← Book details Masarautar Kaizur Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 3 OF 21

Sashe 3

Masarautar Kaizur Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Sanannen abu ne tabbas ba zai kar
i musulunci ba ko me za'a yi masa,amma kuma ina ganin da kuskure a jan shi a jiki da za'a yi, saboda mu shaida ne,babu abin da jinin Baruda suka tsana kamar musulunci,duk wani wanda ya sha ruwan daular Baruda zai tashi da tsanar Musulmai da burin son ganin bayanmu,mai zai hana a yanke masa hukuncin shi kawai,kar ya yi amfani da yardar da muka yi masa ya cutar da mu?"
Girgiza kai sarkin ya
i ya yi, cikin girmamawa ya ce"ya shugaba na,a dai duba magana ta,ban hana a sakawa kazuzi idanu ba,amma ya kamata a ba shi wata dama, tunda har muka iya kamo shi,abin da babu wata daula da ta ta
a samun wannan kwatankwacin nasarar,idan har ya gwada wata halayya muka ji ba mu yarda ba za mu
auki mataki akanshi kawai,amma a matsayin mu na musulmai,sannan manyan babbar masarauta bai kamata a ce mun razana saboda wani bawa da Allah ya ba mu nasara akan shi ba,amma ya kuka ce?"
Shiru fadar ta
auka,kowa yana nazari,zuwa can waziri ya katse shirun da cewa"to shikenan,a gwada shawarar taku,amma ni ina ganin a saka masa idanu sosai,sannan kuma a tsare shi,a yi duk mai yiwuwa don ganin an karya
arfinshi,yadda ba zai iya wani tasiri ba"
Sarki Iyaad ya ce"shiyasa muka bayar da umarnin a killace shi, kafin nan sai da muka tabbatar mun raba shi da duk kayan tsafi da surkullenshi"
Waziri ya sake rissinawa ya ce"ya shugaba na,an
auki matakin da ya dace, ragowar kuma sai mu bar wa Allah "
Sarki Iyaad ya ce"hakan ya yi,muna fatan yadda Allah ya ba mu ikon yin wannan jihadin muka yi nasara akan wa
annan azzalumai, Allah ya ba mu iko da nasara akan wannan babban shai
anin"
Fadawa suka amsa da "Ameen!"daga nan sarki ya rufe taro da addu'a,fa
a ta watse
A hankali toron giwar yake zaunawa akan
afafunshi bisa umarnin dakarun da suke umartarshi,shugabansu ya kama
atuwar sar
ar da aka
aure kejin ya fara
arin kwancewa cikin dakiya,sauran dakarun suka fara
arin taya shi
Bayan gama warware
atuwar sar
ar tsayawa suka yi cirko-cirko suna kallon juna a
an firgice,duk jarumta da taurin zuciyar badakare ya san wanene Kazuzi, yanzu haka ma kallonshi suke yi, wanda shi duk abin da ake yi ko
ago kai bai yi ba ballantana ya kalli wani,har yanzu kanshi a
asa yake,tunda aka shigo da shi cikin birnin Tayaar har yanzu babu wanda ya ga fuskarshi ballantana ya shaida a wanne hali yake ciki
Wani badakare ne ya yi
arfin halin fara
arin saukar da kejin,sauran dakarun ma suka saka masa hannu,suna saukewa kuma shugaban nasu ya yi
arfin halin bu
e kejin
Yana bu
ewa suka ja baya a
an tsorace,kafin
aya daga cikinsu ya yi
arfin halin matsowa yana kallon Kazuzi,da sai yanzu suka kula ashe duk abin da yake faruwa ma idanunshi a lumshe yake,babban dakaren ya saka hannu da nufin fito da shi, sauran dakarun ma suka saka hannu don fito da Kazuzi,amma duk
arin su tamkar suna yun
urin matsar da
aton dutse,ko motsi baya yi
Shiru suka yi,suka tsaya cirko-cirko suna kallon juna,kafin babban badakaren ya yi ta maza ya dubi Kazuzi ya ce
"Sadauki Kazuzi!

Kafin yau kai
in jarumi ne, mai gata da dama,mai sharafinshi a wannan nahiya,wanda ya gagari kowa,amma a yau kai ba komai bane face bawa,don haka sarki Iyaad yana umartarka da ka fito daga kejin nan don a kai ka inda aka warewa bayi irinka"
Maganar babban badakaren ta razana
ananan,don da alamu sun manta wanene Kazuzi,sai dai abin da ya yi tsananin ba su mamaki bai wuce ganin Kazuzi ya yun
ura ba,cikin
anin lokaci ya fito daga cikin kejin ya tsaya a gabansu,kuma har zuwa lokacin idanunshi a rufe suke
Da farko bin shi suka yi da kallo cikin tsananin mamaki da ka
uwa,amma daga baya babban badakaren ya dake ya kama shi,kai tsaye suka wuce
akin da aka tanada don Kazuzi
Ba su kwance masa ko sar
aya ba,daga ta hannu har zuwa ta
afa,suka tura shi zuwa
akin mai tsananin duhu,suka mayar da
ofar da ta kasance ta wani nau'in
arfe mai nauyi suka rufe ta ruf
Kai tsaye wajen Sarkin ya
i suka nufa, cikin girmamawa suka sanar da shi cewa sun kai Kazuzi zuwa
akin da aka tanada don shi,sarkin ya
i Ra'uf ya kalle su yana murmushi ya ce"sannunku da
ari,yanzu sai a kai masa abinci"suka rissina, babban badakare ya ce"an gama ya shugaba na"
DAULAR KAIZUR
A hankali yake tafiya yana bin doguwar hanyar, dakaru uku da ke tsaron lafiyarshi suna take masa baya,yana zuwa daidai inda suke tsayawa suka tsaya ba tare da an umarce su ba, gami da juya baya,sarki Mu'iz ya cigaba da tafiya zuwa cikin duhuwar bayan ya
auki karan a ci bal-bal guda
aya da suke bakin
ofar
ar doguwar tafiya ya yi a cikin kogon kafin ya
arasa inda yake muradin zuwa, murmushi ya yi yana kallon dattijuwar matar da take dur
ushe a kan gwiwowinta,
aure take da sar
a mai matu
ar nauyi,tana sauke numfashi a wahale,kayan jikinta zuwa gashin kanta a hargitse
"MUNAYA!"ya ambata cikin wani irin amo mara da
in ji,
agowa matar ta yi da kanta, cikin
arfin hali ta furta "Barka da zuwa ya shugaba na!"
Bai amsa ba,sai zama da ya yi a wajen da ya saba zama yana kallonta cike da tsana,bata damu ba,ta saba ganin irin wannan kallon daga wajenshi,har zuwa mutanen garin da suke kallonta a duk lokacin da aka fitar da ita daga inda take a kulle
"Munaya!

Tsawon shekaru ashirin kenan kina azabtar da zuciyarmu,akan abin da kika sani ba naki bane tun kafin wanzuwar shi a duniya, menene dalilin da ya sa ba za ki daina azabtar da zuciyoyinmu haka ba? menene dalilin da ya sa ba za ki huta ba mu ma mu huta?

Ki yiwa kanki adalci ki yi mana,ki bayyana inda kika kai ajiyar nan,daga nan za mu sallame ki kema ki huta"
A hankali Munaya ta
ago kanta tana sauke numfashi, ba tare da ta kalle shi ba, cikin sanyin murya ta furta "a yi min afuwa ya shugaba na!

Amma abin da na saba fa
a dai shi zan maimaita,bani da masaniyar inda yake"
Shiru sarki Mu'iz ya yi yana kallonta zuciyarshi tana tafasa,da sauti irin na fushi ya ce"amma kin yarda da cewa da saka hannunki a
atan kadara mafi daraja a kaizur?"
Kai tsaye ta amsa da fa
in"tabbas haka ne ranka ya da
e,ni na fito da shi,amma daga nan ban san komai ba,kuma ba zan iya komai don dawowarshi ba"
#Nusy_bee
08125952284
MASARAUTAR KAIZUR
https://chat.whatsapp.com/Is0HqhjNITL3VZIagV42u7?mode=gi_t
Nusy bee
Young talented writers association YOTA
(Under YOTA'S AMAZING PENS)
Page 3
Sarki Mu'iz ya daka mata tsawa da cewa"ba ki da bakin yi min wani jawabi Munaya!

Ke kika
atar min da
a,ki yarda da hakan,amma ba ki da wasu kalamai da za ki kare kanki daga hakan,za ki cigaba da kar
ar hukunci har zuwa lokacin da za ki bayyana
ana,ko kuma ki bar duniyar,ke azzaluma ce tabbas,amma zaluncin zai rufto miki"ya mi
e a fusace ya fice daga wajen, Munaya ta bi shi da kallo ba tare da ta iya cewa komai ba
Masu tsaron lafiyarshi ba su yi mamakin ganinshi a haka ba saboda kusan duk lokacin da ya ziyarci Munaya hakan ce take kasancewa,suka rufa masa baya don komawa fada,kamar yadda suka saba har suka fice daga wajen babu wanda ya iya magana
*MASARAUTAR TAYAAR*
Da tsananin farin ciki take shiryawa,kuyanginta suna taya ta,a yau tana cike da tsananin farin ciki irin wanda bata ta
a tsintar kanta a ciki ba,ba komai bane ya faranta mata sai kame azzalumi Kazuzi da aka yi,wanda a yau ya dawo bawa a masarautarsu
Zata iya cewa a duniya babu wata halitta da ta tsana,tsana mai muni irin Kazuzi,shine ya kashe
an'uwanta
aya tilo da take tsananin so fiye da rayuwarta,wanda a dalilin rasuwar shi ne zuciyar mahaifiyarsu ta buga itama ta bar duniya,yanzu daga ita sai mahaifinta suka rage a raye,a dalilin Kazuzi Sarautar da suka gada zata bar gidansu suna ji suna gani
"Ya shugaba ta ga abin kama gashin"a cewar wata kuyangar ta,bata yi magana ba sai murmushin da ta yi,ta sanya hannu ta kar
a,ta kama gashin,sannan ta mi
e ta shiga gaba,su kuma suka biyo ta a baya,suka fice daga sashen nata
Sai da suka hau
awataccen keken doki wanda ya kai su har bakin
akin da aka ajiye Kazuzi,babban
aki ne wanda aka gina shi da zallar dutse da jan
arfe,
aki ne wanda ake kai duk wani ta
adarin gagararre a cikin Tayaar
Dakarun da suke gadin
ofar suka bi su da kallon mamaki,saukowa ta yi daga keken dokin,kai tsaye ta tunkari
ofar ba tare da ta yi magana ba,babban badakaren ya
araso gabanta ya rissina yana fa
in "Barka da wannan lokaci ya shugaba ta"
Kallonshi ta yi fuska a tamke,kafin ta yi magana cikin izza
"Ina so na yi magana da dakaren da aka kamo a ya
in Baruda"
Muryarshi har rawa take yi wajen furta "ranki ya da
e su hamsin da uku ne ai,kuma....."
"Ina nufin Kazuzi,babban badakare a Baruda"
Cirko-cirko dakarun suka yi suna kallonta a matu
ar tsorace,ganin haka ta fusata ta ce"ko ba zan samu damar bane?
Chapter 3 · 0% Book details