLAH yasa muna cikin waďanda zai ceta, ameeeeen.)
Lallai yasmeen ta yarda su momcy 'yan gatane, dan family nasu sunada kuďi da ala'ka mai 'karfi tsakaninsu da masarautar saudia,, abinci har rasa wanda zataci tayi, Nawaf sai dariya yake mata wai kartayi 'kauyanci,, itadai shiru tayi masa dan momcy da hajja suna kare mata,, bayan sunci sun 'koshi an gaggaisa da dangi, suka tafi dansu barsu su huta.
Abin yabama yasmeen mamaki dataga an haďasu ďaki ďaya da Nawaf, itakam gsky tanajin kunya,, takira Abdallah ta ce, "yaje yasanar da momcy dan ALLAH araba musu ďaki, dariya Abdallah yayi, ya ce, "Ablah aiko bazasu raba muku ďakiba, dan momcy ma idan sukazo itada papa wlhy ďaki ďaya suke zama.
Idanma na faďa momcy koroni zatayi, kiyi ha'kuri kawai kuyi zaman ku, dan shima Abii ba yarda zaiyiba,, yasmeen ta ce, "ALLAH inajin kunya Abdallah, Abdallah ya fice yana mata dariya.
Bai daďe da fitaba Nawaf yashigo ita harma ta kwanta sannan,, ya shigo yana faďin sorry fancy face nabarki ke kaďaiko, ina wajensu isma'il muna shan hirar zuminci, bayi yashige yay wanka dan azatonsa tayi barci ne..
Bayan ya fito yay shirin barci sannan tayi barcin gsky, sai kawai ya rungume matarsa suka hau barci.
Da asuba tunda yatafi sallah bai dawoba, ta nanan zaune tana laximi saiga wata 'yar yarinya takawo mata dabino guda bakwai, ta ce, "taci, yarinyar ta burge yasmeen, ta zaunar da ita saman cinyarta tana tambayar ya sunanta, yarinya ta ce, sunanta fateema,, woow!! Yasmeen tafaďa, sunanmu ďaya kenan ko, yarinya ta ďaga kai,, duk suna magarne da turanci saikuma larabci ďai2 da yasmeen take sakawa wanda ta iya.
Suna nan zaune Nawaf yashigo dagudu fateema taje ta tarosa ya ďauketa yaďaga sama, suna dariya, yazau bakin gadon yana yana tambayarta tasan yasmeen tace eh, nan sukaita hira shida ita da larabci, yasmeen ta ce, "o ni yar yarinya 'karama ta iya larabcun.
Nawaf yay dariya kajifa xarah da wani zance, to itada yarenta , ke sanda kina 'karama baki iya hausaba, da yaren buzaye??.
Yasmeen ta ce, "na'iya mana, sukai dariya gaba ďaya, ya ce, "fateema jeki amso min dabino nima, tako 'ki'kira da gudu amso dabino, Nawaf yasakko kusada yasmeen yaďan kwantar da kansa a bayanta, cikin taushin murya yace nifa da matsala nazo, yasmeen ta ce, "matsala kuma wace iri??, yay mata zobe da hannayensa cikin kunne ya gwar gwaďa mata suna cikin yin dariya fateema tadawo da dabino, da sauri yasaki yasmeen yana ďan sosa kai, tazo ta haye cinyarsa tana bashi dabinon abaki,, yasmeen ta ce, "kaganka kuwa kuna kama kamar kaika haifeta.
Yay murmushi mai 'kayatarwa yana shafa kan fateema ya ce, "karki damu nima tawa tana nan zuwa,, yasmeen tai 'kasa dakai tana murmushi,, ta ce, "ďiyar waye??, Nawaf ya ce, "ďiyar uncle zaid ce, tunda mamansu tarasu wajen haihuwar 'kanin fateema aka kawosu nan wajen hajja.
Ayya ALLAH yagafarta musu, wlhy harta bani tausayi, su nawane??, su ukune, akwai Nawaf mai sunana, sai muh'd Ariff, sai fateema Wanda tarasu wajen haihuwarsa shima yarasu,, ALLAH sairki ALLAH yaji'kansu.
ameen fancy face.
nansukaita hirarsu harsaida hajja ta aiko su fito suyi break sannan.
Bayan sun kammala break suka ďau gayu, Nawaf yatafi zagawa da yasmeen gidajen dangi, gidansu ummuhabeeba ne na farko, antarbesu da mutunci, ummuhabeeba sai rawar kai ake anga masoyi, yayinda yasmeen ta cika tayi fam, Nawaf ne kawai ya gane halin datake ciki, dayaga zata fashe saiyace ta tashi su tafi,, ummuhabeeba kuma ta ce, "zata bisu itama tayo ziyara, tofa.
Koda suka fito yasmeen saita shige baya, Nawaf ya ce, "k miye haka??, banza tayi masa bata amsaba,, itako ummuhabeeba ko a kwalar rigarta ta buďe gaban mota tashige abinta,, da hausa Nawaf ya ce, "fancy face wai miye haka kikeyi??, baki ta murguďa masa😏batareda ta tankaba.
Ummuhabeeba ta ce, "my luv muje mana, wani haushi ya'kara turni'ke zuciyar yasmeen, wai agabanta akecema mijin ta my luv,, Nawaf yana kallonta tana hawaye ta madubu,, kai kawai ya girgiza dan baisan miya dace yayiba.
Ummuhabeeba ta ce,, A'a yanaga kana nufar ka'aba🕋damune?, muda zamu ziyara,, batareda ya kalletaba ya ce,, "aidama can zamuje nida fancy face, mungama ziyara sai kuma gobe idan ALLAH yakaimu.
Ummuhabeeba taji haushi ta 'kara maimaita sunan wai fancy face, wani ďan 'karamin tsaki taja wanda Nawaf ne kawai yaji, itafa tabiyosune dan azatonta dangi zasu zaga tana kuma bu'katar dangi su tabbatar da soyayya takeyi da Nawaf, tasan dolene asakashi ya aureta.
Amma shine dan wula'kanci yayo masallaci dasu.
Yasamu guri ya tsaida motar, suduka suka fito fuska babu walwala, Nawaf ya ce, "lokacinma sallah yayi, saimushiga muyi sallah idan mun fito saina zagaya dake kiga guraren tarihi ko fancy face??,, bataso tabashi kunya agaban ummuhabeeba dan haka tayi far da idanu ta ce, "hakane habibina,, ummuhabeeba tayi gefe dakanta zuciyarta tana zafi,, yayinda yasmeen ta harari Nawaf,, yay mirmushi yana mata jinjin😃👍🏻.
Haka suka shiga sukayi sallar la'asar,, bayan sunfito yashiga nuna mata wajajen tarihi hannunsa yana ri'ke da nata,, daga baya ummuhabeeba ta ce, "tagaji ya maidata gida.
Ya kalli agigon hannunsa yana murmushi, aii inaga mu bari muyi sallar magriba kawai dan ta gabato, zata iya riskarmu a hanya.
Badan tasoba dole ta ha'kura sukayi sallar magriba accikin masallacin🕋sannan ya maidata gida suma suka koma inda suka fito, yasmeen tanata wani zuzun6ura baki, ita adole kishi ya motsa.....................✍🏻

©2017

💓bilyn Abdul💓
💓Mrs Abdus'salam💓
💓luv u oll my fan's😘💓
[1/12, 9:11 PM] mrs bilkisu: ☆☆☆☆☆☆☆
🎾 NAWAFF 🎾
☆☆☆☆☆☆☆

NA BILKISA IBRAHIM💓

Page👉🏻57 & 58
Chapter 47 · 0% Book details