Sashe 4
Mutallab Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
yashe a asa suka fara cin karo jini na zuba a gefen goshinta an tofinta a banka e Allah Ya sa ba yara a wajan cikin hanzari Sa'adah ta nufeta tana girgizata ta juya ta yi wa Bafullatana alama data bata ruwa bata fahimci komai sai kawai ta kinkimo ruwa bokici guda ta kwarawa Inna Binta ajjiyar zuwa ta sauke a firgice ta mi e zaune tana furta "Dambun Mufee, a kawo auki jama'a dambun Mufee an ta'adda za su kashe ni" ta ame hannunta jikinta ya ji e jagab amma har yanzu dambun na hannunta ta mi e ganin Sa'adah da Bafullatana sai kuma ta ja tsaki "Irin bala'i wallahi Ammo ta haifawa unguwar Birget masifa ai da ai zai dinga kashe mu yana zu e jininmu ku duba wannan yarinyar ma ya kashe ta kari na uku" Idanun Sa'adah ya cika da hawaye amma ta auke kai ba tare data tanka Inna Binta ba. Inna Binta ta watsawa Bafullatana harara wacce ke ta ihu tana ta o Sa'adah ta ja tsaki "Kurman banza da wofi gayya masifar, daga haihuwar kurma sai ta an jagaliya" tana kaiwa nan ta shige da inta ta samu Mufee tana bacci ta yi maza ta tashe ta, tura mata an guntun dambun ta yi a baki bayan ta cinye ta ce "to sha ruwa kiji abin da kika samu sai kuma gobe, ki yi addu'a ki goge Allah ki gode Muhammadur Rasulullah. Banda ina bu e ido a gidan nan kema mutuwa za ki yi saboda yunwa kamar taki ar'uwar" sai kuma saka dariya sosai "Inna mene?" "Tukunyar dambu ta kife dan ubanki da tuni ba ki lasa ba kema" Mufee dai ta bu e manyan idanunta irin na Mutallab tana kallon Inna Binta. Ammo ta dinga bin Sa'adah da idanu ganin yadda take kuka kamar ranta zai fita, Bafullatana kuma ta ha e rai sai girgiza kai take "Ammo don Allah ina Mutallab yake? Da gaske ya dawo an sake shi? Sun wanke shi daga zargin da ake masa, yana ina?" Ammo ta auke idanunta zuwa can gefe tana kallon wani waje daban a akin nata can ta ce "Ki daina kira mini sunansa sallamamman yaron nan a kunnena Sa'adah, ki yi hankali watarana zai iya kashe ki" "Ba zai ta a kashe ni ba, duk lalacewar shi jinina ne an'uwana ne a wannan halin da yake ciki na auka za ki yi murna Ammo? Za ki ja yaronki jikinki ki nuna masa kulawa gudun kar ya sake lalacewa, kar ki ce za ki yi abin da kikai a baya duk lalacewar Mutallab kece wacce kika haife shi, tun yana aramin kin san zuciyarsa yadda yake da zafin nama taurin kai. Kin san yadda yake da ulafucin uwa kodayaushe yana manne dake, me ya sa za ki yi haka?" Mi ewa Ammo ta yi ta nunawa Sa'adah hanya ta ce "Tashi ki tafi gidan mijinki, banga dalilin zuwanku ba ni bani da wani a Mutallab kuma na sani kuskurena ya saka na haifeshi. Wallahi kika sake yi mini maganar tsinannen yaron nan sai na daina amsa gaisuwar ki har abada" tana kaiwa nan ta fice ta bar musu akin, fuuu Bafullatana ta fice daga akin zuciyarta na yi mata zafi Sa'adah ta yi shiru ita dai tana mugun son annin nata ai da ba haka yake ba, ya kamata su amshi hakan matsayin addara! Washegari Malam na zaune a rumfa yana sauraren karatun wani sabon almajirin shi. anyaro ne zauna gefe kusa da Malam yana lissafa sabbin ku in hannunsa an dubu-dubu sai she i yake ya duba yaga dubu biyar cif ya mayar aljihu ya zaro ba ar leda mai cike da gurasa da nama ya ya fara ci yana ajjiye lemo fanta a gefe. Ajjiye bulalar Malam ya yi ya ce " anyaro ina ka samu ku i da nama haka?" "Bani aka yi Malam" kafin Malam ya sake magana anyaro ya mi awa Malam ba ar leda guda mai auke da gurasa a ciki da nama ya ha a masa da dubu biyu ya ce "A yiwa su Mufee girki Malam" Jiki na rawa ya amsa yana bu e bakinsa "Da kyau yaron arzi i, ina ka samu ku i fal haka sana'ar me ka fara?" anyaro ya girgiza kai kawai can kuma ya kalli Malam ya ce "Bana yin sana'a, kyauta ake bani kullum, bani ka ai ba har Muhajeed da Iro" Malam ya yi sak tunani fal ransa ya sake kallon anyaro shekarunsa goma rak a duniya a hankali ya mi e ya yi cikin gida. **** A kusan tare manyan motoci biyun suka tunkaro babban gate in ganin ya rigata kai hancin motarsa ya saka ta rage ta fiya, hannunta aya a saman sitiyarin motar ayan kuma ta an ri e fuskarta a hankali ta lumshe idanunta gajiya ce a jikinta sosai da yar take bu e tu a motar don dai bata san wahalar driver ne. "Fiyya" Ya kira sunanta a hankali cikin muryarsa mai cike da nutsuwa ta bu e idanunta da sukai mata nauyi ta kalli wayarta ta manta video call suke yi ma suna ha a idanu da shi ta auke kan ta gefe tana ya motsa fuska "Fiyya na miki wani laifi ne? Kin sauya" "I am sorry ina driving we'll make a call later" ya zuba mata idanu cike da so da auna yana jin ina ma a janyo ranar aurensu da Fiyya a ce gobe ne? Ya sauke numfashi zuciyarsa na bu e a hankali ya ce I adore you Fiyya" ta bu e idanu ta kalli cikin idanunsa sai kuma ta murgu a masa baki ya bu e idanu sosai sai ya girgiza kai yana dariya ya matso da fuskarsa dab da camerar "Na ji kamar ina sha ar numfashinki...." Ya yi shiru jin ana knocking ofar motar da take ciki, itama ta juya ganin wanda yake tsaye ya saka ta an yi murmushi baya ganinta saboda duhun gilas in motar amma murmushi mai kyau ne a fuskarsa. Ta cikin wayar ya ce "Waye?" Tana aukar jakarta a ta aice ta ce "Yaya Junaid ne" "Ok" ya yi sai kuma ya ce "Fiyya" ta ago idanunta da sukai laushi ta kalle shi dasu can asan ma oshi ya ce I love you Fiyya" da sauri ta kashe call in tana ha e fuska ta auki wayar ta fita daga motar. "Yaya J" yana murmushi ya ce "Manager" ta an yi murmushi kawai ya amshi jakar hannunta "Me kika zo da shi" "Ba kyau bincike J" ya jinjina kai suka nufi shiga gate J ya kalli driver ya ce "Ka shigo mata da motar, she left the key inside the car" Fiyya ta marairai ce fuska tana mannewa jik in J ta ce "Yaya J na gaji sosai" "Sannu Manager, ko goyaki zan yi?" Ta bu e idanu sannu yake ta yi mata har suka shiga babban parlon gidan an samari wajan biyar a zaune a parlon duk dawowar su daga aiki kenan. Wajan tare suka dinga cewa "Sannu Manager" ta shige tsakiyar su tana kwanciya a cinyar Marafa ta ce "Thank you brothers, ku yi mini tausa akwai labari" "Gulma dai ba labari ba, daka dawowa ko wanka ba ki yi ba kin zaunawa mutane a jiki azamar banza" Shiru ta yi masa don basu fiye shiri ba sosai ta juya idanunta rufe, tana jin yadda Marafa ke ta danna mata farar afarta. Yaya J kallonta kawai yake with different thinking running on his mind. Gaba aya suka juya jin tafiya cikin sauri ana sakkowa daga saman bene shiru duk sukai suna binsa da idanu domin basu san ya dawo gidan ba, hannunsa aya zube cikin aljihu farar riga ce a jikinsa ta kakin sojoji a gaban rigar wajan gefe an rubuta A.A MARAFA. "Kee!" Ya fa a a tsawace da sauri Fiyya ta bu e idanunta lokaci aya kanta ta sara sosai tsawar ta ratsa kanta, ta mi e zaune fuskarsa babu walwala kamar yadda itama ta yi kicin kicin da rai "Tashi a nan, stupid kawai" ta mi e tsaye tana murgu a baki ko inda yake bata kalla ba ta nufi saman bene kai tsaye da inta ta nufa idanunta cike da bacci ta fa a saman gado cikin aramin lokaci bacci ya auke ta. Firgigit ta farka jin sautin labaran da ake fa a a gidan rediyo wacce take cikin akin nata, ta mi e tsaye ta auki rediyon ta ame a jikinta tare da lumshe idanunta wasu hawaye masu zafi suna shiga bin idanunta. Ta cikin idanunta take hango fuskarsa a lokacin da rigima ta ha a su da ita sai take ganin kamar yanzu ne komai yake faruwa. Students ne an cika sosai saboda class partyn da ake yi na kammala exam maza da mata babu teacher ko aya tunda ta shigo hall in makarantar tasu take duban inda zata ganshi. Cikin sa'a ta ganshi yana zaune saman window sanye da gajeren wando fari tas sai armless in riga wacce duk aka yanke hannunta gashin kansa rabi a aske ya zubawa wani tafkeken gidan masu ku i idanu ta waje baya ko iftawa kamar an ce ya juya ya ganta tsaye ta zuba masa idanu yaja tsaki kafin ta yi magana an shigo an ce "Mutallab, principal yana nemanka an kai arar ka wai kana son Fiyya" Ya ware idanu abin da bai ta a zuwa tunaninsa ba kenan sai kuma ya cije baki "Shi principal in ubana ne Malam Abdullahi kenan?" Ya juya ya kalleta sosai ya ce "Sai godiya, ni? Kuma ke hauka kenan" "Kai ne mahaukaci" furucin ya fita daga bakin Fiyya "Kuma na yi maka nisa, kasan yadda nake da masoya a makarantar nan amma ni ubana ba soyayya ya kawo ni ba, karatu zan yi ina da buri mai fa i da zan cimma" Ya mi e tsaye yana kallonta daga sama har asa a ransa yana issima abu "Shi uban naki can ta matse masa, karatun banza kawai ka zama mai iko shine" "Ba dai ubana sai dai....." Ya bu e idanu sai kuma ya fasa abin da ya yi niyya ganin hawaye a idanunta abin da bai ta a gani ba. Da sauri ta fice