← Book details Nawaff Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 40 OF 51

Sashe 40

Nawaff Part 1 Complete Hausa Novel · about 5 min read

KIRA......hum akwai wasu mutane dasuke faďar adaren farko ba'a shan wahala,, ban 'karyatasuba bankuma yarda dasuba,, saidai inaso natuna musu cewa dukkan macen data ri'ke martabarta zuwa gidan miji tofa dolene tafuskanci wannan ranar, kuma tabbas wannan wahalar dasuke 'karyatawa saitashata.
Nibanga laifin marubutaba dasuke tsoratar damu akan daren farko, hakan abune mai'kyau, kuma waďanda basuda aure zasuso tattalin nasu budurcin harzuwa wannan rana, domin kwaďayi samun tagomashin albarka da darajar wannan rana, amma ina kira agareku kudaina ďaukar dole sai anmallaka muku wata 'kyauta a washegarin wannan ranar, suma kuma mazajenmu suzama masu daraja dukkan macen dasuka samu acikakkiyar mace.
Amma akwai dalilan dasuke sawa mace tarasa budurcinta koda bata hanyar zinaba.
☆1 ďaukar abu mainauyi yakansamu rasa budurcinmu, amma bazai hana mace taji zafiba koda kaďanne awannan rana, domin itace rana tafarko data fara sanin ďa namiji.
🙈.

☆2 hanya tabiyu itace yawan tsallaka abu, ko hawa bishiya, gudu, ko yawan tsalle2, dakuma horo da akebama yara amakaranta, kamarsu tsallen kwaďo, gwale2 da makaman tansu.
tokam waďan nan hanyoyin sukansa mace ta rasa yanar budurcinta.

☆3 saikuma hanya ta uku,, wa'iyazubillah, ita ce hanyar maďugo, tabas mata sukan rasa budurcinsu ta wannan hanyar, miji bazai ganki da darajaba, gakuma ďunbin zunubi awajen ubangiji,, wasuma basa sha'awar yin aure saboda sheďanci da bushewar zuciya sun kanainayesu.
Ya ALLAH ka tserar damu,, kakuma ganardamu, katsaremana kakanninmu da iyayenmu da yayyanemu da 'kawayenmu da 'kannenmu, da 'yayanmu daga faďawa halaka,, ALLAH yashirya masuyi, damasu sha'awar aikatawa ya ALLAH ka tausasa zukatansu.
Amma mata yakamata mucigaba da gane muhimmancin budurci da tasirinsa acikin rayuwar aurenmu, ALLAH yabama 'yan baya ikon kai nasu budurcin suma inda yadace, ameen🙏🏻👍🏻.

Nawaf ya canja kayansa zuwa jallabiya, sannan yafito domin ďakkoma yasmeen wata rigar danyin sallar magriba.
Afalo yay arba da momcy, tadawo hannunta ďauke da shayi da magunguna, tawuce batareda ta kalli inda Nawaf yakeba, shima baice komaiba yawuce ďakin yasmeen, saidai jikinsa asanyaye, bayaso yaga momcy ko papa suna fushi dashi, ya'karasa ďakin yaďako ma yasmeen wata doguwar rigar, sanda yadawo momcy tana bama yasmeen shayi ALLAH yasoshima da rigar wanka ajikinta.
Ya ajiye kayan saman gadon yana kallon yasmeen 'kasa2, ahankali ta ce, "mom na'koshi, lalla6ata momcy tayi taďan 'kara sannan taba magani tasha ta kwanta.
Momcy tami'ke tafice tana harar Nawaf dayake zaune bakin gado ya rabga uban tagumi.
Bayan fitarta yatashi yakoma kusada yasmeen, ya zame 'karamin tawul ďin data nannaďe kanta dashi dan sumarta ta tsane,, ya wargaza gashin akan filo yana faďin kibarsa haka yasha iska.
Ya tsuggunno ya sumbaci kumatunta sannan ya ce, "naje masallaci saina dawo.
Tana jinsa duk abinda yakeyi amma ko motsi batayiba, bayan fitarsa tayi murmushi tareda zirarar da hawaye,, tabbas batayi ba'kincin abinda Nawaf yaymataba saidai tasha wala, dan Nawaf damugunta yazo mata kokuma gaggawa, amma hakan bazai sa taji haushinsaba kota tsanesa, saima take ganin yanzune zai sota da 'kyaunarta harma da ganin girmanta, tatuna irin sambatu da addu'oin daya ringa zubo mata, yafaďa mata ita kaďaice abin sonsa, kuma yadaďe yana 'kaunarta, shin da gskne kokuwa dan baya cikin hankalinsane??.
To komadai miye lokaci zai nuna, kuma tana sauraren zuwan lokacin, amma tabbas itakam takamu da son mijinta mai tsanani, musamman ma yau daya sake kusanta kansa da ita, haka tayita zancen zuci har barci ya kwasheta.
Nawaf daya dawo daga sallah saiya wuce wajan momcy danya bata ha'kuri, Aďakinta yasameta tana lazumi, yazauna kusada ita yana wani sissinkuyar da kai.
Momcy ta shafa addu'ar tana faďin kai kuma lafiya??, Nawaf ya'kara 'kasa da kai yana faďin sorry momcy, dan ALLAH kiyi ha'kuri da duk laifin dakike ganin nayi miki, na ďauki laifina kuma insha ALLAHU zan gyara, bakuma zan sakeba, insha ALLAHU yanzu zamu zauna lafiya nida yasmeen harma mu sakaku farin ciki, dan ALLAH karkuyi fushi dani plz.
Momcy taja ajiyar zuciya, amma kasandai abbuna baka 'kyautaba ko??, kasan wannan ba halin kwarai bane, matarka tanada hakki akanka, kaima kasani, kuma ka girmeta ka fita hankali, dammi zaka biye mata ku aikata abinda bai daceba, yasmeen yarinyace mai hankali da nutsuwa, kowa ya zauna da'ita saiya sota.
Hakane momcy, nima ďin ko adaďin ina 'kaunarta sharrin shaiďanne kawai, amma insha ALLAHU baza'a sakeba.
To shikenan ALLAH yabaku zaman lafiya yakuma baku zuriya tagari.
Nawaf ya amsa akan la66ansa da ameen, nandai momcy tayi masa nasihohi, sannan yami'ke ya ce, "momcy papa fa??, yana ďakinsa momcy tafaďa, kaje ku gaisa mana,, A'a momcy barsa sai gobe idan ALLAH yakaimu, yau nasan inada laifi awajensa, gashi nabar Yasmeen ita kaďai.
Momcy tayi murmushi ta ce, "to saida safe, idan ta tashi kace inamata sannu.
To my dear mom zataji yafaďa yana fita.

Afalonsa ya isake Abdallah da Anwar wai sunzo dubashi, ya zauna suka gaisa, da tambayarsa ya jiki??, ya ce, "da sau'ki sosai, Anwar ya ce, "abi wai ina abla??.
Tana ďaki tana barci, barci kuma yaya?, tun yanzu ko itama batada lafiyarne??, Nawaf ya girgiza kai yana hararar Abdallah, sai ba'ada lafiya ake kwanciyar wuri, kunga saida safe kutashi ku tafi..
Anwar ya shagwa6e fuska kai abi hirafa mukazo muku, kuma saika koremu.
A'a niba kirarku nakeba, kuje gobe idan ALLAH yakaimu kwazo hirar nima zuwa zanyi na kwanta, badan sunsoba suka mi'ke kowa yana zum'bura baki.
Nawaf yarufe 'kofar yakashe komai yanufi ďakinsa,, wani irin farincikine ke ďawainiya dashi, ya 'karasa kangadon ya zauna kusada fuskar yasmeen, ya tsura mata fararen idanunsa tanata barcinta hankali kwance, ahankali numfashinta yake fita, ta cure waje ďaya kamar ďa acikin uwarsa.
Nawaf yay murmushi yana shafa sumar kanta, data bazu akan filo har saman fuskarta, yasaka ďanyatsa ďaya ya janye wasu gashi dasuka rufe mata fuska, ahankali yafurta ALLAH yay miki albarka yabarmu tare har abada, ALLAH yabamu 'ya'ya masu 'kyawawan halayenki, yadu'ka ya sumbaci goshinta, tasaki wani lallausan murmushi tamkar idonta biyu.
Shima murmushin yasaki, yami'ke yacanja kayansa zuwa nabarci bayan yagama zuba sambatunsa, da zazzagawa yasmeen kalamn 'kauna batareda tasaniba.
Gadon yahawo ya cire mata bargon sannan ya canja mata rigar wankan zuwa ta barci, yay musu addu'a tareda rungume matarsa suka lula duniyar barci.

Da asuba tarigashi tashi, dan haka ta sulale zuwa ďakinta, acan tayi sallah takoma barci harda kulle 'kofa.
Fitarta babu daďewa Nawaf yatashi, ya laluba bata nan, saiya mi'ke yana murmushi, shima alwala yayi yafice masallaci, koda yadawo saiya nufi ďakin yasmeen, amma 'kofar arufe, ďakainsa ya wuce yakwanta shima...............✍🏻

Kuyi ha'kuri yaudai babu yawa ina busy ne.

©2017

💗bilyn Abdul💗
💓Mrs Abdus'salam💓
💗luv u oll my fan's😘💗
[1/12, 9:00 PM] mrs bilkisu: ☆☆☆☆☆☆☆
🎾 NAWAFF 🎾
☆☆☆☆☆☆☆

NA BILKISA IBRAHIM💓

Page👉🏻47 & 48
Chapter 40 · 0% Book details