← Book details Matar Uncle Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 23 OF 27

Sashe 23

Matar Uncle Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Washegari Fatima ta ja mufeda ta rakata gidan Khadija best friend dinta ce sosai.kuma sa’anni ne ,
Hugging din juna sosai sukayi Cike da zallar kaunar juna da kewar juna suka hau hirar yaushe gamo”sai isha’i suka nufo gida.

Daidai lokacin suna shigowa Uncle na dawowa gidan Security ya bude masa bayan mota ya fito cikin takun nan nasa mai Jan hankali ya nufi part dinsa cikin D’an d’aga murya Fatima ta ce “Uncle ha da kyaliya?sai lokacin ya juyo da mamakin kallonta ta na murmushi ta karasa kusa da shi ta ce “Uncle yanzu saikace fa ka manta suna na”D’an murmushi ya yi ya ce”rashin kirkin nawa bai Kai haka ba ai Fatima “
Ta na murmushi ta ce “ni dai ban fada haka ba uncle Ina yini ya kwana dubu”ya na katse kiran da ke shigowa wayarsa ya ce”Alhmdulillah ya karatu mutanen America ko”?ta ce”Alhmdulillah “ya ce”ko har kin kammala”?
ta ce”no there is one year left but I want to continue my masters a Chan I won't even return to Nigeria until I'm done ka ga sai na yi zama d’aya”

“ya ce” no talk of marriage ko alhudu-hudu”ta na Y’ar dariya ta ce”Aure kuma uncle now ?no mun barwa su Ayda “

ya girgiza Kai tare da nufar part dinsa ya na cewa”idan Baki fito da shi ba ni zan Nemo maki ko a kauye .

“dariya ta yi bayan ganin ya bace ma ta ta ce”Uncle kenan saikace shi ba tuzurun ba ne ni masu duka-duka 24 years wa ke zancen nan“ kafin ta shige ciki itama.,

Uncle ko da ya koma Wanka ya yi ya na feshe jikinsa da mabanbanta kalalukan tsadaddun dad’ad’an turarukansa bayan ya yi Shirin bacci.,

wani Frame d’in hoton Ayda da ke bed side drawer ya fito dashi lokacin ta na Y’ar shekaru biyar sanye cikin wata tsadaddiyar riga kanta ba hula gashinta ya zubo har baya ta yi dariya hakoranta sun bayyana yayinda dumples d’inta duka sun Lotsa.

Ya Kai mintuna ashirin idanunsa Akan hoton batare da ya motsa ba kafin ya sauke wata irin ajiyar zuciya ya na mayar da hoton inda ya ke kafin ya kishingida ya kwanta bisa tausassan pilon yana maida kallonsa ga frame d’in da ke saitin kansa hotonsa ne shi da ita cikin shigar bak’ak’en Kaya ya rungumota ta gefen sa dukkanninsu cikin dariya hakoransu a bayyane lokacin zatayi 3years idanunsa Akan hoton k’aran ringing wayarsa ne ya katse masa dogon tunanin da ya lula kafin ya dauka da sallama a bakinsa “bangaren Zahra kamar zatayi kuka ta ce “me nayi ma ka Ya Ali You don't always answer my calls”?

ya na had’e fuska ya ce”nothing”ta ce”Don Allah ya Ali ka dawo Qatar wlh Ina son ganinka sosai saboda Kai na dawo Hutu k’asar kuma ance ka na Nigeria ko na biyo ka Nigeria ka ga har na je wajen dangin umma”ya ce “ina aiki yanzu saida safe “kafin ya katse wayarsa”.

Washegarin ranar su Ayda suka je saloon Ana jibi za a fara event dinsu na farko Mami ta iso tare da muhammad da ya gama karatunsa ya dawo kasar domin Abdallah shi yanayin aiki ya ce sai daurin Auren zai zo”Wanda Fatima Sam bata so haka ba ta so suntaho tare da Mamy domin yanzu mutumin ta ne sosai kullum cikin waya suke amma har lokacin bai fad’a mata yana sonta ba itama batakawo hakan a ranta ba.

Da dare wajen karfe Tara Wata madaidaiciyar jaka fatima ta mikawa Ayda ta ce “
rike mun muje ki rakani farfajiya ki rigani fita kinji”Ayda na amsar jakar ta ce”

to kafin ta Kama hannunta su fito Sannu suka yiwa su ummi da ke ta hira Mamy na ta zolayar Ayda tayi sauri ta fice aunty Laila na kallon fatima da ke Shirin fita ta ce”
Ina zaki”?
Ta ceWaje”ana sanyin nan me zakiyi a waje”?
Kai momy wlh kinfiya takura sai kace yarinya fisabilillahi to waya zanyi “

ta na gama fadar haka ta fice ?
Aunty Laila ta kalli ummi ta ce “kinga ko ummi kad’an ma kenan?”

“Yawwa Ayda don Allah inane waje me sirri a nan gidan inda ba me ganinka”

Ayda ta ce saidai bayan part d’in uncle shine ba me zuwa wajen sai dai wajen duk shukoki ne”

Yawwa haka nake son daman ba ni jakar toh”ta amsa ta na fito da karfen shisha”Ayda na zaro ido ta ce,.

”shisha aunty fatima”ta na harararta ta ce”to tonamun asiri nayi tunanin kina da sirri ai Flavour ne to ba wani Abu ba ku har ynzu Baku Waye ba wlh”

A ran Ayda ta ce”ikon Allah wai yau ni ce ake cewa ban Waye ba”

saida ta rakata bayan wajen allah yasa da haske sosai ta na kallo ta fiddo ta harhad’a kayanta Ayda ko ranstuwa tayi ba ta cinta ta San da Kayan shaye-shaye a kayan nan ta na kallo ya hada abun ta dinga sha saida ta gama abunta tsaf kafin ta mayar “

ta na sauke ajiyar zuciya ta ce”Haba tunda na dawo kasar nan sai yau na sha wlh kamar a k’aya nake jina saura inji kinfadawa wani “

Ayda ta tura Baki gaba ta ce “da kinsan zan fad’a ai da Baki ja ni ba”

fatima na Shirin Kai mata duka ta kauce ta na dariya sai kuma ta kamo hannunta itama ta na dariyar ta ce”

“ni na isa na daki amarya guda wasa nake maki “murmushi Ayda tayi ta ce”wai aunty fatima momy da gaske ba ta zuwa”

Fatima ta ce “jiya ta ma wuce saudia ita da mijinta da yaransa ukku kinga da gaske alamun ba ta zuwa”

Hawaye na Shirin zubo mata fatima ta hade rai ta na saurin goge mata ta ce “meye abun damuwar Toh idan ba ta zo ba akwai abunda za a fasa “

Ayda ta girgiza Kai ta ce “a a amma fa aunty fatima ba ta son Auren fa”

da mamaki fatima ta ce”bata so kuma Toh saboda me bayan D’an D’an uwanta ne”

Ayda ta ce”saboda ba sa shiri da mamansa”

Fatima ta ce”ke rabu da su zasu sauko ni bansanma wainar da ake ciki ba kinsan ni koda nake kasar banason k’ananun maganganu sai ayi Abu a gaba na ma na kasa sanin me akayi ai dai kina sonsa ya na sonki ko”?

Ayda ta gyada kai”ta ce”Toh ki kwantar da hankalinki Allah Baku zaman lfy”Ayda na murmushi ta ce.

“amen aunty fatima ke kadaice wlh kika goyo bayan Auren nan gwarama aunty Aisha da twins“

fatima na yin gaba ta ce “ko meyasa basa so oho kaina ya fara juyawa yi sauri muje bacci zanyi”suna shiga ta shige dakinta da ta sauka tare da kwanciya Ayda ma na su ta shige ta na kwanciya.

Yau suka fara event dinsu na farko masha allah Tundaga kan kawayen amaryar da amaryar batun ba a magana kasan y’ay’an banki sunyi kuka sosai Yayi kyau party’n na su ranar Ayda shigar Red ya subhanallah kafin ka ce me hotunansu da video's sun fara yawo a social media.

Washegari sukayi henna Wanda shima ya k’awatu kwarai da gaske duka biyun faruq bai halaarta ba saboda ya ce dinner da kamu kawai zai je Wanda ba ko sisinsa.

Da daddaren ranar laraba sukayi Night party iya su goma kawayensu sai noor da mufeda sosai sukayi kyau shima amaryar ta yi shigar pink dukkaninsu da budaddun ankon riga da wandon kayan bacci iri d’aya su kuma blue da ratsin pink da sukayi order tuntuni a wajen hasfat collection sosai tsarin decoration din nasu da shigarsu yayi matukar burgeni sai karfe biyu suka gama a gidan aunty khadija hakan ya sa Chan sukayi kwanciyarsu.!

Washegari ta Kama Alhamis akayi Mother’s Day Wanda sosai iyayen Ayda sukayi matukar bajinta tundaga kan y’an uwan maman nata da abokanan ummi manya manyan mashahuran mata masu ji da kansu Ayda ta sha lik’i kamar ba asan darajar kud’i ba sosai ya yi kyau Wanda karfe takwas angama komai domin na yamma aka fara.
Daren ranar misalin Tara na dare Ganin yanda Ayda ta ke cire Kayan da sauri noor ta kalla ta ce.

“Ina zakije haka kike sauri”ta ce”Wajen yaya faruq ya na kofar gida ta ce “to sai kibi a hankali saurin me kike “Ayda ta ce “ya ce na yi sauri shiyasa shirya ki rakani”

noor ta ce a shirye nake ai “dakyal suka taimaka mata ta cire gown din kafin ta mayar da doguwar Riga dama ta Riga ta goge make up dinta gyale kawai ta zira ta Kama hannun Noor suka bi ta kofar kitchen don Allah na gani ta tsani zolayar da kakanninsu momy na daura ke mata .

fuskar faruq Cike da tsantsar fara’a ya ke kallonta rabon da Ayda da ga faruq cikin fara a kamar jiya zuwa yau sai tace bata taba ga fara’arsa ba tunda suke a duniya kamar haka Cike da tsantsar doki da murna ya ce.

“babe muyi sauri ummana ta ce na kawo mata ke yau Tana son tayi miki nasiha da ga ita sai ke wai su al’adar gidan su haka ake “

a ran Ayda ta ce “Allah sarki kila ta sauko itama yanzu Tana son Auren kallon noor ya yi ya ce”muje ko “

Ta shiga baya Ayda na gaba Allah ne kadai ya kaisu gidan lfy domin Rabin tuk’in hankalinsa na ga Ayda.

“koda isarsu zaune suka tarar da Umma a palour ita kad’ai gaban Ayda na tsananta faduwa suka karasa palourn ga mamakinta sai taga Umman ta taso tare da kama hannunta ta ce”maraba da zuwa y’ata ta musamman “

Kan Ayda k’asa ta gaisheta bayan sun zauna gefenta umma ta zaunar da ita tare da tambayarta ya hidimar biki ta ce

”Alhmdulillah umma “Ina yini”Noor ta gaishe da Umman daga gefe Chan har lokacin ba ta zauna !ba”umma ta ce.

”lafiya qlau tsayuwar me kike kisamu wuri ki zauna Y’ar wajen laila ce ko?Noor ta gyad’a kai”

Maida kallon ta Umma ga faruq ta yi da har lokacin fuskarsa kamar gonar audiga don farinciki ta ce”

“Toh tsayuwar me kake da Allah ka bani wuri na gama da y’ata sirri nake so muyi ““
Chapter 23 · 0% Book details