← Book details Nawaff Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 42 OF 51

Sashe 42

Nawaff Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Suma su yasmeen ana 'kuryar ďaki itada tata aminiyar, Ameena ta ce, "yasmeen mike damunkine wai??, yasmeen tayi kwalkwal da idanu tana shirin yin kuka, cikin rawar murya ta ce, "Ameena mugunnan yasameni abanza batareda yafara sonaba kamar yanda muka shirya dake.
Ameena tazaro idanu kai sis... garin yaya hakan tafarune?, yasmeen tafaďa mata yanda sukayi da umma jiya, taďora dafaďin dagafa bashi ha'kuri yay min faďe, dan nidai faďe zan kira wannan wlhy.
Ameena tayi dariya A'a babu wani faďe, mutum da matarsa sai ace yayi faďe, kice 'yar uwa angirma,, yasmeen ta harareta kin ganki ko zaki fara.
Ameena tadafata tana dariya yiha'kuri amarsu, haba shiyyasa naga Nawaf yanata fara'a ga 'kyallin angwanci yanayi.
Harrarta yasmeen tasakeyi, tana kaimata duka da filo, itakuma Ameena tana tuntsura dariya dabata ha'kuri, tari'ke filon tana sassauta dariyarta, kinga yi ha'kuri na daina, yanzudai ya ake cikine??.
Yasmeen ta ce, "ai saina garashi nima, dan bazai shani abanzaba, duk muguntar dayayimin saina rama,, A'a yasmeen kawai kishare, kinga ko ada kema kina masa rashin kunya, kinga kenan kowa yana ta6a kowa, kawai ki ringumi mijinki ku zauna lafiya, fatanmu yanzu kuma muga sakamako kawai, kayan harka na nan zan aiko haleematu takawo miki.
Cikin rashin fahimta yasmeen ta ce, "miye kuma kayan harka??, saida ameena tayi 'yar dariya sannan ta zayyane mata komai, tab ALLAH yakiyaye yasmeen tafaďa, ni nasha wani abu, kina ganin ba'kar wahalar danasha hannun mugunnan jiya, ke kobansha wahalaba babu abinda zansha inma gaya miki gsky, kawai saina zauna nayita ďirkar magani batareda ciwoba, 'katon banza yayta shan romo yana raina mini hankali ko,, aii badan wannan nazo duniyaba 'yammata.
Oh oh yarinya zaki shane, ina zaune zakizomin da zancen, idan ALLAH yabaki fitinannen miji irin mas'ud wlhy dole kisha, kuma ina nan dake zaki bani labarine.
Baki yasmeen ta ta6e ke nifa bazan zauna yamaidani wata kasar takawarsaba,, dan haka kima daina saran zan sakko wataran.
😂'yammata kenan mudai 'yan kallone, yasmeen ta ce, "uhmmmm keni mubar wannan zance kitso najeson yi yaza'ayine?, wake miki kitso?.
Uhmmmm wata yarinyace a 'kasan layinnan, idan kin shirya sainasa su halimatu su kawo miki ita, to shikenan amma kinsan halimatu bata zuwa gidannan saboda momcy ko??.
Hhhh ke bar 'yar iska amma ai batajin kunyar yin zancen Abdallah gaban mami ko?.
A'a shima ai hakan take, ko agaban papa labarin masoyiyarsa yake, ranar inaji modebbo yana masa masifa wai bashida kunya.
Tofa kaji manya su kunyar garesu?, 'k wai kema modebbon kike cemasane??, yasmeen ta ta6e baki keni duk sunan dayazo min nasa faďa nakeyi wlhy, A 'yammata yakama acanja masa suna.
Yasmeen ta ce, "k bayanzuba saiya jigatu sannan, dan idan nabarsa haka yaga lagona.
Hummm yarinya kidaibi ahankali, mazan nan sunada hanyoyin maganinmu kala2, danhaka atafi a slowly..
Suka tuntsure da dariya harda tafawa.
Nawaf yaturo 'kofar yashigo da sallama, Ameena ce kawai ta amsa masa, ya ce, "masu hira bari muje masallaci, kuma kutashi kuyi sallah.
Ameena ta ce, "to, saikun dawo, harya kai 'kofa saikuma yadawo, yadu'ko ya sumbaci kumatun yasmeen, dasauri taďago tana kallonsa saiya ďaga mata gira yana murmushi ya fice.
Ameena tayi dariya tana faďin soyayya ruwan zuma, 'yar uwa kibada kai kaiwai bori ya hau, tunda kuduka kun kamu, harararta yasmeen tayi tashige bayi domin yo alwala.
Ameena taci gaba da dariyarta tana faďin anaso ana kaiwa kasuwa.
Bayan sun idar da sallah suka dawo falo, abincin dasu talatu suka kawo yasmeen ta jera musu akan daining.
Suma su Nawaf bayan sun dawo daga sallah wajensu momcy sukaje suka gaishesu, zuciyar Nawaf tanata dukan uku2, amma abin mamaki papa baimasa faďanba, yasan saboda suna tareda mas'udne shiyyasa ya 'kyaleshi.
Yasmeen ta kalli Ameena, wlhy 'yar uwa inason zuwa gaidasu momcy amma inajin kunya, wannan gay ďin dukshi yaja min wlhy, saitaji Nawaf ya ce, "zomuje narakaki tunda nine naja miki.
Dasauri suka juyo inda maganar tasa take, ashe tun đazu sun shugo suna tsayene kawai suna kallonsu yasmeen.
Su mas'ud suka 'karaso suka zauna, yasmeen ta zuba musu abincin amma ta'ki yadda su haďa ido da Nawaf, ta turama kowa gabansa, ita kuma tazuba ďan kaďan, Nawaf ya kalleta xarah wannan abincin fa??, ta ce, "kamar yaya??, yajawo kujerarsa kusada ita batareda yayi maganaba, yabuďe kulan abincin ya 'kara mata, da sauri ta ce, "wazaici wannan abincin??.
Ke mana, ko kina nufin zancigaba da barinki da yunwa? Tun jiya rabonki dacin abincifa, gama magani nan mas'ud yakawo miki, idan kin gama saiki she.
, ta shagwa6e fuska nifa lafiyata 'kalau, Nawaf ya murmusa nima nasan lafiyarki 'kalau fancy face, saidai yanada 'kyau kisha maganin dan tafiyarki tadawo dai2... ya 'kare maganar ahankali yandasu Ameena bazasujiba.
Ya ďauki cokalin ya ďibi abinci yakai bakinta, ta kauda kai gefe tana faďin kabari zanci dakaina, A'a ban yardaba, ta ce, "ALLAH zanci dakaina.
To naji kar6i wannan saina barki kici dakanki ďin, bataso suyita ja'inja agabansu mas'ud shiyyasa ta kar6a, yawani kashe mata ido ďaya wanda har murmushi yanemi su6uce mata amma saita dake, haka taita tura abincin badan yana mata daďiba, su Nawaf suna hirarsu amma ita tayi shiru abinta, bayan sun kammla suka dawo falo suna hirarsu.
Sai bayan la'asar su ameena suka tafi gida, dan mas'ud yanada aikin dare yau, tunda suka tafi yasmeen taje wajensu momcy tayi zamanta dukda ďunbin kunyar momcy datakeji, shima Nawaf bai dawoba sai bayan isha'i, shima 6angarensu momcy yanufa acan ya tararda yasmeen suna hira itadasu Anwar.
Ya zauna suka gaisa da momcy, su Anwar suka gaisheshi, sunanan zaune shi yana latsa waya sukuma suna hira, soyake su tafi kafin papa ya ritsashi amma yarasa yanda zaima yasmeen maga, yana zancen zuci sai sukaji sallamar papa.
Yashigo falon kowa ya rissina yana gaisheshi, ya amsa yana zama, momcy takawo masa ruwa yasha, yami'ke yana faďin modebbo zonan, jikin Nawaf asanyaye yabi papa ďakinsa, afalo suka yada zango, yasmeen yazauna 'kasa papa yana saman kujera.
Papa ya ce, "modebbo dama abinda kake aikatawa kenan ban saniba??, Nawaf yaďago fararen idanuwansa yana kallon papa, cikin raunin murya ya ce, "papa miya faru??, cikin faďa papa ya ce, "o, bakasanma miya faruba ko??, papa yashiga yimasa faďa tamkar zai dakesa, ta inda yake shiga batanan yake fitaba, saida yaymasa tatas sannan ya ce, "ni tashi kabani waje mutumin banza.
Nawaf ya ce, "kayi ha'kuri papa na amsa laifina amma insha ALLAHU hakan bazata sake faruwaba, kuma mun daidaita itama nabata ha'kuri.
Papa ya ce, "wannan kuma kaika sani, idan kabari ta su6uce maka aikaika jiwo baniba, tashi kabani guri nace.
Nawaf yami'ke yafito dama yasan papa bazai saurareshiba a yau saiya huce.
Yafito falo wajensu yasmeen fuskarsa babu walwala ya ce, "yasmeen tashi mutafi,, ta ďaure fuska katafi ni anan zan kwanafa,, shuru yay yana kallonta, yazata momcy zata mata magana amma saiyaji tayi shiru bata samusu bakiba, ya daure ya ce, "bangane anan zaki kwanaba?, gidankifa?, yasmeen tayi kwalkwal da ido kamar zatayi kuka ta ce, "nidai anan zan kwana kawai.
Jiki asanyaye yafice batareda ya'kara maganaba bare ya ce musu "saida safe", itako mom 'kala batace musuba, daga 'karshema saita tashi ta tafi ďakin papa.
Nawaf yafaďa saman gado yana maida numfashi, yakula mitin aka haďa saboda shi kenan,, zaikuwa basu mamaki, zai nunawa yasmeen shima bai damu da itaba.
Itako tayi kwanciyarta acan abinta, shikam haka yayta zarya tsakanin falo da bedroom, yazata daga baya momcy zata saka yasmeen ta taho, amma shiru kamar an aiki bawa garinsu, daga 'karshe yaha'kura yakwanta.

Haka sukaita 'yar wasan 6uya shida yasmeen har tsawon kwana huďu, tayi zamanta a ďakin momcy, kotana falo dataji sallamarsa saita koma ďaki ta kulle, tun Nawaf yana ďaukar abin wasa har yafara bashi haushi, yakoma bashi tsoro, dan akowace da'ki'ka son yasmeen 'karuwa yake azuciyarsa, gashi kuma ta hanashi damar dazai nuna mata ainahin gsky sa, momcy kuma tayi kunnen uwar shegu dasu, ta'ki tayima yasmeen magana ko kaďan, dukda tana kallon zaman doya da manjan dasukeyi, amma saita maida kanta makauniya.
Itama yasmeen a 6angarenta tana jigatuwa da horon datakemusu dan harda kanta take horawa, kewar Nawaf dukta gallabi zuciyarta, idan yashigo haka zatayita le 'kensa ta kafar makulli, dukta rame akwana huďu, sai wani fari datayi fauu.
Amma haka zata cigaba da daurewa har komai ya daidaita.

Yau dawuri mutan gidan suka kwanta sakamakon gajiya dasukayi, dansunje wani biki, kowa yana ďakinsa kwance wasuma harsunyi barci irinsu yasmeen, Nawaf kam yanacan yakasa rintsawa, ya buďe wardrobe ya ďakko kayan daya cire, wani mukulli yaďakko acikin aljuhun rigarsa yakallesa yay murmushi, tirare ya 'kara fesama jikinsa, yasaka silifas yafice bayan yakashe komai.
Ahankali yatura 'kofa yashiga 6angaren momcy ta 'kofar baya, yashgo ta kichin dan ba'a kulleta dama.
Falon babu kowa anma kashe fitilar, dagaji kasan kowa yayi barci, Nawaf yay murmushin mugunta, yasaka key ďin yabuďe ďakin momcy, yamaida yakulle ahankali, fitilar ďakin akashe take, danhaka yataka ahankali zuwa bakin gadon, wayarsa ya danna ya haska yasmeen dake kwance ta 6ararraje tana sharar barci agadon momcy, yasaki wani 'kayataccen murmushi, yaďaga bargon ahankali yashige, tareda rungume yasmeen zuwa jikinsa.
Afirgice tafarka, tako buďe baki zatayi ihu, Nawaf yay saurin toshe mata baki da hannunsa ďaya, cikin kunnenta ya ce, "k karki taramin mutane ninefa...................✍🏻

Tofa 'ka'karaka 'ka'ka, kudai biyoni kawai😃👌🏻

©2017

💓bilyn Abdul💓
💓Mrs Abdus'salam💓
💓luv u oll my fan's😘 💓
[1/12, 9:00 PM] mrs bilkisu: ☆☆☆☆☆☆☆
🎾 NAWAFF 🎾
☆☆☆☆☆☆☆

NA BILKISA IBRAHIM💔

Page👉🏻49 & 50
Chapter 42 · 0% Book details