← Book details Magana Jiri Ce Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 9 OF 31

Sashe 9

Magana Jiri Ce Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

ci an kori kare daga gindin kanya! Ga shi ragwancinki ya jawo mini asara, wai ba ki iya kiwon kaji biyu sai kin nemi yaro. Mutuniyar banza, sullutuwa!" Sahorama ta ce, "Kai ne mutumin banza, wanda in ya kwanta da magariba ba ya tashi sai gari ya waye da rana tsaka!" Sahoro yana dai daga kwance ya ce, "Wa ki ke zagi, Sahorama? Ka ga lalatacciyar banza, Kafira!" Sahorama ta ce, "An je an zage ka, kai dai ne Kafiri, ba ni ba. In kai da ne, ba shege ba, ka gina rami ka tsattsage ni!" Sai zuciya ta turnuke Sahoro, ya tashi daga kwance ya sauko, ya tarad da matar, sai kokawa kici kici, kica kica. Can Sahoro ya gaji, ya ga bai ka da matar ba, sai ita ke neman tandara shi da kasa. Sai ya ce mata, "To, sakan ni, kin kayar. Na ce ko iyakarta ke nan?" Sahorama ta ce, "Af! To, in sake ka, ni in fadi?" Musa ya ce. "Lalle ne wannan kokawa tana da ban dariya. To, kai gogan da ka je, wane labari ka ce ka ba su na bakauye da wadansu 'yam birni?" Aku ya ce, "Wannan shi ma yana da ban dariya." 31 Labarin Wani Bakauye Da Wadansu 'Yam Birni Wata rana wadansu 'yam birni na zaune, sai ga wani bakauye tafe, yana janye da jakinsa zai kai kasuwa ya sayar. A gaban bakauyen nan kuwa akwai wani dan hoto, shi kuma za shi kasuwar ya yi wasa. Ana tafe ana yi masa kidi, yana jefa garma yana cafewa. Da 'yam birnin nan suka lura da bakauye, sai suka ga ya bude baki yana ta kallon dan hoto, bai kula da ko jakin da ya ke ja ba. Daga nan sai wani daga cikinsu ya ce, "Yanzu fa ba ku sani ba, karbe wa muzin nan jakinsa bai sayi wuri ba, in ina so." Saura suka ce, "In ba kurarinka ba yanzu, yaya za ka yi? А buge dai ba ka iya buge shi ka karba, yanzu ko ba dare ba, balle ka ce ka sace." Sai dan birnin nan ya tashi ya bi bayan bakauye, saura na biye da shi sululu. Ya matsa, ya kwance igiyar da ke wuyan jaki ya daura wuyansa, ya mika wa 'yan'uwansa jakin, suka koro. Gagon naka tun da dai ya ke jin tsauri-tsauri a hannunsa, sai ya yi ta tafiya baki bude, yana kallon dan hoto. 32 daya sata! Da kajin da za mu saya, da yaron da za mu dauko, duk ga su nan sun malale a kasa. Amma dai na isa barka, da sakainan nan da ta yi tsalle ba ta fada mini a kafa ba." Ya dubi matar, ya ce, "Sa hannu, kwashe wannan da ke gudu kasa kafin kasa ta shanye, don mu sami na farawa, kada yunwa ta sa in gintse barcina tun ban koshi da shi ba." Sahorama ta shiga sa hannu tana kwashe zuma, tana zuba dan abin da ta samu cikin wata kwarya, tana lashe rabi tana ba mijin labari tana cewa, "Abin nan fa da na yi yanzu amfanimmu zai yi nan gaba. Don na taba jin wata rana an gayyaci kunkuru wajen aure, don rashin saurinsa da ya tashi bai kai gidan ba sai bayan watanni. Da ya isa ya tarar ana sunan dan amaryar da ya zo bikinta ta haifa. Da aka gaya masa ya ce, "Ba kome, sauri shi ke haihuwar nawa!" Sahoro na kwance bisa gado yana kallonta, tana ta shan zuma da wayo, tana zuba masa surutun banza. Sai haushi ya kama shi, ya ce mata, "Wane labarin banza ki ke ba ni haka, ba kai ba gindi? Wayon a ci an kori kare daga gindin kanya! Ga shi ragwancinki ya jawo mini asara, wai ba ki iya kiwon kaji biyu sai kin nemi yaro. Mutuniyar banza, sullutuwa!" Sahorama ta ce, "Kai ne mutumin banza, wanda in ya kwanta da magariba ba ya tashi sai gari ya waye da rana tsaka!" Sahoro yana dai daga kwance ya ce, "Wa ki ke zagi, Sahorama? Ka ga lalatacciyar banza, Kafira!" Sahorama ta ce, "An je an zage ka, kai dai ne Kafiri, ba ni ba. In kai da ne, ba shege ba, ka gina rami ka tsattsage ni!" Sai zuciya ta turnuke Sahoro, ya tashi daga kwance ya sauko, ya tarad da matar, sai kokawa kici kici, kica kica. Can Sahoro ya gaji, ya ga bai ka da matar ba, sai ita ke neman tandara shi da kasa. Sai ya ce mata, "To, sakan ni, kin kayar. Na ce ko iyakarta ke.nan?" Sahorama ta ce, "Af! To, in sake ka, ni in fadi?" Musa ya ce. "Lalle ne wannan kokawa tana da ban dariya. То, kai gogan da ka je, wane labari ka ce ka ba su na bakauye da wadansu 'yam birni?" Aku ya ce, "Wannan shi ma yana da ban dariya." 31 Labarin Wani Bakauye Da Wadansu 'Yam Birni Wata rana wadansu 'yam birni na zaune, sai ga wani bakauye tafe, yana janye da jakinsa zai kai kasuwa ya sayar. A gaban bakauyen nan kuwa akwai wani dan hoto, shi kuma za shi kasuwar ya yi wasa. Ana tafe ana yi masa kidi, yana jefa garma yana cafewa. Da 'yam birnin nan suka lura da bakauye, sai suka ga ya bude baki yana ta kallon dan hoto, bai kula da ko jakin da ya ke ja ba. Daga nan sai wani daga cikinsu ya ce, "Yanzu fa ba ku sani ba, karbe wa muzin nan jakinsa bai sayi wuri ba, in ina so." Saura suka ce, "In ba kurarinka ba yanzu, yaya za ka yi? А buge dai ba ka iya buge shi ka karba, yanzu ko ba dare ba, balle ka ce ka sace." Sai dan birnin nan ya tashi ya bi bayan bakauye, saura na biye da shi sululu. Ya matsa, ya kwance igiyar da ke wuyan jaki ya daura wuyansa, ya mika wa 'yan'uwansa jakin, suka koro. Gagon naka tun da dai ya ke jin tsauri-tsauri a hannunsa, sai ya yi ta tafiya baki bude, yana kallon dan hoto. 32 Can da dan birnin nan ya ga 'yan'uwansa sun bace da jaki, sai ya ja ya cirje. Bakauye ya ja ya ja, yana has has has! Amma bai waiwaiya ba, yana jin kada ya dauke kansa dan hoto ya yi wani abin mamakin da bai gani ba. Da ya ja dai ya ji jakin bai biyo ba, sai ya waiwaya don ya buge shi su tafi. Dubawan nan da ya yi sai ya ga mutum maimakon jakinsa. Abin ya ba shi mamaki, ya ce, "Kai, me ya faru haka?" Dan birni ya ce, "Ni ne jakinka, tsaya ka ji labarina, domin abin na da ban mamaki. Tun asali ni da ma ba jaki ba ne, mutum ne dan'uwanka. Ina zaune da tsohuwata, sai ran nan kuruciya ta debe ni, na sha giya. Sai na zo gida, ba ta san abin da ya faru ba. Ta yi mini 'yar magana kadan, ba ma ta tashin hankali ba. Ka san wańda ya yi sha bai san inda kansa ya ke ba, sai na zage ta. Ta dafe kai ta dube ni, ta ce, 'Ni ka ke zagi? Ashe har Allah ya kawo mu lokacin da 'ya'ya ke zagin iyaye?' Ka san mai maye sai na ce, 'Na zage ki! Ke wace ce da ba za a zage ki ba?' Sai ta sa hannu kai, ta yi ta kuka, ta roki Allah ya mai da ni jaki. Tun ran nan na ke jaki har Allah ya sa na zo hannunka. Yau ina ga ta gafarta mini ne, ka ga na koma mutum." Bakauye ko da jin haka sai tausayi ya kama shi, ya kura masa ido, ya ce, "Don Allah ka rika bin maganar iyayenka, kada ka yarda kuruciya ta debe ka, ka yi kyalkyalin tsada. Ga ka kyakkyawan saurayi, amma zuciyarka ta munana." Dam birni ya yi sako, yana jin wa'azi, kamar wani mummuni. Da bakauye ya kare ba shi wa'azi ya ce, "To, na ko bi wa'azin nan da ka yi mini." Ya faki idon bakauye, ya yi masa gwalo. Bakauye ya kwance masa igiya ya tafi, ya nufi wajen 33 'yan'uwansa. Suka kai jaki wani gida suka daure, kafin ranar kasuwa su kama shi su kai su sayar. Bakauye ko daga nan bai isa kasuwa ba, sai ya koma gida ya gaya wa matarsa duk abin nan da ya faru. Suka yi ta jin tausayin dam birni, domin wulakantad da shi da suka yi suna tsammani jaki ne, ba dan Adam ba ne. Ran nan bayan kamar kwana uku, ranar kasuwa 'yam birnin nan suka kai jaki su sayar, su sami abin zaman gari. Sai aka yi muwafaka bakauyen nan kuma ya tafi neman jaka. Da ma don ya sami mace shi ya sa ya so ya sayad da nasa namijin. Ko da ya isa ya duba haka sai ga jakinsa na da, sai ya matsa kusa da shi, ya dube shi, ya yi tsaki mts, ya ce, "Allah wadanka! Duk wa'azin nan da na yi maka ba ka lura ba? Mai hali ba ya barin halinsa. Haka ku ke shaye-shayenku, kuna sa mutane asara a wofi. Dubi duk wahalar da ka sha wajena, buga wannan kasuwa, dauki itace kai wannan kasuwa, duk ba ka daddara ba, sai da ka sake yin sha. Ni dai na gane ka. Sai ku yi can da wanda tsautsayi ke bibiya, mu dai muna tudun mun tsira." Ya hauri jaki ya wuce. Dan Sarki ya ce, "Ai ko wannan lalle ya isa bakauye!" Aku ya ce, "Ina ka san ya isa muzi tukun? Ai da sauran labari." Da ya duba bai samu wani jakin saye ba, sai ya komo gida yana kunne da dam birnin nan. Can zuwa maraice, 'yam birnin nan suka karyar da jaki, suka karbi awalaja. Da wata kasuwa ta kewayo, sai bakauye ya samo kuďinsa ya komo kasuwa neman jaka. Yana zuwa kusa da kofar gidan mai gari, sai ga fam birnin nan da ya ce shi ne ya rikide jaki, bakauye ya saya. Ya yi sitati za shi kasuwa, kayan nan sun dauki zargina tsar. Ko da bakauye ya gan shi sai ya gane shi,
Chapter 9 · 0% Book details