← Book details Nawaff Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 15 OF 51

Sashe 15

Nawaff Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read

......yau tun farar safiya faisal yazo gidansu yasmeen, tana tana shara a tsakar gida yashigo, zumbur tami'ke tana fitar da numfashi cikin sar'kewa, saikace wadda tayi gudun fanfala'ke.
A silo ya 'karaso gareta, hannu yakai da zummar ta6ata, ta kauce da sauri tana harara sa, cikin masifa ta ce, "kai malam bakada hankaline??.
Murmushin takaici faisal yayi, ya ce, "indai akan sonkine to banida hankali yasmeen.
Ya dur'kusa agabanta tamkar uwarshi, hawaye nata zirara bisa kumatunsa, cikin raunin murya ya ce, "yasmeen plz ki taimakeni ki dawo gareni, nine kawai nake miki soyayyar gsky, wlhy abinda kikaga yafaru sharrin shaid'an ne, da makircin hisham.
Ta6e baki yasmeen tayi, ta ce, "kaga banida matsala da wannan, kuma ina mai gargad'inka daga yau karka sake koda kuskuren ta6ani, kai kanka kasan ada ban amince ka ta6a jikinaba bare yanzu danakeda aure....
Da sauri abba yafito domin jin hayaniyar tayi yawa, turus yayi domin tozali da faisal tsugunne a gaban yasmeen.
Abba ya 'karaso yana tambayar lafiya dai ko??.
Suduka suka dawo da kallonsu gareshi, yasmeen tafara zubar da hawaye tana nuna faisal, shima dai faisal d'in kuka yake, ya mi'ke ahankali yaje wajen abba, dur'kushewa yayi agabansa ya kama 'kafafunsa yari'ke yana gunjin kuka.
Hannu biyu abba yasa ya d'agoshi, haba faisal babba dakai ka zauna kana kuka?, miya faru kake kukane??.
Hannu faisal yasaka ya share hawayen fuskarsa, yashiga zayyano kalaman nadama daban ha'kuri ga abba, da ro'konsa akan yabashi yasmeen a karo nabiyu zai gyara halinsa.
Abba ya ce, "kayi ha'kuri faisal yanzu banida iko akan yasmeen, mijinta shike da iko da'ita, kayi ha'kuri ALLAH zai babaka wadda ya fita insha ALLAH.
faisal ya langa6e kai yana hawaye, itama yasmeen hawayen takeyi dan jitake tana wani son faisal d'in yanzu.
Ahaka yaseer da umma suka fito suka samesu, yaseer ya ta6e baki danshi faisal baya bashi tausayi ko kad'an.
Itama umma lalashi da nasiha takeyima Faisal, amma faisal ba gane yaren nasu yakeyiba, danshi burinshi kawai abashi yasmeen, itace kad'ai nasihar dazatayi masa tasiri.
Babu dad'ewa saiga hajiya jummai da dadyn faisal.
Suma saisuka kama hawayen dan suna tausayin d'ansu, abba ya ce, "yakamata suje ciki dan wajen akwai sanyi.
Bayan sun zazzauna afalo, su alhaji buba sukacigaba da ro'kon abba akan yabama faisal yasmeen a karo na biyu.
Abba ya ce, "bansan irin bayanin dazan muku ku fahimceniba, amma yakamata ku gane igiyar auren yasmeen ba'a hannuna takeba, bakuma yanda za'ayi nakira yaronnan na tsareshi akan yasaki yasmeen, kofa na aikata hakan tofa auren bai sakuba tunda ni ba mahaifinsa bane.
Kuyi ha'kuri muci gaba da yima faisal addu'ar fatan alkairi....
Afusace alhaji buba yami'ke yana masifa, kai malam yazaka zauna kana jamana rai akan abinda baifi 'karfinmuba, harzaka wanice bayanda zakayi kasaka yaron yasaki yasmeen, shin wai bakada tausayine, baka ganin halin da d'ana d'aya tilo yashigane??, kodan kuna ganin 'yarku tanada 'kyaune??....
Abba ya 'katse Alhaji buba ta hanyar d'aga masa hannu🖐🏻, kaga karka gaya mini magana, ai bani na ce, "faisal ya saki yasmeen bako??, ko kai ka manta da wula'kantani dayayi acikin taron jama'a ba yasaki tawa d'iyar ba!, sannan wanda kake magana na saka yasaketa shine ya share mana hawayenmu!!, to kuma saboda son zuciya saina sakashi yasaki yasmeen saboda faisal ya aureta???..
Hajiya jummai ta ce, "dan ALLAH kuyi ha'kuri, agaban yarafa muke, da'kyar suka lafa da hayaniyar dasukeyi.
Alhaji buba ya ce, "kutashi mu tafi, kuma inaso kasaka a zuciyarka ka mallaki yasmeen ka gama, yana gama fad'a yaja hannun faisal da hajiya jummai sukayi waje.
Kuka yasmeen tafasa ta zube afalo tana birgima, umma tasa hannu ta d'agota tana lallashi, abba ya ce, "mamana kiyi shurinki, babu abinda suka isa suyi miki, kuma nanda sati uku insha ALLAHU kina d'akin mijinki.
Ni ban ta6a ganin jahilan mutane irinsu alhaji buba ba, in banda jahilci yazakuce wani yasaki matarsa d'anku ya aura, bayan kuma shine yafara tozartamu agaban mutane yasiki yarinyar atake agurin da'aka d'aura musu aure.
Umma ta ce, "babu wani jahilci malam son cuciyane kawai yake damunsu, 'kila atunaninsu mu bamu san darajar 'yarba ko???.
To aiko zanyi maganin son zuciyarsu kwananan.

Yaseer kuwa d'aki yashige yashiga kiran number d'in Nawaf, saidai yayi masa kira yakai biyar bai d'aukaba, dan haka ya ha'kura yay shirin makaranta yatafi.
________________________

Alokacin da yaseer yake kiran Nawaf baya kusada wayoyinsa, yana wajen motsa jiki dayake fita akowace safiyar duniya, inhar yana 9ja.
Sai wajen 'karfe 8:00am yashigo gidan jikinsa sanye da farin JC, gajeren wando da 'karamar riga mara hannu, 'kabarsa sanye da takalmin 'yan kwallo, dad'an gudunsa yashigo gidan, yasaka robar ruwan dake hannunsa cikin bola, key yasa yabud'e d'akinsa ya shige.
Saida yasha ruwa sosai sannan yazauna yana zufa ya fitar da huci mai zafi daga bakinsa, ya kwantar da kansa saman kujera ya lumshe idanu, yakai minti5 ahaka daga bisani ya cire takalman 'kafarsa ya ajiye.
Bedroom d'insa yashiga, yacire kayan ya jefa cikin wani dogon kwando, ya bud'e wata 'yar durowa dake kusada bayi (bathroom) tawul ne aciki kala2, yad'akko kalar yellow ya d'aura daga 'kugu zuwa guywa.
Wanka yashiga, ammafa ya dad'e, dan nikam harna fara gajiya ma da jira, ya kai tsawon minti50 sannan yafito, d'aure da tawul d'insa, hannunsa ri'ke da 'karami fari yana goge sumarsa.
Zama yayi yashiga tsara ado, na ce, "kai gay d'inana d'an kwalisa ne gsky.
Kwalliyarma yakai tsawon lokaci yana tsarata saikace mace lol, daga 'karshe yafito sanye cikin 'kananun kaya ya d'ora tafkekiyar rigar sanyi jaa mai 'kyalli saboda yanayin sanyin garin, sai zabga 'kamshi yakeyi.
Zama yayi yay break, sanan ya jawo phones d'insa, ya kira wad'anda suka kirashi baya nan, haryazo kan number d'in yaseer, kira yashiga yi amma ba'a d'agaba, yasake kira, harta kusa katsewa aka d'aga.
Mai makon yaji muryar yaseer sai yajita yasmeen, cikin muryarta mai za'ki ta ce, "mai wayar baya nan!.
Nawaf ya ce, "ina yaje??.
Ita bata gane Nawaf bane, ta ce, "yaje school, amma idan yadawo za'a sanar masa.
Daya kula bata ganeshiba saiyayi niyyar zolayarta, ya ce, "toke wacece?.
Saida taja numfashi sanan ta ce, "yayarsace.
Saida yad'an ta6e baki sanan ya ce, "hummm kodai 'kanwarsa, dan dagajin muryarki "k, yarinya 'karamace.
Cikin 'kufula yasmeen ta ce, "kai malam sai anjima, kabi duk ishii mutane da surutu, d'if ta kashe wayar.
Dariya sosai Nawaf yayi, ya ce, "kai yarinyarnan 'yar bala'ice wlhy, dawata muryarta kamar ta gyare.
Yashiga kwaywayon muryarta yana dariya, tamkar mai kallon film ko wa'ka.

--------------''''''---------------------
Da yamma abba ya kira papa awaya yay masa bayanin komai, game da abinda yafaru da safe, maganar ta bama papa mamaki saikace a wasan kwaikwayo, kasaki mace kadawo kana hauka wai kana sonta.
Papa ya ce, "karya damu zuwa gobe zaizo suyi magana, yasmeen ta tare kawai agindasa, ta 'karasa karatun a d'akinta.
Papa yaji dad'in hakan, yakuma yi farin ciki, koda yagayama umma itama murna taitayi dan wanan shine kawai maganin son zuciya irin na alhaji buba da d'ansu.
Yasmeen kuwa batayi murna da hakanba, dan itafa har yanzu zuciyarta bata wani saisaita mata zama da Nawaf ba, tana masa kallon mugune mara mutunci, darashin girmama d'an adam.
To yasmeen koma dai miye?, lokacine zai nuna wannan.
Chapter 15 · 0% Book details