← Book details Mutallab Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 13 OF 40

Sashe 13

Mutallab Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Fiyya ta kalle shi ta ce "Ita kuma lafiya take bacci a nan? Yaushe ta shigo gidan ai lokacin tashi bai ba?" Captain dai ya yi shiru ta juya ta kalle shi sosai ta ce "Lafiya take?" "Ban sani ba" "To ya naga kana ha e rai duka zaka kawo mini me kai komai naka babu walwala Aliyu ka dubi girman Allah ka dinga murmushi shifa yin murmushi sunna ne ta ma'aiki" ya shafa kan shi yana zuba hannu a aljihu cikin gaskiyarsa ya ce "Ban iya ba wallahi Ummi ki koyan" "Shi murmushin? Allah ya rufa asiri to wannan matarka ta shiga uku" yana dai tsaye bai ce komai ba. "Maama?" "Ummi" "Maama ta shi yammaci za ki yi unci ko ciwon kai idan kikai bacci" ta bu e fararen idanunta suka ha a idanu ta sha kunu sosai tana tura baki ya zabga mata uwar harara ta yi baya zata koma baccin. "Kee" ya kira sunanta ta bu e idanu "Tashi kafin na yi balle da wannan silar afafuwan" mi ewa tsaye ta yi ta murgu a masa baki bata ce komai ba shi kuma ya yi kamar zai juya ya dam o hannunta ta walla ihu daidai nan Daddy ya shigo parlon cikin sauri ya sake ta. "Da kyau Soja gwara ka nuna arfinka akan iyata, yanzu zaka tattara ka koma inda ka fito" Captain ya juya ya bar parlon gaba aya yarinyar haushi take bashi har zuciyarsa. Daddy ya kalli Fiyya ya ce "Maama, yaushe za ki girma ina ganin wawtar wanda ya auki mu a min Manager ya ba ki wallahi" "Daddy kune kuke raina ni wallahi, na girma am matured enough" ya girgiza kai kawai kasancewar t.v. na kunne aka fara karato ta aitattun labarai. Sunan Scorpio aka fara ambata matsayin wanda jami'an tsaro na hukumar FID Federal investigation department suke nema idanu rufe. Dake t.v a hankali ta juya ta kalli mai karanto labaran matashin an jarida dake aiki a gidan t.v na VOA juyawa ta yi ta ce "Daddy an bani aron wayarka" "Ki yi me da ita?" "Wayata zan kira, ina son fita ne wajan Kinal" ya mi a mata wayar ta an jim tana aga hannunta tare da copy na wasu numbersa sai kuma ta mi a masa bayan ta yi deleting tana murmushi "La la la na tuna inda na sata" Ya kalli t.v ya kalleta ya kuma kalli wayarsa, ya dai amsa a ransa yana mai jin tsoro da mamakin kaifin tunanin Maama. Ummi kuma ta ce "Ayi ta neman mutum kamar kiyashi shi kuma ya rasa sunan da zai sawa kan shi sai kunama?" Daddy bai yi magana ba Ummi da abin ke ta cinta ta kalli Fiyya dake shirin haurawa sama ta ce "Maama ta shi me ya yi ne?" "Ummi ina zan sani, idan kika auke yadda ake juya biyar ta zama goma ba abin da Fiyya ta sani" tana cewa haka ta haura cikin sauri tana nanata numbersa dake kanta cikin sauri ta yi wanka ta shirya cikin abaya ta yi rolling tare da fesa turare sauri-sauri take a haka ta sakko hannunta ri e da waya ko jaka bata auka ba. Daddy ya dube ta ya kalli lokaci "Wai zuwa wajan Kinal baya tashi sai yamma? Ita Kinal in nan ta dinga zuwa mana zai fi" "Daddy ba jimawa zan yi ba, na jima ban je ba mun gaisa ba" "Maama bani da nutsuwa haka kawai idan kika fita gari ya hargitse bani number Kinal in nan na kira ta" kafin ta yi magana J ya yi saurin wace wayar Fiyya ya ce "Bari na kira maka ita Daddy" babu sunan Kinal a jerin wanda ta yi waya dasu yau cikin sauri ta amsa ta ce "Number Kinal a kashe yaje fa J wai ni yarinya ce na san yadda zan kare kai na no body can come and hit me" Ta kalli Daddy da Ummi ta juya ta kalli J ta ce "To tsoran na mene ni Safiyya A Marafa?" "Allah Ya tsare Maama jeki" amsawa ta yi da amin ta ra awa J kunne "J akwai gulma yau bari na je na dawo" tana fita harabar gidan mota ta shiga ta yi mata key cikin nutsuwa dake driving har ta fita ganin ta hau kan titi ta dubi bayan motarta ta cikin gilas wata ajjiyar ta sauke mau nauyi ta rufe idanunta ta bu e sai kuma ta auke hanyar ta nufi wani titin daban a zuciyarta addu'a take yi sosai. ***** Eng Ali wali na zaune a parlo cikin wani gidansa da yake ganawa da an siyasa masu mara masa baya a kujerar shi. Ya dubi CSP chief Superintendent of Police ya ce "Ina son ku auke idanunku akan yarana, ko me kuke bu ata zan baku idan arna sukai zan ji da komai" Csp ya ce "Hon yaushe za mu cigaba da zuba idanu an dabarka suna yin yadda su kaga dama a garin nan musamman a unguwar Birget gashi lamarin na shirin haddasa fa a tsakanin an cikin gari da su an Birget, mu jami'ai ne mun san gaskiya muke take ta" "Ku cigaba da takewar su wannan yaran suna da wa'adi dana samu na ci za e ko inuwata babu mai gani a cikin su. Don haka ku rufe idanunku a toshe kunnuwa, zuwa gaba har matsayi zan saka a ara maka mu yi an dabaru" CSP ya jinjina kai Eng Ali wali ya akko ku i mai yawa ya mi a masa yana cewa "Idan kun kama masu dilar wayoyi da kayan maye na san ana mi a su hannun NDLEA ko? Ka tabbatar wayoyin na zuwa wajan Jafar shi kuma zai bawa yarana, kar ka sake sunana ya fito daman ai an asara ne ko an kama su ba za su ta a furta ni suke yi wa aiki ba, lastly magana akan Scorpio in nan yana neman bani ciwon kai bana son ya zama damuwata, idan F.i.d suka riga ku kama shi akwai matsala" "Karka damu hon mun zuba yaran mu ta ko'ina" Eng Ali wali ya ce "Lallai Scorpio ya zo hannu kafin za Cikin sauri Fiyya ta fito daga cikin motarta tana shiga cikin wajan data zo a reception ta tsaya na wasu mintina tana zaune ta fito tana murmushi ta ce "Ikon Allah kamar tare kuke?" Fiyya ta bu e idanunta sosai ta ce "Wa?" "Captain yayanki" Gabanta ya fa i ta kasa cewa komai Kinal ta zauna ta ce "Wallahi zuwan shi biyu fa, nima dai na yi mamaki amma ya ce aiki yake dubawa shi ne ya le o mu gaisa har ma na tambaye shi ke sai bai bani amsa. Amarya ya kike ya sabgogi" "Good. Yanzu lokacin ku ne Kinal siyasa ta matso ana ta fama da habaice-habaice" "Kamarya habaici?" Fiyya ta cire gilas in idanunta ta ce "babu abin da mawa a suka iya sai habaici wallahi ku zagi wanda kuke so kuma ku yabi wanda ku kaga dama" Kinal ta yi murmushi ta ce "A'a ni ba ruwana idan an kira ni dai wa a ina yi amma ai ni ta soyayya nake yi tunda a nan na fi kauri, ina nan ina shirya miki ke da Ashraf" Fiyya ta sauke numfashi ta ce "Ina cikin matsala Kinal ban so fa awa kowa ba wallahi" "Subuhanallahi matsala wacce kuma? A kamfanin ko gida ko wani wajan?" "Kema kin san a gida ba wanda zai mini komai sai mai ba in halin nan, tunda ya dawo ya uzzura mini ko parlo bana fitowa mutum sai ba ar zuciya an wahala kawai aikin kawai" Kinal dai ta zuba mata idanu kafin ta ce "Mene damuwar?" "Kwana biyu da suka shige ana bibiyata kullum idan na fita, harta nan wajan da na zo sai da aka biyo ni, ni ba damuwata kai na ina tsoron su Daddy su sani kin san abu idan ya same ni tashin hankali suke shiga. Kinal ban san su waye ba me kuma suke bu ata saboda bani da issues akan kowa wallahi na ji kawai ina son sanin wanda ke following nawa duk inda na je gwara mu yi fito na fito da shi, da na ce ko na yi hayar an daba nima suna take mini baya?" Kinal ta bu e idanunta sosai ta ce "Daman na fara zargin kina da ta in hankali Fiyya, ke yanzu ina kika san inda an daba suke bare ki je? Bakya tsoro ko shakka ai matsalarki police ne wannan ina ganin a gayawa Captain kawai" tsaki Fiyya ta yi tana mi ewa tsaye "gwara duk abin da zai same ni ya zaman da dai na fa awa Captain ni ina da abin yi" " an daban za ki yi haya yanzu kenan?" "E" sai kuma ta koma ta zauna cikin nutsuwa ta kalli Kinal ta ce "Akwai abubuwan da bana ganewa kwana biyu kamfaninmu ina son na yi bincike duk abin da na samu ba daidai ba wallahi sai na kaiwa hukuma Kinal yatsun hannun mutum na gani a cikin kamfanin fa?" Kinal ta zare idanu waje ta ce "A'a ki fara samun mai kamfanin ku yi magana dashi tunda ke ce Manager" "Sai yanzu na fara tunani, i wonder aka bani Manager a kamfanina bayan akwai maza da yawa sosai da na yi tunanin ko experience ina ne yanzu kawai na ji ina zargi" "Zargin me?" aga kafa a ta ce "I don't know, na fara bincike dole zan gano gaskiya" Kinal ta ce "To ki bi a hankali Please Fiyya we care about you ni ma zani anniversary na makarantarmu FGC dana shigo Kamfanin gobe, har wa a na yi mana yanzu haka wani Eng Ali wali na yi wa wa ar da aka saka ni" shiru Fiyya ta yi tana nanata sunan FGC a ranta "Na ji kamar na san makarantar nan fa" "Ke da ba ita kika yi ba ina za ki sami, ni a can na yi secondary school kinga" "Haka ne bari na je" "To ki kula Please kar ki saka kan ki cikin matsala don Allah Fiyya" murmushi kawai Fiyya ta yi tana ficewa daga cikin studio ***** Kamar an cillo shi haka yaga Mai dawa ya
Chapter 13 · 0% Book details