← Book details Matar Uncle Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 14 OF 27

Sashe 14

Matar Uncle Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

“Dawo gaba”
Ganin yanda ya yi maganar ba wasa ne ya sanyata fitowa kamar wacce kwai ya fashewa tare da yin yanda Ya ce”
Shiru ka ke Jin motar ba ka Jin sautin komai sai na “Al’qur’ani sautin Qiri’ar mahaifin nasa ya ke saurara har wani Lumshe idanu yake yana bi a hankali tamkar muryar da ya ke saurara koma fiye da haka”
Zuba masa idanu sosai Ayda tayi jin yanda ya ke bin karatun Alqur’ani mai girma Cikin nutsuwa ganin ya na nufar hanyar gida ne ya sanyata langabewa tare da cewa”Don Allah Uncle Gidan Aunty Khadija za ka saukeni”
Ba zaki ba”ganin yanda ya yi maganar ne ba wasa a tattare da shi ya sanya taJan bakinta tayi shiru”
SHizif d’inki nawa a Alqur’ani?Ta ji ya jefo mata tambayar”Kamar ba zata bashi amsa ba saboda haushin kin kaita gidan Aunty Khadija ta ce
“60”a tak’aice “zaki kawomun haddar 60 d’in ai don banga alamun hakan tattare da ke ba”
“Sosai cikinta ya kad’u harga Allah karshe karshen nan ba duka zata kawo da ba amma tasan kila fad’a ne ya yi “ta ce”Toh”

Ya na gama parking cikin sauri ta bar Motar ya bita da kallo har ta bacewa ganinsa kafin ya had’e Kansa da settearing mota ya yi minti biyar a haka kafin ya fito,
Kai tsaye part dinsa ya nufa yana zama d’aya daga cikin kujerun palourn tare da fito da wayarsa missed call ya gani barkatai na Abey kawai ya bi kiran bayan sun gama gaisawa yake tambayarsa ranar dawowarsa ya ce “sai lokacin da Ummi ta fad’a”Nusar dashi Yayi game da mahimmanci zaman sa a Qatar ya shaida masa Insha Allah ya gama abubuwan da yake zai dawo “Abey ya ce”Zahra ta ce mun idan ta kiraka ba ka dauka me yasa hakan Adnan “ya ce”ban kula ba ne Abba”ya ce”Toh don Allah ka kirata tunda ka ga maganar aurenku ta na nan jiran dawowarka kawai nake bangarena komai na gama shiryawa Allah muku albarka”ya amsa Ameen “
Kafin suyi sallama daidai kiran zahra na shigowa kyale wayar tayi ta gama ringing dinta kafin ya kashe wayar gaba d’aya ya na d’auko keypad d’insa tare da amsa kiran da ke shigowa”
“Kai yanzu Adnan ka kyauta kenan?Ka shafe kusan sati biyu a k’asar nan amma Baka sanar da ni ba haka matsayina yake a wajenka ko ai ka kyauta sai ka shirya gobe zanzo garin domin ganinka idan Kai Baka bukatata ni Ina bukatar ka”

“Ba haka ba ne Mujahid wlh tafiyarce ta zo mun Kai tsaye amma kaima kasan matsayinka ya wuce haka Allah ya kaimu goben ya kawo mun Kai lafiya”.

Washegari da Kansa ya je Airport tare da dauko Aminin nasa Da iyalansa Kai tsaye gida suka wuce Wanda tun a mota suka fara hirar yaushe gamo mujahid na juyawa ya kalli kyakyawar matarsa ya ce”Cutie nasan bakinsa sa ba ko”?ta ce”eh hero”ya ce “aminina kenan a U.K tare mukayi Degree dinmu na farko mun shak’u da shi sosai lokacin aurenmu ba ya k’asar shekaransa goma rabonsa da Nigeria amma kintuna tafiyarmu honey moon Ina ce maki tare nake da aminina idan kikaga na fita na dad’e lokacin a saudia?ta gyada kai ta ce”Allahsarki Allah barku tare”Adnan ya amsa da amen tare da cewa”amma fa kin wahalar mun da aboki da yawa gaskiya “Ayra dai tayi murmushi batare da ta Kara cewa komai ba inda hirar ta koma tsakanin Adnan da Arman”.(Ayra da Arman na Ni Da Yaya Arman idan Baku manta ba)

Tarba ta musamman Momy tayi musu Domin tun jiya ya fada mata zuwansa murmushi Mujahid ya yi ganin yanda Adnan ke yiwa Amal wasa sai dariya ta ke kafin ya kalli ummi da itama su take kallo gwanin burgewa Arman ya ce”
“Ummi gaskiya mungaji da zuba wa mutumin nan ido gwara ko a ruga ne mu samo masa mata “
ummi tayi murmushi ta na gyara zaman y’an biyun maza da ke jikinta ta ce”Kaima dai ka fad’a Mujahid na rasa me yake Damun Adnan don Allah jibi kaf sa’anninku daga me yara biyar sai hudu sai ukku jibi Kai fa masha Allah gwanin burgewa yara shida me yafi wannan arziki amma shi na rasa me yake damunsa game da batun Aure ba ya ma saka wannan a lissafinsa ya kamata dai ka masa fad’a Kai ma”

Ya na bin Arman da harara ya ce “watau ummi ka zo zugawa ko”?ummi ta ce ba batun zuga Gaskiya ce “idan lokaci ya yi za ayi ai?
Ta ce “Ai Insha allah lokacin ne ya zo shi ma ya maido ka don na gaji da ganinka haka”
Ayda da ke saukowa alamun daga bacci ta tashi Ummi ta kalla tasan Ayda da gigin bacci ta ce”bi a hankali Auta karki fad’i mana na hanaki fitowa bacci bai fita a idonki ba bakyaji sai kin k’ara faduwa irin na rannan””
“Toh ummi yunwa nake ji fa wlh har bana gani sosai “ta fada ta na nufar dining ba tare da ta Lura da kowa da ke wajen ba ummi ta ce”kunkai Har fin d’aya biyun dare bakiyi bacci ba yaya zaku tashi da wuri ina mamakinma idan da makaranta a haka har ku tafi wannan waya dai ta masifa Allah mana maganinta ga breakfast din naki nan”

Zuba mata idanu Ayra tayi “Masha Allah Allah Yayi halitta a nan to ai sak itadai wlh kyakyawar Y’ar india idanunta ya nuna mata a a Indian ma Wanda ya yi kyawun wannan d’aid’aikune wani kishi taji ya taso mata don wlh ko ita da ake fad’ar kyawunta nata nafila ne ashe da taga wanan”
maida kallonta tayi ga Arman ganin hankalinsa ba ya kanta gaba daya ya sanyata sauke ajiyar zuciya dukda ba ta kokonta mijin nata akan kowace irin mace “
Kallon yanda take breakfast din da sauri ya yi hankalinsa gaba d’aya yana kanta ya yi tunanin yunwar da take fada arish din gabanta Yayi mata kadan sai yaga har saura tayi a ransa ya ce”har yanzu Tana nan da rashin son cin abinci da yawa kenan”
tsaki ya ja ganin riga iya gwuiwar da ta fito da ita gashin kanta bakikkirin duk ya bayyana ya sha gyara har gadon bayanta ta tunk’e sai shek’i ya ke don ba ko kallabi kanta“
”maida kallonsa ga Arman da hankalinsa na ga ummi suna cigaba da hirar da baisan me ma suke cewa ba ya yi tare da mikewa ya na Kama hannunsa ya ce”

muje part d’ina Amal da ke hannunsa Ayda idanunta ya fara kaiwa ita dai Tana son kyawawan yara Allah’ya sani

“wow uncle Wannan yarinyar fa don allah ba ni na riketa"ta fada ta na nufar wajen domin amsar ta kallo daya Mujahid yayi mata ya kauda kai a yayinda Adnan ya b'alla mata harara wanda sam bata lura ba hankalinta na ga amsar yarinyar ta mika hannu tare da amsarta wanda jin hannunta ya na gogan fatan nasa ya sanyasa saurin mika mata tare da juyawa ya yi gaba Arman ya bisa yana kumshe dariyar da take cikinsa….✍️

*juma’at Mubarak Allah hadamu da albarkarun ranar Insha Allah yau munshiga hutun weekend sai kuma Monday idan Allah ya kaimu kuyi hakuri posting kullum Bazaiyu ba*🙏🙏🙏

Domin Neman Karin bayani sharhi,or shiga grp 07026166536

*_Miss Hajo ce*_🤙🏿

♠️♣️ *MATAR UNCLE* ♣️♠️

```MALLAKAR```

*HAJARA L SADEQ*
Miss Hajo✍🏾

*ADABI WRITERS ASSOCIATION*

*Marubuciyar*
👇🏾
Auren wata Tara
Ni da yaya arman
Khadijatul sabren
Ribar so
Najmat abiy
Mata tace
Komai mukaddari ne
And now
MATAR UNCLE

*CAPACITY CAPACITY CAPACITY NA CE INA MATA MASU CAPACITYN SUKE NA CE INA CAPACITY A WAJEN MACEN DA BA TA K’AMSHI*?📢 NA K’ARA DA CEWA INA AMARE DA UWAYEN GIDAN DA SUKA AMSA SUNANSU SHALELEN MAI HOUSE KAI HAR MA DA Y’AN MATAN DA SUKE KAN CIN LOKACINSU UWA UBA AMARE MASU NIYYAR SHIGA DAGA CIKI TOH GA BABBAN ALBISHIR GAREKU MANYAN MATA NESA TA ZO KUSA DOMIN HAD’ADDIYAR MAI KAYAN K’AMSHIN NAN WATAU *AREEJBYABEER* TA SHIRYA TSAF DOMIN GWANGWAJEKU DA TURARRUKA KO WANI IRIN LAUNI TUNDAGA KAN *TURAREN WUTA,NA KABBASA,HUMRA,OIL,HALUT OUD,KAJIJI,HUMRA’S GUMELIAN DA SAURANSU* KUNSAN KIMAR MACE DA DARAJARTA BA TA TAB’A CIKA SAI DA K’AMSHI,TURAREN @byabeer YA NA DA MATUK’AR SIRRIKA DA TASIRI GARE KU MASOYA MUSAMMAN WANNAN DA YA KASANCE NA MUSAMMAN DAGA WAJEN Y’AR MUTAN LARABAWA NA TABBATAR KIKA FARA AMFANI DA KAYAN K’AMSHIN arej by Abeer SAU D’AYA TO FA GASKIYA KIN GAMA NEMAN KO WANI IRIN TURARE DON MAI HOUSE DA KANSA ZAI DINGA MAGIYAR A NEMO WANI TA NA NAN A CIKIN GARIN KADUNA *Areej by abeer*
SANANNA CE A HARKAR K’AMSHI TA NA TURA KAYANTA KO WANI STATE CIKIN AMINCI UWA UBA HAR MA DA KASASHEN K’ETARE MUSAMMAN Y’AN UWA MUTANEN NIGER GA KAYANTA DA SAUK’IN KUD’i GA KUMA BIYAR BUK’ATA A ZUCIYAR MASOYI KU TUNTUB’ETA A KAN NUMBER WAYARTA +234 816 492 1522 KO KUMA A SHAFIKANTA NA SADA ZUMUNTA DOMIN GANI DA IDO TIKTOK @areejbyabeer INSTAGRAM @byabeer *SAYAN NA GARI MAIDA KUDI GIDA*

🅿️……………………….*12*

Ya na kumshe dariyar da take cinsa ya ce

“ tsaya mana yallabai saurin me ka ke”

“arman ya fad’a ya na saurin binsa”ai naga kamar waya ka ke ka na dariya shiyasa””

ya fada yana bude parlourn kallonsa Arman ya yi bayan sun zauna har lokacin da dariya a fuskarsa ya ce

”To ai Kai d’inne ka ke bani Dariya wani sa’in kuma haushi kana bukatar Abu na rasa boye boyen me kake”

dogon tsaki ya ja ya na kauda Kai ya ce”kana da matsala Arman “,

“Ai dole na fad’a maka gaskiya wlh idan nine tuni an wuce wajen Kai ni fa idan Ina son Abu kowace hanya zan iya bi don na mallakesa Kai shaida ce domin na gwammace ko zan mutu akan hanyar neman abun amma Kai Ina doraka hanya ka kasa ganewa na rasa girman kan nan naka ma meye ka na cutar da kanka a banza “

“Kai ni fa duk ba wannan ba matsalar da na tunkara ta fi duk wacce nake ciki a baya”

”Cikin kankakanin lokaci Arman ya zama serious tare da zuba masa idanu ba ko kiftawa ya ce”

”me kuma ya faru ko Akan batun Auren zahra ba ka guda ba ka wuce wajen”
Chapter 14 · 0% Book details