Sashe 19
Magana Jiri Ce Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
ciki? Cin danko har da kaza?" Sai kuma fushi ya koma kan Ibrahim, ka san da ma an ce zomo ba ya fushi da makashinsa sai maratayi. Ya ce, "Wa ya tambaye shi ma ne, da ya sa bakinsa? Ka san Ibrahim ya raina ni." Sai ya tashi, ya shiga dakinsu na kwana. Da zuwa sai ya tarad da wandon Ibrahim bisa gadonsa, sai ya jeho shi waje, ya ce, "Raini ke nan ya sa kazamin wandonsa bisa gadona, ya sa mini kyaya." Ya haye gadonsa ya kwanta, yunwa kuwa ta fara dafa shi. Yana nan kwance, wai don ya fito sai Ibrahim ya zo ya ce masa, "Ka yi bako." Ilu ya harare shi, ya ce, "Fita, ba ni wuri!" Ibrahim ya yi murmushi, ya ce, "Abokinka ne ya zo." Ilu ya ce, "Na gaya maka ka tafi ka ba ni wuri tun da girma, ko?" Ibrahim ya wuce, yana cewa, "Na san dai yunwa ta sa ka wannan hushi, ba kome ba." Ashe fa gaskiyar Ibrahim. Ilu ya tashi ya rasa inda zai sa kansa don yunwa. Ya yi shawara ya koma ya ce a ba shi abincin da aka ajiye masa, ya ga in ya yi karaya haka a yi masa dariya. Saboda haka ya jure dai. Can zuwa la'asar ya ji abin ba dama, sai ya dauki wandonsa, ya sulale zai kai kasuwa, sai ya ji motsin ubansa a zaure. Ya ga in ya gane zai ba shi kashi. Saboda haka ya komo ya kurda ta kofar damfami, ya fita. Ya nufi kasuwa wajen 'yan tsumma. Ya tarad da wani mai dinkin mashimfidi, ya ce masa "Kana sayen wandona?" Madinki ya karba ya duba, ya ce, "Kai, karbi abinka" kyallen ai namuzu ne. Tir! Ko Ingila ba sayenka a ke ba, sai Turawa su watsar sadaka. Amma to, nawa za ka sayar mini don in rika kara wa jakina wajen laheru?" Ilu ya ce, "Nawa za ka biya?" Madinki ya ce, "Kwabo hudu. Ko ma na zura jiki ne?" Ilu ya ce, "An ce in bai yi kwabo takwas ba, kada in bari." Madinki ya bude baki kamar zai yi hamma, ya mika wa Ilu 76 wando, ya ce, "Lalle in ka kewaya a sami mai sayensa sule ma. Duba shi, ai sabo ne." Ilu ya lura ba'a ya ke yi masa, sai ya mika masa wando, ya ce, "Kawo kuďi." Aka mika masa awalaja, ya runtse a hannu, ya shiga kasuwa neman abin da zai ci, Magariba ta kusa, kowa ya watse, bai sami kome ba. Sai ya nufi tukubar tsire ya tsuguna, ya sa aka zare masa wajiya ta kwabo huďu, ya ci ya ci har ya koshi. Ya nemi ruwa ya sha. Ya tasam ma gida yana cewa, "Tun da aka zazzage ni, sai na sayad da kayana duka na ci abinci. Ba na sake cin abincinsu sai sun zo sun rarrashe ni." Yana zuwa gida, sai ya tarad da fura mai zuma uwar ta kai masa dakinsa. Ya bude, ya duba, ya diba kadan da ludayi ya kurba, sai ya ji ta coin. Ya ce, "Yau ga ni ina son furan nan, amma in na sha lalle a yi mini dariya." Amma bari in kurba luddayi uku, na san dai ba a ganewa. Ya tsuguna ya sha. Ya gama ke nan, sai ga kanen ya shigo, ya ce, "Ina ka tafi, ga Inna ta ce in kawo maka fura?"" Ilu ya ce, "Ina ruwanka da in da na tafi? Me ka ba ni ajiya? Dauki furarku, ba na sha. Ni sakarai, dan banza, me ruwanku da ni? In je in mutu mana." Ibrahim ya fita ke nan da fura, sai wajiya ta yi ta taso wa Ilu, sai amaí. Nan da nan ciki ya murde shi, ya yi ta murde-murde bisa gado yana kugi, Da uwar ta ji, ta kira Ibrahim suka rugo su ga ko mene ne. Suka tarad da shi sai amai ya ke yi, duk idanduna sun jujjuye, suka tambaye shi abin da ya ci. Yà če, "Na-na-nama." Nan da nan uban ya се a пеmo tsamiya. Uwar ta ruga. Ilu sai kuka ya ke yi yana murde-murde, ya kasa kwance ya kasa tsaye. Nan da nan uwar ta kawo, aka jika, aka dura masa ya sha. Sai ya barke da zawo. Kafin lisha ya sami sauki. Gari na wayewa ya warke sarai. Sai ya tafi wajen iyayen, ya roke su gafara, ya сe daga yau ba ya sake yi musu musu. Aikin makaranta kuwa, su saurari abin da zai faru in an sake yi musu jarrabawa. Daga ran nan ya koma dan kirki, duk ajinsu aka rasa kamarsa. In ka ki jin horon iyayenka, ka ji na Mahaliccinka. Musa ýa duba, ya ga har rana ta kunno, sai ya ce wa aku, "Ка ga dai da zan yi tafiya, ka tsai da ni a wofi, ga shi ka sa na makara." Ya koma ciki da hushi. Duk yinin nan ya hana a kawo wa aku wani abinci sabo. רר Da rana ta fadi, asuba ta yi, aku ya kura ido hanyar da Musa ke fitowa. Ko da ya hango shi tafe da takobi tsirara, sai ya ce, "Daukan ni mu tafi tare." Musa ya harare shi, ya ce, "Ka yi mini amfanin me wurin yaki, dan tsurut da kai haka? An ce maka labari a ke so?"" Aku ya ce, "Ko ba don labari ba, dabara aì ita ce yaki, ba karfi ba. Ina zaton ba ka taba jin labarin yadda bunsuru ya yi dabara har ya kori kura ya gaje gidanta ba ne?" 78 Banza Girman Mahaukaci, Karamin Mai Wayo Ya Fi Shi A cikin wani daji akwai wata kura wadda ke da gidanta mai kyau kwarai da gaske a wani kogo, ta kawata shi da kyau, babu abin da babu a ciki. Sai kuran nan ta sami wani biri, ta sa shi ya rika tsaron gidan nan kullum in ba ta nan, don kada wani abu ya fasa in ba kowa, ko kuwa a zo a yi mata sata. Kullum birin nan ba ya rabuwa da gidan. Ran nan yana zaune sai wani bunsuru da mata tasa da 'ya'yansu uku suka fado nan gidan. Dalilin zuwansu kuwa, kiwo suka tafi har dare ya yi musu, suka rasa hanyar komawa gari, suna kuwa tsoron kada su gamu da zaki ko kura. Da biri ya gan su, sai ya ce, "Kai daga ina? Su wane ne ku? Nan fa gidan kura ne, ku rufa wa kanku asiri ku koma, in ba haka ba kuwa, in je yanzu in gaya mata ta zo ta hau doronku dai dai." Akuya ta dubi bunsuru, ta ce, "Maigida, yau fa abin da mu ke gudu ya auku, mun kawo kammu ga halaka. Da ma mun sani mu dangana da ciyawar da ubangijimmu ya ke zuba mana kullum dare! Ga shi kwadayin son danya ya sa mun kawo kammu a mahalaka." Biri ya dubi bunsuru, ya ce, "Ni fa na gaya muku ku gudu, in ba haka ba, yanzu in tafi in gaya mata." Bunsuru ya harari biri, ya ce, "Mutumin banza, wannan gidan tun daga kakan kakana, Sarkin Masu, na gaje shi. Ba wanda zai kwace shi daga gare ni duk fadin duniyan nan. Je ka, gaya mata mana, ina nan ina jiranta." Biri ya zabura, ya tafi wurin kura. Bayan ya tafi akuya ta ce wa bunsuru, "Mu yi ta kammu, kafin kura ta zo!" Bunsuru ya ce, "Ke ar, mara hankali! Ai yanzu idan muka nuna alamar mun ji tsoro mun kade, ba mu da wurin tsira ko mun gudu. Idan mun ga kura tafe, sai ki ce wa 'ya'yammu su yi kuka gaba daya, in na tambaye ki dalilin kukansu, ki ce suna jin yunwa ne, wai suna son naman kura su ci, ba su cin na jiya, ya rube." Akuya ta amsa ta ce, "To, amma dai ni ban sa wannan za ta fid da mu bа." 79 Da biri ya isa wajen kura ya ce mata, "Ga wani abu nan da iyalinsa, ya zo ya ce wai gidan nan ba naki ba ne, wai na kakan kakansa ne, Sarkin Masu. Na ce ya gudu, kada ki zo ki cinye su. Ya ce ke din me? Ba irin zagin da bai yi miki ba." Kura ta ce, "Ka san shi?" Biri ya ce, "A'a. Amma barewa ta ce wai bunsuru ne." Kura ta ce, "Ko da ban gan shi ba, lalle ba bunsuru ba ne. Bunsuru ba yadda zai yi wannan aiki. Yaya kamarsa ta ke? Ya kai girmana?" Biri ya ce, "Ko kusa, ni ma kadan ya fi ni. Wani irin launi gare shi ja ja, da gasusuwa zaro-zaro, da 'yan kofatai kamar na barewa." Kura ta ce, "In ka tabbata bai fi ni karfi ba, mu je mu gan su. Shin su nawa ne?" Biri ya ce, "Har da 'ya'yansu su biyar ne.duka." Kura ta ce, "Nawa? Biyar! Ko ba su da karfi fa akwai yawa. Sarkin Yawa kuwa ya fi Sarkin Karfi!" Biri ya ce, "Ai duk kanana ne, babban ma da tsawon kafa kadai ya fi ni. Kuma a nan duniya ai babu naman dajin da ya fi ki karfi, in ba zaki da giwa ba." Kura ta ce, "Kai, yi mini shiru! Namun dajin da suka fi ni karfi nan duniya wa ya san iyakarsu? Kai dai mu tafi mu gani, in da riba mu fafata, in kuwa babu mu yi ta kammu." Ko da bunsuru ya hango su sai ya ce wa matarsa, "Tura 'ya'yanki cikin kogo, in sun shige kuma su yi ta kuka baki daya." Da suka shige duk suka barke da kuka baki daya, Ba-a-a-a-a-aa-a! Bunsuru ya ce, "Kai, me ya sami yaran nan?" Akuya ta ce, "Wai sun ce duk cikin naman da ke gidan nan ba su cin naman kowa sai na kura kadai, wai ya fi dadi." Bunsuru уa се, "То, a ba su sauran na kuran nan da na kashe jiya mana su karasa." Akuya ta ce, "Na ba su, sun ce ba su cin naman da ya fara bashi, wai sai sabo su ke so." Bunsuru уa сe, "Tоo, su hakura kadan su bar motsi, don na ji biri ya ce wai kura yau