← Book details Masarautar Kaizur Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 4 OF 21

Sashe 4

Masarautar Kaizur Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ban isa a bu
e min shi ba?"
Murya na rawa badakaren ya ce cikin girmamawa "ranki ya da
e akwai ha
ari a cikin hakan ne,ki yi min aikin gafara shugaba ta"
Kai tsaye ta ce"ina son a bu
e min shi idan har ina da ikon fa
a a ji a cikin birnin Tayaar"
Ba tare da ya sake magana ba,ya mi
e cikin rawar jiki, suma sauran dakarun suka mi
e,aka bu
e mata
ofar, ba tare da ta sake kallon ko da sashen da suke ba ta sanya kai a cikin tangamemen
akin, kuyanginta suka rufa mata baya,suma dakarun hu
u daga cikinsu suka rufa mata baya,ya rage saura biyu a cikin guda shidan da suke gadinta
A can
urya suka hango Kazuzi a zaune,tun daga yadda aka shigar da shi cikin wajen har zuwa yanzu yana nan a zaune kanshi a
asa, idanunshi a rufe, abinci da ruwan da aka kai masa ma ko bi ta kansu bai yi ba
Har yanzu damtsenshi,inda marigayi sadauki Waleed ya sare shi yana
an zubar da jini,duk da cewar an saka masa magani a raunin
Daga baya kuyangin da dakarun suka tsaya,ita kuma ta
arasa gabanshi tana jefa masa wani kallon tsana,kafin ta bushe da wata iriyar dariya,tana dariyar ta
arasa gabanshi, ta sanya hannu ta
ago fuskarshi,ta sanya hannu ta yaye gashinshi fuskarshi ta bayyana
Ya subhanallahi!samun kyakkyawan namiji kamar kazuzi abu ne mai wahala,komai na fuskarshi mai kyau ne da tsaruwa,tamkar wanda ya shiga gasar zana kanshi, gashinshi da ya sauka har gadon baya ya sake
awata kyau da sura da Allah ya ba shi,gashi namiji ne mai cikar zati da mazantaka,muradin
an mata a wancan lokacin
"KAZUZI!haka sunan yake ko?

Barka da zuwa daular Tayaar,a wasu shekaru baya sunan Kazuzi ka
ai idan maya
a suka ji yana ka
a musu hanjin cikinsu, ballantana karo da shi a filin ya
i,sau da dama maya
a suna yi maka la
abi da ka fi dodo illa, saboda yadda kake ragargazar maza kana gamawa da su
A haka karambaninka ya kai ka ka kashe min
an'uwa na
aya tilo da mahaifiyata ta haifa,wanda sanadin hakan ya sa ba
in ciki ya yi silar barinta duniya
A ta
aice dai,ina yi maka kallon makashin mutum biyu, Yarima Nashwaar,wato yayana,da sarauniya Shahida, wato mahaifiyata
Ba sai na cika ka da surutu ba, yadda ka zo masarautar nan a matsayin bawa,na yi maka al
awarin sai ka amsa hakan,sai na tabbatar maka da lokacin wannan ba lokacin da kake tashe bane,ka san shi tashe lokaci gare shi,kamar yadda naka ya zo kuma ya shu
Sai na tabbatar da ka yi rayuwar
anci a cikin masarautar nan,sai na tabbatar da dabba ma ta fi ka
anci da gata a cikin Tayaar
Da gimbiyar Tayaar wato HAYAAT kake magana!!!"tana kai wa nan ta saki fuskar tashi ta mi
e cikin takunta na isa da izza ta fice daga
akin ranta fes, kuyanginta dakarun suka rufa mata baya
Har suka
arasa ficewa daga
akin kan Kazuzi yana
asa kamar yadda suka zo suka same shi,a karo na farko,tunda ya rasa muradin ranshi ya ji ya kamata ya bu
e idanunshi don sake ganin wannan duniyar da ta yi masa yankan baya a lokacin da bai yi zato ba
Shi dai jarumi,maya
i,kuma sadauki KAZUZI IBN MURAAD shine wai aka kawo shi a
aure a sar
a a matsayin bawa,bawan ma na wani birni da ya raina,ya raina jarumansa,duk menene sila?MALLI!
tuna sunan kawai sai da ya ji zuciyarshi ta girgiza,a hankali ya mayar da kanshi ya jinginar yana sauke numfashi da sauri da sauri, menene amfanin rayuwarshi da babu Malli a ciki? meyasa aka kashe masa Malli a gaban idanunshi?shin ta cancanci irin wannan kisan?

Wanene silar mutuwar tata?shine
To indai haka ne bai ga amfanin rayuwarshi a matsayin wani mai galihu ba muddin babu Malli a duniya,ya gwammace ya mutu a matsayin
antaccen bawa da ya rayu cikin farin ciki amma babu Malli a gefenshi,zai yi fatan wa
annan mutanen su yanke masa hukuncin kisa mafi wuya,ko zai rage masa ciwo da ra
in wannan gangancin da ya yi har ya rasa abun da ruhin shi yake marari a kowanne lokaci na rayuwarsa
Malli ita ce farin cikinshi, walwalar shi, ma'anar rayuwarshi,fitilar rayuwar shi,kuma maha
in rayuwarshi,ji yake yi a rayuwarshi zai iya bayar da fansar ranshi akan Malli
inshi ta ji rauni duk kan
antarshi
A yanzu jin shi yake yi a duk duniya
babu wanda ya kai shi ba
in ciki,babu wanda ya kai shi shiga tashin hankali,babu wanda ya kai shi asara a rayuwarshi
"Ruhi na!ruhi na kana ji?

Yaushe za mu je ka kamo min irin wannan barewar da ka ta
a kama min kwanakin baya?ina son namanta,yana yi min da
i sosai, musamman ma idan kai ne ka gasa min da hannunka,sai na ji wani
ano na musamman ya
aru"
A hankali ya mayar da kanshi ya jinginar yana sake lumshe idanunshi, ire-iren shiriritar Malli kenan a duk lokacin da suke cikin nisha
"Ruhi na!

Menene dalilin da ya sa ba ka bar babana ya jagoranci tawagar ya
i ba?

Ba shine Sarkin ya
i ba?ko so kake yi wani abu ya samar min kai?"
Murmushi Kazuzi ya yi ya dube ta ya ce"au haka ne?

Wato shi matarshi bata san soyayya ba da zata bar shi ya fara afkawa ba ni ba?"
an murmushi ta yi tana yatsina fuska,ta zauna a kusa da shi ta ce"ka ga Ni da kai mun kusa aure,ba zai kyautu a ce angon wani abu ya same shi ba,don dai na san ka fi
arfin wata runduna wadda ta wanzu a duniya ma, ballantana a wannan nahiyar tamu"
an murmushi ya yi ya dafa kafa
arta,ya ce"hakanan Sarkin ya
i shima,ya girmi dukkan wata runduna,kar ki manta rundunar Baruda shine ya ba mu horo,har zuwa yanzu an rasa wanda zai iya tunkarar mu ya farmake mu,kai ko da ya iya hakan ma ba zai sha ba"
ar dariya Malli ta yi ta kwanto da kanta gefen kafa
arshi,ta lumshe idanunta tana murmushi ta ce"Duniya ta,kaine komai na,kaine dukkan buri na da cikar burina,ina matu
ar alfahari da kai"Kazuzi ya yi murmushi ya ce"nima ke ce farin ciki na,abin alfahari na, duniya ta,dukkan wani buri na,hasken rayuwa ta,ke ce komai na,sannan alfahari na"
ar dariya ta yi ya mi
e tsaye tana karka
asar da ta ta
a mata tufafinta,ya yi
an murmushi yana taya ta ka
ewa,ta kama hannunshi,ya mi
e suka wuce cikin gari
Doguwar ajiyar zuciya ya yi saboda tunawa da ya yi wadda yake yin wannan tunanin da ita yana murmushi babu ita a duniyar,a karo na farko tun bayan da ya rasa ta ya iya bu
e baki ya yi magana
"Abin bauta!!!

Wanne laifi na yi da girma?me na aikata ka raba ni da rabin rayuwa ta? meyasa?shin na cancanci hakan ne? menene dalilin hakan?

Na za
i zama a matsayin bawa
antacce,ko nima a raba ni da numfashi na kamar yadda ka bari aka raba ni da
awar zuciya ta"ya
arashe maganar cikin wani irin rauni da bai ta
a jin shi ba a tsawon rayuwarsa
"Barka da shigowa ya shugabana!"da kai ya amsawa kuyangar sannan ya ba su iznin ficewa daga sashen da hannunshi,babu musu suka du
a da girmamawa sannan suka fice daga sashen,ya mayar da kallonshi ga Hayat da ke zaune a bakin gadonta tana bin shi da kallon mamaki ganin yadda ranshi ya yi matu
aci
"Barka da shigowa abbana!"ta fa
a tana rissinawa
"Me ya kai ki
akin hukunci Hayat?"
A hankali ta
ago kai tana kallonshi,zata iya cewa rabon da ta ganshi a cikin Irin wannan
acin ran ta manta, cikin sanyin murya ta sake rissinawa,ta ce"a yi min afuwa ya shugaba na,na yi wani al
awari ne,shine na je na cika"
"Amma kin san cewa Kazuzi ya fi ha
ari ha
ari?kin san cewa Kazuzi ya fi shai
an?ya fi sharrin maya
an abokan hamayya dubu?

Kin san wanene Kazuzi da kika tunkari inda yake ke ka
ai ba tare da tsoro ba?

Yanzu da ace wani abu ya same ki fa?ko kin yi tunanin ya rissina ne saboda an kamo shi an kawo shi nan a matsayin bawa kawai?"
Hayat ya sauke numfashi, cikin girmamawa ta ce"ina neman afuwa abbana!

Amma tabbas na daukar wa kaina al
awarin sai na ga ya dur
usa a gaba na,sai na bautar da shi na wula
anta rayuwarsa saboda a dalilin shi na rasa duniya ta,
an'uwa na magajin Sarautar Tayaar da mahaifiya ta, kana ganin na bar shi ya tafi a banza kenan?

Abby idan na yi haka bana jin na kyautawa
an'uwa na"ta
arashe hawaye suna zubo mata daga idanunta
Lokaci guda zuciyar sarki Iyaad ta buga sakamakon tuna wannan asarar da ya yi,amma sai ya dake,ya dube ta cikin tausasawa,da Muryar lallashi ya fara fa
ata!

Ki yi ha
uri da rayuwa,ki kasance mai yafiya da tausasawa
Mu masu jihadi ne, wa
anda suke ya
i don
aukaka kalmar Allah,ashe idan haka ne mutuwa rahama ce a gare mu
Raki ne,ko na ce kai
arar Allah,ashe a matsayin mu na musulmai sai mun yarda da cewa shahada a wajen ya
i ita ma nasara ce sannan za mu cim ma nasara?

Ba mu fa
i ba, kamar yadda Allah ya fa
a a Alkur'ani ba mu rasa shahidanmu ba,ciki kuwa har da
an'uwanki
Hayat!wannan ba lokacin
aukar fansa bane, lokaci ne na godiya ga Allah,zuwa gobe za'a la
ana wa ribatattun ya
in mu kalmar shahada,muna fatan gaba
aya za su musulunta,daga wannan lokacin za muyi musu Barka da shiga musulunci ne,ba fansa za mu
auka kamar yadda kika ce ba,in sha Allah"
Sake rissinawa ta yi,cikin girmamawa ta ce "ka gafarce ni abbana!
Chapter 4 · 0% Book details