← Book details Matar Uncle Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 4 OF 27

Sashe 4

Matar Uncle Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Washegari ko school ba ta je ba koda ummi ta tambayeta lafiya cewa tayi bakomai kallon aunty hasana tayi ta ce”Aunty hasana yau zan rakaku wajen gyaran jikin “To amaryar yaya faruq ko kema gyaran za Asoma maki”Dariya ta yi ta na rufe fuska tare da tashi ta ce”Bari na je na shirya koda ta fito har sun shirya direct wucewa sukayi hadadden wajen gyaran jikin don duk ta rage damuwa amma dukda haka da damuwa a ranta ita ma ko saida aka mata gyaran subhanallah zo kuga irin masifar Kyan da Ayda tayi kamar ka sace ka ruga ita kanta da ta kalli kanta a madubi tasan ta Kara masifar kyau kunsan kyau ya hadu da gyara aiko nan tace itama wlh bata yarda ba sai anyi mata na kwana ukku sanin rigimar Ayda ya sanya hasana da husaina biya mata itama ayi mata yayinda su kuma ake musu na wata guda Angon husaina ya maidasu gida ya na tsokanar Ayda ta na cinye musu abincin gida ta zama katuwa.

A Washegari tunda sassafe ta shirya kamar koda yaushe ta fi son shigar Abaya sosai tayi kyau cikin Egypt abaya dinta mai matukar tsada da kyau kasantuwarka ga Wanda Allah ya Yiwa hasken fata ita tayiwa rigar kyau ba wai rigar tayi mata kyau ba sosai ta haskata Abunka ga bak’in Abu ya had’u da farar halitta
Zaune ta samu ummi tare da kawayenta suna gagganin lefe gaishesu tayi tare da zama ta na daura kanta bisa kafadar ummi tare da cewa”Ummi na Ina kwana”Lfyqlau Autar ummi har anyi Shirin school din da sassafe yau za a fita”Gyada Kai tayi tare da cewa”yau 8 muke da lectures”to kinyi breakfast “?
Gyada Kai tare da tsokanar ummi da cewa”gaskiya ummi kafin biki sai nakaiki an gyara miki gashin nan naki furfura Yayi miki yawa kar ace umminmu ta tsofe “Dariya ummi ta yi ta na Kai mata dankwashin wasa ta ce “za ajimu fa takwara tashi kiban waje ja’ira “Dariya ta yi ta na mikewa tare da nufar hanya ta ce “Tunda kika haifi su Momy ai kingama tsufa “girgiza Kai tayi tare da murmushi “Dattijawan arziki abokan ummi sukayi dariya tare da cewa”ai da gaskiyarta shekara hamsin da biyar ai ba wasa ba donma Allah ya boye shekarunnamu ba acewa ma muntara manyan d’iya da jikoki”murmushi ummi ta yi a ranta ta na zancen zuci.
Kasantuwar ba waya a hannunta Kai tsaye gidan su jawahid ta ce driver ya sauketa a motar jawahid suka wuce school kwata kwata lectures dinma ba fahimtarta take ba 12 suka gama zasu shiga wata 4 daman kawayensu lectures daya suke su bazama yawo gari Ayda jawahid Khairat sai Ubaida su hudu ne dama group din nasu wanda tun daga secondary school suke tare dalilin amintarsu sukaki yarda a raba musu school kowa ta fadawa mahaifinta ga inda suke so kasantuwar abunda suke so iyayen ke so ba wani musu suka bisu da ra’ayinsu Sab’anin jawahid da kawancensu na daban ne don tun yarinta kowace makaranta tare sukayi sai cikon ta biyar d’in nasu Ruky itakuma y’ar zaria ce a nan Alqalam suka had’u karatu ya kawota a Sardauna Estate ta ke da zama sai 6 suka gama yawonsu sun dauki hanyar gida kenan Ayda ta kalli jawahid da ke driving ta na bin wakar Auta waziri tare da langabewa ta ce”Besty ba fa gida za ki sauke ni ba gidan su yaya faruq zaki rakani”

Wani banzan kallo ta watsa mata tare da cewa”Rashin sanin ciwon kan za aje a bazar ko?Tura Baki gaba tayi tare da cewa”Nidai kawai ki rakani don Allah karkice a a “Andaiji kunya wlh wai kamar ke namiji ke bawa wahala mtwswww ni wlh da ni nake da kyanki ai nafi karfin Faruq ya dinga wahalarwa Allah kyauta kilama asiri ya miki”
Ayda na hade fuska ta ce”nidai naji bance ki aibantamun shi ba rakiya kawai nace kimun ”Cike da takaici jawahid ta juya akalar motarta hanyar gidansu faruq Wanda tasan gidan sanadiyar Ayda don itace y’ar rakiyar biko duk lokacin da suka samu matsala haka zata tilastata ba don ta na so ba……..✍️

*Idan kin karanta kiyi sharing sauran grp please*🙏

_*Miss Hajo ce*_🤙🏿

♠️♣️ *MATAR UNCLE* ♣️♠️

```MALLAKAR```

*HAJARA L SADEQ*
Miss Hajo✍🏾

*ADABI WRITERS ASSOCIATION*

*Marubuciyar*
👇🏾
Auren wata Tara
Ni da yaya arman
Khadijatul sabren
Ribar so
Najmat abiy
Mata tace
Komai mukaddari ne
And now
MATAR UNCLE

*Shafin nan naku ne kyauta Maryam Lolo,Halematuuuu,Maman saddik’a,Ruky Magaji,Asiya sani,Sopy mrs Haru,Alkhairin Allah ya Kai muku har gadon baccinku*

🅿️……………………….*4*

Horn sukayi mai gadi ya bude musu tangammemen get din gidan babban gida ne sosai saidai bai Kai na ummi kyau da girma ba.
Ba a son ran jawahid ba suka shiga cikin ainahin part din gidan don da cewa tayi ita ta jirata a mota ta mata magiya Akan ta rakata ciki da sallama a bakinsu babban palour ne na alfarma y’an mata ne su hud’u zaune kowacce da waya a hannunta karamar cikinsu ce ta wara idanu tare da rugowa da gudu ta na rungume Ayda ta ce.

“oyoyo besty sai lokacin sauran yan matan suka Lura dasu bayan sun zauna Raudat ta na hararar Ayda ta ce “yaushe rabonki da gidanmu Ayda kinfi wata biyu ba ko shekaranjiya saida Abban mu ya gama tambayarki “

ta na zaro ido ta ce”kardai kinmun had’i da shi kince ba na zuwa?jidda mai akalla shekaru 23 ta amshe zancen da cewa”yanzunma dalili yakawota kinsan bata zuwan banza saida dalili”tura Baki gaba tayi ta ce”Kai aunty Jidda haka ma zaki ce zuwa nayi in ganku fa ni ba wani dalili " ta ce "Allah sa"kallon babbar cikinsu da tunda ta kalleta sau d’aya ta mai da hankalinta ga waya ta ce “Aunty Asiya Ina yini “hankalinta har lokacin na ga waya ta ce”lfy ya y’an gidan”Ta ce”suna lafiya”
“Raudat ta je ta kawo musu abun tab’awa ruwa kawai suka sha Inda Jawahid ke danna wayarta saukowar mahaifiyarsu ce ya sanya gaban Ayda faduwa.

cin karo da fuskar Ayda ya sanya Umma tayi kicin kicin da fuska kamar an aiko mata da Sakon ranar mutuwarta ta na zama tare da had’e rai.

Ayda gabanta na faduwa ta ce”Umma Ina yini”ba tare da ta kalleta ba tace”lafiya “Shiru Ayda tayi a ranta Ta na tunanin ta ya zata samu ta hadu da yaya faruq ga Umma ta sauko sanin Halin umma ba jituwa suke da Ayda ba ya sanya Raudat jansu dakinta sai a sannan hankalin Ayda ya kwanta ba bata lokaci suna shiga cikin sauri ta ce”ta ce”sis don Allah taimakamun zakiyi yaya faruq nake son gani”Dariya raudat ta yi ta ce

”wlh daman a Raina na San wajen sa kikazo anyi Halin da aka Saba ko”Harara wasa tayi mata ta ce”nidai ba ruwanki kawai ya za ayi na Gansa na San da duk magrib ya na gida ba inda yake zuwa shiyasa na zo”Kin ko yi sa’a yau ya na gida wlh kwana biyu ba ya fita sai zaman daki ayi sallah sai muje ko?

Nauyayyar ajiyar zuciya ta sauke ta ce”Eh amma bana son Umma ta gani kuma kinga ga shi ya na
Palour kuma dole sai ta palour zanbi “Ke Umma Ana magrib ta ke shigewa ciki bata zaman palour sosai idan Abba yana nan”

Ajiyar zuciya Ayda ta sauke Ana gama magrib kamar yanda Raudat ta fada duk sauran yayin nasu ma basa nan haka Umma wannan damar Ayda ta samu ta nufi dakin faruq kusan cin karo sukayi zai fito zata shiga wani irin hade fuska Yayi tamau tare da cewa”

“Ubanme ya kawoki waje na ko kin dawo ne ki Kara chusamun sauran bakincikin da Baki gama ba”Lokaci guda hawaye masu dumi suka zubo mata tare da saurin girgiza Kai ta ce”don Allah ka yi hakuri yaya faruq magana zamuyi”Kofa ya nuna mata yayinda zuciyarta ta kafe ta ki tafiya sai ma karasa shigewa dakin tayi tare da zama gefen gado “kinsan Umma ta zo ta sameki a nan Fad’a zatayi ki tashi ki tafi na ce”Ya fad’a a zafafe”Cike da taurin rai ta ce “ni fa ba inda zanje ”wlh ko ki tafi ko na nakada maki shegen duka munafuka maciya amana idanma wayarki kikazo amsa kinyi zuwan banza don keda ita har abada mayaudariya Allah ya Toni asirinki Ashe ba karamun munafurtata kike ba Samarin da suka dinga kiranki sunfi talatin kuma d’aya bayan d’aya na dauka na zazzagesu tare da shaida musu ni ne ajalinsu na Kara ganinsu da ke sannan na karya sim dinki dan nasan wayarce ta kawoki tashi ki ba ni waje ni “

Batayi mamaki ba kuma tasan daman hakan zai faru don tasan dole za akirata kuma dole zai karya sim dinta amma ita kam wlh saiya bata wayarta tunda ba shi ya saya mata ba duka 2 months da sayar wayar zai amshe mata”cikin kwantar da murya ta ce”to yaya faruq ka yi hakuri mana tunda har gida na biyo na Baka hakuri ba shikenan ba tunda ka dau mataki na maka alkawari bazan Kara kula kowa ba amma don Allah kayi hakuri ka daina fushi da ni kasan bazan jure ba please ta fada hawaye na zuba daga idanuwanta “

Jikin faruq ne Yayi sanyi Tare da dawowa ya Zauna ya ce”kinsan duk wannan abun da nake saboda sonki na ke Ayda don Allah ki mun alkawari kin daina kula kowa “gyada Kai tayi ta ce”na daina yaya faruq”Goge hawayen to”gogewa tayi tare da kirkirar murmushi ta ce ka hakura”gyada mata Kai Yayi ya na murmushi tare da kama hannunta ya ce “na yi kewarki “Cikin narkar da murya ta ce”Na fika azabtuwa da kewarka yaya faruq don Allah ka daina fushi da ni wlh Ina cutuwa da yawa”Ya na murza tafin hannunta ya ce” na daina”yanzu muje na maidake gida dare na yi kar umma ta samemu a nan “
Chapter 4 · 0% Book details