← Book details Magana Jiri Ce Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 5 OF 31

Sashe 5

Magana Jiri Ce Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

ta ji haka sai ta girgiza kai ta ce, "A! Wannan ko kusa ba shi yiwuwa. Yaya Sarki zai bar mana amanarka, sa'an nan mu saba?" Ko da Musa ya ji haka sai duk ransa ya baci, ya harari aku ya ce, "Har ke dan tsugunin nan naki kin isa ki hana ni zuwa wurin dan'uwana? Karyarki ta sha karya!" Sai ya kama ta, ya murde kan, ya yar. Yana jefad da ita sai mijin ya farka. Musa ya juya wajensa, ya ce, "Kai kuma me ka ce? Na zo in gaya muku ne zan bi Mahmudu yanzu.' Da akun nan ya ji haka, sai ya dubi matar, ya ga abin da ya auku gare ta. To, ga shi Sarki ya bar masa amanar yaro, in ya bari ya fita, lalle ya ci amanar Sarki. Ya ga kuma in ya hana yaron nan 11 tafiya, lalle abin da ya auku ga matarsa zai auku gare shi. Yana nan yana tunanin wadda za ta fisshe shi, sai Musa ya сe, "Ban ji ka ce kome ba, ko kuma kai hana nin za ka yi, yadda matarka ta tashi hana ni?" Aku ya daga fiffike, ya duka, ya ce, "Mamakin abin da ya sa ka ba mace shawara na ke yi. Ai magana irin wannan sai mu tsakanimmu maza. In ba rashin hankalin mata ba, ina mutum zai ce za shi ga dan'uwansa, sa'an nan a hana shi? Yi maza ka tafi, kada ka ji tsoron kome. Ba shakka dai ka cika dan kirki, tun da ba ka saba abin da tsohonka ya hore ka da shi ba, da ya ce kome za ka yi ka shawarce ni. Ga shi ka san ni ba kome ba ne, amma don ka cika umurnin ubanka ka zo. Da ma abin da a ke so ke nan kawai ga dan kirki ya bi maganar iyayensa da malumansa. Dan zaki da ya bi halin 'ya'yayen zamani, ya ki bin maganar magabatansa, ai ka ga yadda ya kare." Musa ya ce, "Dan zaki? Wace magana ya ki bi? Su ma dabbobi suna wata magana ne?" Aku ya ce, "A! Suna yin irin tasu mana. Bari ka ji yadda suka yi." 12 Labarin Wani Bororo Da Dan Zaki Wata rana namun daji suka taru suna shawarar ta kofar da ya kamata su rika fitowa 'yan Adam, don su kubuta daga tarkokinsu. Kowa na kawo tasa ana kushewa, sai dila ya ce, "Ва abin da ya fi, sai a yi makaranta nan dawa, mu da muka sha gwagwarmaya da mutane, muka gane makircinsu, mu rika koya wa na baya irin dabarummu." Sauran dabbobi suka yarda da wannan magana. Daga nan sai kura ta ce, "To, wa za a sa? Ai ka san wannan aikin sai mu." Zaki ya ce, "To, gaya mana irin dabarun da ki kan yi ki kubuta daga mutane, sa'an nan mu gani in hanyoyinki na da amfani ga sauran su bi." Kura ta ce, "Ai ba wata dabara da ta ke raba ka da mutum, sai idan wuri ya kure maka ka bude hakora ka tasam masa. In ko akwai 'yar tazara, ka sanke ka yi ta kanka." Zomo ya ce, "Allah wadan wannan dabara taki. In ke kina da karfin tasam musu, mu muna da shi ne?" Ya dubi zaki, ya ce, "Allah ya ba Sarki nasara, mafitarmu daya ce, idan kowa ya yi rami a kasa, ya yi masa kofa kamar goma duk nesa da juna. Ka ga in an rutsa ka nan sai ka bulle nan, in an datse nan sai ka bullo nan." Bauna ta dubi zomo, ta yi murmushi, ta ce "Kadai, yaro dai yaro ne. Kana maganar a gina rami, ni ina ka ga ramin da zan iya shiga?" Dila ya ce, "Ce ma kya iya shiga, to, in kun gamu a wajen kiwo fa? Ko kuwa don tsoro sai a bar neman abinci?"" Zomo ya ce, "Ai wannan sauki gare shi. Da kum gamu ya sa karnukansa suka biyo ka, sai ka yi gaba kamar ka wuce, ka ta da kura ka komo baya, ka sami gidan gara ka make gindinsa, sai ka saje da shi." Wannan magana ta zomo ta ba kowa haushi, har giwa ta tashi take shi, ba ta sani ba. Ta harare shi ta ce, "Kai sakarai, in kai kana iya makewa a suri, mu fa? Kai karnuka suka dame ka, me 13 aka yi aka yi karnuka? Cikin abubuwan ba tsoro har a gama da karę? Wannan ba dan'uwammu ba ne, kwadayi ya kai shi cikin mutane har ya yarda suna wulakanta shi kamar ba dan halas ba? Kai ma zomo, ba ka san maganar da ka ke yi ba." Kowa ya yi ta kawo dabararsa, don a sa shi malamin dawa, amma in saura suka bincika, sai su ga shi kadai ta ke wa amfani. Can an rasa wanda za a zaba, sai dila ya yi tsalle ya fado gaban manyan dawa, ya ce, "Allah ya kiyashe ka daga sharrin mutane, ni za a ba malanta, domin duk makircin mutane ba wanda ban sani ba." Kura ta ce, "Ba a tambaye ka yawan magana ba. Ka fadi dabarun da ka ke yi kana tserad da kanka mu ji, in mun yarda." Dila ya dubi zaki, ya ce, "Allah ya daukake ka, na san kuka na cikin abubuwan da ke tona mu ga mutane, saboda haka in na yi kuka gabas sai in ruga in koma yamma, in na yi a yamma sai in koma kudu. Ban taba tsayawa inda aka ji na yi kuka ba, balle a biyo." Zaki ya girgiza kai, ya ce, "Lalle kana da dabara a wannan wuri, amma in ka yi barci fa? Ko kuwa kullum ba ka yi, sai ka yi ta gudu ka je nan, ka je nan?" Dila ya ce, "Allah ya ba manyan dawa nasara, ai ni ba na barci sai tsakiyar ganyayen doka. In da ko fara ta fadi na ji kyamas sai in farka, in na ga ta tsaya in tsaya, in zuciyata ba ta ba ni ba in ruga." Zaki ya ce, "Lalle kana da dabara." Kura ta ce, "Manyan dawa, ai ko wajen shan ruwa mutane na cutarmu. In ya ce yana da dabara a fili ta wajen shan ruwa fa?" Dila ya ce, "Ai ni ba na shan ruwa yadda ku ke yi. In na ji kishirwa sai in tafi rafi, in tsoma wutsiyata cikin ruwa, in fito waje in tsotse, in koma in sake tsomawa. Haka na kan yi ta yi har in koshi, amma ban gane wa in dukad da kaina ba. Irin wannan shan ruwa da ku ke yi, ai ita ce baya ba zane. In wani ya lababo daga baya, ai barna ta auku." Damisa ta ji haka sai ta ce, "Mhm, ai ba nan mutane su ke sha da arna ba, sai wajen yin tarko. Babban abin da ba mu san kansa ba ke nan." Dila ya ce, "Ni dai abin da na tsare, shi ne duk inda na ga itace ya sarke, ba alamar ganye, ba alamar saiwa a gindinsa sai in sake hanya. Na san lalle itatuwa ba su tsira sai da saiwa da ko ganyaye, ko sun bushe a ga alamar inda su ke. In ko ina tafiya, na ga wani abincina a inda ba safai ya kamata a same shi nan ba, sai in hade kwadayina, in kewaya in wuce shi." Zaki da sauran dabbobi suka ce, "Lalle, dila, mun yarda kai ne 14 malamin dawa." Suka tara 'ya'yansu a makaranta, dila ya yi ta koya musu wayo iri iri. Kullum in darasi ya fado a kan dabarun da ya kamata su yi su kubuta daga mutane, sai dan zaki ya tashi, ya ce don mutum, wannan dan karamin alhaki, shi ba ya bata lokacinsa ga jin labarin makircinsa ba. In dila yana rarrashinsa ya tsaya ya karu, sai ya ce, "Ni dai don mutum Allah ya kawo ranar da za mu gamu da shi, ran nan yá kwashe kashinsa a hannu. In same shi in keta cikin, in karairaya kasusuwansa, in cinye namansa, in sha jininsa in more!" A kwana a tashi, ran nan dan zakin nan na yawo, da shi da dan rakumin dawa, sai suka hangi wani Bararo tafe da kayan tsabgu da igiyoyin dangwali mai yawa, sun yiwo tashi, ya bar 'yan'uwansa a baya, yana sauri ya riga su isa mashekari, ya fara zaben wuri ya yi bukka. Yana tafe yana 'yan wake-wakensa da Fillanci, yana kirari shi kadai kamar mahaukaci. Ko da rakumin dawa ya hango shi, sai ya ga bayanin da dila ke yi musu na mutum lalle wannan ya zama shi ne, saboda haka ya gudu ya shiga daji. Dan zaki kuwa ya tsaya, yana kallon wata irin halitta dabam da wadda bai saba gani ba. Da Bororon nan ya yiwo kusa, sai dan zaki ya ce masa, "Kai, tsaya! Cikin namun daji, kai ne wa? Tun da na tashi ban taba ganinka ba. Kai ko gaisuwa fada ba ka zuwa?" Bororo ya ajiye kayansa, ya fadi gaban zaki ya ce, "Ni ne Kuzajje. Abin da ya sa ba ka ganina fada, kunya na ke ji, ga kowa da kafa hudu, ni ko sai biyu, ga kowa da wutsiya, ni ko fimfirin. Dubi gashinku layalaya, ni ko tik da ni, kamar na fito daga wuta." Dan zaki ya ce, "To, ina za ka da wadannan itatuwa?" Bororo ya ce, "Kura ta kira ni in je in yi mata gida, don tana tsoron mutum." Dan zaki ya ce, "Shin don Allah ina zan bi in gamu da mutum yanzu? Shi na ke nema ruwa a jallo, kwana da kwanaki ban gan shi ba." Bororo ya durkusa, ya ce, "Yau da gobe dai ai ka gan shi, yallabai. Amma ai tsoron karo da irinku ya ke yi. M, kada ka tsai da ni, ina sauri in je in yi wa kura aikinta, ko ba don tsoron mutum ba ma, ga rana ta fara zafi. Ba abin da ya fi gida dadi." Dan zaki ya ce, "tsaya ka yi mini gidan tukuna in ji, sa'an nan ka wuce wajen na kura." Bororo ya ce, "A'a, yallabai ai ba ni da dama tun da muka yi alkawari
Chapter 5 · 0% Book details