← Book details Matar Uncle Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 1 OF 27

Sashe 1

Matar Uncle Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

♠️♣️ *MATAR UNCLE*♣️♠️

```MALLAKAR```

*HAJARA L SADEQ*
(Miss Hajo✍🏾)

*ADABI WRITERS ASSOCIATION*

Marubuciyar*
👇🏾
Auren wata Tara
Ni da yaya arman
Khadijatul sabren
Ribar so
Najmat abiy
Mata ta ce
Komai mukaddari ne
And now
MATAR UNCLE

*GODIYA*
Bismillairrahnanir Raheem dukkan Yabo da godiya su Kara tabbata ga Allah (Swa)Tsira Aminci su tabbata ga shugabanmu Annabi muhammad (S a w)Ina godiya ga Allah s w a da ya sake Bani ikon dawowa duniyar rubutu bayan tsawon lokaci da na shafe Allah ba ni ikon rubuta abunda zai amfani al’ummar musulmi Yayi Hani da hannuna wajen rubuta zunubi kurakuren da ke ciki Allah ya yafe Mun.

*GAISUWA*

Sakon gaisuwa da jinjina gareku daukakin Masoyan miss hajo a duk inda kuke Ina muku fatan alkhairi tare da babban albishir da wannan sabon littafi nawa mai suna *MATAR UNCLE* Wanda nake da tabbacin Insha Allah zai amsu a gareku miss hajon ce dai ba ta sauya ba ta na nan yanda kuka santa🤣kunsan bata da burin da ya wuce ganin ta nishadand’arta da zukatanku dan farincikinku shine nawa kar in cika ku da surutu I love u all Ina kaunarku inajinku chan cikin zuciyata sai mun hade a comment senction🧐

*GARGAD’I*

*Ban lamunta ayi mun amfani da littafi ta kowace siga ba ba tare da izini na ba hakkin mallakar nawa ne ni kadai masu satar mun littafi suna dorawa a youtube ba tare da izinina ba na barku da Allah wannan Karin aka kuma wlh zan dauki mummunan matakin da ban tab’a D’auka ba duk mai bukata ya nemu izinina*

*DEDICATED TO MY SISTER MARYAM L SADEQ*

1:july:2025/Tue

*BOOK ONE*📕👆🏻

🅿️………………………*1*

*QATAR*🇶🇦
(DOHA)

Sanyayyen iska ne mai had’e da lumshewar sararin samaniya ke kad’awa wanda ya k’ara samarwa garin ni’ima mai dad’in gaske,

zaune ya ke cikin k’atoton lambun gidan da ya k’awatu da ababen more rayuwa,

idanunsa sanye yake cikin farin glass yayinda hankalinsa na kan laptop ba ya ko d’agowa saboda yanda hankalinshi ya yi nisa ga dukkan alamu Abu yake mai matukar mahimmanci.

K’aran ringing wayar sa ne ya sanyashi dakatawa daga abunda ya ke ta cikin glass yake kallon wayar kafin ya sauke wata boyayyiyar ajiyar zuciya ya na Kara wayar a kunnansa,da sallama

Bayan gama sauraren duk maganganun da Abiy ke fada masa kafin cikin nutsuwa mai tattare da lafuzza masu nuni da tarbiya cikin harshen larabci ya mayar masa da ya na zuwa gidan nasa Insha Allah.

Mikewa ya yi tare da nad’e laptop din gabansa wanda sai a sannan na kare masa kallo dogo ne sosai kallo d’aya zaka masa ka ga karfaffen jarumin gwarzon namiji farine kal yana da manyan idanuwa tare da siririn hancinsa da zajensa da ya zagaye kyakyawar fuskar sa kasantuwar gyara da sajen yake sha sosai ya kara baiyayyanar da baiwar kyawun halittar da Allah Yayi masa kallo d’aya zaka masa kaga asalin kyakyawan balarabe kamilallen mutum ne wanda kallo d’aya zaka masa ka tabbatar da ba wasa a tattare dashi ba shi da sakin fuska haka Sam tsarin shekarun haihuwarsa a k’alla bazai gaza 37 ba.

Kai tsaye hanyar da zata sadashi da ainahin part din kasaitaccen gidan da mallakarsa kasan sai mashahurin mai kudi ko kuma mai fad’a Aji a k’asar Sosai na karewa komai na palourn kallo majority off white ne babu Abu d’aya zaka kalla a palourn bai burgeka ba komai ya tsaru kunsan dai yanda daular larabawa take da son k’awa.

Kai tsaye bedroom dinsa ya nufa da ya gama haduwa da komai na more rayuwa Wanda girman d’akin ma kad’ai ya isa ya tsoratar da mai karatu palour na musamman ne a cikin dakin mai dauke da kujeru da plasma sai gefe wajen karatu da ke dauke ababen zaman karatu.

A gaggauce ya yi wanka kasantuwar magrib na karatowa bayaso ya rasa jam’i sosai Yayi kyau cikin farar shaddar Gezna hannunsa sai shek’in tsadaddiyar agogon da ya makala yake yayinda gaba d’aya d’akin ya karad’e da kamshin turarensa mai matukar masifar gigitar kamshi,

tsadaddun wayoyinsa guda biyu ya saka cikin aljihu cikin izza da takama yake taku tamkar jinin sarauta fuskarsa sam ba annuri koda ya fito Kai tsaye tsadaddiyar motarsa kirar lambogini ya tunkara wanda da hanzari mai gadi ya bude masa get tare da barin harabar gidan.

saida ya biya ya yi salla a masallacin kofar gidan kafin ya karasa gidan Abiy gidane na alfarma kallon securityn da ke zagaye da gidanma kadai ya isa ya tabbatar maka da mamallakin gidan jikakkene a mulkin kasar Wanda ko a daular larabawa kasan mallakar wannan gidan sai mashahurin mai kud’i.

Kai tsaye shak’akken palour Abiy ya tunkara Zaune ya tarar da balaraben farin dattijon da a k’alla shekarun haihuwarsa zai Kai 63 cikin gimamawa da tarbiya ya gaisheshi ya amsa tare da shafa kansa cikin harshen larabci ya umarcesa da ya zauna bayan sun zauna ya kallesa cikin Kulawa ya ce”Muhammad Ali na Kira ka ne ba don komai ba sai dan wata alfarma guda da nake nema wajenka?

Cikin sauri ya d’ago tare da kallonsa sai kuma ya b’ata fuska ya na kallon gefe ya ce “Ka wuce neman Alfarma a waje na Abiy umarni kawai za ka ba ni ni kuma na zartar,domin Kai d’in ai uba ne a wajena ”

Murmushi kamilallen dattijon ya yi ya ce”tabbas ina jinka tamkar D’an da na Haifa a cikina Muhammad Ali Baka da banbanci da su Ramadan amma hakan bazaisa na tilasta maka abunda Baka so ba,dole na ce ina neman alfarmarka domin abu ne mai girman gaske nake so ya k’ullu tsakaninmu Ina son Ka Auri y’ata Zahra domin k’ara karfafa dankon zumuncin da ke tsakaninmu na tabbata ko yaya ya ke raye zaiyi farinciki da hakan!

Lokaci guda wutar kansa ta dauke kafin ya ji wani irin Abu ya soki zuciyarsa wanda saida ya rumtse idanunsa duk yanda ya so saisaita nutsuwarsa kasawa ya yi domin tamkar saukar aradu aka haka ya ji maganganun Abiy bai tab’a tsammanin hakan daga garesa ba dakyal ya iya daidaita nutsuwarsa kafin ya d’ago zaiyi magana Ya dakatar dashi ta hanyar cewa.

“Banyi maka tilas ba Muhammad Ali idan ka na ganin baka son zahra ka fada mun Kai tsaye bazanji komai ba saboda duk ku biyun d’aya kuke a wajena”

Karo na biyu kenan da ya dago tare da zubawa Abiy manyan idanuwansa ba ko kiftawa “Toh da wani ido ma zan iya kallonsa na ce bana kaunar y’arsa bazaiyu ba”Ya fada a cikin zuciyarsa

nauyayyar ajiyar Zuciya ya sauke kafin ya dago a karo na biyu ya na kallon abiy da har yanzu shi ya ke kallo ya ce “bansan da wasu kalamai zanyi amfani da su wajen gode maka ba Abiy nagode kwarai da gaske Allah ya biyaka da gidan Aljanna ”

Murmushi Abiy ya yi ya na Sakin ajiyar zuciya ya ce”ni ne zanyi maka godiya Muhammad Ali Allah maka albarka Insha Allah Bazaa’a dauki dogon lokaci ba wajen gudanar da Auren ba”

”Sam saurarensa yake amma hankalinsa ba ya tattare da shi ya tafi wani waje daban “Auren zahra !!!!ya maimaita a cikin ransa kafin ya ce “bazaiyuba!

sam koda ya koma gida gagara bacci ya yi sosai kwalwarsa ta chazu bai tab’a tunanin Al’amura zasu kasance haka ba,

wayarsa ya dauka ya na kafe wani hoto da kallo ba ko k’iftawa ta ya zuciyarsa za ta iya rayuwa da wacce baya so”!bai tab’a son zahra a cikin ransa ba dukda kulawa da soyayyar da take nuna masa matsayin kanwa ya dauketa yasan tabbas ita zata fad’awa Abiy ta na sonsa ta ya zai ma iya rayuwar Aure da zahra bayan Sam tarbiyar yarinyar ma kanta ba ta masa ba wani dogon tsaki ya ja tare da dafe kansa “Tabbas Dole na gujewa Auren nan!”.

*NIGERIA*🇳🇬
(KATSINA)

Sosai ta tsirawa wayar hannunta idanu ba ko kiftawa gaba d’aya hankalinta na ga karanta comment din da ake ta yi mata a posting hotunanta da tayi minti talatin baya amma comment sama da 500 sosai jama’a ke zuzuta baiwar kyawun da Allah Yayi mata kowa na fad’ar albarkacin bakinsa,
wani irin dogon tsaki taja tunowa da duk comment dinnan da take sha dole ta sauke sa kafin ayi mata Chaa kamar wacce ta haifi d’an shege.

Deleted ta danna tana kuma jan dogon tsaki tare da kallon jawahid da ke gefenta ta ce”Wlh y’an gidanmu basuyi ba Ina son social media amma sun tusoni gaba sunki barina na yi rawar gaban hantsina kina gani fa idan nayi posting a take ya ke zuwa viral comment din da nake sha ba na wasa ba ne amma saina sauke”
ta karasa fad’a tamkar zata fashe da kuka saboda tsabar takaici.
Wacce ta kira ta jawahid ta bata amsa da.

“ki hakura da social media dinnan Ayda tunda kowa na gidanku baya so sannan Faruq ma kinga dagun da kuke sha Akan hakan kuma ni kaina bana ganin laifin Faruq ta wannan bangaren saboda ko ni namiji ne haka Zanyi Ayda kina da kyan da ko mace ta kalleki sau d’aya sai ta kuma kallonki Toh me zaisa bazasu killaceki ba “

Tura Baki gaba tayi ta na mikewa ta ce”nasan ai haka sakice saboda ke social media daman bata gabanki “itama mikewar tayi ta na gyara tsayuwar handbag dinta ta ce “gaskiya na ke fad’a maki mace mai mutunci da tarbiya bata tallar kanta a duniya kin kasa gane ba mutuncinki ba ne “

“Ni dai naji dad’in abun baki isa kimun wa’azi ba Boko tare islamiya tare gudun hadda tare yanzu ma gudun lectures tare kinga baki fini ta nan ba”

Dariya mai sauti jawahid tayi tare da cewa “Kinsan dai nafiki jin wa’azi dai ko?Harara ta bi ta dashi tare da maida kallonta ga makekiyar motar da ta faka gaban parking space din restaurant d’in Tana rejecting sabon kiran da ke shigowa wanda sunan waziri ya bayyana ga screen din wayar.

“Toh fa kamar motar waziri nake gani “cewar jawahid “Ayda na tsatsare gira ta ce “Eh jiya ya dawo saura ki sakar masa fuska ki na masa dariyar nan taki da kika saba ya dauki kansa wani shege “
Chapter 1 · 0% Book details