← Book details Matar Uncle Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 8 OF 27

Sashe 8

Matar Uncle Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Duk suka amsa da ameeeen “Momy dai shiru tayi don damuwace a ranta Aunty Laila ta kalleta kafin ta maida kallonta ga ummi ta ce”Sai maganar Amera Ummi wlh Wannan Aurenma So take ta kasosa “Kamar wacce aka zabura momy ta kalli Aunty Laila fuska had’e ta ce”Meye haka Aunty Laila don Allah karkiyi wata magana ba na ce miki na gyara ba maganar ta wuce ”Ai wlh ko me zakiyi saidai kiyi amma saina fad’awa Ummi kwata-kwata barrister ba Jin dad’in zama yake da ita ba duk hanyoyin da zata bi ta kuntata masa ya gaji ya saketa shi ta ke wlh bawan Allah nan wuya kawai take basa hakuri ya ke da ita fiye da yanda bakya tsammani ummi shi kuma wai nauyin ya fad’a maki ya ke munyi magana sosai da shi akwai matsala gaskiya “saurin barin wajen Momy tayi baki d’aya ummi ta bita da harara tare da cewa”Idan zaman gidan kikeso ai sai kidawo Gaki ga shi maganganun mutanema kad’ai sun isheki a fara miki irgen Aure da bakisan ciwon kanki ba”Aunty Laila ta ce”ni sai inga wlh amera kamar Han yanzu wancen Marar mutuncin mutumin ne a ranta idan kika Lura gaba d’aya bata son zaman aure kinga haka akayi wancen na Alh mudassir dukda laifinta kad’an ne ni wlh barrister ma nafi tausayawa saboda yanda yake mugun sonta bawan Allahn nan da wani ne tuni ya saallamota gida ko ya k’ara aure”Ummi ta ce”Anya kuwa Laila Mutumin da ko zancensa bata so a tada koda wasa kike ga take so har yanzu a a gaskiya na fi zargin kawai don ta ga ta na da kyau kuma jikinta na da kyau har yanzu ba a cewa ma tayi aure bare har ace ta haihu ta na da budurwar y’a shine yake daukarta take ga inma ta fito wanda ya fisa zata aura nidai shi na fi zargi amma zan Kira barrister idan hidima ta lafa muyi magana”Aunty Laila ta ce “ai bazai fad’a maki komai ba da wahala Nima wlh dakyal saida abun ya kaishi bango ya sameni yake faffad’amun Kamar me tsoranta wai amma don Allah karda ko da wasa na ce shi ya kawo karanta”.ummi ta ce “ai daman bana son ya fad’amun d’in zandai masa nasiha ne cikin hikima na basa hakuri”.

Lokacin su Ayda kuma suna Daki suna ta hira su ukku gaba daya yanda Ayda take bawa noor labarin rayuwar da suke a makaranta sai taji bata da inda take da sha’awa kamar itama ta shiga Makarantar tasu har doki take Cike da zakuwa ta ce”Wlh Nima nan zan dawo da karatu Ina komawa zan fadawa dadyna ya samamun addmission”Yawwa Y’ar gari” Ayda ta fada suna tafawa”Murmushi Mufedah tayi ta ce”amma wlh kika kuskura kika biyewa group din su Ayda ba karatu zakiyi ba don kingansu nan c’o dinsu daga mai biyar sai mai hudu Ayda ce mai sauki ta ke da biyu a semester daya kafin ta gaba”tab to ai ni daman ba kokari gareni ba fa ni bana son karatun daman kawai don a shakata zan shiga” Ayda na zaro ido sai kuma ta sa dariya ta na kallon Mufeda ta ce “tab kinga wacce ta fini ni ba laifi ina D’an son karatun saboda ko banza ance graduate ce ni amma Sam ba na Kaunar karatu ke idan na shiga Ana lectures ji nake kamar na shako malamin da duka Sam na tsani karatu Nima wlh”Mufedah ta ce “wlh karatu na da amfani Ayda da kinji tawa da kun nutsu kun mai da hankalinku shi lokaci ne da shi sannan ke fa Ayda kina da kokari da gangan kike nema ki maida kanki marar kokari kin biyewa shirme kinsan dai baki tsaya kika tab’uka abun azziki ba ba ta yanda zaki fita da result ”

“Noor ta ce”ke da fa gaskiyarta kudai da kukaga zaku iya kuci gaba Allah taya mukam dadi biyu zamuci ga graduate ga ba abimu bashin rayuwa ba ko bamu amshi result ba wani ya sani”

Dariya Ayda ta sa suna kashewa da Noor suna cikin hira Aunty khadija ta shigo da waya a kunnanta ga alamu da mijinta take waya wata takwas baya akayi bikinta y’ar ummi wacce daga ita sai Mufedah shiru duk sukayi da hirar ganinta saida ta katse wayar kafin ta mai da kallonta garesu ta ce”ga alamu munafurci ake hadawa injiwo shewarku ynzu kuma duk kuyi shiru “dariya sukayi Ayda ta ce”ba wani munafurci mrs Habu zuwan yaushe”ta na yatsine fuska ta ce”tun dazu na zo muna tare da twins ne A bedroom dinsu yanzu ma zuwa nayi ku taimakamun y’an k’annena cikinku wata ta soyamun wainar fulawa“gyara kwanciya Ayda tayi Tana rubda ciki bisa pillow ta ce"ni ga shi aunty khadija ban iya ba ai da na soyawa umborn dinmu"harara ta dalla mata ta ce "zaki iya a gidan miji ai uwar son jiki ni daman ba ke na ce ba "dariya Noor ta yi ta ce"Ai kam dole mu tashi muyi aikin d'anmu ko y'armu aunty khadija wata nawa ne"da harara ta bisu tare da cewa "bansani ba nidai don allah kuyimun kafin baby ya zo daukata" Ayda ta ce"baby habu ai ko yazo dole ya jira aikin dansa"Pillow ta buga mata ta ce"marar kunya zamu had'e watanki kusan guda rabonki da gidana"wlh aunty khadija makaranta nima ina son zuwa ita ke hanawa"ta na nufar kofa ta ce"da anyi magana kice makaranta sai kace karatun take"domin itama Alqalam din ta ke Level 4 saura 3months ta gama.

Ana saura kwana hud’u a fara biki Kanwar ummi mai biya mata da ke aure a kaduna wacce suke kiranta da mami ta zo daga ita sai babban D’anta Abdallah mai kusan 30years itama Yaranta hudu ukku maza mace d’aya Halimatu suna ce mata Amna tayi mata aure kasuntuwar ba kasar suke zaune da mijinta ba yasa bata samu zuwa ba D’ayan kuma muhammad yana karatu a london yana da 27 years sai autanta Sadeq mai 16years shi kuma ba na zaiyi candy kasancewar yana zana waec ta Hana sa zuwa tunda ta zo gidan ya Kara rikicewa don Badai kaud’in magana ba idan Tana magana daga nesa ma sai ka jiyota ga wasa da dariya saidai ita akwai fad’a idan ka tabota bata da hakurin ummi Sam Ayda na gefenta faruq ya shigo dawowarshi daga wajen Aiki kenan da sallama a bakinsa saidai fuska hade “Oh ni zulaihatu faruq daman kana k’asar ko nemanmu bakayi ko a waya”yana zama daya daga cikin kujerun palourn ya ce”kinzo zaki fara mitar ai kya tsaya ma mu gaisa tsufa yana Neman ma ya kamaki wlh Ina yini anzo lfy ya hanya”ya fada a jere”A a mutuwa nayi na dawo karewar tsufa marar kunya”Yar dariya ya yi ya ce “Allah huci zuciyar mami”kafin ya mai da kallonsa ga sauran duka ya gaishesu suka amsa Cike da kulawa Tare da tambayarsa wajen aiki ummi ya kalla da ke harararsa ya ce”Ina yini Hajiyarmu maganin kukanmu “ba wani zak’in baki da zakamun ka gama zagayen zagayen yanzu ai mun had’e ai kasan nace maka karkazo bada wayar nan ba”ya na ciro wayar a aljihunsa ya ce”ni na isa na sab’a umarnin uwar manya da yara ga ta Allah huci zuciyarki “ya fada ya na Mika mata nauyayyar ajiyar zuciya a boye Ayda Ta sauke ta tsura masa ido Wanda sai a sannan ya kalleta ya ce”ga wayar nan na yarda kici gaba da rikewa na saka miki sabon sim amma wlh na Kara kamaki da laifi makammancin wancen saina miki karaya hudu na baki ruwan sanyi kin kasa doruwa sannan karki kuma saka security koda yaushe kuma zan amsa wayar nayi duk binciken da ya kamata fatan kinji abunda na fada maki”?!

Jiki sanyaye ta gyada kai momy ta bisa da hararar takaici tare da Jan siririn tsaki Wanda kowa saida yaji faruq ya Taba baki ya ce “oho dai kinji abunda na fada maki”Mami ta katsesa da waye ohon”ni dai ba da kowa nake ba kinga karki jamum”Aunty Laila ta ce”ai shiyasa mukayi shiru ubanta na bata umarni wa zaisa baki”Batare da ya kalleta ba ya ce

”ku kuke jan yara su Raina mutane wlh”aunty Laila ta ce “ka ga ba rashin kunya nace ka mana ba kunfi kusa ya wajen su yaya”ya ce”yana Abuja amma gobe zai dawo ya ce nan zai fara biyowa ma kafin ya kalli Ayda ya ce ki sameni a mota minti biyar sauri nake saura ki batamun lokaci “

“Cikin sauri ta ce”Toh”Momy kamar ta shaketa yana barin palourn ta dalla mata harara ta ce”sakarai da kika rako mata sai ki tashi ki bishi”tura Baki gaba tayi tare da bin bayansa momy ji take kamar ta hadiya zuciya ummi ta ce”ki rage nuna kiyayyar nan a fili Amera ba kyau”

mikewa tayi kamar tasa kuka ta ce”Wallahi ummi bazata tab’a Auren faruq ba muddin kuma Ta auri faruq wlh ba ni ba ita har gaba da abada saidai ta chanza wata uwar amma Tana Auren faruq na sallama masa ita tunda na fada ba sau d’aya ba sau biyu a daina barinta zance ummi kin kasa fahimtata ai shikenan”!

bata jira me ma zasu ce ba tabar palourn ummi ta ce “kiyayyar nan ta amera da Habiba yarinyar nan kafiya ne da ita taki manta abunda ya wuce”mami ta ce”ni fa Banga laifin amera ba wlh duk abunda ta yi ta na gaskiya ai ko ni indai ina mumfashi saidai wani ikon na ubangiji zai sanya ta auri faruq Aunty Laila ta ce”gaskiya kam Allah musu zabi mafi alkhairi”suka amsa da amen”suna jinjina yanda ummi take son nuna kamar komai bai faru ba.
Chapter 8 · 0% Book details