← Book details Matar Uncle Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 5 OF 27

Sashe 5

Matar Uncle Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

“gyada kai tayi tare da mikewa ya bita murnar sun shirya Sam ya mantar da Ayda tare da jawahid sukazo Kai tsaye motarsa ya dauka tare da mayar da ita gida sunjima a cikin mota suna hira har karfe Goma bai mata maganar wayar ba itama bata masa ba tasan zai maido mata idan ta lallabasa ta na Shirin fita ya janyo hannunta ya na hade fuska ya nuna mata kumcinsa,
Ta gane me yake nufi hakan ya sa ta yi kasa da kanta gabanta na faduwa Allah ya sani bata kaunar ire-iren abubuwan nan da yaya faruq ke mata “hade fuska tamau Yayi tare da cewa”bazakiyi abunda na sakaki ba”girgiza Kai tayi kamar zatayi kuka ta ce”yay..”da Allah Yiwa mutane shiru fita”ba musu ta fita ta na tura Baki gaba a ranta ta ce “mutum sai masifa “

“daga Ina kike har karfe goma Ayda Bance 8 tayiwa kowa a gida ba duk inda yaje “ummi Ina haraba fa tun 8 din”Kedawa?Yaya Faruq”Sau nawa zan hanaki zan ce a mota Ayda bakyaji ko?kodan kinga Ina wasa dake”ummi yaya faruq ne fa”ta fada a shagwabe”Faruq d’in to daga yau karna kuma ganin kun shige motar nan da ba Aganin komai idan bazakuyi zancen a harabar waje ba ai ga palour nan kinji na fada maki?Gyada Kai tayi ta ce”Toh ummi”

tare da zama gefen Mufedah da ke Galla mata harara ta ce”aramun wayarki in Kira jawahid “don sai sannan ta tuna Ta barota a cha shaf ta manta “Bazan ara ba tunda bikon da kikaje baiyi amfani ba “kar alasa ki bada d’in”

ta fada ta na hayewa sama tare da Aron ta aunty hasana ta Kira jawahid ta na Jin muryarta ta hau balbaleta da masifa”ai wlh kin Kara cewa na rakaki watau kinma mayar Dani shashasha soyayya ta debeki kawai kika tafi kika barni “Dariya Ayda tayi ta ce”sorry besty ai dai yanzu kin koma gida”ta ce”bansaniba “dakyal ta shawo kanta ta hakura.

Bikin hasana da husaina na ta karatowa saura kwana goma Wanda busy duk yayiwa ummi yawa zaune take a bedroom dinta ta na waya kallo d’aya zakayi mata kaga tsantsar damuwa a cikin fuskarta kwalla na zuba daga idanuwanta ta cigaba da cewa.
”wannan ya nuna mun kenan ba da kowa kake fushi ba Adnan da ni kake fushi watau har yanzu ba ka manta da abunda ya Riga ya wuce ba?ba wata magana da zaka fadamun na Aminta da ita Adnan na lallab’aka na yi maka nasihar duk wani lallashi nayi maka amma ka ki saurarona shikenan kar kazo Insha Allah wannan shine karo na karshe da zan gama rokonka Akan kadawo gareni shekaru goma kasan ko irin halin bakin cikin da kuncin da nake ciki a dalilin rashinka rayuwa nake amma ba yanda nake so kullum zuciyata makale take da tunaninka bani da walwala kamar ko wani D’an adam duk don saboda Kai Adnan kodan Baka haihu ba bakasan halin kuncin da iyaye suke shiga ba idan y’ay’ayensu suka guje su “

saida ta ja numfashi kafin ta goge sabbin hawayen da suka zubar mata “zatayi magana maganarsa ta katse na ta tsayawa tayi tana saurarensa kafin ta sauke Nauyayyar ajiyar lokaci guda murmushi ya subce mata Cike da mamaki ta ce “da gaske sati mai zuwa kamar haka Ina tare da Kai”shiru tayi alamun sauraro kafin ta furta kalmar “Alhamdulillah alhamdulillah Allah nagode maka Allah Yayi maka albarka D’ana Allah ya dawomun dakai lafiya cikin aminci Kai amma najima banji abunda ya sanyani farinciki kamar haka ba Allah Yayi maka albarka “
Farincikin da ummi ta shiga kasa musaltuwa Yayi da hanzari ta katse wayar tare da saukowa palour inda ta samu yaran nata suna ta harkokinsu Cike da doki ta ce”Albishirunku!
Har doki da murna suke wajen cewa “ummi goro”Saida ta sauke ajiyar zuciya kafin ta saki murmushi ta ce “Adduar da muka dade munayi tsawon shekaru Allah ya amsa Ranar Juma’a mai zuwa idan Allah ya bamu aron rayuwa Adnan zai dawo kasarnan “

Hasana da husaina ce sukayi saurin zaro idanu tare da cewa”Don Allah Ammi da gaske ba wasa ba!
“Na taba muku irin wannan wasan daman bai taba fadamun cewa zai zo ba duk lallashin da nake masa kusan kullum sai a wannan Karon kuma tabbas din zaizo saboda nasan Adnan ba ya magana Biyu Kai alhamdulillah Allah nagode maka”

Cike da doki su da suka sanshi suka ce “Alhamdulillah Allah mungode maka Allah dawo dashi lafiya Amma ummi bazaki Bari ya Kara komawa ba idan yadawo gaskiya munyi kewar uncle da yawa?
cewar aunty husaina “Haba husaina fad’i ma ai batawa Insha Allah ya dawo kasar nan shi da barinta sai Allah bazan Kara yarda ya tafi ba”

“Ummi wai Uncle ne zai dawo”Farinciki ya kasa batuwa a fuskar ummi ta ce”Shi Ayda uncle dinku dukda nasan ba lallai ki tuna sa ba tunda shekara goma ba wasa ba ce saboda lokacin Baku da wayau ke da Mufedah”.

Shiru tayi ta na son tuna kamannin uncle d’in nata amma akwai abu biyu da ta kasa mantawa game dashi a rayuwarta lokacin da ya kaita primary school bayan gama nursery dinta ya sauya mata makaranta inda wajen saka suna headmaster ya ce”ya sunanta Kai tsaye ya ce”Maryam muhammad Ali “Sai kuma lokacin tafiyarsa wanda ya kasa barin memory dinta kuka ta ke sosai a jikinsa gab da tashin jirginsu wanda har sik’ewa take don kuka ya yi dai ta lallashinta da maganganu amma ta kasa rike maganganu sai hoto da ya daukesu a wayarsa su kadai ta rike amma gaba daya ta manta komai game dashi hatta kamanninsa “

“yanzu ko zan Kira aminiyarsa na mata babban albishir “maganar ummi ta katse mata tunaninta a yayinda ummi ta doka kira
saida ta katse kafin ta kuma Kira jin ta katse ta kira ne ya sanyata saurin cewa”albishirinki Amera”Daga bangaren ta amsa da “goro Ummi”Amininki ya amince rana ita yau zaidawo a cewarsa zai zo biki nasan hada kokarinki ya amince zaizo yanzu yaushe za ki taho ke?daga bangaren ta ce”ummi ai yanzu muka gama waya da shi yake fadamun kinsan ummi zance bayan ke babu wanda ya kaini farinciki da dawowar Adnan”

Da murmushi a fuskar ummi ta ce”ai nasani Amera rabi duk kokarinki ne Allah dai ya muku albarka yanzu yaushe zaki taho daga Lagos din yakamata ace kunxo da wuri an shishshirya abubuwa biki sai karatowa yake duk kunki zuwa Abubuwa sunyimun Cha”Daga Chan bangaren kamar zatayi kuka ta ce”Ummi shi ne nake ta kokarin ya barni na taho ko saura kwana goma ne yakiya don Allah ummi ko magana zaki masa”A a ki lallabasadin dai da kanki ba sai na sa Baki ba sai ku taho tare da Lailah”
“to Insha Allah kafin dai Friday din nasan na zo”ta ce”Allah ya sa agaida mun da Barrister “ta ce “zai ji ummi”Ayda na sauraronsu a ranta ta na Jin haushin nemanta da momyn takiyi kwana nawa bata da waya ko ta nemeta ita ma ko shiyasa taki nemanta,…….✍🏾

*Juma’at kharem Allah sadamu da dukkan Albakatun dake cikin ranar*🙏

_*Miss Hajo ce*_🤙🏿

♠️♣️ *MATAR UNCLE*♣️♠️

```MALLAKAR```

*HAJARA L SADEQ*
Miss Hajo✍🏾

*ADABI WRITERS ASSOCIATION*

*Marubuciyar*
👇🏾
Auren wata Tara
Ni da yaya arman
Khadijatul sabren
Ribar so
Najmat abiy
Mata tace
Komai mukaddari ne
And now
MATAR UNCLE

🅿️……………………….*5*
A ranta ta na Jin haushin me ya sa momyn ba ta neme ta ba itama kuwa shi yasa tak’i nemanta bayan komawarsu d’aki kallon Mufedah da ke gefent ta yi tare da cewa”Don Allah aramun wayarki”nuna mata wayar a side drawer ta yi ta dauka daman ta haddace number Waziri a take ta karanto tare da danna masa Kira Jin muryarta ta na Jin irin Nauyayyar ajiyar zuciyar da ya sauke kafin ya ce.

”babe me ya sa zakimun haka kinsan an sanya maki aure kika dinga wahalar da zuciyata”Kenan an sanya mata aure Yaya faruq ya ce”ka na garin ?iya abunda ta iya cewa kenan”Eh ki bani amsa da gaske ne an kusa bikinki ko kuma?kamar ya na gabanta ta girgiza Kai ta ce”ba gaskiya ba ne ya fada maka ne don ka rabu da ni”To shid’in waye “D’an uwa na ne”?Kuma Saurayinki ko?Ta ce”Eh”ya ce”hmm Toh mu zuba Allah ya ba me Rabo Sa’a Yayi tunanin barazanar sa zata tsoratani “

Ce“yanzu dai ba wannan ba gobe mu had’u a miet Corner Karfe hud’u ba waya hannuna”ya ce”Allah ya kaimu”washegarin yanda ta fada haka akayi daga school ta wuce suka hadu da waziri Wanda ta Kara tabbatar masa daba haka ba ne”bai kamata ba ace Baki da waya babe ba girman ki ba ne muje a sama maki ko 15 ce”cewar waziri
”ta yi saurin girgiza Kai ta na hade fuska ta ce”idan Ina bukatar ka sayamun na fad’a maka ai ynzu dai ba na bukata “Toh me za akawo maki ki ci yau dai muna tare har Magrib tunda kinga wajen nan ya na da sirri “ta ce no 6 zan koma “yana sakar mata murmushi ya ce”Haba Babe Toh saki ran mana An had’e fuska dukda a kowani yanayi cikin kyau kike amma kinfi kyau da fara’a “Bata saki fuskar ba sai k’ara hade fuska ta yi ta ce”shawarma bread da tea kawai zanci”ya ce yau har naman baza aci ba?ta gyada masa Kai “ya mike zai fita ta ce “aramun wayarka “ya Mika mata ya na barin wajen “cikin sauri ta Danna kiran wata number da hanzari bayan dauka ta ce “Vappie Ayda ce gobe 6:00pm mu had’u a S cape Banda waya hannuna wannan ba wayata ba ce karka kira”Ya ce “Allah kaimu darling kamar kinsan nayi kewarki da yawa”tayi saurin katsewa ganin tahowar Waziri tare da blocking number ta goge“Washegari yanda ta fada lokacin suka had’u da vappie shima ta warware masa maganar Faruq don shi ya tsorata sosai”kusan 50k ya kashe musu a ciye ciye daman shine dalilinta na kula samari kullum a ciki kowa da ranar fidda ita hauka ta ke ta Bari yaya faruq ya maka sakakka duk ya kore mata su shima ya ce zai saya mata waya ta ce bata so! A haka duk ta dawo da wasu daga cikin samarinta .
Chapter 5 · 0% Book details