← Book details Matar Uncle Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 10 OF 27

Sashe 10

Matar Uncle Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

kallon mutanen da ke saukowa kawai suke Wanda Allah Allah suke su hango sa.
A hankali ya ke taka matattakalar jirgin tare da lumshe ido kafin ya bude a hankali yana shakar daddad’an iskan da ke kadawa ga mahaifar tasa wata natsuwa ce ta dirar masa lokaci guda kafin ya karasa saukowa cikin wani irin fitinannen taku mai matukar Jan hankali “YAH ALLAH” Noor ta furta cin karo da kyakyawar halittar da saida numfashinta ya dauke na y’an dak’ik’u kafin tadawo hayyacinta ”Daman Ana samun namijin novel a zahiri “Cewar noor mufeda da ke gefenta ta ce “ “ga zahiri kingani “Noor ta ce”Daman Uncle Balarabe ne da gaske ashe da momy ta fad’amun”

sanye yake cikin kanunun kaya da sukayi masa masifar kyau ba hula a kansa sai gashinsa da yasha gyara hade da kasumabarsa da itace Abu mafi kallo da ta Kara kawata baiwar kyawun da Allah Yayi masa lumshe ido ya sake a karo na biyu kafin idanunsa ya sauka ga mutane mafi mahimmanci a rayuwarsa bai tab’a Jin yayi kewar mahaifiyarsa da ahalin nasa ba kamar yau karon farko tun bayan shekara goma da yayi murmushi tare da ware hannayensa ganin ummi ta nufo sa wata irin runguma tayi masa kamar zata maidashi ciki a yayinda shima Yayi mata irin natan
wata irin kewa da soyayya da kaunar mahaifiyartasa ce ta bijiro masa baisan lokacin da wasu hawaye masu d’umi suka zubo masa suka sauka Akan fuskar ummi da ta dago domin ta Kara gaskata ba mafarki take ba Muhammad Ali dinta ne yadawo shine rungume jikinta”

girgiza masa Kai tayi itama hawayen take tare da goge masa ta ce”bana son zubar hawayenka Adnan yau ranace ta farinciki a garemu da ahalinmu baki d’aya “

“ummi ki yafe mun”ya fad’a cikin zazzakar muryarsa mai Kama da busawar sarewa

Ayda da har lokacin a Cike take fam ko inda suke bata kalla ba sai sararin samaniya da ta tsurawa ido tana hango yanda duk sauran wanda sukazo tare suka nufesu kowa na masa sannu da zuwa.
Da nuna zallar farincikin dawowarsa momy ma rungumesa tayi Cike da zallar farinciki lurar da nayi kaf wajen yafi shakuwa da momy haka duk ya gaggaisa da yan uwansa.
ganin ya na waige waige ne ya sanya ummi yin murmushi tare da cewa”D’iyarka kake nema ko”shiru Yayi baice komai ba Wanda ummi tasan ita din yake nema maida kallonta ta yi ga Ayda Da ke zaune jikin wani dakali ta ce”Ka ganta chan shalelenka ta girma Adnan“! Kallonsa ya maida ga inda ummi ta nuna masa……………✍🏾

*Domin Neman Karin bayani ko shiga grp 07026166536*

*Idan kin karanta ki daure kiyi sharing sauran grps please*

_*Miss Hajo ce*_🤙🏿

♠️♣️ *MATAR UNCLE*♣️♠️

```MALLAKAR```

*HAJARA L SADEQ*
Miss Hajo✍🏾

*Marubuciyar*
👇🏾
Auren wata Tara
Ni da yaya arman
Khadijatul sabren
Ribar so
Najmat abiy
Mata tace
Komai mukaddari ne
And now
MATAR UNCLE

🅿️……………………….*8*

A hankali ya juya kallonsa gareta bai kalli fuskarta duka ba ya dai ga gefen fuskarta sosai Yayi mamakin girman nata a ransa yana tunana randa aka haifeta ,

”Amera mu je ko”cewar Adnan ganin sunyi tsaitsaye Hararar wasa momy tayi masa ta ce”Aunty Amera dai”D’an murmushin da bama zaka ce Yayi ba ya yi kafin ya bi bayan su ummi don har sunyi gaba yana kallon yanda momy ta rike hannunsa gam ya ce”To ki sakeni mana disturber ko akace maki guduwa zanyi”sunannan bazai fita a bakinka ba Adnan ai idan kaga na sakeka to mota na saka ka karka kuma guduwa nemanka ya Kara mana wahala “

saida zai shiga mota sa’annan Ayda ta kare masa kallo Idanunta a kansa ba ko kiftawa ganin yanda momy ke farinciki kamar anyi mata albishiri da gidan aljanna ya sanyata Tabe Baki ta ce”Wannan murnar da take a kansa ai saita kusa kashe mutum.

Motar da su Mufedah suka zo ta bi driver ya ja suka wuce gida
Kasantuwar baya gudu Abdallah da ya dauki su ummi ya fi gudu ya sanya suka riga su zuwa don lokacin da su Ayda suka iso tuni har sun isa palour Jiki sanyaye Ayda ta shiga palourn kamar wacce kwai ya fashewa a ciki bata kalli ko mutanen da ke palourn ba ta nufi hanyar wucewa Sama.

“dawo nan Ayda”Muryar ummi ta katseta tare da cewa “Fushin ne har yanzu ba a huce ba Haba autar ummi zo zauna naji meye”ummi ta fada ta na kamo hannunta tare da zaunar da ita gefen ta sai a sannan Adnan ya dago cikin y’an sakwanni ya kare mata kallo kafin ya maida kallonsa ga noor da mufeda da ke gaishesa ya ce”Alhamdulillah ya school”suka ce “Lafiya qlau”ya ce”Masha Allah yana kallon Aunty Aisha da tayi fuska ya ce”Maman Iman Ina yini”murmushin yake tayi ta ce”Ina yini uncle anzo lafiya”domin ba da ita aka tarbosa ba ya ce”Alhmdulillah ya me gidan”ta ce “yana lafiya”nan su hasana da husaina ma suka gaishesa ya amsa da tambayarsu ya hidima Aisha ta fara barin d’akin ummi ta bita da kallo Allah sarki in Banda Adnan ya gujewa Auren Aisha da fa yanzu wad’annan yaran nata duk nasa ne dondai komai na Allah ne shima Allah zab’a masa mafi alkhairi ta Lura har yanzu da tabon Adnan a zuciyar Aisha don ta so shi kamar ranta ya watsa musu k’asa a ido Karshe ma ta na zargin hada gudun Auren ya sa yabar k’asar.

maida kallonshi ga momy da ke ta jere jeren kuloli ya yi a hankali kamar baya motsa labbansa ya ce”

“Wazai cinye maki kayan nan kinfa San cikina”Momy na zuba masa dambun shinkafar da yaji vegetables don tasan shine favorite food dinsa ta ce “Ai ko Baka isa ba komai na nan sai kaci”langwabar da Kai Yayi kamar yaro ya ce”To ai sai ki saka inyi jinya”Koma me zaka ce saikaci abincin nan ko na maka d’ure”

Tuba nake babbar Yaya amma sai na fara zuwa na watsa ruwa”Kai dai ka ce ka na nan da halin nan naka na kin cin abinci gaban mutane muje part din naka to na Kai maka Chan”ta fada ta na daukar kular tare da mikewa,idon noor ko D’aukewa bayayi Akan Adnan don ta Lura miskiline na karshe gaisuwar da sukayi mashi ma a dakile ya amsa “.

”ummi tayi murmushi Aunty Laila ta ce “Ai dole muja baya mukam Amera da Adnan ai sai Allah “mami ta ce”Bakiga ya maidamu fanko ba ba tamu yake ba”sai a sannan ya kallesu ya ce”sorry Mamy aunty laila tuba nake “

Ayda na Jin muryarsa ta tabe baki ta ce”kamar mace ko magana ma kamar bayaso”Tana tura Baki gaba Tana binsu da kallo har suka haye sama kafin ta maida kallonta ga ummi kamar zatayi kuka ta ce.

”ummi har fa wayata ta fasa”rabu da ita ki lallabata har ta tafi wayar nan dai sai a hakura da ita tunda an tisota gaba faruq ya amshe satittika tadawo an kuma fasawa na saya maki wata je ki ku fara shirinku naji sunce anjima zakuyi wani event a gidan Khadija na mata ko?gyada Kai tayi jiki sanyaye ta mike ta nufi dakinsu ko kallonsu su Mufeda dake musu magana batayi ba

Koda ta koma daki gado ta fada tare da sanya marayan kukan da bata yi ba kawai yau ta tabbatar momy bata sonta ta tsaneta wani irin zafi take ji a ranta ga faruq tasan ya shaku zai dauka da gangan ta kashe masa waya a fili ta furta “na gaji koma me zakamun kayimun ka kashe ni ma na huta “

kuka take sosai sosai ta bawa Noor da Mufedah tausayi Cike da damuwa ita da mufedah suka shiga lallashinta tare da rungumeta dakyal suka samu tayi shiru cikin kuka ta ce”momy ta tsaneni mufedah bansan laifin me nayi mata ba “

Noor na share mata hawaye ta ce”ba tsanarki momy tayi ba Ayda Ba ta kaunar taren ki da yaya faruq ne saboda wani dalilinsu da ya had’asu da mahaifiyarsa sannan da irin cin zalin da yake maki.

”to Ina ruwan mahaifiyarsa da shi ai ko Allah ba ya Kama bawa da laifin da ba nasa ba sannan yaya faruq fa jinintane mafi kusa kuma Ina sonsa sosai itama ta sani me yasa bazatayimun uzuri ba sannan ba ruwan kowa da abunda yakemun a haka naji na gani “

Numfashi Noor ta ja kafin ta ce”kiyi hakuri ki dinga addua zamu tayaki yanzu ki bar kukan nan muje mu tafi gidan aunty khadija mu soma Shirin mu”dakyal suka lallasheta suka tafi da cewa tayi bazata je ba

Sosai night party din nasu Yayi kyau kuma ya tsaru komai anyi gwanin burgewa da tsarin tarbiya sunyi abunsu cikin class

A gidan aunty khadija suka kwana duk yanda Ayda ta dinga sauya number ta na kiran wayar faruq k’in dauka Yayi Karshe ma kashe wayarsa ya yi gaba d’aya Wanda sosai ta k’ara shiga damuwa.

Washegari misalin karfe sha biyu na rana d’umbin al’umma suka shaida daurin Auren Hasana da husaina tare da angwayensu Wanda sai a sannan mutane suka gaggaisa da Adnan Wanda daga daurin Auren Yayi sauri ya zame gidan gonarsa don shi mutum ne da a rayuwarsa baya son hayaniya,

sosai Yayi kewar gidan gonar nasa inda ya tarar da dukkan abunda ya Bari ya hayyafa sosai ya tabbatar da ummi na kula da dabbobin nasa lumshe ido Yayi ya na shafa kan kyakyawan police dog din nasa Yayi mamaki da har zuwa lokacin nan da bai manta sa ba don ya na zuwa ya nufo sa.

waje waje saida yaje ya duba
lambun gidan gonar ya tare inda aka ciro masa kayan itatuwa Cike da nishadi da annashuwa yake ci har wani lumshe ido ya ke don sosai yake Jin wata nutsuwa na Kara ratsa sa.

Daidai lokacin kiran momy ya shigo wayarsa bata Bari Yayi magana ba ta ce Ina kaje wai Adnan tun dazu Ana nemanka”ina gidan Gona”?ya bata amsa

”Haba Adnan Ana biki ka tafi wani waje ga shi kowa na son ganinka ai yakamata ka zo ka gaggaisa da y’an uwa mutanen Daura ma sai tambayarka su ke”
Chapter 10 · 0% Book details