Sashe 2
Mutallab Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
sauka har saman fuskarsa BESTIE haka ya ji saukar muryarta a kunnensa kamar yanzu ne suke tare da ita. Ya sake lumshe idanunsa yana jin saukar dariyarta sosai ya tuna lokacin yana zaune shi ka ai a cikin class ranar aka dawo hutun makaranta shi ka ai ne zaune ciki yana sanye da farar riga sai wando blue black ya ora afarsa aya saman benci tare da yin baya. A hankali ta shigo cikin class in hannunta ri e da lunchbox da textbook sai school bag data goya, hijab inta daidai da irjinta ita ce ta fara shigowa da mamaki take kallonsa zuciyarta na bugawa ta je ga zauna inda yake ta zuba masa idanu sai kuma ta ce "Ka yi holiday assignment?" Ya bu e manyan idanunsa bai ce komai ba ta sake asa da murya ta ce "Na san bama ka yi ba ka daina ha e mini fuska, ka naso a yi ta fa a da kai da teachers" nan ma bai kula ta ba a hankali taci sautin da cikinsa yake yi sai ta jawo lunchbox inta ta bu e tare da tura masa gabansa ta ce "Your breakfast, ka ci kafin a shigo na san baka karya ba" sai a lokacin ya bu e idanu ya juya gaba aya yana kallonta sosai ta yi asa da murya kamar zai yi fa a sai kuma a hankali ya ce "Kuma ga mayunwaci ko?" Ta yi murmushi ta ce "Da yar na jure ban biyoka gida ba, na yi kewar ka sosai bestie" ya yi mata shiru sai kuma ya ha e fuska sosai yana janyo abincin yaga dankali ne aka soya da wai ya yi an tsaki ya ajjiye spoon in ya dam a ya kai bakinsa ta yi saurin kama hannunsa ta ce "Kai baka iya komai bane? Sai a yi maka dariya cin abinci da hannu" ya ware idanu sai kuma ya murtuke fuska ya ture hannunta a hankali duk da muryarsa a kumbure take ya ce "Ki daina kusanta kan ki dani, ni fa ba an iska bane" "Laaa Allah Ya baka ha uri kai duk abin soyayya baka iya ba" a ta aice ya ce "Ke kika santa" ta ja baya tana aga hannu ta ce "Lalala to shikenan ni dai addararka ce, na fa a a gida a yi mini aure, ka san me na ce?" Ya girgiza mata kai kawai yana sake dam o dankalin yana dannawa cikin bakinsa saboda yunwa ko gani baya yi sosai ta bu e gorar ruwa ta mi a masa a hankali ta ce "Na ce su yi mini aure wallahi bana son karatun nan, na ji aure nake so kuma na fa a musu kai nake so, amma wai ban isa ba karatu ya zama dole kuma shekaruna sun yi ka an amma ai ma girma shekararmu 15 years fa, ko kai baka isa aure bane?" Ya yi mata shiru sai ta fashe da kuka sosai ta ce "I love you so much Bestie, don Allah ka aure ni zan zauna dakai a duk yadda kake ka taimakawa rayuwata" ya zame hannunsa tas ta mi a masa tissue ya goge ya ja baya yana lumshe idanunsa har yanzu students basu fara shigowa ba, ta an yi gaba kamar za ta shige masa ya cikin tsawa ya ce "Zan kwa e ki kuwa" "But what if i told you i love bestie? You mean the world to me, wallahi aure nake so ba karatu ba" ta fa a tana shasshe ar kuka sai a lokacin ya kalleta fuska babu walwala ya dubi yadda take kukan sosai ya ce "Ke, babanki ne ya mutu? Ko uwarki ce?" Ta girgiza masa kai ya sake ha e fuska yana rarraba idanu a cikin ajin kamar mai neman wani abu can ya ce "To kece za ki mutu kenan?" Ta girgiza kai sai kuma ta ce "A'a" "Kukan fa?" "Na soyayyarka ne bestie ta irjina ka ji wallahi ni ce addararka ba zaka gane hakan a yanzu ba, da ina da ikon cire abin da nake ji a irjina da na yi hakan ina jin dama na mutu na huta kuma idan ban aure ka ba zuciyata zata iya bugawa" "To gwara ta buga na huta da na ci, shekaruna 15 za ki lalata ni da batun aure, ke tashi ki ware daga nan auki kwananki kar ki ara kawo mini abinci" ta mi e jiki a sanyaye zata bar wajan ya nuna mata lunchbox in daya cinye komai "Ko da i bai yi ba abincin" Sai a lokacin ta kyalkyale da dariya kamar ba ita ta yi kukan ba, dimples inta na lomawa ta ajjiye masa 500 ta yi waje tana cewa "You're my darling jarumina, i love you Mai dawa da jeji" ta fa a tana sake yin dariya tare da yin waje....... Ya yi saurin dafe kansa jikinsa na rawa yana jin dariyar nata na yi masa amasa kuwwa a kunne kamar yanzu ne take yi jikinsa ya auki rawa sosai daidai lokacin aka tura shi cikin motar shiga babu biya, aka nufi kuto. Tun kafin a shigar da shi suka ci karo da wani sa o daya basu mamaki ainun suka tsaya suna kallon juna sosai cike da tsoro da shakku musamman Sp Gali ya juya ya kalli wanda ake zargin a karo na farko yaga ya yi wani irin murmushin kefen baki wanda ya bada sauti kamat na tsaki yana murza kai gefe. Cikin sauri Sp Gali ya ce "Amma wane ya yi hakan? Bayan ba a gama bincike an tabbatar da hakan ba, mene matsayin ran yarinyar daya kashe ina matsayin iyayenta" "Sp Ghali ka yi abin da aka ce, kuto ta wanke shi daga zargin da ake yi masa ku sake shi ya tafi gida baku da ikon ri e shi" Sp Gali ya girgiza kai cike da damuwa ya ce "Sir kana nufin bashi ya kashe ta ba" cikin tsawa ya ce "Ko shine ya zaka yi? Ka yi abin da ya dace a matsayinka na jami'i Sp Ghali karka matsa" jiki a matu ar sanyaye Sp Ghali ya kunce shi tas ya ce "Congratulations. Ka sani shari'a sa anin hankali ce" shi dai bai ce komai ba ya ciri biron gaban rigar Sp Gali ya fara yi masa rubutu a tafin hannunsa dam zuciyar Sp ta buga ganin ya rubuta kalmar SCORPIO kafin ya yi magana tuni ya juya ya fara tafiya cikin sauri duk da rashin kuzarin da yake dashi yana jin inda iskar anci ke ratsa jikinsa yana sha a tare da kaiwa hunhunsa. Kano/Birget Dambe suke yi a tsakiyar tsakar gidan mata wajan uku ne kowacce da aurin irji ga tukunyar abincin dake saman murhu. Banda sautin hayaniyarsu babu abin da ake ji hatta Malam dake waje da Almajirai yana jin yadda suke aibata juna da zagin juna hakan ya saka ya mi e ri e da bulala yana ajjiye allon hannunsu da yake rubutu ya yi cikin gidan. "Ke har kin isa ki ce za ki hana Mufeederh abinci a gidan nan? Wace ke?" Cikin agawa Inna Binta ta ce "Ni Binta matar malam ki fa a mini nawa Mufee ta bayar aka ha a wajan yin abincin nan? Ke uban yaran nan bai bada ku in abinci ba, ba zai yiwuwa yara su ha a ku i ku i a siyo dusar awara a yi dambun nan ki ce wai na zubawa Mufee ba ar banzar yarinyar da bata da kunya, kina kallo sauran an'uwanta suka fita nemo ku i ita ta yi kwanciyarta tunda ar mai ce ai yanzu sai ta ci hantar ubanta Malam gashi can yana zaman banza ba fuss" Mama dake arin ganin ta wafcin dambun a kwano ta ce "Da in abin dai ba yaranki kawai suka ha a ku in ba, hadda Saudat ko Zaituna?" "A'a ba ruwan Zaituna tun jiya nake ganin hazo-hazo a idanuna cikina banda salati ba abin da yake, Saudat da ciwon ciki ta kwana Olser ta buge ta saboda yunwa ki yi ta kan ki kawai wannan rayuwa Allah dai ya fisshe mu, amma yunwa za ta yi ajalin rabin jama'a a wannan zamanin" Mama Zaituna ta fa a tana turo kwanan Saudat da nufin a zuba mata ta an tsakura a ciki ta yafa a nata cikin. Inna Binta ta shammafe ce ta yi sama da tukunyar kasancewar ta sharifiya ta ce "Wallahi sai Mufee ta ci abincin nan" Mama Zaituna ta ce "To Allah Ya isa daman kun saba cin kayan Allah Ya isa in sha Allah sai ta yi aman shi" Inna Binta ta ji an cau a mata bulala a uwawu ta yi saurin dire tukunyar ta ce "Kan uba wanne mai tsautsayin ne haka?...," shiru ta yi ganin Malam ya ce "Kina sake magana ina ara cau a muku shasha kawai mara kan gado" Ya juya wajansu ya ce "Mayu marasa godiyar Ubangiji kawai akan abinci duk ma ota da unguwa sai anjiku" Inna Binta ta ce "Yaushe rabon da muga sisi taka banda masifar tsiya kana bamu za mu yi haka ne?" Kan ta ya yi da bulala ta yi saurin waftar dambun a hannu ta yi aki tana "Ohho dai na iba na mai da mugun miyau" Haushin karnuka suka ji wanda rabon da su ji shekaru uku kenan gaba aya suka juya wani ihu Mama Zaituna ta yi tare da fatali da dambun da ake ta yin masifa akan shi har zaninta na kuncewa zuwa asa ta yi saurin juyawa zata akko ta zame da awan albasa ta fa i dif a asa Kasancewar atuwa ce sosai ta fasa ara da jan uwawu ta shige akinta hankali tashe. Shi kansa Malam sai da zuciyarsa ta motsa saboda tsoro ya dinga kallon karnukan da idanu yadda suke aga jela tare da zaro harshe waje jibga-jibga dasu sai zagaye wanda ya shigo suke yi. Da yar Malam ya ja numfashi ya ce allabi anmalam nake gani haka? Ya suka sake ka basu kashe ka ba, ni na auka ma tuni ka mutu wallahi, ikon Allah" sosai kansa ke masa ciwo kamar zai rabe ga wani ciwo da jikinsa yake yana jin fatarsa na rawa, ya yi ba i