← Book details Masarautar Kaizur Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 7 OF 21

Sashe 7

Masarautar Kaizur Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Kar ki manta daular Tayaar a duk nahiyar nan babu wani gari wanda yake fa
a da zalunci irin namu, alhamdulillahi kuma muna yin nasara
Ba mu kawo Kazuzi cikin daular Tayaar ba sai don mu cusa masa sha'awar musulunci, tunda kamar yadda muka sani musulunci ba'a yin shi da dole,kuma ko da ana yinshi da dole har yanzu Kazuzi bai yi lalacewar da za'a saka shi yin abu da
arfi ba
Amma ke menene shawararki?"
Kallonshi ta yi, cikin raunin murya ta ce "Abby ya nuna baya ra'ayi, meyasa ba za ku
yale shi ba?"
Murmushi sarki Iyaad ya yi,sannan ya sake dubanta ya ce"kina da labarin Sarkin ya
i da ya rasu,wato Sadauki Ilyas?"
Take fuskarta ta washe da murmushi, idanunta akan shi ta ce"na sanshi, idan ban manta ba da ni da yaya na Yarima Nashwaar ya
auke mu a matsayin jikokinsa,yana matu
ar kula da mu a wancan lokacin
Na sani shi ma mun rasa shi a wani ya
in da Tayaar ta gwabza da Baruda "ta
arashe fuskarta tana nuna alhini
Sarki Iyaad ya ce"to shi wannan bawan Allan da kika sani mahaifina a ribar ya
i ya samo shi kamar yadda aka samo Kazuzi,babban maya
i ne,kuma fitaccen jarumi a daularsu kamar dai Kazuzi,amma da babana sarki Nufail ya yi duk mai yiyuwa sai gashi an samu abin da ba'a yi tunani ba,bayan kasancewarshi Musulmi mai ibada a kowanne lokaci ya kasance shine mai jagorantar ya
i,kin san menene ya janyo mana nasara a wancan lokacin?"ba tare da ta yi magana ta girgiza kai a hankali
Sarki Iyaad ya ce"to jimirin jira ne,don sai da Sarkin ya
i Ilyas ya shekara bakwai da mu yana bin addinin shi na bautar wuta,a wancan lokacin mahaifina ya fuskanci
alubale da dama,ya jure maganganu daga wajen mutane,amma sai gashi rana tsaka burin shi ya cika,sadaukin ya kar
i musulunci,har ma ya ja Sallah a masallaci,shin ni ba kya son na kafa wannan tarihin ne?"
Cikin sanyin jiki ta girgiza kai,sarki Iyaad ya ce"to ki
auki Kazuzi a matsayin da kike
aukar kuyangin ki da dakarun da suke tsaron lafiyarki, yadda kika mayar da su aminanki,masoyanki,makusantanki haka nake so ki mayar da Kazuzi,in sha Allah lokaci yana zuwa da za mu samu nasarar canja masa ra'ayi kamar yadda muka chanjawa sadauki Ilyas"
Rissinawa ta yi tana fa
in "fatan nasara mai
orewa Abby!"
Sarki Iyaad ya yi
an murmushi yana fa
in"fatan rayuwa mai albarka da ma'ana yata "daga nan ya juya da niyyar ficewa daga
akin
Gimbiya Hayat ta bi shi da kallo,ta gamsu da maganarshi,amma tabbas sai ta hukunta Kazuzi ko yaya ne, musamman da ya janyo Abby
inta abin alfaharinta ya
aga hannu da niyyar marinta
*DAULAR KAIZUR*
"Ya shugaba ta!mai martaba ne ya ce a yi masa iso"
aga kai gimbiya Amna ta yi tana kallon jakadiya da kanta yake a
asa,ta ce"ki yi masa iso Nayyab"Nayyab ta sake rissinawa sannan ta mi
e ta fice daga turakar
Bayan
an da
u sarki Mu'iz ya shigo da sallama, sarauniya Amna ta rissinar da kai ta amsa,ya
araso ya zauna kusa da ita, cikin girmamawa ta ce"Barka da zuwa ya shugaba na"
"Barkanki da warhaka sarauniyar Kaizur!"
"Jakadiya ta ce ayi maka iso"
Sauke ajiyar zuciya mai nauyi ya yi cikin damuwa,ta
aga kai tana kallonshi,a hankali ya furta"na kasa jurewa ne,dole na taho mu yi magana"
"Kan batun yarima Sahal?"ta fa
a a raunane tana kallonshi
Shiru ya yi kanshi a
asa,ta yi
an murmushi mai ciwo tana girgiza kai ta ce"tunda na ji a jikina a kwanannan,na yi mafarkai da yawa,ga yawan fa
uwar gaba na san
ana ya fa
a mugun hannu,zuwa yanzu na san na rasa Yarima na"zuwa lokacin sosai take kuka
Girgiza kai sarki Mu'iz ya yi da sauri,ya ce"wannan hasashe ne kawai sarauniya,ina cikin damuwa ne kawai saboda tsawon lokacin da muka
auka muna neman shi amma har yanzu babu labari,na yi duk mai yiyuwa amma babu nasara
Yarima Sahal yana raye,shine kawai tabbacin da nake da shi,amma banda haka da tuni na ha
ura,komai na bawa mu
addari ne"
Sarauniya Amna ta jinjina kai ta ce"haka ne mai martaba
Amma idan da hali ina so mu gana da Munaya, wata
ila mu samu wani haske "
Sarki Mu'iz ya girgiza kai ya ce"babu Abin da ganawa da Munaya zata haifar sai damuwa,da alamu wa
anda suka saka ta aikin sun shirya, shiyasa ita ma ta shirya,sam bata tsoron ko da mutuwa, shiyasa bana son abin da zai ha
a ni da ita yanzu"
Girgiza kai sarauniya ta yi,ta ce"kar mu yi haka, abu ne na ribar mu,idan yarima Sahal ya salwanta mu ne muka shiga matsala,idan ya bayyana amfanin mu ne,mu je mu tattauna da ita,ina fatan zata yarda ta ba mu
arin haske"
Girgiza kai sarki Mu'iz ya yi,ya ce"mu je,amma bana jin hakan gaskiya, amma ni na riga na yanke hukunci,ba zata
ara shekara
aya a
aure ba,zata ba
unci inda su Umayr da Ya'a
ub suka je"bata yi magana ba sai jinjina kai,sarki Mu'iz ya mi
e tsaye, itama ta mi
e suka fice daga turakar
*DAULAR TAYAAR*
"Barka da warhaka ya shugaba ta"
Kallonshi ta yi sosai, kafin ta fara magana a dake"ribatattun ya
i da aka kamo daga Baruda,an raba musu wajen aiki ne?"
Dakare Amjad ya ce"tukunna dai ya shugaba ta,amma yau in sha Allah za'a raba musu"
Sauke ajiyar zuciya ta yi,kai tsaye ta ce"to wannan zindi
in badakaren,ina so a saka shi cikin jerin masu yi min hidima "
A firgice shugaban dakaru Amjad ya kalle ta,a
an tsorace ya ce"ranki ya da
e babu kasada a cikin hakan?"
"Umarni na bayar,bana bu
atar a tambaye ni,saura kuma ka kai ni gaba,tashi ka fice,na sallame ka "babu musu shugaban dakaru ya rissina sannan ya mi
e ya fice daga lambun nata cikin zullumi da fargaba
Har yanzu sadauki Kazuzi abin tsoro ne, ba'a gama sanin wanene shi ba,ta yaya ita mace mai rauni ta ce wai a saka Kazuzi ya yi mata hidima?shi dai yana ganin da kuskure a hakan
Hakan ne ya saka ya yi fatali da umarninta,bai yi
asa a gwiwa ba ya samu Sarkin ya
i da maganar
Murmushi sarkin ya
i ya yi,a ranshi yana fatan abin da yake gani ya tabbata, gimbiya Hayat ta sau
a musu hanyar jan ra'ayin Kazuzi,don haka ya ce"ka bi abin da ta ce, sauran kuma mu bar wa Allah, in sha Allahu babu wata matsala"dakare Amjad ya rissina sannan ya mi
e ya bar wajen
A ranar aka rabawa sababbin bayi wajen aikinsu,ciki har da Kazuzi,da aka tura shi tsaron lafiyar gimbiya Hayat
Ta ji da
i sosai da labari ya iske ta, tana zaune a
awataccen lambunta,amintattun kuyanginta sun kewaye ta ta aika
aya daga cikin asalin dakarun da suke gadin lambunta cewa ya kira mata Kazuzi
Babu jumawa suka
araso,a fizge ta kalle shi sannan ta mayar da kanta gefe
irjinta yana bugawa,tsawon lokacin da ta
auka tana yi masa tijara bata ta
are masa kallo ba sai yau
Cikakken namiji mai cikar zati,dogo ne sosai,mai
irar jiki mai matu
ar kyau,duk da cewa sanye yake cikin kayan bayi amma sai taga sun yi masa kyau tamkar ba bawa ba,sosai ta ga ya yi mata kwarjini tamkar ba bawanta ba,dogon gashinsa da ya
aure a tsakiyar kanshi ya sake shi ya zuba gadon bayansa,iska sai ka
a shi take yi
A dalilin haka ta kasa yi masa rashin mutunci da
iban albarka da ta shirya,yana zuwa gabanta bai yi wata-wata ba ya zube a
asa, kanshi a
asa ya ce "Barka da wannan lokaci ya shugaba ta!"
Shiru ta yi da farko tana bin shi da kallo, kafin ta yi juriya ta ce"ka iya ladabi kamar gaske,amma ka ha
a ni fa
a da mahaifi na!"
Bata yi tsammanin zai ba ta amsa ba,amma ta ji ya ce"ki gafarce ni ya shugaba ta"
Da mamaki take kallonshi kafin ta ce"na san zuwa yanzu ka yi nadamar abin da ka yiwa
an'uwa na da mahaifiya ta ko?"
Ba tare da shakkar komai ba ya ce"Kazuzi baya aikin nadama ya shugaba ta"
Da mamaki take bin shi da kallo,su ma kuyangin nata kallonshi suke yi, kafin ta sake dakewa ta ce"anjuma za mu fita yawon sha
atawa zuwa dajin Lahur,sai ka kasance cikin shiri"
Ya sake rissinawa gami da amsawa da fa
in "an gama ya shugaba ta"
Cikin
osawa ta dube shi ta ce"na sallame ka, za ka iya tafiya"
Ya sake rissinawa ya ce"na barki lafiya ya shugaba ta"daga haka ya mi
e tsaye, cikin takunshi na dirarren namiji mai izza ya bar wajen
Da yamma ta shirya kamar yadda ta saba lokaci zuwa lokaci,ta yi ado mai kyau,suka shiga keken dokin da suke fita da shi ita da kuyanginta, Kazuzi da wasu dakaru su biyu suka bi bayansu a dawakai zuwa dajin Lahur
Hayat tana tsananin son ganin tana yawatawa yadda take so, amma mahaifinta sarki Iyaad bai cika son hakan ba, shiyasa yau da ya yarje mata take cike da farin ciki
Daga ita har kuyanginta da ta mayar da su tamkar
an uwanta sai shawagi suke yi cikin kwanciyar hankali,sam ba su kula da wata damisa da take fakon gimbiya Hayat ba,sai gani aka yi ta daka tsalle cikin zafin nama ta yi kanta.....
(Damisa zata lamushe gimbiya
Comments da likes suna qaranci sosai
ko na tafi Hutu ne
#Nusy_bee
08125952284
MASARAUTAR KAIZUR
https://chat.whatsapp.com/Is0HqhjNITL3VZIagV42u7?mode=gi_t
Nusy bee
Young talented writers association YOTA
(Under YOTA'S AMAZING PENS)
Page 7
Wata firgitacciyar
ara gimbiya Hayat ta yi a tsorace,kafin ta zame ta zube kasa sumammiya, tuni kuyanginta suka cika dajin da iface-iface, lokaci guda komai ya yi tsit tamkar babu wani mahaluki mai rai a cikin dajin
Ba komai bane ya faru face tsalle da Kazuzi ya yi, cikin wani irin tsananin zafin nama ya cafke damisar, ba tare da
ata lokaci ba ya yi jifa da ita
ewa damisar ya yi yana gurnani yana kallon Kazuzi, Kazuzi ma kallonshi yake yi fuskarsa babu yabo babu fallasa,damisar bai bi ta kan Kazuzi ba ya sake nufar inda Hayat take kwance,da wani irin
arfi Kazuzi ya sake dam
arshi,ya ja shi da
arfi, ba tare da
ata lokaci ba aka kaure da kokawa tsakanin Kazuzi da damisar, lokaci guda damisar ta farke
aurin da aka yiwa ciwon hannunshi na damtse,kuma a take jini ya
alle a hannun
Kallon hannun ya yi sannan ya sake kallon damisar,yana murmushi ya ce"yanzu hankalinka ya kwanta?
Chapter 7 · 0% Book details