← Book details Matar Uncle Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 7 OF 27

Sashe 7

Matar Uncle Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Hawaye na zuba daga idanun momy ta ce”Wlh ummi haushinta nakeji ta rasa Wanda zata so sai faruq mutumin da bamu da makiya sama da mahaifiyarsa sannan don Allah ummi tun ba yanzu ba nake Neman alfarmarki ki daina barin Ayda zanje da faruq ba ma shi ba da kowama don Allah “
“Wannan duk ya wuce amerah bana son tada abunda ya wuce zance kuma bazan hanata ba tunda ba kwadata zamuyi mu ci ba”amma dai ummi…“daga mata hannu tayi ta ce”bana son Jin komai tarenta kuma da faruq idan akwai alkhairi a ciki Allah ya tabbatar idan kuma babu Allah lalata abun”Babu ma wani alkhairi”cewar aunty Aisha “Aunty Laila ta ce”shine kawai muci gaba dayi musu Addua amma gaskiya zuri’ar Habiba Zuri’ar mu ce amma bakayi fatan ka Kara hada zuri’a da ita don Sam halinta ba na dauka jifa yanda fir ta karfi da yaji ta rabamu da D’an uwanmu mu dashi sai nesa nesa ga ta hanasa zama da mata inma Yayi saitayi yanda tayi ta fitar masa ji fa don Allah yaran nan biyu tunda iyayensu suka tafi Dasu yaya ya bar musu su ta rabasu da shi abun gwanin ban tausayi nan suka cigaba da tattaunawarsu irin ta y’an uwa.
Ayda ko jiki a sanyaye Tana Jin zuciyarta ba dadi don sosai momy ta b’ata mata rai ta isa wajen sabon saurayinta Wanda suka sanyawa sugar dady ita da kawayenta don a kalla ya haifeta ba walwala sukayi hirar ganin bata da walwawala ya sanyasa tambayar “lafiya”Tana dafe kanta da ke Sara mata ta ce “kaina ke ciwo”Cike da kulawa irin na dattawannan ya ce”Shikenan badamuwa beauty gobe na zo Allah ya sauwake akwai gajiya tattare dake na lura kije ki huta “Cike da Jin dad’i ta ce”to nagode saida safe”sukayi bankwana koda ta koma suna nan yanda ta barsu ko kallonsu bata yi ba ta haye sama momy ta ce “kungani ko haushinmune taji mun aibantasa “Mufedah ta ce”don Allah momy ki yi hakuri ba ma fa wajen faruq taje ba “Ayman da suna wasa dazu ya ganta ya ce”Wajen wani tsoho ne ma ya zo wajenta ”Dariya mufedah da Noor sukayi Noor ta ce”kaikuma uban sa ido ko”ya tura Baki gaba ya ce”Ai gaskiya ce tsohone wlh yagirmi dadynmu “sai a sannan ummi tayi dariya ta ce”tofa samarin na Ayda hada tsaffi aka fara kulawa “Aunty Laila itama na dariya ta ce”ja ira ta gudu ai da mun zolayeta “aunty Aisha tace “ni wlh dadi na ma daya da ba shi kadai ta nacewa ba ta na kula wasu”Mufedah ta amshe da cewa”aiko Akan kula samarin suke samun matsala ba abunda baiyi mata ba Akan hakan ya daketa zagi hantara ba abunda baya mata amma wlh bata daina kulawa ni namayi mamaki da ummi take Barinta “Murmushi ummi tayi ta ce” ni nasan dalili na kyaleta duk wannan raye rayen kan da take kyaleta nayi kuma Ina da dalili shiyasa kukaga kamar wai ko bana son tsawatar mata ku ai kunsan waceceni Akan tarbiya ta fada ta na kallon su momy”dariya momy tayi ta na kasa da kanta aunty Laila ta ce”gaskiya kam ummi kin sha wahalar Mu kam saidai Allah ya biya ki da gidan aljanna musamman Amera da Aisha “momy ta ce”Kai aunty Laila wlh saidai ki cire kanki amma Ina sane ba wai na manta ba duka ummi tafi Shan wahalarki a kanki fa ummi ta fara duka “jefawa momy pillow aunty Laila tayi ta kauce noor na dariya ta ce”to momy ki bari a bamu labari mana “Hararta aunty Laila tayi ta ce”ohhh wayau so kike ki ji labari kije ki fadawa babanku ya Kara Daure muku kuyi abunda kukaga dama ni tashi ma ki bani waje “Tana dariya ta tashi tana cewa”ai sai na lallaba ummi ta fada mana wlh na je na bawa Daddy Labari ”suna barin wajen aunty laila fuska da damuwa ta kalli ummi ta ce”wlh ummi har yanzu matsalar nan bata warware ba har yanzu Abban su Fatemah bai chanza ba……..✍️

*Share fisabilallah*👍🏾

_*Miss Hajo ce*_🤙🏿

♠️♣️ *MATAR UNCLE* ♣️♠️

```MALLAKAR```

*HAJARA L SADEQ*
Miss Hajo✍🏾

*ADABI WRITERS ASSOCIATION*

*Marubuciyar*
👇🏾
Auren wata Tara
Ni da yaya arman
Khadijatul sabren
Ribar so
Najmat abiy
Mata tace
Komai mukaddari ne
And now
MATAR UNCLE
🅿️……………………….*6*

“Har yanzu abban su Fatimah bai chanza ba kuma wlh duk na fara gajiya gaba d’aya wlh tarbiyar yaran nan a raunane take ummi yanzu haka fa Fatima ban isa inyi mata fad’a ba shisha haka suke sha da kawayensu har su rik’a posting In nayi magana ta ce Flavour ne karshe ma cewa tayi ban Waye ba har yanzu ni daman ba’a san Raina ya fitar da ita karatun nan ba Allah ummi hankalina ba a kwance yake ba zargin yarinyar nan shaye-shaye suke nake na masa magana ya ce sharri zanwa y’arsa flavor ne ba wani Abu ba haka ake nikuma gaba d’aya nasan Dabi’un da take ba na sak lafiyayyu ba ne yanzu haka last week daga Noor tayimun laifi na mareta wlh gaban idonta ya Rama mata banyi aune ba Nima sai saukar Mari naji harna had’a Kaya na zantaho kuma ya dinga lallashina Yanzu haka Haidar nema yake shima ya sangartasa fir shi daman ko Ina suna tare dalilin da ya Hana na taho da shi ma ko ina suna tare kullum suna fad’a da malaman makaranta wlh ummi Ina cikin tashin hankali basaji amma ban isa nayi musu magana ba karshe ma hademun Kai suke ya zuga su su dainamun magana rayuwa zata tafi a haka kike ga ummi Ni matsalar fatima wlh tafi damuna idonta ya bude fiye da yanda bakya tunani a american nan shigar banza ko kamar ba yar Muslma ba Ga Noor itama yana shirin turata itacema mai sauki sauki don Bata son b’acin Raina ita da sauki”

Nauyayyar ajiyar zuciya ummi ta sauke ita kanta lamarin Laila na damunta ta na kwantar da murya ta ce”kici gaba da musu addua Kawai lailah ki Hana idonki bacci ki nemawa yaranki shiriya don Allah shine kawai zai shirya Miiki su da taimakonku to tunda mahaifinsu ya Gaza ku hadu ku tarbiyantar da su sai ki barwa Allah komai tunda yaga kokarin da kike maganar Noor kuma barta a hannuna nasan yanda zan masa admission zan sama mata a makarantar su Ayda ta dawo arewa da karatu karmu yarda ya fitar da ita gaskiya tunda yanajin magana ta nasan hikimar da zan masa shi kuma Haidar Yaro ne ki jasa jiki sosai shakuwarki tafi karfi Akan na uban tunda ke fa tare kuke rayuwa a cikin gida ya kasance ya fi shakuwa dake don sauranma ke kikaja sukafi shakuwa da son uban sbd akwai yaran da idan uban ya nuna son a fili kema nuna musu soyayyar bawai yawan hantara ba to a sannan ne zaki samu ki tarbiyartar dasu Cike da hikima da wayau ita kuma fatima zan Kara kiranta muyi magana ki Kara hakuri rayuwar aure bata taba tafiya 💯 ,”kafin ta numfasa ta dora da cewa “Wlh laila ko wani aure yana da nasa jarabawar saidai na wani yafi na wani duka ne kuma ya Kara dukanki na Baki go ahead ki taho gida Nima na gaji da dukan nan girma kuke kar abun Yabi jiki har diya da jikoki dukda Ana dadewa amma ya Kara dukanki ki taho gida kawai saina dauki mummunan mataki Akan wannan ba a aure da duka ko cin mutunci”!

wata Nauyayyar ajiyar zuciya aunty laila ta sauke ta ce”Insha Allah ummi duk zanyi amfani da abubuwan da kika fadamun nagode Allah ya barmana ke ya ja da ranki don wlh ummi ke Y’ar aljannace Insha Allah ba abunda muka nema muka rasa daga iyaye kinmaye mana gurbin uwa da uba Baki Bari munyi kukan maraici ba kin rikemu tamkar y’ay’anki komai kin mana a rayuwa Allah dai ya biyaki da gidan aljanna”duka sauran suka amsa da amen ummi ta ce”bana son godiyar nan lailah ni ba iya matsayin kanne na daukeku ba Inajinku matsayi biyu tamkar y’ay’an da na Haifa nake jinku a cikin Raina Allah dai ya Kara had’a kawunanmu ya jikan iyayenmu da rahama”
Chapter 7 · 0% Book details