← Book details Matar Uncle Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 6 OF 27

Sashe 6

Matar Uncle Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read

Ana sauran sati guda biki duk sauran y’an uwan ummi da wasu daga cikin Y’ay’ayen y’an uwanta suka hallara lokacin da sukazo su Ayda suna yawo da kawayenta ko sch ma ba su samu damar zuwa ba sai gab da magrib ta nufo gida da driver don kamar a alkakai takejin deriver nan da aka hadata dashi,nata na musamman domin ummi ta ce bazata basu mota ba hakan ya sa Ayda ta ce ita saidai a ware mata driver ta daban ummi tayi mata yanda take so d’in ganin da farko ta so driver su hada Baki ya dinga kaita inda ta ke so zata Kara masa albashi Wanda ya shaida mata bazaiyi hakan ba bazaici amanar uwar d’akinsa ba iya makaranta da inda ummi ta umarta kad’ai zai dinga kaita hakan yasa ta ke dabara ya na kaita makaranta daga Chan ta wuce inda ta ke so domin ummi na da time table dinsu ta san lokacin zuwan su da tasowarsu haka driver shima ya na time table din ummi ta basa dalililin da yasa saidai ta hakura da lectures don wani Karin sai tayi fin one week ma ba tare da tayi attending lectures ko d’aya ba”.

Da sallama ta shigo palourn turus tayi cin karo da manyan bakin da ke garesu kusan Cike palourn.
ummi sai farinciki take karasawa palourn tayi Aunty Laila ce ta fara mata Oyoyo “Hugging din ta Ayda tayi da dan murmushi a fuskarta ta ce”Aunty irin suppressed haka ban San yau zakuzo ba ai da bazanje school ba”Da murmushin zallar Kaunar Ayda a ranta ta ce”ai suprised din Ummi mukayi daughter shiyasa”

d’iyarta da zatayi kusan sa’anni da ita ta kalla tare da harararta ta ce”Baki gaisheni”Itama hararar ta mayar mata ta ce”Allah kiyaye kinma Raina ni”kaiii yaushe idon ki Yayi tsauri yarinyar nan 7months fa na Baki “Dariya
Tasa tare da cewa “Toh meye a 7months Kalli fa wlh yanzu haka nafiki girma “”

Ayda na maida kallonta ga momy da tayi fuska ta ce”kibar doya ce rainon Lagos amma ba don haka ba da baxaki hadani da ke ba “

ta mai da kallonta ga Aunty Aishaa da ke saukowa da gudu ta ruga tare da rungume ta ta ce”Wayyo dadi aunty hadake saukar yaushe”da fara a fuskarta ta ce”duka yau muka sauka mukayi supresed dinku “
“Kai amma kun kyauta wlh aunty Ina mutuniyar Farhat”Ta na hannun Ayman sunfita sai a sannan Ayda ta kalli momy da suke da hira da ummi kamar ta shige cikinta kanta na bisa kafadarta ta ce

”Ina yini momy anzo lafiya “Alhmdulillah ya makaranta”Ta amsa cikin ko in kula”ta ce”Alhmdulillah” ”Toh Allah huta gajiya”ta fada ta na mikewa tare da zumburar Baki gaba ta gefen ido momy ke kallonta
samun Mufedah tayi tare da Iman babbar Y’ar aunty Aisha “.

“Aunty Ayda tun dazu ke muke ta jira tun fa 3 mukazo ya akai aunty Mufedah ta rigaki dawowa”sarkin tambaya kin tsaya mugaisa ko tambayoyin zaki fara”iman ta tura Baki Tana cigaba da game a wayar Mufeda ta ce”Munb’ata “kamota tayi tare da bata peck a kumatu ta ce “sorry Daughter ni na isa jeki kuyi wasa a waje”ta fad’a Tana mata wayau “ba musu ta mik’e tayi waje”mufedah ta ce”ya zaki koreta “Tana bud’e jakarta ta ce “Abu zan gwada maki ”

Ta na gama bude jakar ta fiddo dalleliyar iphone 15 sabuwa dal a kwalinta tana karkad’a wayar da murmushi a fuskarta ta ce “Haba yarinya ya zan Bari kaina ya kulle nayi sabuwar waya”

?zaro ido Mufedah tayi ta ce15pro nake gani Ayda waya saya maki”Dariya ta sa ta ce”wa fa zai sayamun kike tunani?ta ce “kaina ya kulle waya saya maki”
Ta ce”Wallahi saurayi nayi yau da haduwarmu da sayan wayar awa biyu ba ayi ba anjima ma yace zai zo ga gidan duk na ga a Cike”

”ta fada ta na yatsine fuska”da tsoro a fuskar Mufedah ta ce”Kaii gsky Ayda Bakiji wlh ko tsoro ma bakyayi to idan su ummi suka gani kice musu me”ba mai gani saidai idan ke kika fada musu lokacin da yaya Faruq zai kawomun tawa nikuma saina sayar da wannan na sha shagalina da kudin”Mufedah dai duk ta tsorata ta ce “saidai ki sayar da waccen tunda 14pro ce daman kina korafin level dinki ya wuce ta”ta na daura towel da nufar toilet ta ce “wlh ko 15pro dinma zan lallaba ne amma sai nayi 16pro hankalina zai kwanta “koda ta fito daga wanka shiri tayi sosai tayi kyau cikin blue din Egypt abaya don tafi sakasu bata fiya son Dubai sosai ba kwalli kawai ta kurta sai lipstick da ta sanya a lebenta tayi rooling gyalen kamar ka sace ta ka ruga flat shue tasa kasancewarta doguwa batason saka dogon takalmi ya subhanallah sak ta fito tamkar horul ayn da aka siffanta mana su gaskiya ba namiji ba ko mace ta kalli Ayda saita burgeta balantana namiji irinsune halittan da duk hassadar mai hassada Toh fa bai isa ya kusheta babu makusa a tattare da ita.

turarruka masu dadin kamshi ta fesa tanajin kiransa na shigowa wayarta ko kula wayar batai ba saida ta gama shirinta tsaf kira na biyar tukwana ta amsa cikin zazzakar muryarta mai matukar sanyaya zuciyar mai sauraro ta furta”Okay Ina zuwa ba jimawa”

Kallon kanta tayi a madubi tare da yin murmushi ita kanta ta san tayi kyau mayar da wayarta tayi jaka tare da fitowa cikin takun nan nata na kasaita mai matukar Jan hankali juya idanu tayi tare da tura Baki gaba kafin ta sauko palourn ganin duka kowa yana palourn sai hira ake yayinda Noor da mufedah suna gefe suna ta hira “

Masha Allah daughter wannan irin kyau haka ko duk mu akaje akayiwa kwalliyar “murmushi ta yi tare da zama kan hannun kujera ta na satar kallon momy da tayi kamar bata ganta ba ta ce”A a aunty zanyi bak’o ne dai”ah Kice faruq ne zaizo ja’iri ko a waya ba ya kiranmu muna gaisawa a haka kuma yake son mu bashi d’iya dukda shima d’in namu ne”

”Aunty Aisha ta amsa charab da cewa”Allah ubangiji ya kiyaye wlh mudai bazamu basa ba aunty donfa bakya yawan zuwa Baki San irin dibar albarkar da yake mata ba yanzu haka ba waya hannunta ya amshe idan ya daka mata tsawa kamar mala’ika tsoronsa take kamar rai da ajali wannan mai mugun halin irin na uwarsa zamuyi fatan bawa zukekiyar kanwarmu da ta fita zakka”Ummi na hada fuska ta ce”

“bana son irin maganar nan Aisha meye na siffantasa da mahaifiyarsa sa’arkice “to ai ummi gaskiya ce na fada mudai a family dinmu ba mai irin halinsa wajen mamansa ya gada wlh”Dariya aunty Laila ta sa da cewa”To ai gaskiya ta fad’a ummi halin faruq kusan duk na Habiba ne kawai dai Allah rufa asiri ya mana zabi mafi alkhairi “
ta amsa da amen tare da kallon Irin yanda Ayda Ta hade rai momy ta yi tare da dalla mata harara ta ce”kunga muyi shiru aunty Laila kar ta kullacemu kinsan aka tab’a faruq da uwarsa kamar ranta”Kara shakuwa sosai Ayda tayi da maganar momy tare da gunguni kasa kasa ta mike zata fita ta ce”Zagi na zakiyi ba gunguni ba dawo ba inda zaki”Nan ma bata ce Kala ba sai ummi da ta hade rai ta na kallon momy ta ce “bana son Haka Amera me yasa wai kike mata haka tsawon watanni bakuga juna ba amma kinzo kallon arziki bata isheki ba kuma yanzu kina neman ki hauta da fad’a meye haka ke Ayda wuce ki tafi karki shanya mutum a waje ”
Chapter 6 · 0% Book details