← Book details Matar Uncle Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 11 OF 27

Sashe 11

Matar Uncle Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

“Amera ni fa kinsan bana son hayaniya Ina hutawa anjima ai zan dawo”ba ason ran momy ba taki jansa da magana tasan ba dawowa zaiyi ba ta ce”to shikenan don Allah kar kayi dare take care”Yana lumshe ido ya ce”Toh Mom”murmushi tayi daga bangaren tace “Allah maka albarka “Y’ar dariya Yayi marar sauti tare da cewa”Baki daina son girma.

Bangaren su Ayda saida suka raka kowacce amarya gidajenta masha allah komai Yayi yanda ake so tundaga kan gidajen da kuma kayan da aka zuba ko makiyi yasan ba makusa saidai fatan zama lfy bayan gama Nasihohin iyaye suka tafi suka barsu da yaran “

Ayda da ke zance da sabon saurayinta a gidan husaina tun dazu Noor da ke nufowa wajen ta kalla bayan sun gaisa da shi ta kalli Ayda ta ce”momyna ta kira tace mudawo gida mu barta da kawayenta su zasuyi sayan Baki”

Cike da zakuwa saurayin ya ce “to muje na saukeku”kallon Noor Ayda tayi ta ce”yiwa Mufeda magana to”

A motar sabon saurayin Ayda suka koma gida Wanda su Noor suka wuce gida ita kuma ta tsaya suna ci gaba da zance Wanda duk hirar saurayince bata biyesa daidai lokacin dannowar motar Adnan gidan ganin irin hasken da ya dallesu dashi wanda ba alamun kashewa ne ya sanyata sallamar saurayin ta na Jan tsaki
Ko Waye zai dalleta haka don rainin hankali

palourn Cike ta sameshi da dangi tundaga dangin iyayen su ummi da kakanni masha Allah mutanen na da zumunci Ayda ganin suna ta zolayantan da suka saba ya sanyata zamewa ta koma ciki

kamar yanda ta yi jiya yau ma kira yakai biyar tayiwa faruq a wayar noor bai dauka ba sai taji duk kunci ya mamaye zuciyarta

Cikin kwana biyu kowa dangi na nesa da na kusa duk sun koma mami ma da Abdallah sun dauki hanyar Kaduna haka aunty Aisha itama ta bi mijinta da yazo daurin aure bai koma ba hakan yasa Washegari ta bisa suka wuce kano inda take aure.

Bak’i dai ya rage daga momy sai aunty laila da suke Auren gari daya estate d’aya sune ma zasu k’ara kwana biyu.

Zaune suke a palour suna ta hira su hud’u Mufedah,Aunty Khadija sai noor Ayda dai hankalinta duk ba jikinta yake ba ya na wajen faruq ganin shigowar momy da kuloli a hannunta ne ya sanya suka tsagaita kallon Ayda tayi ba yabo ba fallasa ta ce”amshi ki kaiwa uncle d’inku part dinsa “

kallon momy tayi da mamaki duk su hudu sai ita zata zab’a ta Kai masa”Momy kamar tasan tunanin me take ta ce”Eh saboda ke kadaice mai tsaurin idon da bakije kin gaishe sa ba kin masa Sannu da zuwa tun zuwan sa shiyasa na Baki ki Kai masa daga nan ki gaishesa “

A hankali ta amsa jiki sanyaye tayi waje ba tare da amsawa momyn ba

Ta kai minti biyar bakin kofar ta kasa shiga ta kasa knoking gabanta takeji na faduwa saida ta rumtse ido kafin ta fara knoking Jin anbata umarnin shigowane ya sanyata tura kofar a hankali cikin siririyar zazzakar muryarta tayi sallama “wa ailakumussalam”ya fad’a tamkar ba shi Yayi maganar ba don gaba daya hankalinsa na kan laptop.

lumshe ido tayi Jin wani irin sanyayyen kamshi da ya hadu da ac na tashi a palourn “kai gaskiya kamshi rahama ne”
Ta fad’a a cikin zuciyarta kamar gunki haka taci gaba da karewa dakin kallo komai na dakin off white ne fes fes tamkar ba a taba shiga dakinba babu alamar kazanta ko daud’a da zakace ta taba samun mahallin zama sosai tsarin kayan dakin da komai suka burgeta musamman lather kujerun da sukayi matukar karshen haduwa tamkar d’akin shugaban k’asa.

Gyaran muryar da akayi ne ya dawo da ita hayyacinta don sosai ta lula wata duniyar ta daban sai a sannan ta kallesa sanye yake cikin kananun kaya jiens da t-shirt sai sirirn farin glass da ya sanya wanda kana ganin kwayar idanunsa tura baki gaba tayi a ranta ta ce”Don yana da kyau shine yake girman Kai Alhalin ko ni da ake cewa Ina dakyau amma bana irin haka”

“ta fada kasa kasa yanda ba mai ji karo na farko da ya D’ago ya kalleta cikin y’an seconds ya k’arewa street gown din jikinta kallo sosai red atamfar ta amsheta tayi mata kyau normal daurin D’an kwali ne kanta ba gyale tab’e baki Yayi ya na kauda Kai ya ce.

”baki iya zama ba”A ranta ta maimaita maganar saidai kwarjinin da Yayi mata ya sanyata kasa cewa komai ta zauna kasa bisa lausassan carpet din dake malale a tsakiyar palourn kasantuwar suna facing din juna ya sanyata kallonsa kamar mai shirin yin kuka ta ce”Ina yini uncle anzo lafiya”

yana lumke laptop din dake gabansa ya kalleta tare da cewa “ban anshi gaisuwar nan ba tunda ba daga zuciyarki ta fito ba”Toh uncle daga Ina ta fito”daga bakin amerah mana”Kasa tayi da kanta Tana tura Baki kafin ta dago ta na narkar da fuska kamar zatayi kuka ta ce”daman Ina son zuwa na zo na gaishe ka Hidimar biki ta Hana”Saida ta kusan minti guda da maganar har ta cire rai da zai bata amsa ya ce”………..✍️

_*Miss Hajo ce_*🤙🏿

♠️♣️ *MATAR UNCLE* ♣️♠️

```MALLAKAR```

*HAJARA L SADEQ*
Miss Hajo✍🏾

*Marubuciyar*
👇🏾
Auren wata Tara
Ni da yaya arman
Khadijatul sabren
Ribar so
Najmat abiy
Mata tace
Komai mukaddari ne
And now
MATAR UNCLE

🅿️……………………….*9*

Har ta cire rai da zai bata amsa sai kuma ta tsinkayi muryarsa da cewa”ya karatu”kanta k’asa ta ce”Alhamdulillah “j s s nawa kike?tana shagwabe fuska ta ce”

“uncle js s kuma level 1 fa nake zan jona two” ya D’an wara idanu irin mamakin nan ya ce”

“serious “murmushi tayi da ta lotsar da dimple dinta guda biyu tare da bayyanar da wushiryarta ta ce”Allah uncle “ya ce”Masha Allah Allah ya bada sa’ar karatu”

Ta amsa da amen tare da d’an tura kulolin kusa dashi ta ce”momy ta ce”na kawo maka”Rankwafowa yayi wanda har sunajin numfashin juna wani irin lumshe ido Ayda tayi Jin wani daddad’an kamshin dake fita daga jikinsa

komawa Yayi ya zauna bayan ya maida kulolin gabansa yana daddagawa shinkafa da Miya ce da ta sha green beans da carrot a cikinsa da dafaffen dankalin turawa daga sama gefe miyar yankakkun kayan miya ce da ta sha kifin geangwani sai kamshi take gefe kuma hadadden cowslow ne murmushi yayi yana maidawa ya rufe a ransa yana jinjina iya girki na amerah don yasan girkintane kuma course din umminsu ne”

maida kallonsa ga Ayda yayi da a zuciyarta ta ke Allahsa karya sallameta don kamshin dakin ba karamin dadi yake yi mata ba
“Ko hira zaki tayani kikayi zaune”Girgiza Kai ta yi ta ce”a a “to tashi ki tafi”Dagowa tayi ta kallesa idanunsu suka sartse cikin na juna shi ya fara janye nasa idanun ya k’ara cewa”Ki tashi ki tafi kar ummi ta nemeki “mik’ewa ta yi ba tare da ta tanka masa ba tabar d’akin ya bita da kallon mamaki har yanzu mamakin girman yarinyar yake kafin ya shingida jikin kujera tare da Lumshe ido ya tafi wani tunanin na daban.

”koda ta isa part dinsu samun ummi tayi tare da aunty Laila gefen ummi ta zauna ta na dora kanta bisa kafadarta ta ce”ummi wani saurayina ya ce zai kawomun waya don Allah ki yarda na karba”lokaci guda ummi ta hade rai tamau ta ce”ban yarda ba karki sake ki amsa kuma naji labarin makammancin haka ranki zaiyi mugun b’aci zan saya maki cikin satin nan Insha Allah kowace iri kike so nayi busy ne da yawa shiyasa ”

”Toh ummi nagode”ta fad’a ta na mikewa tare da barin bedroom din gaba d’aya dakinsu ta koma inda ta samu su Mufedah na ta fira kallonta Noor ta yi ta ce,
“har kin dawo”Gyada musu Kai tayi ta na kwanciya jiki sanyaye mufedah ce ta ce “me kuma ya sameki kikayi sanyi haka“Ita dai Ayda ba ta Kara ce musu k’ala ba ta juya ta kwanta Tana ta shak’ar kamshin turaren d’akin uncle Dan ita kanta da ta shiga jikinta kamshin yake”

Noor ta ce”wlh na so ace ni Aunty Amera ta aika na Kai masa Allah Uncle ba karamun haduwa ya yi ba bakison yanda lokaci guda na kamu ba wlh”

ta fada ta na kallon mufe ta ce”wlh noor kin ishemu da zancen uncle saikace sa’anki ke ko kunya ma bakya ji”

Ayda da batayi niyyar saka musu Baki ba ta sanya dariya tare da cewa”iska na wahalar da me Kayan Kara bai ma San kina yi ba ki rasa Wanda zakizo sai kusan sa’an mamanki ai ya maki tsufa ni ai wlh nafison D’an matashi 28,29 tayi nisa 30 kamar dai yaya faruq Wanda zaku ci duniyarku da tsinka amma Allah na tuba kamar uncle ai zaman uba da d’iya zakuyi ji fa yanda yake mummurtukewa tayama za a iya zaman aure da shi”

”noor ta ja dogon tsaki tare da cewa “ke wlh bakisan meye so ba ai irin su uncle wlh ko Shekara 60 Yayi Ina so Wama zai ce ya kusa 40 irinsu wlh sunfi iya soyayya da ririta mace hajiya Yaya Faruq din banza wlh Yanzu Haka Uncle ya fisa Kyan jiki saikace shine mai 29 d’in ma nesa ba kusa ba ga kyau ga aji ke ni Ina son namijin kamar uncle wlh ai *MATAR UNCLE* ta gama morewa don ta gama samun rabon duniya saidai ta nemu lahira amma a duniya dai wlh Allah ya gama mata komai kinga uncle dai ga kyau,nasaba,Gayu,tsafta aji,ilimin boko har Matsayin Dr yakai ilimin addini mahaddacin Alqur’ani mai karshema har rubuta sa ya yi uwa uba arziki shi da dukiyar mahaifinsa gwamnati ma saida ta gada har yau ba asan Adadin dukiyar da mahaifinsa ya bar masa ba da ansha kwana saidai wasu su k’ara fitowa kuma shi d’aya tillo D’an sa ke komai ma uncle ya had’a Ana zancen mazan kirki da Allah zaki kawo mana zancen Faruq zararre magana ake ta maza masu capacity Hajiya ki daina saka mana Baki”
Chapter 11 · 0% Book details